← Book details Inda Rai Da Rabo Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 83 OF 198

Sashe 83

Inda Rai Da Rabo Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ko gizau Hajiya Haule batai ba saima murmusawa data kumayi kana tace “Bakaso ka bak’anta kanka a idanun danginka shine kai amfani da aminiyar sirri domin ta d’auki alhakin laifinka.... Ka sani munyi tarayya ne a wannan bak’in laifi kuma dawowar Ma’aruf ba rayuwarmu kurum yake barazanar tarwatsawa ba harda naka rayuwar... Kayi tunani idan d’an uwanka yasan abinda ka aikata ma d’ansa... Shin mai zai d’aukeka....? Kayi tunani idan mahaifiyarka tasan abinda ka aikata ma d’an d’anuwanka shin a wani sahu zata ijiyeka....? Idan ‘ya’yanka suka san wannan bak’in sirri naka shin da wasu idanu zasu kuma dubanka....? Duk wannan abin dubawa ne Alhaji.... Ni dama na riga nasan yanzu Hafiz ya gama tsanata domin kaw a nasa tunanin niceda alhakin gurb’ata masa rayuwa.... Yanzu idan wannan batu ya bayyana ya fito fili shikenan Hafiz zai tsana duka iyayensa, don haka musan abinyi... ‘Ya’yanmu bazasu tab’a sanin gaskiya ba....”

Baba Alhaji yayi shiru yana nazarin kalaman Haule.... Hannayensa hard’e ta baya kansa a k’asa, lokaci guda ya d’ago yana dubanta kana yace “Haule ki sani zuciyata ta cika da kishi da hassada a baya, karki mance yanda mahaifiyarmu keson Usman da d’ansa Ma’aruf, nayi tunanin idan na b’atar da d’ansa hakalinta zai dawo gareni da iyalaina amma koda yaushe mahaifiyarmu tafi fifita d’anuwana sama dani, a idanun danginmu gaba d’aya shi yakeda girman da ya kamata ace nikeda ita....” Shiru yayi na d’an lokaci kana ya kuma d’agowa ya dubi Haule yace “Ban tsammaci cewa Ma’aruf na raye ba harma zai dawo garemu.... Nayi tunanin kun gama dashi tun a wancan lokacin....”

Haule ta murmusa had’ida gyara zama tace “Aminiyar Sirri ita ta yaudaremu gaba d’aya.... Duk munyi tunanin Ma’aruf ya halak’a tuntuni, bata halaka shi ba saima tsiratar dashi da tai... Yanzu abu guda zamuyi mu wanke kanmu mu zame kanmu daga cikin laifin....”
Baba Alhaji ya dubeta yace kaman yaya “Kaman yaya...?”

Haule ta nurmusa ta gyara zamanta da kyau kana ta soma fad’in “Lami da aminiyar sirri su zamu d’aurawa alhakin laifin... Ita dama Lami batada wayo batada ra’ayin kanta sai abinda na fad’i mata, ita kuma Aminiyar sirri Hajiya Hannatu mahaifiyar Ma’aruf tanada dalilai masu k’arfi da zata yarda tabbas ita ta rabata da d’anta tsawon shekarun nan.... Abu mafi sauk’i a nan ni yanzu zan nuna cewa nayi nadama ne bisa abubuwan da nayima Zulfa’u a baya, kaima zaka nuna kaji dad’in nadaman da nayi sannan ka gyara alak’arka da d’an uwanka, abu na gaba ka nemi Ma’aruf ya auri d’aya daga cikin ‘ya’anmu Sahariyya ko Naja’atu.... Kaga shikenan mun rufe bakin kowa ruf don babu yanda za’ai koda asirinmu tonuwa zaiyi Ma’aruf yace zai maka sirakansa a kotu....”

Baba Alhaji yayi shiru yana nazarin Hajiya kafin ya d ‘ago yana dubanta yace “Anya Haule.....? Anya Usman zai kuma yarda ayi wannan had’in bayan ga yanda ta kasance da Zulfa’u da Hafiz....?”

Haule ta d’an hareresa kana tace “Wannan karon ba irin auren Zulfa’u da Hafiz za’ai ba, wannan karon zamu nuna duka munason abun ne sannan shima Hafiz d’in zamu sa ya kuma neman auren Zulfa’u don a daidaita komai, kada ka mance idan auratayya ta shiga tsakanin ‘ya’yanmu shikenan mufa mun tsira... Kuma nunawa zamuyi hakan shi zai k’ara dank’on zumunci, ga Sahariyya ga Naja’atu ka bashi auren d’aya daga cikinsu....”

