← Book details Inda Rai Da Rabo Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 184 OF 198

Sashe 184

Inda Rai Da Rabo Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Wane irin k’ara Muhibbah ta saki had’ida jifan tv d’in tana mai furta “Wllhi k’arya kenan... Ma’aruf baka isa ba... Wllhi baka isa kai nasara ba muddin ina raye... Nayi azaman ganin downfall d’inka kuma sai na gani... Babu gudu babu jada baya... Kai kanka ka sani bana sadaukar da fad’a cikin sauk’i.... I’ll ruin your reputation is a promise..!!” Ta k’arashe tana tsananin huci wanda da gani kasan miyagun k’wayoyi sun fara zautar da kwanyarta....

Bash ne ya shigo yana shu’umin murmushi yake duban tv d’in lokaci guda yake furta “Seems your husband is now the hero of the country... Ya tashi Daga d’an siyasa ya koma mai kamen masu laifi.... Kar fah ya gangaro zuwa kanki...!” Ya k’arashe yana shu’umin murmushi....

Muguwar kallo ta b’allawa Bash kana tace “He wouldn’t dare to do that.... I’m the mother of his children... Bai isa yamin abu makamancin haka ba... Kuma kafin yaga downfall d’ina sai naga nasa....!”

Bash dai murmusawa kurum yai kana yace “Muhibbah kar fad’anku da wannan mijin naki ya b’ata mana kasuwancinmu, Kinga manyanmu Daga sam ba zasuji dad’I ba....”

Muhibbah ta b’alla masa harara kana tace “Na fad’a maka koda wasa bazai tab’ani ba... Babu abinda za’a fasa... Gobe za’a fitar da kaya, idan na caski wad’annan dalolin zan d’ibi yarana mu gudu mu bar k’asar... Engr bazai sake ganinmu ba....!”

Jinjina kai Bash yai kana yace “I hope so domin I can’t afford to lose this millions....”

Da wannan batu suka kwana a ransu na fitar da k’wayoyinsu zuwa k’asashen k’etare... Saidai kaman yanda suka shirya ba haka abin ya kasance masu ba... Ana tsaka da hada hada kaman kasuwanci gaske ake kwatsam jami’an tsaro suka bayyana.... Kan kace mai sun buk’aci kowa ya k’ame... Muhibbah da Bash da basu jima da isowa ba suka dubi juna.... Shamzy ma dubansu tai tana mamakin yau polisawa ne a kantinsu... Bash ya b’allawa Muhibbah kallon tuhuma... Lokaci guda ya d’anyi k’asa da kansa kad’an yana mai furta “What is this Muhibbah...? Mai jami’an tsaro suke a nan...? Setting d’inmu up kikai...?”

Muhibbah na muzurai take furta “Ta ya za’ai nai haka Bash... I have no idea mai ya kawosu nan...!”

Lokaci guda ta k’arasa ga Jami’an tsaron tana mai furta “Em officer Lafiya mai ya kawoku nan... Bazai yuwu ku shigo cikin Kantina kuna d’agawa customers d’ina hankali ba... We are not selling any illegal item here... As you can see wannan shago ne na kayan k’arau....!”

Officer ya jinjina kai kana yace “In that case we are going to search the area..”

Dik k’ok’arin Muhibbah na ganin ta cire tsoro tattareda ita saida ‘yanhanjinta suka murd’a... Ta daburce lokaci guda, ta shiga k’ok’arin hana jami’an tsaro gudanar da aikinsu saidai batada ikon yin hakan....
Take sukaci gaba da search d’insu tareda jagorancin Detective Najeeb... Haka suke ciro gidan ‘yankunnaye da sark’a suna zazzagewa suna tsaga soson ciki da ake d’aura sark’ok’in bisa... A cikin search d’insu suka samu wasu... Take d’ansanda guda ya k’adadi yana sarawa ogan nasu had’ida furta “Positive Sir...!”

Innalillahi wa inna’ilaihi raji’un...! Ai take Muhibbah ta soma masu bore tana fad’in sharri aka k’ulla mata... Ko saurarenta ‘yansanda basuyi ba suka shiga kamensu da masu cinikin nasu....

