← Book details Inda Rai Da Rabo Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 71 OF 198

Sashe 71

Inda Rai Da Rabo Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Batakai aya ba suka jiyo sallamar bak’uwar murya, ba kowa bace illa Salma nurse daga asibitin da aka sallami Raihanah....

Mamani ta washe baki tana fad’in “A’a lale lale... Ma’aikaciyar jinyace a gidan namu....”

Salma na murmushi ta ida k’arasowa ciki tana mai gaida Mamani...
Mamani tace “Yanzu kuwa nake jajen waye zai wanke ciwon jikata tinda mun komo gida saiga Allah ya kawoki....”
Salma ta kuma murmusawa tace “Ai Mamani tuni Dr Sameer ya d’aukeni hayar yin hakan....”

Raiha dake zullumin wankin ciwo sabida zafi tayi saurin d’ago kai tana duban Salma...
Salma taci gaba da fad’in “Mamani Dr ko bai biyani ba zanyi duk abinda ya sakani sabida tsananin kirkinsa da ganin ya taimaki duk wanda ke cikin matsala... Balle ace har ya zab’eni na kula da k’anwarsa ai ni abin alfaharine a gareni...” Tanayi tana sassane kai alamun kunya...

Mamani tace “Allah sarki Ma’aruf jikana, ta ko ina yabonsa ake... Allah dai yaci gaba da karemin shi....”

Salma ta amsa da “Ameen Mamani....” Kana takai dubantaga Raiha tace “Raihanah ya jikin... Nazo mu fara koh...”

Murmushi mai kamada yak’e Raihanah ta mata kana tace “Da sauk’i sosai....”
Salma ta murmusa kana ta kwab’e mayafinta ta shiga had’e kayan dressing...

***

Shi kad’ai yake huci yana tururi bayan yaji labarin da Hajiya ta zayyane masa gameda mutuwar d’iyarsa Kausar cewa Zulfa’u da k’anwarta Nabilah su sukazo suka tari fad’a da tashin hankali garin fad’a suka jefa masa d’iya a tukunya... Kada ya zargi kowa da laifin kisan d’iyarsa face Zulfah da danginta....

Ko sallama bai sami zarafin yi ba ya fad’a sashen Mamy yana mai dokawa Zulfa’u kira cikin tsananin karaji da b’acin rai...
Babu shiri Nabilah ta fito jin muryar Ya Hafiz kaman zai d’age gidan....

“Ya Hafiz lafiya kake kiran Addah Zulfah haka....?” Nabila tace tana mai dubansa cikeda mamaki ganin yanda k’wayan idanunsa suka kad’a sukayi jazir....

SameenaAleeyou📚

*INDA RAI*
_................DA RABO_

58

*©️Sameena Aleeyou...✍🏽*

Ko zarafin amsa Nabilah bai samu ba yaci gaba da dokawa Zulfa’u kira cikin tsananin karaji...
“Ki fito nan ki fuskanceni Zulfa’u...!!”

A tare Aunty Lami da Zulfah suka k’araso haraban sashen, ganin yanayin Hafiz ya mugun d’agawa Zulfah hankali... Aiko kaman wanda yake jira yayo kanta gadan gadan Aunty Lami tai saurin shiga tsakani....
Fad’i take “Hafiz lafiyarka.... Wai meke faruwa ne l....?”

Yana nuna Zulfah da d’an yatsa cikin tsananin huci yake furta “Bazan tab’a yafe miki ba Zulfa’u, bazan tab’a yafe miki ba... Kin cuceni kin rabani da gudan jinina Kausar.... Why...? Meyasa Zulfah... Sabida na sakeki, sabida baki k’aunata shine bari ki d’au fansa akan d’iyata... Kin cuceni... Ban tab’a danasanin had’a iri dake irinta yau ba.... Kuma wllhi kinj na rantse sai na d’au fansar mutuwar Kausar...!!”

Zulfah dake tsaye hawaye na gangaro mata cikeda tsananin mamaki take fad’in “Ya Hafiz mai kake nufi... Shin kana tunanin zan iya kashe rai balle gudan jinina... Ya Hafiz Kausar rayuwatace, ta yaya zakai irin wannan tunanin....?”

“Shut up...! Rufewa mutane baki munafukar banza....!!” Ya k’arashe yana mai zabura zai finciko Zulfah dake b’oyewa bayan Aunty Lami... A daidai lokacin da Sameer ya shigo... A d’ari yayi jifa da jakar hannunsa ya finciko Hafiz ya watsa shi gefe guda....

Hafiz da baisan ko wanene Sameer ba ya d’ago yana mai ci gaba da huci yayi kan Sameer ya dunk’ule hannu yana k’ok’arin kaiwa Sameer naushi Sameer ya rik’e hannun da k’arfin gaske shima hucin yake su duka biyu suna aikama juna muguwar kallo Hafiz yake furta “And who do you think you’re..? Kai waye da zaka shiga tsakanin miji da mata... Auho d’aya daga cikin ‘yan iskan samarukan nata masu bin matan mutane ne koh... Toh baka isa ba bari kaji na fad’i maka....” Ya k’arashe yana kokawan k’wace hannunsa daga rik’on da Sameer ya masa amma ya kasa ko guzau...

