← Book details Inda Rai Da Rabo Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 84 OF 198

Sashe 84

Inda Rai Da Rabo Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Cikin sauri ta mik’e ta fice a guje tana mai fashewa da kuka bata zarce ko ina ba sai wajen Ammi, Ammi na zaune saman rug tayi d’ai d’ai ga laces zube gabanta sai d’add’agawa take waya manne kunnenta da alama da mai kayan take wayar, yayinda Kubura ke faman gyare gadon Ammin....
A guje Yesmin ta shigo ta fad’a kan Ammi tana kuka harda shesshek’a....
Cikin sauri Ammi ta katse kiran tana mai sanarda matar da suke wayar zata sake kiranta....

“Lafiya.... Ke Yesmin ki tashi kimin bayani.....”
Cikin kuka Yesmin ke fad’in “Ammi Khalid ne....”
Cikin d’an daburcewa Ammi tace “Khalid..? Mai ya sami Khalid d’in...?”

“Cewa yayi babu abinda zaiyi dani Ammi... Ammi I did everything I could for him to love me back amma yak’i cewa yayi baya min kallon mace banida abinda yake so jikin mace....” Ta k’arashe tana mai kuma fashewa da kuka....
Kubura tamkar ta daka tsalle haka taji, ta shiga k’arewa kanta kallo tana mai ayyanawa cikin ranta mace irinta Khalid ke buk’ata...
Ammi kaw gajeren tsuka tai kana tace “Kedai bakida wayo sam Wllhi Yesmina, saikace bakisan halin Khalid ba, Yo da baison naki zai amince da aurenki ne...? Banda abinki shi namiji ai d’an lallami ne, Kar kiyi k’asa a gwiwa kici gaba da binsa a sannu sai kiga ki samu kansa, share hawayenki ki bar kuka yanzu zanje na samesa muyi maganar lefe, sadaki da sauran hidima dama Daddynsa yace duk zaiji dasu... meye abin kuka bayan ya kusa zama naki gaba d’aya... D’akin da ya koreki d’inma ya kusa zama naki, da sannu zaki koya masa yanda zai soki....Share hawayenki banson ganinsu kinji koh...” Yesmin ta jinjina kai cikeda jin dad’i tana mai furta “Thank you Ammi na you the best...”

Kubura ta rakasu da harara daga Ammin har Yesmin, cikin ranta take furta Khalid d’ina bazai tab’a sonki ba bak’ar mayya....

***

“Magana fah nake maka Khalid amma kayi banza dani...? Ko nima karata zakai daga d’akin naka...Inyi...?” Ammi ta k’arashe tana watsa masa kallo...

Fuzar da iska ya d’anyi kana yace “Ammi nifa bani da choice ita Yesmin d’in ba tana nan ba, ta zab’i duk kayan da take so zanyi transferring kud’in to account d’in Siyama idan yaso sai suje da Yesmin d’in ta zab’i kayayyakin da duk take so to her own choice...”

Ammi ta kad’a kai kana tace “Kenan bazaka d’auketa kuje tare ba, ai kai ya kamata ka tayata sayayya ka tayata zab’a tinda kaine mijin nata kuma kwalliyar ai ma kai za’ai bama Siyama ba...”

Shafa sumar kansa ya d’anyi ga wani irin nauyi da kan nasa ya masa sakamakon kwana da yini da yai yana aikin abu guda tunanin Nabilah....
A hankali ya furta “Ammi Ammi please ki k’yaleni haka nan, don’t push me to do something that later I’ll regret....”

Baki sake take dubansa kana tace “Inye... Eh lallai Khalid ni kake kallon tsaban ido kake cewa na daina pushing d’inka... Toh yayi, naji bazan bazaka je sayayyan lefe ba amma ka sani dole ka shirya ka maidata Abuja....”

A zabure ya d’ago kai yana dubanta... Jinjina masa kai tai alamun jadaddawa kana tace “Sarai kaji abinda nace, idan Yesmin ta tashi tafiya gida kai zaka kaita, iyanin ka gaishe da iyayen nata had’ida godiyar baka d’iya da sukai tinda kai bakasan abinda ya kamata ba....” Tana ida fad’in haka bata jira cewarsa ba ta fice...