Muhibbah na fincika tana fad’in su sanar da ita munafukin da yai mata cune kwatsam sukai idanu hud’u da Engr.....

Fincika ta shigayi tana tsananin huci take fad’in “It was you... How dare you Ma’aruf... Ta ya zakai haka ma uwar ‘ya’yanka.... Bazan tab’a yafe maka ba Ma’aruf....!!!” Ta k’arashe tana mai fashewa da kuka....

Girgiza kai kurum Engr yake cikeda tausayinta, lokaci guda yake furta “I’m sorry Muhibbah... But I have no other choice... Bazan iya zama ina gani kina aikata b’arna da tarwatsa rayukan al’umma ba... Muhibbah I can’t turn a blind eye... Ba haka naso al’amra su kasance ba but you weren’t listening to me Muhibbah... Wannan shine sakamakon ayyukanki... Kiyi hak’uri kije ki amsa laifukanki ni kuma na miki alk’awari I’ll never leave your side Muhibbah... We would face this together har ki gama serving sentences d’inki... Idan har da gaske kinyi tuba na hak’ik’a...!” Ya k’arashe cikeda tausaya mata...

Cikin kuka take furta “You did this on purpose Ma’aruf... So kake dama ka cireni daga cikin rayuwarka dan ka kasance da wancan bamagujiyar amaryar taka, shine bari kamin k’age... Sarai ka sani laifin smuggling k’wayoyi zai shafe mutum sama da shekaru goma sha biyar a gidan yari shine zaka wani ce tare zamu facing komai... Ka cuceni ka cuceni Ma’aruf... Wllhi bazan tab’a yafe maka ba, kuma bani buk’atan dik wani taimako daga wajenka... I’ve my own money da zan d’auki very good lawyer da zai kareni gaban Alk’ali dan wllhi bazan tafi prison ba, zan fito kuma zan k’wace yarana daga gareka... Mugu kawai azzalumi mai sak’a alkhairi da sharri... Bayan dik abinda Baba Mutallab yai maka ta haka zaka saka masa cin amanar da ya d’auka ya dank’a maka... Wllhi bazan tab’a yafe maka ba Ma’aruf..!!” Ta k’arashe cikin tsananin kuka yayinda ‘yar sanda macen ta kuma hankad’a k’eyar Muhibbah tana fad’in “Shige muje.. Criminal..!”

Lumshe idanunsa yai a hankali sanda aka shige da Muhibba wasu irin hawaye masu tsananin d’umi suka gangaro masa...

****

ABUJA

Jiki a matuk’ar sanyaye Siyama ta d’ago tana kuma duban Daddy da Ammi da suka ida mata nasiha kan tai hak’uri Ta amshi k’addarar rayuwarta yanda yazo mata, ta zauna da mijinta da abokiyar zamanta lafiya.... Share k’wallan da suka gangaro mata Siyama tai kana ta kuma k’arasawa jikin Daddy Ta rik’o hannayensa lokaci guda take furta “Daddy please forgive me... Kuma kace Aunty Daula ta yafe min... In sha Allahu I’m a changed person now...!” Ta k’arashe cikin tsananin rawar murya....
Janyo kanta gefen k’irjinsa Daddy yai yana mai furta “Come here my little princess.... Baki min komai ba sannan Daula ma bata rik’eki ba.... Dukanmu ‘yan adam ne masu aikata kuskure kinji koh.... Ki sami Mijinki ki bashi hak’urin dik abubuwan da kika aikata masa marassa kyau... Ubangiji yai maki albarka Mamata...!” Ya k’arashe yana shafa kanta...
Hawaye suka kuma gangarowa Siyama, lokaci guda ta rungume Daddy tana mai furta “I love you so much Daddy...!”
Daddy yace “I love you too my Baby...!”

Ammi dake gefe d’an yatsarta ta saka ta goge hawayen da suka gangaro mata daidai sanda Ijlaal ta shigo ta fad’a jikin Siyama a guje tanai mata oyoyo had’ida furta ta tafi batai mata sallama ba kuma tayi kewarta sosai...

