← Book details Inda Rai Da Rabo Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 171 OF 198

Sashe 171

Inda Rai Da Rabo Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Aunty B Ta koma gefe ta zauna tana k’ek’ata dariya a hankali, harda hawaye... Daga yanda take zaune tana jiyo Ihun Ammi tana jan Allah ya isa ma ‘yar uwarta Hanne a bisa wannan turba data d’aurata bisa... Sad’af sad’af Aunty Bara’atu ta fice daga gidan ta kulle ta nufi kwalta ta d’auki cab ta tafi asibiti... Sai dariya take cikin mota idan ta tuna yanda Ammi ke rok’on gafara da neman tsira... Tai k’wafa a hankali kana tace “Daga yau kun shiga taitayinku munga su Haule ma...!!” Ta kuma tinstirewa da dariya....

****

Akram ya dubi Hafiz a karo na biyu kana yace “No Hafiz we are leaving this place together, bazan tafi ba tareda kai ba....!”

Hafiz ya kuma girgiza kai kana ya mik’awa Akram layar d’aya daga cikin yaron Babba guda d’aya wanda suke amfani da ita su b’ace Wanda suka sata da k’yar cikin aljihun yaran Babban kafin su fice operation.... Hafiz yace “Akram one of us must leave this place... Alive.... And it has to be you....Just go Akram...!!”

Akram ya kuma girgiza kai had’ida mik’awa Hafiz layar yace “Hafiz bazan tafi ba tareda kai ba.... Bazan tab’a tafiya na Barka ba....!!!” Ya k’arashe idanunsa na k’ok’arin kawo ruwa had’ida jifar da layar yana mai furta “You know.. I’m not leaving either..!

Girgiza kai Hafiz yake yana k’ok’arin maida k’wallan da suka ciko masa idanu kana yace “Akram will you please stop being so stubborn...! karfah ka manta tafiyarka na nufin ceton d’inbin Al’umma ne tinda mun riga munji plan d’insu... Kuma Sawwama da mahaifiyarta zasu linking d’inmu to hideout d’insu na cikin gari... Mai amfanin idan muka zauna dukan biyu muka bari azzaluman mutanen nan suka hallak’a mu.... Kuma hakan na nufin mun barsu suci gaba da fasadi a doron k’asa kenan....Akram you need to get out of this place right now..!!!” Hafiz ya k’arashe cikin murya mai kaushin gaske....

Akram da hawaye ke zubo masa a zuciye yace “Hafiiizzzz!!!!”
Hafiz ya jinjina masa kai yana share hawayen da ya gangaro masa kana ya k’araso da sauri suka rungume juna, lokaci guda kuka mai k’arfi ya k’wace masu....
Cikin muryar kuka Hafiz Ke furta “Im sorry Akram I got you into this.... Ka yafe min... Kuma dan Allah idan kaje kacewa Zulfa’u ta yafe min... Ka rok’a min gafara a wajen kowa kaji....!!!” Kuka yaci k’arfin Hafiz....

Akram na hawaye yake furta “I’ll come back for you Hafiz.... Zan dawo na fiddakai in sha Allah kaji....!!” Suka kuma rungume juna kaman kar su rabuda juna... Lokaci guda Hafiz Ke b’anb’are Akram d’in daga jikinsa yana fad’in “Just go... Go now Akram..!!!” Lokaci guda Hafiz ya dank’a layar hannun Akram kana ya juyar da fuskarsa yana hawaye sosai... Shima Akram d’in na hawaye ya juya a guje ya soma gudu....

SameenaAleeyou📚

*INDA RAI*
_...............DA RABO_

*104*

*©️Sameena Aleeyou...✍🏽*

Da tsananin mamaki Laila Ke duban Sultan kana tace “Sultan ba wannan ya kawoni ba, sanin kanka ne bama ‘yar wannan wasa nida kai.... So kake kace min da gaske aure Sameer d’in yai....?!”
Da gefen idanu Sultan ke dubanta yana bisa kujerarsa mai juyawa ta ganin majinyanta... Ya dad’a k’obarewa yana kuma juyi bisa kujerar kana yace “K’warai kuwa... Aure maiji da lafiya... Yarinya shakaf for your information... Kinga Laila zamanki a nan bazai yuwu ba... Siyama zata iya zuwa asibitin nan any moment tinda bamuyi ga yanda zamu had’u ba, na dai sanar da ita da zaran ta shigo garin ta kirani... So kawai Ki tafi you can’t be seen here...!” Ya k’arashe yana mai had’e tafukan hannayensa biyu waje guda ya saita fingers d’insa saitin bakinsa still yana kuma juyi akan kujerar tamkar wani basarake...
Da tsananin mamaki Laila Ke dubansa kana tace “And what about our plans...? Mai kake nufi Sultan...?!”

Da tsananin mamaki yake dubanta kana yace “Come on Laila don’t be stupid, ai babu wani pending business da ya rage tsakaninmu... With or without you Siyama bazata tab’a komawa Sameer ba, especially now da yai aure... So Kinga I don’t need you anymore....!” Ya k’arashe yana mai tab’e baki had’ida bud’e hannayensa alamun ko in kula...

