← Book details Inda Rai Da Rabo Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 194 OF 198

Sashe 194

Inda Rai Da Rabo Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ta d’an kuma d’ago kai tana waige waige.. Text ya kuma shigo mata... Shin anya bazataje taga waye wannan bawan Allah da ya dameta ta sanar dashi Tanada aure ba, toh ya ma akai yasan tana nan... Wata zuciyar tace toh idan kuma da gaske ba mutum d’in bane fah...? Take dai taji zuciyarta tana k’arfafa mata gwiwa da tajeta... Ta sauk’e ajiyan zuciya a hankali kana ta nufo hanyar da akace tabi...
Wani ikon Allah k’aytaccen waje ta tsinci kanta wanda har saida yafi yanda Ta fito k’ayatuwa.. Tsoro ya soma cikata anya ba birnin mutanen b’oye take ba... Wai meke faruwa ne da ita...? Ta tambayi kanta tana mai kuma waige waige... Sak’on ne ya kuma shigo mata yanda yace ta juyo bayanta kad’an zata hangosa...
Gaban Zulfa’u ya tsananta fad’uwa... Da k’yar take kaikaitowa har dai ta ida jiyowa gaba d’aya yanda ta hangi wani teburi mai d’aukeda fulawowi wanda yasha tsari iyaka tsari harta su wine glass cups gasu nan a jere, saikace wacce ta fito date irin na turawa...Gabanta ya kuma tsinkewa ga wani view na rana da ya kusa fad’i daga can k’arshen teku tana hangowa... Gefe kad’an ta hangi bayansa, sanye yake cikin three quarter da fara k’al d’in shirt wanda gaban rigar an rubuta _I am urs_ sabida duhu bama ta ita hangosa gaba d’ai sai hasken rigar nasa take hangowa... Hannayensa sakale cikin aljihu ya bada baya yana hangen yanda iska ke kad’a ruwan teku had’ida kyawawan bishiyan kwakwa da sukaima wajen kawanya....
Gaban Zulfa’u ya kuma yankewa ya fad’i, ji tai k’afafunta sun soma takowa zuwa yanda yake... Tana soma takowa kaw wasu wuta suka fara haskawa Daga k’asa dik yanda Ta taka masu kaman candles cikin kwalba.... Dik yanda ta saka k’afarta daga gefe gefe wad’annan wutacan suna haskawa... Wani irin murmushi ne taji yana zuwa mata had’ida sanyi cikin zuciyarta wanda zata ce ita kanata batasan yanda zata misalta kalan abinda takeji ba, yanzu kam ko shakka babu ta fahimci shine... Wato dai Engr shine Mr Unknown d’inta... Ta kuma sakin murmushi a hankali tana mai k’arasowa yanda yake....

Tana ida k’arasowa ya wani juyo cikin slow motion yana mai zare beach glasses d’in da ya rufe idanunsa dashi wanda suka kuma fito da yarintarsa bama kace yakai shekarun da yake ba....

Gabaki d’aya ta zama speechless sai ido da take binsa dashi, ganin tai sororo da ita ya sanya Engr d’an kwanto da kansa kusanta kana yace “You look beautiful, I love you...!” yai maganar yana mai d’aga mata gira guda....
Sadda kanta kurum tai bata daina murmushin ba, lokaci guda take furta “So you’re Mr Unknown....?”
Engr ya kuma murmusawa yana mai kamo hannayenta duka biyu kana yace “And now I’m Mr well known...!”
Wannan karon murmushi mai d’an bayyana hak’wara tai kana tace “Ka tsoraceni you know...!” Tai maganar cikeda shagwab’a....
Murmushi mai bayyana hak’wara yai wannan karon shima kana yace “Toh ke menene ba abin tsoro ba wajenki, ko kin mace abinda kika min cikin jirgi...”
D’an darawa tai kad’an had’ida rufe fuskarta da tafukan hannaye...
Ya d’an murmusa shima kana ya kamota ya sakata cikin jikinsa had’ida rungumarta daga baya, su duka biyun suna facing view d’in ranar nan data kusa fad’i ga iska na kad’a ruwan teku a hankali... Kansa ya d’an d’aura saman kafard’arta, lokaci guda ya lumshe idanunsa yana shak’an k’amshinta mai sanyaya zuciya....
Itama d’in lumshe idanunta Ta d’anyi a hankali kana ta furta “This place is beautiful...!”
Ya kuma d’aura duka hannayensa saman cikinta had’ida d’an dad’a matsota kad’an kana yace “And ya k’ara kyau da ya amshi bak’uncin kyakkyawa irinki....!”

