← Book details Inda Rai Da Rabo Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 105 OF 198

Sashe 105

Inda Rai Da Rabo Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Bayan ya gama shirinsa a nan yanda aka sauk’esa guest room kasa fitowa yai parlorn domin cin abincin, tsaye yai a window yana mai nazarin rayuwa, sallaman Mahaifinsa ya dawo dashi daga duniyar tunanin da ya tafi....
“Khalid, kai muke jira, fito muci abinci...”
Cikin taku a hankali ya k’araso had’ida zama saman gado...”Daddy you go ahead and eat ni inaga ba yanzu ba....”
Bai amsa shi ba saima zama da yai gefensa, shiru ya ratsa tsakani kaman babu mai cewa komai...
Gyaran murya mahaifin nasa yai kafin ya soma fad’in “Akwai abinda kake buk’atan sake sani ne...?”
Fuzar da iska ya d’anyi had’ida kauda kai gefe yana mai murza tafukan hannayensa tamkar mai murza mai kana yace “No Daddy, I’m in no position to question any of your decisions.... Kuma kan abinda ya faru d’azu a parlor kai hak’uri....”
Dafasa kad’an Daddy yai zuciyarsa na masa sanyi, tin tasowar Khalid yake ganin Khalid yaro maras jin magana har yake fifita Siyama sama dashi, ya kasance yafi yarda da Siyama sama dashi, ashe dai k’iriniyace kawai irinta yarinta amma a zahirin gaskiya d’an nasa mutumin kirki ne wanda kuma yasan yakamata dikda k’arancin shekarunsa.... Hannun Khalid guda Daddy ya kamo kana yace “Do you want us to go out... Any place you’ve in mind....”
Wannan murmushi mai bayyana hak’wara Khalid yai kana yace “A’a Daddy babu yanda zamuje, muna nan a nan tareda family d’inmu... I want to meet my sisters....” Ya k’arashe murmushi kwance saman fuskarsa....
Daddy yaji dad’i harda d’an bubbuga kafad’ar Khalid kana yace “K’annen ka sun dawo daga islamiya, nayi mamaki da bakaji k’iriniyarsu ba, koda yake you really are preoccupied shiyasa bazakaji hayanaiyarsu ba...”
Ya d’an murmusa kad’an shima ba tareda yace komai ba...
A tare suka nufo parlorn shida mahaifinsa... Yaran gaba d’aya suna saman dining table don already lokacin dinner ne... Mahaifiyarsu sai fama dasu take da gani yaran akwai k’iriniya babu laifi.... Hango wani mutumi da sukai tareda mahaifinsu ya sanyasu zuba masa ido ga kuma kamanni da yakeyi da Daddynsu... Ijlaal tace “Mummy who’s he...?”
Mahaifiyar tasu ta d’an rank’wafo kad’an saitin fuskan yaran, cikin murya k’asa k’asa take furta “Girls go and say hello to your brother...”
Gaba d’aya kallon mamaki suka bita dashi kafin Humy ta ije fork d’in hannunta kafin tai magana mahaifiyar tasu ta kuma masu alamu da idanu kan suje su gaida Khalid...
A tare suka fito daga cikin kujeran suka nufo Khalid da ya kasa janye idanunsa daga barin dubansu... Saida suka k’araso gabansa Humy ta d’an ja baya kad’an tace “Wait how comes bamu sanka ba...? Da gaske kai Yayanmu ne... And ina kake all these while... Mummy ce mamarka kaima...?” Khalid yai tsaye yana duban yarinyar da jinjina wayonta... Daddy ne ya d’anyi gyaran murya ganin Khalid yai tsaye sakare kana yace “Kids ku k’yale Yayanku ya huta yai tafiya ya gaji... Muje koh....” Ya k’arashe yana mai kamo hannayensu, Ijaal ta saki hannun Daddy ‘yar k’aramar ta k’arasa da gudu ta rungume Khalid tana mai furta “Welcome Yaya... Kar ka sake tafiya ka barmu kaji, dama a sch su Nazira suna cewa sunada brother... Nima nace masu yanzu inada brother..?” Tai maganar tana mai langab’e kai...
Samun kansa yai da sakin murmushi kana ya durk’usa ya rage tsawon sa gabanta, hannayenta ya kamo kana yace “Of course you can...” Annuri ya cika fuskokin illahirin mutanen parlorn... Khalid ya dafa fuskarta kad’an kana yace “And you are...?”
Humaira tai saurin cewa “She’s Ijlaal and I’m Humaira but you can call me Humy...” Khalid ya murmusa yana jin son yaran na shiga cikin ransa a hankali
Ijlaal tace “Zance masu my brother is handsome and he has muscles duk wanda ya bullying d’ina a sch zai rama min....” Wannan karon dariya suka d’anyi gaba d’aya kana Khalid yace “Of course I won’t allow them to bully such a beautiful princess like you....”
Ijaal na Washe hak’wara tace “Da gaske Yaya nafi Addah Humy kyau...?”
Juyawa yai ya kalli Humaira da mood d’inta ya d’an canza kana ya saki murmushi ya mik’a mata d’aya hannun yana mai furta “Come here...” Da sauri ta k’arasa Daddy dai table ya shige wajen matarsa suna kallon draman yaran nasu cikeda jin dad’i....
Khalid ya dafa kansu su duka biyu kana yace “I know you must’ve watched that cartoon... What’s its name again...?” Ya d’anyi shiru kaman mai tinani kana yace “Frozen..” Harda tsallensu sukace “Yes Elsa and Ana....”
Khalid ya jinajina kai murmushi bai bar saman fuskarsa ba kana yace “Good, just like Elsa and Ana you both are beautiful princesses...” Yaran suka rungumesa gaba d’aya suna fad’in “We love you brother..” Rungumarsu yai wani irin sanyi na ziyartar zuciyarsa.... A b’angaren Daddy ma dad’i ne ya mamaye zuciyarsa, hukuncin da ya yanke na zuwa da Khalid baiyi kuskure ba, kafin washe gari yaran sun sake sun saba sosai da Khalid gwanin nan sha’awa...