Tsaye kurum Laila tai tana binsa da kallon mamaki, lokaci guda ta buga kan table d’insa kana tace “K’arya kake Sultan baka isa ba...!!! Kanaso kace dik video d’inku da Siyama da na d’auka a park da kuma cikin da Ta zuban bazai maka amfani bane...? Kai har ka isa kace zaka yadani...? How dare you Sultan....!!!”

D’an kuma tab’e baki yai kana yace “Bance fah bazai min amfani ba, yeah for sure zaimin amfani, it will make Sameer even more furious... But what I want to you to understand here is that... Sameer ya riga ya sami madadin Siyama, Ke babu abinda zai dake... Dama a haukarki bayan yasan tare kuke komai da Siyamar maybe ma kece kika zigata ta zubar masa da ciki and all those contraceptions da taita d’irka, Toh mai zai dake... Ke ni fah bari kiji na fad’a miki wllhi ko auren Siyama nai naga k’afarki a gidana ‘yansanda ne zasu rabani dake... So gwarama Ki sani tin yanzu da zaran na auri Siyama toh kun gama k’awance....!” Ya k’arashe with his full confidence yana mai kuma jaddada mata...

Laila da hawaye ke k’ok’arin ciko idanunta girgiza kai kurum take tana furta “You’re unbelievable Sultan... I can’t believe you’re doing this to me... How dare you used me...!!!” Ta k’arashe cikin daka tsawa hawaye na gangaro mata....
K’asaitaccen murmushi Sultan yai kana yace “You know Laila... Just get out of my office...!” Ya k’arashe yana mai nuna mata k’ofa daga yanda yake zaune...

Laila da tuni hawaye sun wanke mata idanu nunasa da d’an yatsa take lokaci guda take furta “Wllhi k’aryarka tasha k’arya Sultan... Idan har bazan sami Sameer ba Toh kaima bazaka sami Siyama ba... Wllhi sai na sanar da Siyama komai from the very start... Dik kalan abubuwan da muka k’ulla tare wajen ganin mun raba aurensu da Sameer... Wllhi kayi kad’an Kaga downfall d’ina Sultan... Just watch me..!!” Ta k’arashe tana mai kad’a yatsarta saman fuskarsa cikin tsananin huci... Lokaci guda tasa kai zata fice daga office Sultan yai saurin janyota baya, lokaci guda yake dubanta fuska a matuk’ar murtuk’e ya damk’eta sosai ya had’eta jikin gini... Lokaci guda yake furta “Is that a threat...??!” Ya kuma murmusawa a hankali kaman bashine ya murtuk’e fuska ba lokaci guda yake ci gaba da fad’in “Well sweetheart, If you think you know me...you are quite mistaken... You don’t want to have me as an enemy... So zaifi miki kyau idan kikai abinda nace... Just stay.. away from Siyama... Babu Ke babu ita... End your fake friendship with her... Idan kuma ba haka ba...!” Ya kuma murmusawa kana yace “Then I’ve no choice than to show you my true color...!!” Ya k’arashe yana mai jifa da ita gefe.... Laila ta mik’e da k’yar tana watsa masa mugun kallo... Lokaci guda ta finciki k’ofar ta fice tana mai furta “This is far from over Sultan....!”

“Fita munafuka... Get out, I don’t want to see your face ever again...!!” Ya k’arashe yana mai tura k’ofar da k’arfin gaske...

Siyama da tuni ta lab’e daga bayan wata k’ofar taugune tai a wajen tana danne kuka mai k’arfi da yazo bakinta.... Banda Innalillahi zuciyarta bata iya ambato komai.... Hannu guda Siyama ta d’aura akanta had’ida toshe bakinta da d’aya hannun dan kar kukan da take ya fito.. Kukan da bata tab’a irinsa ba tsawon rayuwarta... Shin haka duniya ta koma... Cin amana daga mutanen da ka aminta dasu... Laila babbar k’awarta ce haka nan Sultan babban abokin mijinta Sameer ne... Shin ta ya zasu masu wannan cin amana mai girma, ashe duk tsawon shekarun nan basuda burin da ya wuce suga sun rabasu itada Sameer... Dik mugayen shawarwari da Laila ke bata gameda Sameer d’in ashe dan ta rabasu ne ta mallakesa... Ashe Sultan cin dunduniyar Sameer yake ba abokin k’warai bane matarsa yake so.... Innalillahi wa inna’ilaihi raji’un... Shin Maiyasa cin amana ya wanzu tsakankanin al’aumma.... Shin Ta ya zakai haka wa mutanen da suka aminta dakai suka d’auki dukkanin yardarsu suka baka... Shin wannan wace irin zalunci ne mafi muni....!!! Kuka ya kuma zuwa wa Siyama.... Cikin sauri ta mik’e ta sid’ad’e ta fice daga Office d’in gudun kada Sultan ya ganta.....
Chapter 171 · 0% Book details