Sashe 157
Inda Rai Da Rabo Part 1 Complete Hausa Novel · about 4 min read
A can gidan Abbah kaw dik yanda suke tinanin zasu sami Mamani sunje amma babu Mamani babu labarinta, harta mutanen Kazaure sunce bataje can ba dan tin a biki da suka rabu da ita cikeda fushinta basu kuma jin d’uriyarta ba, hankalin Abbah dasu Baffah Wada yakai k’ololuwa wajen tashi, k’arshe dai Abbah cewa yai dole a bada cigiyan Mamani, ta ko ina abubuwa babu sauk’i, lokaci ne da ya zamto tamkar na farin ciki amma ta wasu fuskokin akasin Farin ciki ne... Wasu irin tashin tashin na hankula suka tsinci kansu ciki... A b’angaren Lami ma tashin hankali maras misaltuwa take ciki, itada shara a gidan basuda maraba, babu maibi takanta dan damuwan dake gabansu kad’ai ma ya ishesu... Haka takanyi jigum a d’aki tana tinanin abinyi, dik zaman gidan ya isheta ta gundura, ta tabbata har abada zaman gidan bazai kuma mata dad’i ba saidai ta mutu ita kad’ai a d’aki dikda cewa tayi imani dan hankalin Mamy bai tattareda ita ne a halin yanzu sabida b’acewar Mamani amma ta tabbata da yanzu Mamy tayita tausarta tana bata baki dikda ma ita akaima laifi, tasan halin hak’uri da kirki irin na Mariya... Amma wannan cin amana da tai mata da yawa take, harga Allah tana kunyar fuskantarta... Uwa uba Abbah da takeji kaman ta tattari i nata i nata ta tafi ta bar gidan Kafin ya saketa, Toh Wai idanma an saketa ita ina zataje tace an saketa a halin yanzu.. God’e god’e da ita sai ta hau tattaran k’afa taje tace an saketa... Ta share hawayen da suka kuma zubo mata... Tabbas yau d’in tana nadama da bata tab’a yin irinta ba tsawon rayuwarta...
***
A guje tabi bayan Hafiz tana kuma fuzgo rigarsa tana fad’in “Wllhi baka isa ba, mai kake tinanin zakai... So make a kamamu mu k’arashi rayuwarmu gidan Yari ko mi....?”
Hafiz ya fincike rigarsa bai daina huci ba yake furta “I’ll be very glad idan hakan ta kasance... Na tabbata idan aka kamaki da laifin garkuwa da d’an Adam mahaifiyarki zata had’iyi zuciya tinda Ke kad’aice d’iyarta, Kinga banida sauran damuwar ganinta cikin gidan mahaifina....” Ya k’arashe yana huci....
Girgiza kai Sawwama take lokaci guda take furta “Lallai na yarda baka cikin hankalinka Hafiz.... Idan kai wani abu foolish both nidakai will end up in jail... Haka kake so...?”
Hafiz ya murmusa kad’an kana yace “ Toh ni kuma wata rayuwa ce mai dad’i ta ragemin a halin yanzu... I’ve lost everything, every single thing... Na rasa d’iyata Khausar sannan na rasa Zulfa’u... What else... Ki fad’amin mai kuma nake tsoron rasawa...?!!”
Ya k’arashe cikin daka tsawa hawaye na tsartowa daga idanunsa, lokaci guda yaci gaba da fad’in “I have nothing to lose.... So Idan bazakije ki tilastawa mahaifiyarki ta tafi ta k’yalemin iyaye na ba... I’m gonna show you what I’m really capable of..!” Ya k’arashe yana mai ficewa cikin sauri...
Sawwama tabi bayansa tana doka masa kira amma inaa ko tsayawa baiba.... Sawwama ta koma cikin gida a guje tana lalumen wayan salulanta...
***
Hab’arsa d’aure saman hannayensa biyu da ya dunk’ule waje guda... Da alama yayi nisa cikin tunani... Lokaci guda ta aje masa ruwan tea d’in gabansa had’ida zama gefenta kad’an.... Ya sakar mata sassanyar murmushi had’ida furta “Na gode Matar....!”
Ta d’an saki murmushi a hankali tana mai sadda kanta, zata juya kenan taji ya ambto sunanta... Gabanta ya yanke ya fad’i, yauce rana ta farko data tab’a ji ya ambaci sunan nata... Ta juyo hankali tana mai amsawa...
Gefensa yai mata nuni dashi yace tazo ta zauna....
Gabanta ya kuma tsinkewa but she can’t say no to him... A hankali ta tako har kusan nasa... Before tai aune taji ya kamo hannunta ya zaunarta kusansa sosai... K’irjin Zulfa’u yaci gaba da bugu.... Shiko Engr k’uri yai mata yana babu ko k’yafta idanu, dik sai tajita ba’a sake ba, ya d’an kurb’i tea d’in kad’an da gaba d’aya ya mance da zafin tea d’in sabida yanda ya shagala da kallon amaryar tasa... Zafin da yaji saman harshensa ya sanyashi d’an sakin k’ara kad’an had’ida cire cup d’in daga bakinsa yai saurin ajewa k’asa, hakan yasa Zulfah tai saurin waigowa tana tambayarsa mai ya faru, daidai ya d’ago kenan bayan ya ije cup d’in fuskokinsu suka had’e waje guda... Tsinin hancinsu suka had’e su duka biyun suna jiyo hucin numfashin juna...... Wane irin yanayi ne maras fasaltuwa suka tsinci kawunansu ciki.... Zuciyoyinsu suka ci gaba da bugawa, so take ta janye fuskarta amma ta kasa, k’arar da wayarsa tai ya sanyata saurin janye nata fuskar zuciyarta bata daina bugawa ba... Engr yai k’ok’arin saita kansa had’ida janyo wayar saman table... Jin ya soma amsa waya ya sanyata tattaro duk wani strength d’inta tana k’ok’arin tashi amma sai ji tai hannunsa saman nata ya rik’ota, hakan ya hanata ci gaba da tafiya... Tai saurin rintse idanunta k’irjinta naci gaba da bugu, batada wani zab’i dole ta dawo da baya ta zauna a d’arare... Da alama da jami’an tsaro masu binciken Akram yake wayan... Ta k’ura ma yatsun hannunsa idanu yanda ya sakalesu cikin nata, ko motsi mai kyau ta kasa sabida tsananin nauyinsa da takeji....
SameenaAleeyou📚
*INDA RAI*
_................DA RABO_
*99*
*©️Sameena Aleeyou...✍🏽*