A d’aki Daddy yake labartawa Daula halinda ake ciki na maganan auren Khalid d’in da draman da ake da mahaifiyarsa... Tausayin Khalid ya cika zuciyarta, Khalid yanada zuciya mai kyau he deserves to be happy, zataso ya auri macen da yake so... Ta d’an muskuta kana tace “Toh yanzu shikenan kuma sai ka zuba ido a aura masa macen da bai so, haba Abu Humaira ta ya zakai ma d’anka haka...?”

Sauk’e ajiyan zuciya Daddy yai kana yace “For secondo ban tab’a goyon bayan Khalid ya auri Yesmin ba cikin zuciyata, nadai nunawa mahaifiyarsa hakan ne don mu rabu lafiya, kinsan banason hayaniya...”
Mood d’inta ya d’an canza, shin har yaushene mijinta zai daina tsoron matarsa ya soma gudanar da al’amransa tamkar maigida a gidansa... Ganin tayi shiru tamkar wacce tai nisa a tunani yasa Daddy rik’o hannunta kad’an kana yace “Nasan mai kike tunani, Daula wllhi duk yanda naso na takawa Farida birki bana iyawa... Inada zafi a waje wa mutane amma when it comes to Farida nafi k’ank’ara sanyi, duk decision d’in data yanke ji nake yayi... Kimin addu’a please....” Ya k’arashe kaman wani k’aramin yaro... Tausayin mijin nata ya cika zuciyarta, da ciwo Kaga babban mutum haka ya koma tamkar wani lusari.... Rungumo kansa cikin k’irjinta tai kana tace “Kar ka damu Abu Humaira, jarabawace Allah ya baka ikon ci, wataran komai zai zama labari da izinin Allah, bazan gushe ba ina mai maka addu’a da samun sauk’i cikin lamuranka....Amma ga shawari gameda auren Khalid...”
Wannan karon d’agowa Daddy yai yana dubanta sosai....

