← Book details Inda Rai Da Rabo Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 170 OF 198

Sashe 170

Inda Rai Da Rabo Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Muhibbah ta kuma takowa gabansa kana tace “I want you to sabotage my husband’s campaign... Inaso jami’an tsaro su kama muggan miyagun k’wayoyi a wajen campaign d’insa ta yanda duniya zata fahimci shid’in ba mutumin kirki bane kaman yanda suka d’auka... Ina so abin ya kasance tamkar shid’in raba miyagun k’wayoyi yakewa matasa.... I want to see him on the ground...!” Ta k’arashe tana tsananin huci...
Murmushi Bash yai had’ida gyara tsayuwarsa kana yace “Why do you want ruin your husband... I thought duk munaso yaci zab’e ta yanda sana’armu Zata bunk’asa ba tareda kowa ya saka mana idanu ko ya zargemu ba tinda mukeda gwabnati... Why the sudden change of mind...?”
Muhibbah na huci take furta “Engr ya koreni... So ni kuma ka sanni.. The word losing is not even in my vocabulary.... Shisa nake so Kafin ya wulak’antani ni zan d’aid’aitasa...!”

Bash ya murmusa a hankali yana shafar hab’arsa kana yace “Idan har hakan bazai shafi business d’inmu ba ai ba matsala bane... You have my unconditional support....Zan saka yarana su shiga ayarin campaign d’in mijinki... Za kuma mu kira jami’an tsaro mu sanar dasu akwai miyagun k’wayoyi a wajen... Daga nan kinga shikenan....”
Muhibbah ta murmusa kana tace “Jibi zai fita campaign a yanda na sani... Ka sanar da yaranka su zama ready...!”

Murmushi Bash yai kana yace “And what do I get in return....?”

Murmusawa Muhibbah tai kana tace “A big reward idan har hakan ta kasance....”

Ya kuma murmusawa yana shafa hab’a kaman wani tsohon maye kana yace “Consider your husband ruined...!” Daga haka dariya Muhibba ta kece dashi cikeda jin dad’i....

***

ABUJA

Babu wanda Siyama ta masa sallama sun waye gari suna shirye shiryen tafiya Asibiti amma babu Siyama, haka Ijlaal data farka babu Siyama kuka taita masu dan daren jiyan tare suka kwana cikin jikin juna, Aunty Hanne kaw tana zuwa sassafe suka k’ule a d’aki itada Ammi a cewarsu sune k’arshen tafiya asibiti... Duk an watse dake da safe suke tafiya asibtin, su Ijlaal ma sun tafi makaranta..
Haka kurum AuntyB taji zaman su Ammi su biyu daga ita sai Hanne a gidan bai mata ba....Hakan yasa taceda Daula su fara gaba daga baya Shayibu zaizo ya kaita... Aunty Daula kam bata kawo komai ba sukai gaba abinsu...

Har saida su Ammi sukai tinanin k’afa ya d’auke gaba d’aya kana suka lab’ab’o suka fito... Aunty Hanne ta d’aga Bakin zaninta ta zaro k’unshin magani a leda ta mik’awa Ammi... Ammi tai zuru tana dubanta tana juya ledar... Loakci guda take furta “Ya Hanne nifah kinsan abubuwan tsubbun nan naki tsoro suke bani, shi kuma wannan na menene...?”
Tsuka Anty Hanne tai kana tace “Ba don abubuwan tsubbun da nake baki ba zaki samu kan mijinki ne ki dinga abinda kikaga dama a gidansa... Ba don magungunan nan ba ce miki akai Mijinki zai aure a b’oye gudun kar ki sani ne...? Toh yanda yai auren nan a b’oye wannan magunguna su zasu datse auren mijinki da wannan shu’umar yarinyar... Ita kuma yarinyar da suka lik’ama Saifullahin daga baya maji da ita... Dan ita ban d’auketa wata aba ba ma...!”