Nan ma dai murmushin tai kana Engr ya d’an juyo da ita suna fuskantar juna, lokaci guda yake furta “‘Yanmata ji mana... Can I take you out for a date...?” Yai maganar yana wani d’aga gira da kashe idanu...
Sosai ya bata dariya ganin wannan yanayi Daga wajensa, saikace bashi ba, ga wani yarinta da ya sauk’o masa..
Ta d’an juya idanunta kad’an had’ida sakalo hannunsa cikin nata kana tace “Well, no....!”
Engr ya d’anyi rau rau da idanu kana ya marairaice fuska yace “But why...?”

Juya idanu Ta kumayi cikin salo kana tace “Because I’m already taken...!”
Ya d’anyi still yana duban yanda acting d’in yai bala’in amsarta kana ya gyara tsayuwarsa yace “By who if I may ask...?”

Zulfah Ta kuma gyara tsayuwart kad’an itama had’ida sakalo hannayenta saman wuyarsa kana tace “By the most handsome, generous and honest man I’ve ever seen in my life...!”
Engr dake murmushi yana duban fuskarta kunkuminta ya kuma matsowa cikin jikinsa kana yace “Who’s that man da ya siye zuciyar wannan kyakkyawar with all those qualities you’ve mentioned....?”
Zulfah na murmushi suna d’an motsawa kad’an su duka biyun tamkar masu rawa kana tace “He’s right here I front me.... And I love him with all my heart.... I am yours.. !” Ta k’arashe tana mai karance haruffan gaban rigarsa kaman yanda yake a rubuce...

Murmushi ya kasa barin fuskar Engr, ganin abin yake tamkar mafarki... A hankali ya sumbaci bakinta, murya can k’asar mak’oshi yake furta “I love you... My number one....So much..!”
Lokaci guda ta shige cikin jikinsa suka kuma rungume juna suna masu lumshe idanu, zallan soyayyar junansu ne ke ratsa zukatansu... A haka suka isa table d’in suka d’an tab’a abincin daga bisani cak ya d’auketa tana zillewa bai ajeta ba har saida suka isa k’ayataccen d’akin nasu....
Wane irin soyayya mai tsafta had’ida maturity Engr Ke nuna mata.... Ta yarda tabbas shid’in masoyinta ne... Dik yanda Ta d’auki soyayya ashe ya zarce nan dan ita zatace bata tab’a yinta ba sai yanzu.... Kulawa da tattalin juna kam sunyisa a wannan tsibiri, wata irin rayuwa suka tsinci kawunansu ciki wanda zasuyi fatan su dawwama cikinta.... Saida suka shafe sati biyu masu kyau suna nunawa juna tsantsan k’auna mai tsafta a wannan ni’imataccen waje da zai dawwama cikin tarihin rayuwarsu kafin daga bisani suka dawo k’asa mai tsarki yanda suka gudanar da aikin umrarsu suma, kwanaki da bazasu kai goma ba suka k’ara a nan Saudia dan tini likitan a zai duba Ammah ya dubata kuma Alhamdulillah ta sami lafiya, a saidiyar ma sabon shafi soyayya suka bud’e kaman kullum su tabbata a haka, har wani haske da k’warjini Engr ya k’ara, kana ganinsa Kaga family man... Haka zai jidesu gaba d’aya suyita zaga malls suna sayayya, daga bisani suka d’aga zuwa k’asarsu ta gado Wato Nigeria....