***

KANO

Ya Abida ta kuma duban k’anwar tata a karo na biyu kana ta girgiza kai tace “Wai shin har yanzu baki daina zuwa min da wannan zancen ba...? Sanin kanki ne abinda kike nema bazai tab’a yuwa ba... A sanadiyarta Iyayenmu suka mutu da bak’in cikina... A sanadiyarta na rasa d’ah na mafi soyuwa a gareni, a sanadiyarta na rasa mijina... A sanadiyarta na rasa duk wani farin ciki da na kasance cikinsa a baya.. Duba duba kiga girman gidan nan babu kowa cikinta, dagani sai tarin dukiya... Babu Magaji... Babu kowa sai halittun tsuntsaye... Tin daga ranan da na rasa Ma’aruf na saka ma raina nima na zama macecciya.... Nake zama cikin gidan nan bana fita ko ina bana sauraren tv ko radio bana rayuwa tareda kowa.... Jira nake nima tawa ta sameni... Na rasa komai, na rasa komai Bara’atu sai tarin dukiyar da Abbas ya mutu ya barmin wanda shima nayi imani da bak’in cikina ya mutu koda bai fad’a min ba... Wacece sila...? Duk wannan abubuwan da suka faru k’anwatace sila..!!!” Ta k’arashe cikin tsananin kuka..... Da sauri Aunty B ta rungumeta tana mai furta “Shiyasa nace miki lokaci yayi da zaki ci gaba da rayuwa kaman kowa Yaya, lokaci yayi da zaki mance komai, ki rungumi k’addara wala’alla Ma’aruf d’inki na raye kaman yanda Ma’aruf d’in Ya Mariya yake raye, kar ki mance bayan tulin shekarun nan Ya Mariya ta cire Rai daga samun Ma’aruf d’inta sai gashi ta sameshi, Yaya wala’alla naki Ma’aruf d’in ma yana raye... Daga shi har Fatima bamu sake jin d’uriyarsu ba bayan wad’annan shekarun.... Jikina yana bani basu mutu ba, zamu samesu zamu sake had’uwa dasu kaman yanda muka had’uda Ma’aruf k’arami... Lokaci yayi da zaki fita daga wannan rami da kika binne kanki ciki.... You’ve to live again dan Allah Yaya....” Ta k’arashe cikin tsananin raunin murya mai cikeda kuka....
Ya Abida ta kifa kanta tana tunin d’anta mutanen data rasa a rayuwarta a shekarun baya.....

Har Aunty B ta koma gida bata daina kuka ba, tashin hankalin da ita kanta batada cikakken wayo sanda abubuwan suka faru ya dawo mata Sabo, wani al’amari ne da k’addara ta riga fata aukuwa.... Su kuma kalan tasu k’addaran kenan... Shin shi musulmi ba’a sanshi da hak’uri da d’aukar k’addara bane a duk yanda tazo masa...? Shin maiyasa tasu k’addaran tazo a haka...? Shin maiyasa ‘yaruwarta bazata zama mai yafiya da d’aukan k’addara ba....? Ta lumshe idanunta a hankali hawaye suna masu gangaro mata... Wannan itace k’addararsu..... A haka Zulfa’u ta shigo ta taddata.... Zama tai gefenta zuciyarta nai mata rauni, da matuk’ar wuya kaga hawaye a fuskar Aunt din nata sai abu yakai mak’ura, hannu ta mik’a kana ta rik’o na Aunty B tace “Aunty meke damunki dan Allah... Ki sanar dani....”
Murmushin k’arfin hali Aunty B tai kana tace “Zulfa’u wata rana zuri’armu zata cika, mutanen da muka rasa a baya zasu dawo garemu... Shin Zulfa’u ana mutuwa a dawo...?”
Mamaki ya cika Zulfa jin irin maganganun da Aunty take marassa kan gado....
Dafe hannayen nata tai kana tace “Aunty bansan meke damunki ba, amma ki sani you can always count on me, sabida kema ko Yaushe kina tsaya mana dagani har ‘yan uwana cikin jin dad’i ko akasinsa, Aunty kema bazan barki ba a lokacin da kike buk’atan wani....”
Rungumeta Aunty B tai sosai Hawaye naci gaba da kwaranyo mata..... Cikin zuciyarta take addu’an Allah ya kawo masu wata rana da ahalinsu zasu zama k’ark’ashin inuwa guda kuma su yafi juna....

***
Chapter 105 · 0% Book details