Sashe 196
Inda Rai Da Rabo Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read
Ganinsu a haka ya d’an saka Raihanah sadda kanta ita kaw Ijlaal a guje ta tafi ganin Siyama ta farka, nan suka shiga rungume juna suna fad’in irin kewar juna da sukai, Raihanah ta k’araso tana gaidasu Sameer na tsareta da idanu dan sai yanzu yake fahimtar wasu changes tattareda ita, ga wane irin cika data k’ara, baidai ce komai ba sai k’are mata kallo da yake wanda ita kanta saida ta tsargu da wannan irin kallo da yake binta dashi, gaisawa dai kawai take da Siyama amma ta sani idanunsa k’yam suke akanta dan harta ‘yan yatsun hannunta Ta kula dubansu yake daki daki.... Hakan bai hanata gudanar da abubuwanta kazar kazar ba dan bataso ya fahimci ta gane yana mata kallon k’urilla.... Lemon with hot water kaman yanda Dr Ahmad Tahir yace shi za’a soma bata idan ta farka hakan yasa Raihana mik’ewa tana k’ok’arin had’a mata dikda muguwar hajijiya dake yunk’rin kada ita ga mijin nasu ya tasata gaba da kallon k’urilla....
Ganin tana d’an dafe kanta sanda take k’ok’arin janyo flask na ruwan zafi ya sanya Sameer saurin mik’ewa yana fad’in ta bashi ya k’arasa had’awa, k’in sakar masa tai saima cewa da take ya barshi zata iya.... Ya tsareta da idanu sosai yana fad’in ta bashi flask d’in... A shagwab’e take mak’e masa kafad’a tana fad’in itafa zata iya.... Sameer yai mata k’uri yana duban cikin idanunta, Sai sannan hankalin Siyama dake ta biyewa Ijlaal yayo kansu, tai kwance tana duban yanda su duka biyun suke rige rigen kyautata mata, a hankali Ta saki murmushi mai sanyi.... Saidai nan ta hangi Raihanah tamkar tana layi jiri na shirin kada ita... A d’ari Sameer ya tarota ta fad’o hannunsa.... Ya shiga d’an jijjigata yana ambato sunanta... Daga Siyama har Ijlaal hankali tashe suke dubansu....
A hankali ta soma bud’e ido tana kuma dafe kanta... Daidai sanda Dr AT ya shigo ya taddasu haka... Nan ya kirawo nurses guda biyu suka taimakawa Raihanah zuwa next room.... Sameer da gaba d’aya a birkice yake ya mik’e yana duban AT dake rik’e da result d’in Siyama, kafin yai magana Siyama tace “Partner go... Just go to her, je kaga meke damunta....Nikam Alhamdulillah ai...besides ga Baby na tareda ni...” Ta k’arashe tana kuma janyo Ijlaal..
Ya d’an shafi fuskarta yace “Are you sure...?”
Jinjina masa kai tai tana murmushi.... Murmushin shima ya sakar mata yana mai kuma shafar fuskarta... A tare suka fice da Dr AT yana fad’i masa sakamon result d’in Siyamar wanda yai kyau sosai... Daga AT har Sameer d’in test suka buk’aci nurses su gudanarwa Raihana, Sameer dake zaune gefenta idanunta a lumshe yatsun hannunta ya kamo yana kuma duban k’umban da kyau... Shi kad’ai ya saki murmushi yana mai ayyanawa cikin zuciyarsa... Amma dai bara ya jira yaji daga bakin Dr AT.... Jim kad’an kaw saiga AT rik’eda result... Sameer ya mik’e yana tambayarsa meke faruwa....
Murmusawa AT ya d’anyi kana yace “Sameer mai tagwayen mata....” Sai kuma ya mik’a masa result d’in yana zolayarsa da fad’in “Ko shima na karanta maka ne tsoro kake...”
A tare suka d’an murmusa kana Sameer yace “Tinda na rigada nazo nan kaine likitan a nan so just tell me...”
Murmusawa AT ya kumayi kana ya mik’a masa hannu alamun musabaha yana mai furta “Congratulations Madam is carrying your baby.... You’ll soon be a father....”
Jin abin yake kaman a mafarki da gaske dai shine zaiyi d’ah.... Kai Ubangijinsa ya cika abin godiya, Ya yayewa matarsa Siyama cutar da take fama dashi sannan at the same time ya albarkacesu da samun RABO.... Ashe da RABON yaga jininsa.... Take yaji hawaye na Farin ciki suna gangaro masa, tabbas tsanani na tareda sauk’i kuma ance mahak’urci mawadaci... Baisan sanda ya rungume Dr Ahmad Tahir ba yana mai cikeda Farin ciki had’ida godewa Ubangijinsa....
