← Book details Inda Rai Da Rabo Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 123 OF 198

Sashe 123

Inda Rai Da Rabo Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Washegari kaw wajajen k’arfe goma na safiya suka fito cikin shiri, tuni suka tadda abinci kala kala tamkar wanda sukai order da sunan breakfast... Su Baba Alin an dad’e ba’a gamu ba tuni aka gyara zama akaja girki, ko wanne sashe na gidan tafiya mai d’an nisa zakai kafin ya sadaka da wani sashe don haka sam basu jiyo hayaniyar cincirindon ‘yan siyasa daketa kai komo a harabar gidan ba... Banda kukan tsintsaye ma dake saman bishiyoyin da yai k’awanya wa sashen nasu basa iya jiyo komai... Suna tafe Baba Ali na zuba zancen in yai kud’i zaiyi kaza zaiyi kaza yayinda Baffah ke neman Sameer a waya dan sanar dashi cewa sun ida shiri shi suke jira...
Akram da isowarsa gidan kenan ya hangi mutane na fitowa daga gate d’in da zai sadaka da b’angaren bak’i na cikin gidan.... Baisan dalili ba amma ganin wad’annan matasan ya d’aga masa hankali... Toh bak’i ne akai a gidan....? His Excellency nada bak’i amma ace bai sani ba...? Su waye wad’annan...? Kasa samo amsar tambayarsa yai ga k’irjinsa dake tsananin bugu, yana gani suka taho ta gefensa zasu rab’a su shige yai saurin kifa kansa ga wayarsa yana shafawa lokaci guda yana satan kallonsu k’asa k’asa
Baba Ali sai bin d’inbin jama’an dake cike mak’il a gidan sahu sahu da kallo yake, Baffah na muskutinsa yana fad’in “Kai haba wannan irin kallo saikace ba daga garin gwamna ka fito ba...” Dik yanda suka gifta sai sunyi sallama ma mutanen da suka tadda.. Nan suma suka samu wasu empty kujeru dake barbarje haraban gidan angle angle suka zauna suma... Firansu sukaci gaba da yi hankali kwance yayinda a b’angaren Akram hankalinsa ya gaza kwanciya... Su waye wad’annan da yaga sun fito daga sashen bak’i masu mahimmanci...? Zamansu da kad’an motar Sameer ta kutso kai cikin gidan dan tuni sun sanar dashi gidan da suke ya kuma ce ya sani dan Gidan Engr Ma’aruf MUTALLAB ba b’oyeyye bane a garin.... Take bugun k’irjin Akram ya k’aru, bai gama daskarewa ba har saida Sameer ya bud’e marfin mota ya fito... Koda ace sau d’aya suka tab’a had’uwa bazai mance fuskarsa ba domin kaw ko sati ba’ai ba Zulfa’u tai introducing d’insu ma juna, ya tina yanda Sameer d’in ya tsattsaresa da tambayoyi a matsayinsa na mai neman auren k’anwarsa... Toh mai ya had’asa da wad’annan mutanen...? Mai kuma ya had’asu da Engr..? Badai Engr ya fahimci su d’in sunyi tarayya wajen soyayyar mace guda bane... Idan ba haka ba what’s all this...? Yai saurin kauda kansa gefe ganin sun mik’e da alama ficewa zasuyi.... Yana nan a haka ya hangi Engr ya fito daga sashen cikin gida.... Akram ya rasa wanne zaiyi baya fata shida Sameer su had’u gaban His Excellency, hakan can ruin his plans... Da sauri ya zaga bayan motar da yake tsaye jikinta ya lab’e yana hangesu daga nesa yanda suke gaisawa, bai iya jiyo mai suke cewa amma yana iya hango yanda fuskokinsu suka cika da annuri... Yana nan a haka a lab’e wayarsa data soma ruri ta razanesa.. A d’an firgice ya cirota cikin aljihun wandonsa yana duba mai kiran nasa... Yusuf abokinsa ne dake main gate cikin motar Akram d’in yana jiran fitowar Akram su shige... Kaman munafuki haka ya d’aga wayar cikin yin k’asa k’asa da murya.. Daga d’aya b’angaren Yusuf ya soma fad’in “Ya na jiku shiru ko yau oga ya makara ne...?”
Cikin k’asa k’asa da murya Akram Ke fad’in “Yusuf kamin wani aiki... Akwai wata mota k’irar BMW da yanzu zata fito mai launin bak’i dan Allah kabi bayansu kaga yanda suka nufa dan na tabbatar da hasashe na...”
Yusuf yace “Ban gane ba.. Toh tafiya campaign d’in namu fah....?”
Cikin daburcewa Akram yace “Shisa nace kabi bayansu kasan su waye su d’in tinda ni banida halin yin hakan, wannan fita dole ce akaina, k’auyuka biyu zamu zaga yau da his Excellency, ai kaga I can’t come up with any excuse... Kawai kabimin bayansu and find out who they are..” Bai jira cewan Yusuf d’in ba ya katse kiran yana mai kuma lek’ensu yanda suka shige motarsu ta Sameer na jagorantarsu... Yana ganin sun shige ya fito daga mab’oyarsa yana hangan Engr dake gaisawa da jama’a...
Shiru yai na wani d’an lokaci, yai nisa cikin tunani.. Toh kodai Muhibbah nada wata masaniya ne kan wannan al’amari...? Toh ko dai ba abinda yake tunani bane... Da ace hakan ne yasan by now da Engr ya tsaresa da batun.. Toh kodai ya zuba masa idanu yaga gudun ruwansa ne...? Lokaci guda ya shiga girgiza kai yana mai ayyanawa cikin zuciyarsa Engr can never find out about his plans...Yayi alk’awarin bazai sanar dashi komai ba har sai bayan ya mallaki Zulfa’u... Da wannan tinani ya k’arasoga Engr d’in yana wani k’asa k’asa dakai yana gaidashi, tuni Engr ya mik’a masa hannu sukai masabaha dan shi baison wannan tsananin girma da Akram ke basa kasancewarsa mutum mai sauk’in kai da k’aunar Al’umma... Babu jimawa convoy d’in motocinsu suka soma ficewa sahu sahu, akasarin motocin lambar Mutallab19 suke da, ma’anar 19 d’in kuwa shine shekarar gudanar da zab’en nasu wato shekara ta dubu biyu da shatara miladiya....
Abinka da mai farin jini da yalwar alkahiri zo Kaga yanda gari ya kacame da nuna k’aunaga matashin d’an siyasan....

