← Book details Inda Rai Da Rabo Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 89 OF 198

Sashe 89

Inda Rai Da Rabo Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

D’an jim Sameer yai yana mai karantar mahaifin nasa kana ya d’an muskuta yace “Abbah ka tabbata babu komai... Abbah naga yanayinda Baba Alhaji ya fice... And I heard him shouting at you....”

Abbah ya d’an murmusa cikeda jin dad’in yau gashi da d’ansa wanda damuwarsa ya damesa....
Gyara zamansa ya d’anyi had’ida gyaran murya kana yace “Ma’aruf, banaso ka d’aga hankalinka... Wannan tsakaninane da d’an uwana kaji koh... So tari hakan takan faru tsakanin ‘yan uwa daga k’arshe zasu kasance a turba guda sabida su ‘yan uwan junane... Kaji koh....”

Ba don ya gamsu ba ya d’an jinjina kai yace “Amma Abbah I worried so much about your health... Shiga damuwa ko tashin hankali ba naka bane sam, shiyasa nake so naji idan zan iya taimakawa....”

Abbah yai shiru tamkar mai nazari na wasu ‘yan dak’ik’ai kana ya ambato sunan Sameer...

“Ma’aruf...!”

“Na’am Abbah...” Sameer ya amsa had’ida d’agowa ya dubi mahaifin nasa...
Abbah yaci gaba da fad’in “Wato Ma’aruf Baffanka ya bijiromin da wani al’amari ne mai wuyan sha’ani....”
Sameer ya jinjina kai a hankali cikeda son jin abinda Abban nasa ke sanar dashi... Yayinda Abbah yaci gaba da fad’in “Ya bijiro min da batun yanaso ya baka d’aya cikin yaransa ka aura...”

Jin maganar yai tamkar sauk’an aradu, yai saurin d’agowa yana duban mahaifinsa had’ida had’iyar miyau d’in da ya daskare masa lokaci guda a mak’oshi.... Shi kuma aure... Aure yanzu... Aure dai.... Waima su waye ma yaran Baba Alhajin... Shi yama mance bazai iya cewa gasu nan ba, toh Wai ma yaushe ya gama da rigimar Siyama balle har yajega wani k’arin aure... Hasalima shi baida tsarin aje mace sama da guda a gidanshi, yasan Siyama tanada wuyar sha’ani amma yayi imani soyayyar da sukedashi ma junansu is very strong wanda baya haufi duk yanda sukakaiga samun sab’ani daga k’arshe zasu kasance tare sabida wannan k’auna mai tsanani dake tsakaninsu.... Muryar Abbah ya dawo dashi daga duniyar tunaninda ya tafi...

“Kar ka damu Ma’aruf, alwashi na d’auka bazan kuma tilastawa d’aya daga cikin ‘ya’yana auren wad’anda basa so ba bayan abinda ya faruga ‘yar uwarka Zulfa’u.... Na riga na sanar dashi bazan iya tilasta maka ba shine dalilin da yasa kaji yanata fad’a har yake ikirarin cewa zumuncinmu na gabda tsinkewa muddin nak’i amince masa kan maganar had’a yaranmu....”

Zufa ya shiga tsartsafowa Sameer, wannan shine tashin hankali wanda ba’a saka masa rana, tabbas ko kad’an bazaiso ya zamto sanadiyar yankewar zumuncin iyayensu ba....Toh amma shin Wai ya zai ne...? Bai kaiga lalumo amsa ba wayarsa ta d’auki ruri daga asibiti ake kiransa ana nemansa urgently... Bai samu zarafin k’arasa maganar da sukeda Abbah ba ya fice babu shiri, Abban ya masa fatan sauk’a lafiya.... Har ya isa asibiti har ya shige surgery d’in da aka kirawosa akai maganganun Abbah basu daina masa Yawo a kwanyarsa da kuma dodon kunnuwarsa ba....