Ammi tai jigum tana juya maganin kana tace “Amma dai Babu na kisa a ciki ko Hanne kinsan dik bak’in kishina bazan kashe rai ba....”
Nan ma tsuka Anty Hanne tai kana tace “Ke da anyi magana sai kice babu na kisa... Tsaya kiji idan zaki sha giya kisha Ta dubu Farida ki daina wani tsoro tsoro...”
Ammi tace “Naji dai... Babu na kisa, babu mugun cutarwa su rabu kawai abinda nake so kenan...”
Anty Hanne tace “Babu na kisa, saidai da zaran kin barbad’e wad’annan a kusurwowin gidan nan, da zaran mijinki ya fito daga jinya ya shigo gidan zaiji ya tsanesu daga ita har yaran nata ina mai tabbatar maki saidai subi ‘yanuwansu su koma yanda suka fito....”
Ammi tace “Hakan yamin dan bazan juri kallon wannan kayan k’ask’ancin ba....!”

Haka suka nufi ko Wanne kusurwa na gidan suna barbad’awa har suka shige store d’in kitchen.. Aunty B dake biyedasu cikin sand’a suna shigewa store d’in ta janyo k’ofar da sauri ta rufe kif k’ofar tai jamming dasu Ammi ciki.... Hankali tashe suka shiga bugun k’ofa cikeda firgicin waye ya rufesu gashi basuga kowa ba dai... Ga duhun store gashi babu wani wadataccen vent.... Ammi ta dubi Anty Hanne tace “Hanne kodai aljanu ne suka rufemu.. Kinga bugun duniya bamuji d’uriyar kowa ba...!”
Anty Hanne tace “Anya kuwa Farida... Kodai yaranta basu tafi makaranta bane...?”
Kaman daga sama suka soma jiyo wata irin dariya mai ban tsoro tana furta “Ku sani Ramin mugunta k’urerre ne... Yau kun hak’i kabururukanku da kawunanku...Hajahjjahhhhhaaahhh..!!!!” Aka kuma tuntsurewa da wata irin dariya....
Ammi da tuni jikinta ya d’auki rawa, a matuk’ar tsorace take fad’in “Bawan Allah dan Allah waye ka..kai... Kai mana rai... Kada ka kashemu a wajen nan....!”
Dariyar aka kuma fashewa dashi kana muryar taci gaba da fad’in “Ni ne wanda yasan sirrikanku da kuka bisne....” Tiryan Tiryan muryar ya karanto laifunkansu da abubuwan da suke kuma k’ullawa,... Yanzu kam ba Ammi kawai ba harta Anty Hanne ‘yan hanjin cikinta sun kad’a jin wannan mutumi mai wargajejen murya yasan komai nasu... Ammi ta had’iyi miyau da k’yar kana tace “Bawan Allah kai mana rai wllhi mun tuba....!”

Muryan ya kuma fashewa da wata irin bahaguwar dariya kana yace “Maiyasa Zanyi rangwame wa matar data kasa rangwantama d’anta da mijinta... Maiyasa zanyi rangwamewa azzalumai masu cutar da bayin Allah a doron k’asa.....Hahhhhhahahahahahahahhha!!!!” Muryar ya kuma sakin wani irin dariya....
Ammi da tuni ta soma sakin fitsari ta shiga d’aga kai sama ko zataga mai wannan magana....
Ta ramin k’ofa Aunty B ke lek’enta kana ta kuma saita voice changer na wasan su Ijlaal taci gaba da bud’e murya da taimakon abin tana ci gaba da fad’in “Ina kallonki Farida saidai Ke baki kallo na.... Kuma ‘yar uwarki da kika aminta da ita bata k’aunarki....Cin dunduniyarki take... Ki tambayeta Gata gabanki....”

Ammi ta kuma razana ta juyo tana duban Anty Hanne dake faman girgiza kai tana fad’in “Ni... ni... No Farida bazan tab’a cin amanarki ba....!!”

Muryar yaci gaba da fad’in “Hahhhajahahaha mugu shi yasan makwancin mugu.... Faridah...!!!!”

Ammi jiki na rawa tace “Na...na’am....!!!”
Muryar yaci gaba da fad’in “Shin Hanne Ta baki garin magani ki zuba a ko wacce kusurwa ta gidan nan ko bata baki ba....?”

Jiki na kyarma ga uban gumi dake keto mata Ammi tace “Anyi haka... Wllhi ta bani...!”

Muryar yace “Kuma kinbi ko wata kusurwa kin barbad’a.... Anyi haka ko ba’ayi haka ba...?!!!”