Siyama ta kuma matse yarinyar cikin jikinta tana mai fad’in “Oh I’ve missed you too my little angel.... I’m sorry I had to leave without saying goodbye the other time... Kiyi hak’uri bazan sake ba kinji...!”

Turo baki yarinya tai tana mai kuma shigewa cikin jikin Siyamar take fad’in “Aunty please don’t leave us ever again.... Wait..! Aren’t family supposed to be living together..? Maiyasa zaki tafi Toh....?!” Ta k’arashe tana kuma turo baki gaba had’ida yin rau rau da idanu...
Duban Ammi da Daddy Siyama Ta d’anyi taga dai zuba masu idanu suma sukai murmushi saman fuskokinsu...
Hannayen Ijlaal Siyama ta d’an kamo kana tace “Princess do you remember the other time you asked me if I have a husband..?”

Ijlaal ta jinjina kanta alamun eh.. D’an dafa kanta Siyama ta kumayi kana tace “Well, yes I do have a husband... And I have to go and live with him...” Ta k’arshe murmushi saman fuskarta bata daina shafa sumar Ijlaal ba...

Ijlaal ta d’an tab’e baki kad’an kana tace “Is that so... Then I’ll follow you to your husband’s....Don’t you want me there...?” Ta k’arshe kaman mai shiri kuka...

Siyama ta qare idanunta had’ida fad’ad’a murmushinta kana tace “That would’ve been very very beautiful my princess... Idan Daddy da mummy zasu barmu of course tare zamu tafi...! Ta k’arashe tana mai kuma janyo yarinyar cikeda farin ciki...

Ijlaal ta juya tana duban mahaifin nasu cikin ‘yar tsallenta take fad’in “Please please Daddy say yes...!”

Aunty Daula ce ta shigo parlorn rik’eda tray na fruits tana mai fad’in “Aiko da mun huta da fitina maza akaiwa Aunty Siyama tacan...”

Gaba d’aya d’an darawa sukai Siyama na fad’in “My baby batada fitina... She’s the most calm girl in the entire Nigeria... Right princess...!” Tsalle Ijlaal ta kumayi ta haye jikin Siyama tana murna...

Ammi ke tambayar Aunty Daula ko Nabilah ta ida shiri dan anjima da dare ake shirin kaita gidan mijinta Khalid dake nan Abujan....

SameenaAleeyou📚

*INDA RAI*
_................DA RABO_

*109*

*©️Sameena Aleeyou...✍🏽*

Aunty Bara’atu da Siyama ke tayata shiryawa... Wai har Siyama ce ke nad’a mata lafaya, oh Allah mai iko shin waye zai tab’a zaton Nabilah da Siyama zasu zauna inuwa guda.. Lallai ikon Allah ya wuce gaban wasa, ita kanta Nabilar duban Siyama kurum take yanda take ta k’ok’arin shiryata Wai saikace ba Siyama ba... Siyama dai fah Matar Ya Ma’aruf kuma ‘yar uwar Khalid da ta d’auki karan tsangwama ta saka mata yau gasu nan kaman basu tab’a k’yamatan juna ba, kai gaskiya babu abinda za’ai da k’iyayya da gaba... Kubura ce ta turo k’ofar ta shigo sai wage baki take tana fad’in “Yau dai sai gidan angon biyoo (bear) sharupkan d’in Nigeria.... Aje can ayita zuba soyayya muna nan muna tagumi...” Siyama ta watsa mata harara sai kuma ta dara a hankali dan harta Nabilar ma dariya ta bata... Siyama tace “Yanzu kin aje makaman yak’inki kenan kin rungumi K’addara.....”

Kubura ta wani murmusa a dole taji kunya kana tace “Ni kaza...kar kisa amaryar beyoo ta zauneni...wllhi Aunty Siyama dama wancan uwar iyayi d’in taki ce banso ya aura amma Ammi ta dage... Ai wllhi yafi k’arfin class d’inta... Amma yanzu tinda ga teddy ai hikenan, suje suci soyayyarsu muna nan muna zuba tagumi....”
Darawa suka kumayi Siyama na fad’in “Zaki maimaita a gabanshi....” Tana maganan tana duban k’ofa yanda Khalid ke k’ame ya hard’e hannaye...
Chapter 184 · 0% Book details