← Book details Inda Rai Da Rabo Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 178 OF 198

Sashe 178

Inda Rai Da Rabo Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Hanyar da yasan zai iya samunta yabi yana mai falfala gudu bisa kwalta.... Commotion d’in da ya hanga ya sanyashi yin slow....
Take ya paka motarsa a gefe ya nufi dandatson mutanen cikin sassarfa... Aiko nan ya hangi motar Siyama an kwankwatsa ga mutane chaaa sai cecekuce ake a wajen.... Babu shiri ya nufi wajen yana neman ta yanda zai ganta... Nan ya hangota tsaye cikin mutanen sai jefa masu masifa take itama da shike ba tayar baya bace, d’ayan har yana cewa zai suing d’inta.... Sameer ya k’araso yana mai girgiza kai had’ida tambayar ba’asi... Take d’ayan ya basa bayanin yanda abin ya kasance, yaci gaba da fad’in “Tasan bata a hayyacinta Ta hau kwalta wllhi bazan yarda ba sai ta biya ni damages dan Bazan d’auki asara ba...”
Siyama taci gaba da huci tana fad’in “Motar taka dika nawa ne... Kai kud’inta a biya... Kan wannan amalanken ne zaka bud’e baki kana min shouting aka... Who do you think you are...?!!”
Mutumin ya kuma zabura.. Sameer yai saurin tare gaban Siyama yana mai baiwa mutumin hak’uri had’ida masa alk’awarin za’a biyasa dik wasu damages d’insa... Da taimakon Sameer aka samu mutumin nan ya k’yale Siyama... Ita bama ta lura da jinin dake bin goshinta ba yanda glass ya tsaga sai masifa take tana juye dik wani b’acin ranta da bak’in cikinta ga mutanen nan....
Janyo hannunta Sameer yai yana fad’in “Ya isa haka Siyama... Shige muje....!”
Zata fincike hannunta yai mata wani ido babu musu ta shige fuuu kaman zata kifa k’asa... Haka suka zauna cikin motar babu mai cewa komai har dai taga Sun d’au hanyar gidansu Sameer d’in.... Lokaci guda Sameer idanunsa naga kwalta yake fad’in “What do you think you are doing Siyama...? Yanzu ba don Allah ya kiyaye ba who knows what could’ve happened to you...!” Cikin d’an fad’a fad’a yai maganar...

Shaye da mamaki take dubansa kana tace “Oh! Really now Sameer...? Now you care about me... Toh na mutu ma mana tinda baka damu dani ba....!!”

Idanunsa naga kwalta, cikin tsananin b’acin rai yake furta “Don’t... Don’t you dare change the subject... Baki ganin abinda kikai koh... Kuma kinyi laifi maimakon ki bada hak’uri kina dad’a ingizasu....!”
Katsesa tai da fad’in “Please don’t add to my headache...!!!”
Girgiza kai kurum yai yana mai danne zuciyarsa....

Ganin sun shigo close d’in gidan ya sanyata kuma karkatowa tana dubansa kana tace “Meye haka kuma...? Mai kake tinanin kanayi Sameer... Ni fah bazan shiga gidan nan yarinyar can tana ciki ba... Idan bazaka kaini can gidanmu ba Toh ka kaini gidan Daddy na... Amma bazan shiga gidan nan da yarinyar nan ciki ba...!!”

Bai amsata ba sai ma horn da yai aka bud’e masa gate.... Siyama tai masa k’uri tana kallon ikon Allah yanda Partner d’inta ya mugun canzawa, tayi imani da da ne yanda tace haka za’ai amma Wai yanzu shike mata abubuwa a gadarance... Wata zuciya kuma tace toh keda kike neman yafiyarsa, ai bisa kawai kiyi hak’uri... Tina Raihanah da Tai ne ya kuma cuzguna mata zuciya...