Kame kansa yai had’ida zama cikin kujera gijif yana mai furta “God! This is getting too stressful.... what have I gotten myself into, anya banyi gangancin amincewa da auren Yesmin ba....?” Ya lumshe idanunsa a hankali yana mai ambaton Allah....

***

Kano

A tare Mamani da Sameer suka shigo d’akin, Hafiz na ganinsu ya saki murmushi... Harda d’an gyara zamansa yana masu sannu da zuwa... Sameer ne ya amsa gaisuwar nasa yana mai k’arasawa jikin drawer had’ida aje manyan ledojin dake hannunsa, lokaci guda ya isa jikin gadon yana ma Hafiz d’in sannu da jiki... Hafiz ya amsa da sakin fuska yana mai masa godiya da fad’in maiyasa zai d’aura ma kansa wahala haka yayo sayayya...
Sameer na murmushi yace “Kai haba babu komai, ya jikin naka dai... Dr din bai shigo bane...?”

Hafiz yace “Da sauk’i sosai, ya shigo round d’azu yace X-ray d’in sai an sakeyi...”

Sameer ya jinjina kai yana mai furta “Karfa ka damu babu wani abu kaji koh...”

Mamani ta katsesu da fad’in “Wato ka sami d’an uwanka ka mance da cewa nima gaisheka nazo ko...? Toh idan ban fasa jinyar nayi tafiyata ba, d’an uwan naka ya tsaya yayi jinyarka.....” Ta k’arashe tana k’arasowa d’ingis d’ingis Sameer na taimakata lokaci guda murmushi saman fuskarsa....
Hafiz d’inma murmushi yake kana yace “Haba ‘yar tsohuwata kinsan nayi kewarki da yawa...”

Mamani ta k’araso tana masa sannu da jiki kana ta yab’e baki tace “Lallai wannan mata taka ta cika hatsabibiya Hafizu, koda shike hakkine hakkin Zulfa’u ne ke bibiyarku daga kai har uwar taka, ince itama yanzu nikeji an sallameta a asibiti sabida Sawwama da hatsabibanta sun kusan rabata da rayuwarta...”
Hafiz ya d’an mik’e da sauri yana duban Mamani kana yace “Hajiya suka daka....?”

Mamani tace “Bakaji da kyau ba kenan...?”
Daidai sanda wayar Sameer ya d’auki ruri ya d’an fice daga d’akin...

Hafiz ya shak’i iska da k’yar had’ida fuzarwa lokaci guda ya lumshe idanunsa, ya waresu yana duban Mamani tamkar wani maraya kana yace “Gaskiyarki ne Mamani hakkin Zulfa’u ne.... Shi yake bibiyarmu....”

Mamani ta jinjina kai tace “Naji dad’i daka fahimci haka..... Na bud’e maka lemun ne....?” Tai maganar tana k’ok’arin d’auko lemon kwali da suka shigo dashi....

Bata iya bud’ewar ba sai mik’a masa da tai tana fad’in “Abubuwanku na zamani ungo nan ni ban iya bud’ewa....”

Hafiz ya amsa yana murmushin kasancewar tsohuwar taredashi lokaci guda Mamani ta gyara masa pillow dake kishingid’e bisa, Hafiz ya d’an kurb’i drink d’in kana ya sace duban Mamani dake faman zuba yace “Mamani nace ina Zulfa’un take...? Batasan banida lafiya bane batazo ba...?”

Shek’ek’e Mamani ke dubansa kana tace “Tazo tai maka wata uwar....? Ince ka sallameta a rayuwarka gaba d’aya....?”

Kusan k’warewa yayi da drink d’in kana yace “Mamani sallamarta fah kikace....?”

“Aw na maimaita maka ne....?”

Fuzar da iska ya d’anyi kana yace “Mamani nifa ina son matata kuma ai sakin da na mata ba cikin hayyacina nai ba.... Kuma ma ai duk laifin Hajiya ne....” Yai saurin kamo hannayen Mamani yana mai rau rau da idanu yake fad’in “Mamanitah please don Allah ki taimaka min kisa baki matata ta dawo, idan Zulfa’u bata dawo rayuwata ba mutuwa zanyi Mamani kinga likita yace zuciyata dab take da kamuwa da cuta.... Don Allah Mamani kisa baki Zulfa’u ta dawo gareni....”

