← Book details Inda Rai Da Rabo Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 85 OF 198

Sashe 85

Inda Rai Da Rabo Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

“Akram....” Ta kirawo sunansa tana mai d’an waige waige....
Tsayawa cak yai yana dubanta cikeda mamaki don tinda yake tareda mijinta yau kusan shekaru goma bai tab’aji ta ambaci sunansa ba koda wasa sai yau, tsakaninsa da ita saidai ta watsa masa kallon k’ask’anci ko gaisheta yai a gadarance take amsasa yau sai gashi ta ambaci sunansa dole abin ya basa mamaki....
D’an gyara tsayuwarsa yai kana yace “Da ni kike magana Hajiya...?”

Muhibbah ta k’araso kusansa tana mai jinjina kai kana tace “Can I have a word with you...?”

Kuma daidaita tsayuwarsa yai kana yace “Yes... Sure....”

Muhibbah ta kuma waigawa gefe da gefe kana tace “I want you to be completely honest with me....”

Akram ya d’an jinjina kai yace “Ina saurarenki Hajiya...”

Muhibbah ta jinjina kai tace “Inaso ka fad’a min what exactly my husband is up to... And don’t lie to me....”

Mamaki maganar nata yaso basa, ya d’an gyara tsayuwarsa kana yace “Hajiya... Ban fahimci abinda kike nufi ba...”

Wannan karon d’an nurmusawa tai kana tace “Nasan ka fahimci abinda nake nufi sarai, domin kuwa sanin kanka ne akwai abubuwa da dama da mijina ke b’oye min wanda kai baya b’oye maka... So tell me mai yake shiryawa....?”

D’an kauda kai gefe Akram yai kana yace “A gaskiya kiyi hak’uri domin kuwa wannan ba hurumina bane, tsakaninki da mijinki ne wannan...”

Banda uwar harara babu abinda take aika masa, bata zaci wannan wawan zata sami matsala dashi ba.... K’ak’aro murmushi tai kana tace “Kar ka damu da tsakanina da mijina ai ni ce na tambayeka, so just tell me...”

Nan ma shiru Akram yai kana yace “A gaskiya kiyi hak’uri Hajiya.... Ni zan wuce.....” Yasa kai daga haka..

Shayeda mamaki Muhibbah take dubansa, a ranta take ayyana lallai wannan banzan ya cika d’an rainin hankali... Har ya soma tafiya ya sinkayo muryarta tana furta “Kai Akram kake ko wa... Umarni nake baka a matsayina na matar uban gidanka idan kuma baso kake ka rasa aikinka ba....”

D’an waiwayowa kad’an yai kana yace “I’m sorry.... I’m also following orders here... Hajiya kiyi hak’uri.... It’s really confidential....”

Murmushin yak’e ta saki kana ta matso kusansa sosai tana wani kannare idanu had’ida d’aura hannu a kunkumi kana tace “You seems very tough....Kaga a fuska kafi kama da salihai marassa son hayaniya da tashin hankali just like your Boss....”
Ganin tana kuma k’ok’arin kawo fuskarta kusan nasa ya sanyashi saurin matsawa da baya cikeda tsoro had’ida firgici....
Maimakon ta bada tazara tsakaninsu saima murmusawa da tai tana mai kuma ci gaba da kannare masa idanu kana tace “Ya dai.... don’t you like women.... Oh c’on pretty boy Don’t tell me tsoro kake....?” Tai maganar cikin sigan rad’a...
Izuwa lokacin k’afafun Akram sun soma rawa... Fitowar wata Cook daga can gefen shuke shuke ya ceci Akram daga tarkon Muhibbah tai saurin saita kanta kana tace “Kana iya tafiya Akram... Ina saurarenka idan komai ya zama ready....”

Bai iya bata amsa ba sai sa kai da yai cikin sauri yana k’ok’arin ficewa daga gidan....
Muhibbah ta kalli sabuwar Cook d’in da ta kawo ba tareda sanin mijinta ba don shi cewa yai a rage ma’aikatan gidan musamman masu girki ita kaw ba iyawa tai ba hasalima ko ta iya bazatayi ba... Kiranta tai ta k’araso da sauri kana tace “Vanessa ba na hanaki yawo cikin gidan nan ba...? Ko so kike ki rasa aikin ki...?”
Matar tai saurin girgiza kai tana mai bata hak’uri....
Harara Muhibbah ta dalla mata kana tace ta shige ta bata waje kafin ta canza zuciyarta ta sallameta....
Har saida Vanessa ta shige kafin Muhibbah taja wani dogon tsaki ta nufi sashen bak’i yanda mijin nata yake...

***

Shiru Abbah yai yana sauraren d’an uwan nasa da batun da yazo masa.... A hankali ya sauk’e ajiyan zuciya kana yace “Yayah wani hanzari ba gudu ba... Bawai nak’i batun a maida auren yaran nan bane, zanfiso a tambayi ita Zulfa’un aji daga bakinta idan ta amince ta yarda zata kuma auren Hafiz a karo na biyu... Sannan Zulfa’u yanzu bazawarace hakkin zab’an miji a hannunta yake a shari’ance, ni a halin yanzu ma Yaya gaskiya alk’awari nayi babu d’ahnah guda da zan kuma ma auren dole, idan suna so falillahil hamdu ai hannunka bazai rub’e ka yanke ka yar ba, idan kuma basa so toh a gaskiya Yaya ina ganin hak’uran shi yafi alkhairi... Batun shi Ma’aruf kuma zanji ta bakinsa, idan ya amince yana son d’aya daga cikin Sahariyyar ko Naja’atun ba matsala bane, kamar yadda kace k’ara dank’on zumunci ne kuma Ma’aruf zai yarda cewa lallai ‘yan uwansa na k’aunarsa dukda cewa yayi shekaru ba taredasu ba... Amma Yaya saifa idan yace yana so.....”