Yana ida parking ya fito ya zagayo mazauninta ya finciki marfin motar had’ida fuzgo hannunta, lokaci guda suka nufi cikin gidan Siyama na fincika tana fad’in ita bazata shiga cikin gidan ba muddin wannan kucakar yarinyar na ciki.... Ta balcony Raihanah ke lek’ensu gabanta na tsananta fad’uwa... Allah ya sani ko sunan Siyama taji sai gabanta ya fad’i balle ta ganta... Babu shiri ta juya ta koma d’aki a guje Ta fad’a kan gado tana maida numfashi... Take ta kuma d’aure hannu aka tana tino cewa d’azun fah da tai gyaran d’akin Ya Ma’aruf ta mance d’ankwalinta da zobenta a can... Ta rintse idanunta kurum tana karanto innalillahi..!

Bai zarce da Siyama ko ina ba sai d’akinsa... Ya isa ya d’auko first aid na gidan ya soma treating ciwonta fuskarsa a murtuk’e... Ita kaw sai b’alla masa harara take, cikin zuciyarta tana ayyana cewa yanzu haka ya gama cin amanarta da wannan kucakar yarinyar, ga d’akin tas tas yasha gyara na musamman dan shi kansa Sameer d’in saida ya fad’i haka cikin zuciyarsa sanda suka shigo....
Siyama bata ida tinanin ba ta hangi d’ankwali linke saman gadon da k’aramar zobe bisa... Kuka ne kurum taji yana zuwa bakinta.... Da gaske dai Sameer d’inta yanada wata bayan ita... She’s not ready to share him... K’uri tai masa yanda yasha mur sosai yana k’ok’arin rufe ciwon nata da bandage... Zuciyar Siyama taci gaba da tafarfasa... Lokaci guda take ci gaba da fad’in “So she was here... Maybe ma you two spent the night together.... Kai ko kunya bakaji ba Sameer... Just look at yourself...!”
Da tsananin fuci yake dubanta kana yace “I don’t have time for your stupid tantrums... And don’t think sabida naje na d’auki yana nufin mun dawo normal like before bane... Sabida mutum uku nai haka Mummy, Daddy and Raihana...!” Yai maganar yana mai jinjina kai alamun tabbatarwa kana taci gaba da fad’in “Yes Siyama ki gode masu, if you’re still my wife... It’s because of them... And one more thing Siyama... You’re not in any position to question my authority... Wannan ya zama gargad’inki na k’arshe....Treat your wounds yourself.. !!” Ya k’arashe yana mai jifa mata bandage d’in a fuskarta....

Siyama ta saki baki tana binsa da kallo, wane irin kuka na zuwa mata.... Jiki a sanyaye Ta kwanta bisa gadon tana cazgan kuka....

Juyin duniya Mummy tai Siyama ta fito taci abinci tak’i fitowa... K’arshe Raihanah ita ta d’auki abincin ta nufi d’akin Sameer dashi ba tareda Mummy Ta sani ba....
Raihanah tai knocking a k’ofa amma shiru ba’a kulata ba.... Ta sakeyi nan ma shiru.... Har kaman zata juya da abincin sai kuma taji an bata izinin shigowa....

A hankali ta tura k’ofan ta shigo sallama saman bakinta tikda lugude da k’irjinta keyi yawa zai tarwatse tsaban tsoro....

Kallo d’aya Raihanah taiwa Siyama taji gabanta ya wani irin tsinkewa... Siyama sanye take da d’aya daga cikin kayan mijinsu, Black long sleeve check da ya kuma fito da hasken fatarta, gashin kanta mai tsananin tsantsi da shek’i a jik’e yake dik ya kanarnard’e alamun yanzu Ta murjesa da towel, daidai da jeans d’in jikinta na Sameer ne dan jakan kayanta na cikin nata motar bata samu ta d’auko ba bayan accident d’in da ya auku...
Folding hannun rigar taci gaba da yi tana mai k’arewa Raihanah kallo daga sama har k’asa.... Babu Wai tasha jinin jikinta da ganin yanayin halittar yarinyar dan sam bata k’are mata kallo ba sai yanzu... Babu shakka Allah yai mata kyaun diri da Babu d’a namijin a bazaiso mallakar mace irinta ba...
Siyama taci gaba da watsa mata mugun kallo tana mai zagayeta, yayinda Raihanah ta kasa katab’us saima karkarwa da jikinta keyi tana tuhumar kanta anya batayi ganganci shigowa ba....
Wani tsawa Siyama ta darara mata wanda ya sanyata kusan kifa tray d’in dake hannunta....