Shek’ek’e take dubansa kana tace “K’wak’walwarka ta sami matsala koh....? Toh ka jini da kyau koda ace Zulfa’u ta zab’i komawa gidanka bazan bari ba.... Bazan kuma zama na zuba idanu kaida Haule ku kuma kassara mata rayuwa ba, kaidai Allah baka lafiya kurum ka nemi wata ka aura...”

Fuska babu walwala yace “Ni matata nake so, ita kad’ai.... Kawai idan kin daina sona ne bazaki taimaka min ba sai ki fad’a min.....”

Mamani ta tab’e baki tace “Eh lallai ka kuwa d’auko Dala ba gamo..... Toh bazan taimaka ba Ubana, wani yace kai wasa da damarka sanda ka sameta, saima kaji ana sanarwar aurenta ka kuma yin danasani....” Ta k’arashe tana gyara mayafinta... Banda mugun kallo babu abinda Hafiz ke aika mata, shigowar Sameer da Dr ya katsesu....

***

Zaune yake a parlorn ganin bak’in nasa, shi kad’ai sai faman sak’e sak’e yake..... He couldn’t get over it, duk yanda yayi ya yakice tunanin cikin zuciyarsa abin yaci tura... Kaman wanda aka sinkaya ya janyo wayar salulansa dake bisa centre table.... Layin Akram ya kira ya sanar dashi yana son ganinsa... Akram ya amsa cikeda risinawa sannan ya sanar dashi yana zuwa right away...

Jim kad’an Akram ya k’araso, Muhibbah dake tsaye saman balcony d’inta idanunta k’yam sashen ganin bak’in na mijinta domin kaw gaba d’aya a ‘yan kwanakin ta fahimci yana acting very strange, ta k’udiri niyyan gano abindake damun mijin nata, kuma tasan through Akram kawai zata iya sanin komai.... Cikin sauri ta sauk’o k’asa ta nufi section d’in ganin Akram ya shige....

Cikeda risinawa Akram ya gaida maigidan nasa, Engr ya masa nuni da kujera kana yace “Bismillah shigo ka zauna....”

Akram ya k’araso ya zauna yana mai tunanin ko tafiya ce ta taso masu...

Engr yace “Akram wani aiki nake so kamin a matsayinka na wanda na yarda dakai....”

Akram ya d’an dubesa jin maganar nasa sounds serious dukda cewa shi d’in ba mai magana maras amfani bane amma yau d’in yaji wani irin jadaddawa cikin muryar Uban gidan nasa....

Engr yaci gaba da fad’in “Inaso kamin wani bincike....”

Akram ya jinjina kai a hankali yana mai amsawa da alright...

Engr Ma’aruf yaci gaba da fad’in “Akan matar nan that work with the radio station....”

Gaban Akram yayi wani irin yankewa ya fad’i, zuciyarsa ta shiga harbawa da sauri da sauri, sinkayo muryar uban gidan nasa yai sanda yaci gaba da fad’in “I mean everything about her, her family background and all....Nasan ka tab’a fad’a min batada aure a yanzu, I need to know more... I mean more about her, ka fahimta...”

Akram ya jinjina kai a hankali kana yace cikin sark’ewar murya “Oh...Ok your excellency.... Right away.... Zan binciko maka komai in two days time in sha Allah....”

Engr ya jinjina kansa kana yace “Shikenan kana iya tafiya....”

Kasa mik’ewa Akram yayi da fari domin kaw duru duru ya soma gani, da k’yar ya iya mik’ewa...
Engr ya dubesa da kyau kana yace “Are you alright...?”

Akram ya jinjina kai cikin sauri kana yace “La....Lau nake your Excellency.... Zan tafi yanzu...”

Engr ya jinjina kai kana yace “Good...” Kana yace “Ka kira Kabir ka fad’a masa I need him to reschedule all my activities na gobe.....”

Akram ya jinjina kai yana mai furta “Ok... Ok Sir...” Lokaci guda ya fice gabansa bai daina tsinkewa ba...

Yana fitowa Muhibbah tai saurin bin bayansa....

SameenaAleeyou 📚

*INDA RAI*
_................DA RABO_

*68*
Chapter 84 · 0% Book details