AT na ficewa Raihanah Ta bud’e idanu a hankali, nan taga Sameer zaune gefenta yana kallonta murmushi saman fuskarsa.... D’an dafe kanta kad’an tai kana tace “Mai ya sameni, Ina Aunty Siyama.... Tasha tea d’in...? Bara naje na bata....” Ta k’arashe tana k’ok’arin sauk’owa.... Bai bari ta sauk’a daga kan gadon ba sai rungumota da yai yana fad’in “Partner you stay right here...”
Dubansa tai jin ya ambaceta da Partner.... Ta d’an dubesa kad’an kana tace “Nima Partner d’inka ce...?”
Ya sakar mata murmushi yana mai shafan fuskarta kana yace “Of course you’re my Partner... We’re life partners...”
D’an Jim tai kana tace “Does that means kana so na kaman yanda kake son Aunty Siyama...?”
K’uri yai mata cikeda tausayinta dan lately yai neglecting d’inta gaba d’aya harma bai fahimci cewa tana d’aukeda juna biyunsa ba balle ya bata kulawan da ya dace... Koda shike halinda Siyama ta tsinci kanta ciki na cuta shi ya karkatar da tinaninsa dan bai tab’a kawowa bazai rasa Siyama ba... Shafa fuskarta ya kuma yi ganin hawaye na gangaro mata kana yace “Raihaan have I ever told you tin sanda na soma bigeki da mota sanda na soma d’ora idanuna kanki.... Tin lokacin na kamu da k’aunarki.... So never doubt, kar ki tab’a kokoton son da nake miki kinji koh...”
Ta jinjina kai a hankali tana mai dubansa.... Janyota ya kumayi cikin jikinsa yana mai shafa bayanta a hankali.... Tana kwance cikin k’irjinsa take fad’in “Wai menene ya sameni..? Nifa na warke mu koma wajen Aunty Siyama....”
Kanta na cikin jikinsa yake fad’in “No ki huta a nan... Babu abinda ya sameki Babynmu ne ya sanyaki fainting...”
Ta d’an d’ago tana dubansa....
“Baby...?”
Jinjina mata kai yai murmushi saman kyakkyawan fuskarsa....
Hannunta ya kuma kamowa yana mai ci gaba da fad’in “You’ll soon be a mother.... You’re pregnant My love...!”
Jin abin tai wane iri Wai ita keda ciki.... Ta kuma dubansa tana kuma duban kanta.... Lokaci guda ta d’an kai hannunta saman cikinta tana mamaki...
D’ago fuskarta yai kana yace “Do you love our child...?”
Ta saki murmushi a hankali tana mai girgiza masa kai, a hankali take furta “So much.... But idan na haifeshi ko menene zan baiwa Aunty Siyama ne....Ita zata zamto mamanshi ko mamanta... Please ka amince min...”
K’uri yai mata k’aunarta na kuma fizgarsa...
Siyama da basu San da shigowarta ba tintini... Ta k’araso cikin d’an d’ingisawa ta dafa kafad’ar Raihanah....
D’agowa Raihanah tai tana dubanta nan taga hawaye saman fuskar Siyama... Lokaci guda Siyama ta d’an kwanto ta rungumeta wasu hawayen na kuma gangaro mata... Su duka biyun hawaye suke..... Sameer ne ya had’esu gaba d’aya ya rungume yanda ya hangi Ijlaal tsaye gefe, janyota yai itama ya rungumesu gaba d’aya zuciyarsa na masa wane irin sanyi yana mai mik’a godiyarsa ga Ubangijin Rahama....
Sati guda Siyama ta k’ara a asibiti aka sallameta, gashi dik wanda sukazo duba Siyama sai ta sanar dasu Raiha nada ciki, gaba d’aya ita ke d’aukin cikin saiko Sameer dan Raihanah kam fama da kanta kurum take, dikda Siyama bata ida warkewa ba batai k’asa a gwiwa wajen kulada Raihanah ba, ita da Sameer an rasa waye gwani wajen bata kulawa na musamman... Wani sa’in dukansu biyu suke d’aura kunnuwansu saman cikin Wai suna jin ko ya soma motsawa, haka Raihanah zatai ta dubansu tana dariya.... Oh shakka babu rayuwa tai dad’i sai san barka....
**