***

Kasancewar basuda aji k’arfe goma shabiyu har sai k’arfe biyun rana yasa suka nufi masallaci kafin ai sallah suyi su kuma nemi abinda zasuci before su koma class...
Suna tafe suna labarin ajin da suka fito dashike gaba d’aya suke tafiyar hardasu Safwan da Al’amin coursemates d’insu.... Nan suka ratse wani cafe don sayan handouts na ajin da zasu shige later sabida malamin ba mutunci bane dashi yanzu sai ya kori mutum muddin bakada material d’insa...
Su Safwan suna gefe suna aikin musu kan wani equation data kasa balancing masu yayinda Nabilah da Yusrah suka shige shagon....
Nabilah cewa tai “Wllhi jiri nikeji bazan iya tsayuwan shop d’in nan ba don nasan basu dashi a k’asa zasuce sai sunyi photocopy, kya karb’a ki taho mana dashi... Ki sameni a masallacin...”

Yusrah ta jinjina kai tana mai furta “Love fever ke damunki yarinya amma kink’i yarda....”
Harara ta watsa mata kana tace “Kyaji dashi, wannan ke ta shafa...” Bata jira cewar Yusrah ba ta fice ta k’yaleta shagon yanda taketa faman kyakyata dariya... A waje ta taddasu Safwan suka tambayeta Yusrah fah, tace dasu zata sameta masallaci.. Nan suma suka had’a hanya donsu Hostel suka nufa tinda ba aji har sai k’arfe biyu...

Tin daga can ya hangeta tana tafe tareda wasu samaruka har biyu, sanye take cikin d’inkin atampa riga doguwa had’ida madaidaicin hijab d’inta da ya tsaya a daidai gwiwarta mai kalan ruwan k’asa.... Wani sanyi ne yaji ya ziyarci zuciyarsa bayan da ya shige babban ajin da suka saba gudanar da lectures ciki baiga kowa ba sai gashi ya taddata a hanya bata bar haraban wajen gaba d’aya ba, yasan tabbas ba k’aramin sa’a ya taka ba, saidai hangota da wad’annan samari da yayi ba k’aramin sosa masa rai yayi ba musamman da yaga yanda fuskokinsu ke cikeda annuri alamun sunajin dadin firan da suke....
Wayarsa ya d’aga ya shiga dialing layinta....

SameenaAleeyou📚

*INDA RAI*
_...............DA RABO_

*70*

K’aran horn kawai sukaji a bayansu, dab dasu kaman mai motar na shirin bin kansu.... Ko gizau batai ba saima ci gaba da tafiya da tayi, su Safwan kaw Cikin sauri suka waiga baya suna mamakin wannan mai motar da duk fad’in hanyar dake makarntar ya zab’i yabi bayansu....
Al’amin yaja muguwar tsaki, a fusace ya kauce yana mai duban motar yake fad’in “Dalla Malam lafiya...? Ko ta kanmu zakabine...?” Yai maganar yana duban motar don ba ganin mai motar yake ba dashike glass d’in motar mai duhu ne....
Nabilah da ta gama cika tazo wuya cewa tai, “Ku k’yalesa yabi takanmu kawai ya wuce....”
Safwan ya murmusa kana yace “za’a ba za’ai haka ba, mu matsa mu basa wajen ya shige...”

Nabilah tace “Aiko wllhi bazan matsa ba saidai yabi takaina tinda dai hanyar bata gidansu bane...” Kaman wanda akace ya k’ara danna horn d’in... Zuciyarta sai faman tafarfasa yake, ita kad’ai sai hura hanci take tana huci tana tunanin kalan rashin mutuncin da zataiwa mai motar nan muddin ta juyo....

Cikeda tsiwa da masifa ta waigo tana mai furta “Mai zai hana kabi takaina ka wuce idan dai har nan ne kawai hanya a fad’in makarantar....”