Dawowarsu Nigeria Zulfa’u ta tare gidanta, su Atika dasu Aunty Zulai suka kawo mata ziyara, Atika sai tsiya take mata Wai Allah yasa an k’unso masu tsarabar D’an Maldives ko na Saudia...
Atika taci gaba da fad’in “Mutuniyar Excellency Ma wllhi har wani haske da kyau kika k’ara, Wai me Excellency yaita baki a can Maldives d’in ne...?”
Harara Zulfah ta galla mata kana tace “Kedai kyaji dashi... Allah ya shiryeki... Gayacan a parlornsa muje na rakaki Ki tambayesa da kanki....”
Zaro idanu Atika tai tana k’unshe baki lokaci guda take furta “Rufa min asiri bankai nan ba wllhi.. Kar kisa sojojin his Excellency su bundugeni....”
Darawa sukai a tare daidai sanda maids d’inta guda biyu masu sanye da uniform irinta ma’aikatan restaurants suka shigo kitchen d’in tana ci gaba da sanar dasu abinda zasuyi....
Atika dai sai dubanta take tana kuma jinjina lamarin... Al’amarin Allah kenan, yau Zulfa’u ce haka ta zamto babbar mace... Allah mai yanda yaso, mai baima wanda yaso d’aukaka a lokacinda yaso...
Koda su Atika sukazo tafiya saida his Excellency da matarsa suka cikasu da goma na arziki, abin ba’a cewa komai, tinkan Engr ya shiga office yaci gaba da hidiman Al’umma, zukata sun samu natsuwa albarka ya yalwatu, da alama gwabnati ne da za’ai tafiya ta matasa harmada dattawa saidai Allah son barka...

***

A can b’angaren Siyama kaw a ‘yan kwanakin bata gane jikinta, wane irin ciwon ciki mai tsananin gaske take yawan fama dashi wanda idan ya tashi mata bata iya tab’uka komai, tuni su Raihana da Sameer sun koma can Kaduna wajen Siyama yanda akai referring nata zuwa can Asibitin Koyarwa na Ahmadu Bello dake Zaria... Gwaje gwaje aka gudanar yanda aka gano Siyama na d’auke da cutar cancer ta mahaifa sakamakon magungunan hana d’aukan ciki da taita amfani dasu har sukaje suka toshe bakin mahaifar yanda suka taru suka haifar mata da wannan matsala...Allah sarki Zo Kaga tashin hankali wajen wad’annan bayin Allah, harta Raihanah saida ta shiga natsanancin tashin hankali maras misaltuwa, babu kaman Sameer da yafi kowa shiga tashin hankali ko ita Siyamar bata kaisa shiga tashin hankali ba, tabbas kowa ya tausayawa Siyama gabaki d’aya Zuri’a

Sameer na zaune gefenta hannayenta cikin nasa, tana kwance saman gadon marassa lafiya.. A haka shima bacci ya soma satansa sabida daren jiya sam bai rintsa ba.... A haka su Ammi da Mummy harma dasu Raihanah da Ijlaal suka turo k’ofar suka shigo....

Sameer ya bud’e idanunsa a hankali yana dubansu, take yaji zuciyarsa ta kuma raunana sanda ya maido da dubansaga Siyama dake kwance har kokacin idanunta a lumshe da alama bama taji shigowar nasu ba, Ammi ta kauda kanta gefe kad’an tana matsan k’walla... Lokaci guda Mummy ta k’araso gareshi had’ida dafe hannunsa, k’ok’arin k’arfafa masa gwiwa take da fad’in “Stay strong Son.... Siyama zata sami lafiya kaji.... Kaci gaba da mata addu’a....”
Jinjina kansa kurum yake amma shi kad’ai yasan mai yakeji cikin zuciyarsa....

Ijlaal ta K’araso jiki a sanyaye takai hannunta ta dafa Siyama dake kwance saman gadon...
A hankali yarinyar take furta “Aunt Siyama, please you need to get better... I miss you so much, I want you back at home.... Mummy tace you’re now my Mummy, please Ki dawo wajenmu kinji Mummy na... I love you so much...!” Ta k’arashe tana mai kwantar da kanta saman k’afafun Siyama....
Allah sarki dik wanda zaice bai zubda k’walla cikin d’akin nan ba yayi k’arya, zukatansu suka kuma raunana....
Kamo Ijlaal Sameer yai yana k’ok’arin maida nasa hawayen yake sharewa yarinyar nata hawayen lokaci guda yake furta “Mummynki would get better kinji Ijlaal, kici gaba da mata addu’a kinji...!”
A hankali yarinyar ta jinjina kanta tana mai kwanciya cikin jikin Sameer da tuni wasu hawayen sun gangaro masa...
Chapter 194 · 0% Book details