Baba Alhaji ya maida hularsa baya don ba haka yaso ba, yaso da zaran yazowa Abbah da batun yayi na’am ba tareda wani shamak’i ba... D’an jinjina kai yai kaman mutunin kirki kana ya sauk’ar da ajiyar zuciya yace “A zatona Usman bazan baka umarni kace zakayi shawari ko zaka nemi zab’in ‘ya’ya ba... Yaran da mu muka haifesu basu suka haifemu ba... Haba Usman shin har Yaushe ka zamto haka...?”

Abbah ya d’anyi shiru kad’an kana ya gyara zamansa had’ida soma fad’in “Wato Yaya duk bank’i abinda kazo dashi ba... Amma baka duba munyi hakan da farko baiyi kyau ba... Ko ka mance da fari ikonmu muka nuna kan Zulfa’u da Hafiz amma k’arshe mai ya haifar...? Ina ganin iyaye suna tapka babban kure wajen tilasta wa yaransu auren wad’anda basaso sannan musulnci cewa yayi budurwa a shawarceta kar a bata mijin da ita bata so, tanada hakki a bata zab’i itama, ita kuwa wacce ta tab’a aure ragamar zab’an mijinta a hannunta yake... Shi kuwa Ma’aruf baka ganin idan mun tilasta masa auren wacce baya so bazaisa ya kallemu da wata manufa ba tinda yaron nan ba hannunmu ya tashi ba, cinsa shansa karatunsa fad’i tashinsa duk bamu sani ba, hasalima haihuwarsa kawai mukayi... Shi baka tunanin bazaiga munyi karan tsayewa rayuwarsa ba...? Sannan iyayensa na can da suka rainesa watak’ila sunada mu’amala kyakkyawa da fahimtar juna tsakaninsu... Baka tunanin ya kamata muyi koyi dasu... Sannan Yaya Ma’aruf yanada iyali, bamuda tabbacin idan yanada ra’ayin zama da mace sama da guda.... Wad’annan dalilai kad’ai Yaya ya isa mu d’agawa yaran nan k’afafu mu barsu su zab’i wad’anda suke so kar muyi karan tsayewa rayuwarsu tinda bamu zamuje mu zauna masu ba.... Kai hak’uri Yaya ban...”

Dakatar dashi Baba Alhaji yai ta hanyar d’aga masa hannu kana ya mik’e yana sab’a babbar riga lokaci guda yake fad’in “Dakata Usman banaso na kuma jin komai... Har nine zaka watsan k’asa a idanu kawai don nazo neman alfarma wajenka.... Na jima da sanin cewa baka d’aukeni da wata daraja ba..... Kaje jik’a ‘ya’yanka ka shanyesu.... Amma ka sani muna gab da raba zumunta ta har abada dani dakai....”
Daga haka ficewa yayi fuuu kaman zai tashi sama... Mamy dake k’ok’arin shigowa rik’eda flask d’in ruwan zafi ta kawo masu shayi, tana gaishesa ko amsata bai sami zarafin yi ba ya fice kaman zai kifa da k’asa ba daina furta Aikin aikin wofi ba....

A hankali ta ije flask d’in tana duban mijin nata da alamun tambaya....

Abbah ya fuzar da iska a hankali had’ida lumshe idanunsa....
Mamy ta sami waje daga gefensa ta zauna....
“Abbah lafiya dai koh....?” Ta fad’i fuskarta d’aukeda damuwa....

“Inafah lafiya Hannatu.... Kina jin zancen da Yaya ya kuma zuwa min da ita.....?” Abbah yace yana mai duban Mamy.....
Jinjina kai Mamy tai don tasan hakan zata faru bayan bayanan Baba Alhajin dataji a asibiti can wajen duba Hajiya Haule da sukaje....
Matsowa tai sosai kusan mijin nata had’ida dafa hannunsa dake aje saman cinyarsa kana tace “Ka kwantar da hankalinka mijina, kuma kada kasa damuwa a ranka... Munayima ‘ya’yanmu addu’a kuma nayi imani bazasu tab’e ba sannan da sannu zasu sami abokan zama na k’warai..... Wannan ba abin d’aga hankali bane kaji koh....”
Tai maganar sihirtaccen murmushi kwance saman kyakkyawar fuskarta...

K’uri Abbah ya mata yanajin sanyi da wani irin kwanciyar hankali cikin zuciyarsa, a hankali yakai hannu ya shafi fuskarta kana yace “Allah ya maki albarka Hanne na.... Hak’ik’a kin tuna min shekarun aurenmu na fari... Kafin b’acewar Ma’aruf...”

Mamy ta kuma murmusawa tana mai dubansa itama...
Chapter 85 · 0% Book details