Cak tai burki ma kalaman nata sakamakon bud’e marfin motar da yai ya sako k’afafunsa ya fito, yana sanye da lallausar yadi mai ruwan toka d’inkin half jampa ta masa kyau sosai, kansa babu hula sai b’akin sumarsa da yaiwa kan nasa k’awanya....
Tai k’ok’arin d’auke kanta daga barin duban nasa kana ta d’an dubi Al’amin tace “Kuje kawai Al’amin sai mun had’u anjima a class...”
Safwan yace “Are you sure...?”
Jinjina masa kai tai ba tareda tace komai ba....
Ganin abokan tafiyar nata sunsa kai yasa Khalid soma takowa hannayensa mak’ale cikin aljihun wandonsa....
Fuska a tamke take duban wani gefen sanda ya k’araso....
Kallo ya bita dashi kafin ya d’anyi gyaran murya had’ida maida hannayensa duka biyu baya ya d’an rank’wafo yace “Kin kyautama kanki da kika sallami samarukan naki....”

Maganan da yayi ya sanyata d’ago idanu tanai masa mugun kallo, ganin shid’inma ita yake duba babu ko k’yafta idanu ya sanyata kuma kauda kai gefe kana tace “What brought you here...?”

“Isn’t it obvious... Bazan jure rashinki ba teddy bear.... Tell me who are those guys...?” Ya k’arashe yana bin bayansu Safwan da kallo....

Girgiza kai tai a hankali kana tace “Wannan ba matsalarka bace.....”

Khalid ya tsareta da idanu kana yace “Kar na sake ganinki taredasu.....”

Galala ta d’an dubesa had’ida yin ‘yar bazaurar murmushi kana tace “Did you hear yourself now....? And since when ka fara gindaya min doka...?” Tai maganar tana hura hanci hannunta guda rik’eda kunkumi...

Khalid ya saki murmushi don abinda yakeso kenan yaga wannan tsiwar tata da yai kewa kwana biyu... A hankali ya soma takowa dab kusanta, Nabilah taci gaba da huci tana aika masa mugun kallo dukda tsananin bugu da k’irjinta keyi...Saitin kunneta yake rad’a mata “You know teddy dear... I’ve missed this... So much... Amma nafi kewarki, nasan kema kinyi kewata... Lets end this now don nasan we both can’t do without each other.... I know you love me teddy bear koda ace baki fad’a ba but I know you does... So much cos I see it into your eyes....” Ya k’arashe cikin tsananin kashe murya tamkar mai rad’a...
K’irjin Nabilah yaci gaba da bugu da sauri da sauri... Cikeda huci ta d’ago kanta da hannunta tana mai furta “Kaga Khalid listen....” Aya tai ma kalaman nata sakamon k’aran da ya saki had’ida rik’e hancinsa alamun ta bige masa hanci.... Ta waigo a zabure tana dubansa cikeda kulawa yanda ya dafe hancinsa yana furta “Auuchh what’s with you...”
Cikeda kulawa take furta “Sorry sorry yi hak’uri please... Does it hurt...?”

Ganin yanda duk ta daburce yasa Khalid jin wani sanyi cikin zuciyarsa a hankali ya saki hancin nasa da har ya d’an canza launi zuwa ja.... K’uri ya mata da kyawawan idanunsa ba tareda ya iya d’aukesu ba, sosai yanayin storo yake mata kyau dashike bata cika shiga yanayin ba, idanunta sosai suke masa kyau ita ta shiga yanayin... Ganin ya mata k’uri ya sanyata k’ok’arin saita kanta kana tace cikin k’asa k’asa da murya “I guess you’re alright... Please ka tafi, class zan koma anjima kad’an...”

Khalid ya murmusa da gefen bakinsa a hankali kana yace “Are you sure you want me to leave....”

Ta juyo a hankali tana dubansa kana ta jinjina kai tace “Yes ka koma wajen matarka da zaka aura.....”
Chapter 89 · 0% Book details