Baba Alhaji ya kuma dubanta yace “Toh idan shi Ma’aruf d’in baiso fah...?”

Hajiya Haule ta yatsina fuska tace “Auren biyayya zaiyi domin ga dukkan alamu yaron yanada nutsuwa, kuma na tabbata idan ka sami d’an uwanka da wannan batu bazai maka jayayya ba domin sanin kanka ne Usman na ganin girma da kimanka bacin duk abubuwan da kake masa....”

Baba Alhaji ya jinjina kai had’ida murmusawa yace “Shiyasa nake sonki Haule kin iya kawo solution ma komai... Yanzu daga nan wajen d’anuwana zan wuce na fara neman gafaransa bisa abinda ya wakana tsakanin Hafiz da Zulfa’u kafin daga bisani na bijiro masa da batun auren d’ansa Ma’aruf da d’aya daga cikin ‘ya’yana domin k’ara dank’on zumunci....”

Haule ta fashe da dariya tace “An gama, nima daga yanzu nayi hankali na zama saliha Haule...”

Suka fashe da dariya a tare....

Naja’atu dake rakub’e jikin k’ofa a kunnenta komai ya faru, wasu irin hawayene ke kwararowa daga idanunta, ta kasa yarda da abinda taji iyayenta sun aikata..... Ta rintse idanunta wasu hawayen suka kuma kwaranyo mata, fasa shiga d’akin tai sai komawa da baya da tayi idanunta basu daina zuban hawaye ba.....

SameenaAleeyou📚

*INDA RAI*
_................DA RABO_

*67*

Sallaman Mamy harmada Aunty Lami ne ya katse hiran Baba Alhaji da Hajiya Haule.... Tuni Haule ta koma ta narke kan gado yayinda Baba Alhaji ya mik’e yana mai amsa sallamarsu had’ida masu iso.....
Kan kace mai Haule ta shiga tattaro bakin zani tana mai sake kuka tamkar an kunna engine, Baba Alhaji da idanunsa ke kannare yana duban yanayin Mamyn cikin sauri ya soma fad’iwa Hajiya Haule...
“Haba Haulatu kukan nan ya isa haka, tin shigowata kike abu guda, shi ciwo ba’a masa kuka addu’a ake.....
Cikeda makirci ta soma fad’in “Inyi dole nayi kuka Alhaji... Kuka ya zamemin dole, ace duk abubuwan da nayima Zulfa’u itace ta taimaka min, bata barni bakin kwalta na halak’a ba koma wajen wancan tsinanniyar matar Hafizun....”
Katseta yayi cikin zaro idanuwa kana yace “Kina nufin matar Hafiz ne ta maki wannan wulak’anci sannan Zulfa’u ce ta taimakeki....?”

Haule bakin zani a hannu ana goge hawaye take jinjina kai, cikin muryar kuka take furta “Saima kaga d’iban Albarkan da wannan tantiriyar yarinyar tamin, ashe annoba Hafiz ya auro ya kawo cikin gidansa bamu sani ba... Ohni Haule nayi uwa nayi mad’auki saida ya saki baiwar Allah Zulfa’u.... Matar arziki ‘yar uwarsa ta jini....” Ta k’arashe tana mai kamo hannayen Mamy... Banda bugu babu abinda k’irjin Aunty Lami keyi... Mai Haule take nufi...? Shin abinda idanunta ke nuna mata gaskiya ne...? Haule na neman yafiyar Mamy gabanta....? Lokaci guda k’irjinta ya kuma bugawa tamkar an sauk’e mata k’aton guduma..... Tinaninta ya katse sanda taci gaba da sauraro muryar Hajiya Haule dake rik’eda hannayen Mamy tana hawaye...

“Wllhi sharrin shaid’an ne, ni dama tin can bana k’in auren Hafiz da Zulfa’u... Hanne ki yafeni ki rok’ar min Zulfa’u ta yafeni...”