Ammi na matuk’ar kyarma tace “Anyi wllhi ta bani kuma na barbad’a....”

Muryar yaci gaba da fad’in “Koda ta baki ta sanar dake maganin da zai kori kishiyarki da yaranta ne... Haka ne ko ba haka ba....?!”
Cikin sauri Ammi ta jinjina kai tana furta “Haka ne yallab’ai...!” Dan yanzu bata mamakin wannan murya da tafi dangatata da ta mutanen b’oye yasan duk abubuwan da suke shiryawa....

Muryar yaci gaba da fad’in “Toh wannan magani bana korar kishiyarki da yaranta bane kaman yanda ta fad’a miki....!”
Gaban Ammi ya bada Dumm!!! Ta waigo sosai tana duban Anty Hanne dake muzurai tana mamakin sharrin da ake k’ulla mata gaban idanunta...

Muryar yaci gaba da fad’in “Kinaso kisan amfanin wannan magani...?!!”

Murya har na rawa Ammi tace “Eh... Eh Yallab’ai inaso na sani....!!”

Muryar ta kuma kecewa da dariya kana tace “Wannan magani da kika barbad’a da hannayenki a ko wacce kusurwa ta gidan nan bata komai bace face ta mutuwar d’anki Khalid...!!!”

Ammi ta saki k’ara tana yarfe gumin dake kuma keto mata, lokaci guda Ta duk’a saman gwiwoyinta tana kururwa take fad’in “Kamin rai kada ka kashe min tilon d’ah na na rok’i arzikinka....!!”

Muryar ya kece dariya kana yaci gaba da fad’in “Bani zan kashesa ba dan mutuwa da rayuwa bata hannuna kuma kema bata hannunki... Saidai kece zaki zama sanadiyar mutuwar d’anki da kanki... Dan wannan magani da kika barbad’a da zaran d’anki Khalid ya shigo gidan nan zai mutu... Hanne tayi haka ne dan Khalid d’in bai aure d’iyarta Yesmin ba, ta zab’i a kashe Khalid kowa ya rasa tinda ‘yarta bata samu ba... Kinga alhakin mutuwan d’anki na wuyanki....!!!” Muryar ya k’arashe yana mai kuma bankewa da dariya...

Hannu bibbiyu Ammi ta dafe kai tana furta “Wayyo na tuba... Wayyo Allah Khalid d’ina... Dan Allah ka taimaka min na fice na cire magungunan nan.... Wayyo ni Farida...!!”

Muryar ya kuma kecewa da dariya kana yace “Kema bazaki fita ba balle ki hanasa shigowa...!!” Ya kuma kece dariya...

Ammi ta d’aura hannaye aka tana furta “Na shiga uku na lalace ni Farida... Khalid kamin rai kada ka shigo gidan nan....!!!” Ta juya ta kalli Aunty Hanne da mamaki ya kasa sakinta... Ammi tayo kanta tana furta “Kin cuceni Hanne... Kin cuceni... Ki rasa abinda zaki saka min dashi sai hallak’a d’anah dan kawai baison wannan mayyar d’iyar taki.... Wayyo ni Farida wllhi Khalid ya mutu mutuwa zanyi nima.... Hanne kin cuceni kin d’aurani a turban halak’a....!!!”

Anty Hanne na kuka take fad’in “Wllhi sharri ne ta ya zan miki hakaFarida, ta ya zan kashe Khalid... Khalid fah d’ah na ne... Wllhi ba maganin kashe Khalid bane....!!!”
Inaaa fincika Ammi take tana fad’in “Kar ki matso kusana Hanne... Kin cuceni kin ci amanan zumunci... Wayyo Khalid dan Alla kada ka shigo...!!” Ta zabura ta nufi k’ofa tana jijjigawa da iyaka k’arfinta amma ta kasa koda motsawa abinka da gini mai aminci.... Ammi fah gaba d’aya ta fice hayyacinta... Ita yanzu bata kanta take ba... Ta Khalid d’inta take kada ya shigo wannan gida tinda idan ya shigo toh fah saidai a fidda gawansa.... Ga unguwanni ihunka banza yanayin ginin ma kawai bazai bari aji meke faruwa ba, gashi kowa sabgan gabansa yake....
Chapter 170 · 0% Book details