Siyama taci gaba da fad’in “Munafuncin banza da wofi kin wani d’auko abinci nik’i nik’I kega mai hankali ko..? Idan kinaso Ki nuna min kin cika mai hankali sarkin kirki Toh Ki rabu da mijina shine zan tabbatarda generosity d’inki... D’ago ki kalleni....!”

Kasa d’agowa tai sabida hawaye dake ziraro mata... Siyama ta murmusa a hankali kana tace “Badon cushe ba babu abinda Sameer zai dake... You’re not even his type... Ke ki dubi kanki ki k’are ma kanki kallo Sameer ba daidai ke bane.... Kinga yanda nake sanye da kayansa toh haka muke nidashi Magnets...!” Ta k’arashe tana mai alama da hannayenta lokaci guda taci gaba da furta “Now get out... Wuce ki fita kafin na kwab’a miki abincin nan a fuskarki..!!”

Raihanah dake kuka sosai cikin sauri ta juyo ta fito daga d’akin d’aule da tray d’in... Saidai a daidai staircase Siyama ta kuma kiranta ta tsaida ita... Takowa yanda take Siyama tai. Kana tace “Wait... It was you... So kece kika d’auki wayarsa a asibiti kwanakin baya da na kirasa....?!” Ta kuma murmusawa kana tace “Wato kin jima kina bibiyan mijina har wajen aikinsa...”

Raihanah da hawaye ke gangaro mata girgiza kai tai kana tace cikin rawar murya “Ba bibiyarsa nake ba shine likitan da yai treating ciwona sanda na k’one... Ki yarda dani Aunty Siyama wllhi ba bibiyarsa nake ba....”

Siyama ta kuma murmusawa a hankali kana tace “So you’re even aware of my husband is a plastic surgeon... Barin dad’a k’onaki da abincin nan sai yai treating naki da kyau....!” Ta k’arashe tana mai fatali da tray d’in abincin dake hannun Raihanah... Allah ya rufa asiri abincin babu zafi... Hakan yai daidai da fitowar Mummy... Sosai taiwa Siyama fad’a hardai k’arshe fad’an ya juye ya koma nasiha mai ratsa zuciya....

Mummy taci gaba da fad’in “Siyama this is not you... This is not who you are.... Ina Siyamar da na sani mai taimakon marayu da mabuk’ata...? Don’t allow yourself to get carried away by your emotions... Raihanah batada laifin komai, hasalima k’ok’ari take taga ta kyautata miki... Siyama dik abinda kwanciyan hankali bai badashi ba toh ki sani tashin hankali bazai badashi ba...”

Siyama ta d’ago idanunta masu zuban hawaye kana tace “Mummy maiyasa Sameer zai kawo wata cikin rayuwarmu idan ba daina sona yai ba...” Ta k’arashe cikin rawar murya...

Kamo hannayenta Mummy ta kumayi kana tace “Sameer loves you Siyama... He never stopped loving you... He always does... Da ace bai sonki da bazaije ya d’auko ki ba.... So please kar Ki baiwa mak’iyanku dama su cimma burinsu na ganin sun rabaku kinji...!”

A hankali Siyama ke jinjina kai had’ida kwanciya cikin jikin Mummy hawaye na ziraro mata...
Tabbas idan tana k’aunar Sameer batada zab’in da ya wuce tai hak’uri Ta amshi k’addararta a yanda yazo mata dikda tasan hakan abune mai matuk’ar wahala....

***

KANO

Suna ida waya da inspector Bala wata wayar ta shigo masa... Da tsananin mamaki yake bin wayar da kallo ganin ba kowa bane yakeda wannan layi nasa na musamman.... Dikda bugu da k’irjinsa keyi hakan bai hanasa d’aga wayar ba... Tamkar wanda aka zabura ya kuma mik’ewa tsaye yana furta “Akram.... Akram is that really you....?! Akram tell me mai ya faru dakai....?!”
Chapter 178 · 0% Book details