Sameer bai daina huci ba yana kallon cikin k’wayan idanun Hafiz yake fad’in “The moment you intend to hurt my sister again sannan ne zaka san the real meaning of the word pain... I’lol forget we are cousins....!!!!” Ya k’arashe yana mai jifa da hannun Hafiz d’in wanda saida ya kusan fad’uwa k’asa

Gaba d’aya duban Sameer d’in suke da tsananin mamaki don basu tab’a ganinsa cikin irin wannan yanayi ba, babu ya Aunty Lami wacce tuni taji ‘yan hanjinta suna juyawa, yanda taga kalan zuciyar Sameer tabbas duk randa yasan sune sukai sanadiyar rabuwarsa da iyayensa kashinsu ya bushe don sosai ta razana da ganin fushinsa....
Nabilah kaw tamkar ta zuba ruwa a k’asa tasha haka taji... Kame hannaye kurum tai tana kallon yanda yau Yayansu ke karb’awa ‘yar uwarta ‘yanci irin yanda babu wanda ya tab’a tsaya mata...

Hafiz da yanzu ya fahimci ko wanene Sameer mik’ewa yayi yana sakin murmushi mai kamada warning, kana yace “Aw ashe ka dawo kenan... Ka gama yawon barikin naka ka dawo... Sai yanzu ne zaka karb’a mata ‘yanci... Ka makara ai....”
Bai kai aya ba Sameer dake tsananin huci ya tako gabansa a hankali kana yace “Do not try me....!”

Hafiz ya kuma murmusawa kana yace “Your Sister is a monster Ma’aruf... She’s nothing but a curse...!” Wata wawiyar naushi da Sameer ya aikawa Hafiz a baki da hanci ya hanasa ci gaba da magana...
Hankali tashe Zulfah ta shiga janye Yayanta tana kuka sosai take fad’in yayi hak’uri... Aunty Lami ta fice a guje kiransu Mamy a can sashen Abbah don tuni Hafiz ya fad’i k’asa jini na fitowa daga bakinsa da hancinsa...

Mik’ewa yayi a zabure yana fad’in “Your Sister is a killer... She killed my daughter... Ta kashe min d’iyata ta kashe Kausar...!!!”

Sameer na huci Zulfah na kuma janyesa yake fad’in “You take back what you said you imbecile....!”

Daidai lokacin su Najah da Marliya da shigowarsu kenan daga Islamiya ....
Najah da tuni ta soma hawaye ta k’arasa a guje ta rik’e Yayanta Hafiz... Lokaci guda take fad’in “Yaya Hafiz Zulfah batada laifi... Ka daina cewa ita ta kashe Kausar.. Kausar lokacin mutuwarta ne yayi....”

“Shut up Naja’atu you don’t know anything... That monster killed my daughter... Hajiya ta fad’a min komai how my daughter die because of her selfishness...” Ya k’arashe yana nuni da Zulfah dake tsananin kuka....

Cikin kuka Najah ke fad’in “Addah Zulfah batada laifi, idan ma masu laifin kake son sani ba kowa bane illa Matarka Sawwama da k’anwarka Sahariyya, those two are the cause... Su suka jefa Kausar da Raihanah cikin ruwan zafi... Su zaka tuhuma not Addah Zulfah...” Ta k’arashe cikin tsananin d’aga murya...
Jikin Hafiz yayi sanyi sosai, hawaye suka ci gaba da zuba masa.... Ya d’ago idanu yana duban Najah wacce itama hawayen take .... Naja’atu ta jinjina kai a hankali kana ta sassauta murya tace “Yaya Addah Zulfah mahaifiyar Kausar ce bazata tab’a kasheta ba... Tana k’aunarta fiye dakai... Rabatada d’iyarta da akai lokacin da take raye ba’a barsu sun kasance tare ba ya isa jefata cikin damuwa.... This is not you Ya Hafiz, na tabbata deep inside kanada zuciya mai kayu....”

Ba Hafiz dake tsaye yana zuban hawaye ba harta Sameer saida yaji gaba d’aya gabb’ansa sun masa sanyi, suna gani Naja’atu ta janyo d’an uwanta suka fice tamkar rak’umi da akala...
Sameer ya dube ‘yan uwan nasa da gaba d’aya sukai tsaye suna dubansa in a strange way.... Dafa Zulfah da har lokacin zuban hawaye take yayi, a hankali ya furta “Everything will be alright kinji koh... I’m here now, bazan kuma barin wani yaci zarafin d’aya daga cikinku ba... Never...”
Zulfah ta rintse idanunta a hankali yayinda Marliya ta k’araso ta janye hannunta suka shige d’aki..
Nabilah ta saki murmushi tana mai kallon Sameer har ya b’ace ma ganinta kana tabi bayansu Zulfah da Marliya...

Aunty Lami data ruga a guje kiransu Mamy ashe ba Mamy ta tafi kira ba lab’ewa tai tana kallon yanda ta kaya tsakanin Sameer da Hafiz... Ta shafe zufan da ya keto mata had’ida sauk’e nannauyan ajiyan zuciya.... Tana ganin sanda Sameer ya nufi sashen Mamani kana ta sad’ad’o ta wuce d’aki ta lalumi waya tana neman layin Hajiya Haule....

***
Chapter 71 · 0% Book details