Zulfa’u da sauk’arta kenan daga adaidaita zata shige ofishinsu motocin su MUTALLAB sukazo zasu wuce k’ofar ofishin nasu, mutane ta ko ina hannu ake d’aga masa ana gaidashi...
Tsaye tai bakin wajen itama tana dubansu dikda cewa ta makara yau d’in amma dole ta tsaya kallon d’an siyasan da bata tab’a k’auna irinsa ba, watak’ila idan a rabon yau d’in ta ganshi ido da ido sai ta ganshi... Atika nata damunta da waya inaa ko kula wayar tata batai ba... Sautin wak’ok’insa da mawak’an gawurtattun ‘yansiyasa suka wak’esa shine kawai Ke tashi... Dik dandatson muatenen da suka shige sai ya masu alamun gaisuwa da hannayensa....
A haka har suka k’araso kusan gidan radio d’in sosai yayinda Zulfa’u ta shaga da kallonsa... Yau Allah ya nufa taga Mutallab da idanunta, ta kasa tab’uka komai sai duban da take binsa dashi yanda yaketa amsar gaisuwan mutane... Kaman daga sama Akram dake cikin motar yana tuk’awa ya hango wata tamkar Zulfa’u... Dama tinda suka iso kusan gidan radio d’in nasu yake jin gabansa na fad’uwa ga kuma wad’ancan mutanen da yasa Yusuf ya bisu ya bincika masa su waye su... Abinda yafi basa mamaki shine yanda ta kafe idanunta ga samar motar tana kallon Engr dake d’aga ma d’inbin masoyansa hannu... Ji yai kaman ya kwali motar da bala’in gudu saidai kuma baida ikon yin hakan.... Sannu a hankali idanun Engr suka sauk’a kan wannan baiwar Allah data kasa janye idanu daga Barin dubansa, wani irin abu ne yaji yana tsargar masa sanda idanunsu suka sark’e waje guda, yayinda a b’angaren Zulfa’u bugun zuciyarta ya k’aru, k’warjininsa ya cika mata idanu... K’ok’arin janye idanunta tai amma sai ta kasa ga k’irjinta dake bugu da sauri dasuri...
Kasa janye idanu yai daga barin duban nata, wani abu wanda bazai iya kwatantawa ba na kuma tsargar masa.... Akram ya d’aga kai sama yana duban Engr lokaci guda ya kuma kai dubansa ga Zulfah dake tsaye har lokacin duban Engr take wane irin sihirtaccen murmushi da bai tab’a gani daga gareta ba kwance saman kyakkyawar fuskarta... Cikin sauri ya janyo wayarsa ya shiga k’ok’arin dialing layinta....
Hakan yasa tai k’ok’arin lalumar wayarta dake cikin jaka, daidai nan Atika ta k’araso tana fad’in “Amma kinsan Aunty Zulai tana d’akin gudanar da shirye shirye ke take jira... Kuma yau d’in kece bak’uwarmu ta mako...”
Zaro idanu waje tai kana tace “Ke dan Allah wai interview za’ai dani...?”
Atika tace “Sake tambayata... Kinga dan Allah muje amarsusu....”
D’an murmusawa tai tana mai bin bayan motocin da kallo.... Atika ta kuma kai dubanta gareta tana d’an murmusawa take fad’in “Ashe tawagar oganku ne dole ki tsaya a nan kiyi ta raba idanu ko zaki hango ango...”
Harara Zulfah ta galla mata kana tace “Abinda kika iya kenan ai jin baki....” Tasa kai ta shige cikin radio station d’in zuciyarta nai mata wani irin sanyi haka kurum, ita kad’ai sai sakin murmushi take, yau tayi ido hud’u da Engr Mutallab, governor d’insu mai jiran gado da yardar Allah...
A haka ta isa d’akin gudanar da shirye shiryen, annashuwa fal zuciyarta, hakan sai ya bata daman amsa duk tambayoyin da aka mata cikin sauk’i da shauk’i...
A b’angaren Engr ma hoton fuskar budurwar can ya kasa b’acewa daga k’wayan idanunsa... Mai yasa yakejin kaman ya tab’a ganin fuskar wani waje... Kaman ya san mai irin fuskar... Maiyasa kuma ya kasa cire hoton fuskar daga k’wayan idanunsa..? Maiyasa zuciyarsa ta kasa daina tuno wannan fuskar... Could it be ya tab’a sanin mai irinta wani wajen ne...? Toh a ina zai sani...? Wata zuciya tace kaid’in mai huld’a da jama’a da dama ne... Watak’ila ka tab’a ganin mai irin fuskar ne... Toh amma tambayar mai yasa kake jin yanayin da kake ji....? Wannan amsarce ya kasa samowa har suka isa yanda zasuje....

***
Chapter 123 · 0% Book details