Girgiza kai Mamy tai had’ida rik’o hannayen Hajiya Haule kana tace “Ni ban k’ullaceki ba Hajiya, sannan Zulfa’u ma bata k’ullaceki ba, ai duk d’an adam ajizine, gaba d’ayanmu muna kure... Mukayi laifuka ma Ubangijinmu ma ya yafe mana ballanta mu ‘yan adam da muke ajizai... Ban tab’a rik’eki ba haka d’iyata ma bata tab’a rik’e kowa cikinku ba ko a baya da ta fuskanci k’yama da tsangwama daga dangi... Don haka ki kwantar da hankalinki fatanmu duka shine ki sami lafiya... Allah ya yafemu gaba d’aya...”
Haule na share hawaye take amsawa da ameen yayinda taci gaba da fad’in “Ina Zulfa’un take... Ina d’iyata, na rok’eta gafara da bakina tinda Allah ya bani damar ci gaba da rayuwa bayan na zaci rayuwata ta k’are hannun mahaukaciyar matar Hafiz...Ohni Haule zan jima ina jin zafin abinda nayima yaran nan... Suna son juna da k’arfi na rabasu na sanya Hafiz ya rubuta mata takardar saki....”
Batakai aya ba Baba Alhaji ya tari zancen da fad’in “Kinga irin mugun halin naki koh Haulatu... Ni dama nasan haka kurum Hafiz bazai saki matarsa ba idan ba umartansa kikai ba.... Zanje na sami d’an uwana na kuma basa hak’uri na fad’i masa wannan duk sharrinki ne Haule...”

Hajiya ta kuma kamo bakin zani tana furta “Alhaji Wllhi na tuba.... Bada son raina bane sharrin shaid’an ne...”
Ita kaw Aunty Lami kallon kallo kurum sukema juna itada k’awarta Haule, tabbas Haule nada tarin bayanai da zatayi mata....

***

KADUNA

Kishingid’e yake saman sofa dake a cikin d’akinsa, idanunsa duka biyu a lumshe, tin daga ranar da suka soma had’uwa yake kan tunowa, ya tuna duba na farko da ya mata yaji wani abu ya tsargar masa tin daga tsakar kansa har zuwa ‘yar yatsarsa dukda cewa tab’o ya rufe mata Fuska, a lokacin ya zaci razana ne ya haifar masa da wannan yanayin, sai yanzu yake tabbatar ma kansa abinda ake kira love at first sight shine yanayin da ya tsinci kansa... Gaba d’aya rayuwarsa bai tab’a jin irin hakan ga wata mace ba, ta ya zai cireta a zuciyarsa rana tsaka, just how...?! A hankali ya sauk’e nannauyan ajiyan zuciya had’ida furta “I love you... I love you Teddy Bear.... So much....”

Kaman daga sama yaji ana murd’a handle d’in k’ofar... Ya d’an bud’e idanunsa da suke a lumshe ba tareda ya mik’e ba yana mamakin waye zai shigo masa d’aki babu neman izini....
To his greatest surprise ba kowa bace illa Yesmin, an cab’a uban kwalliya sai kwarkwasa ake... Ya ma rasa mai zaice tsaban tsananin takaicin yarinyar da yakeji....

Ganin bai tankata ba bai koreta ba ya sanyata samun k’warin gwiwan zama gefen k’afafunsa... Tamkar wanda aka zabura haka ya mik’e yana wani irin huci yake dubanta....
Maimakon ta mik’e saima sakin murmushi da tai had’ida gyara zaman gashin kantin dake kanta da tai...

“My Kay.... Dama kan batun wedding preparations d’in nan ne, kaga I want something big... A very grand....” Bata kai aya ba ya katseta da fad’in “Uban wa ya baki izinin shigo min d’aki....?”

Dubansa tai had’ida shagwab’e fuska kana tace “Haba my Kay gani fah nayi yanzu nida kai mun zama d’aya... Aurenmu fah duka duka watanni ya rage, and I’m here to plan our wedding together kafin na wuce Abuja, already Momy nata cewa na koma don a fara gyara maka ni....” Ta k’arashe tana juya idanu...

Murmushin takaici yai kana ya d’ago ya dubeta daga sama har k’asa...
Fuskarsa dab nata yake furta “Oh really! A gyaraki..? For who....? Me...?” Ya saki murmushi a hankali had’ida shafar hab’arsa kana yace “Well I’m not interested... Kicewa Aunty Kar tayi asaran kud’inta, cos to me ke ba mace bace, bana miki kallon mace balle har ajega gyaraki....Now get out of my room, and don’t you dare.... Kada ki kuskura ki sake shigo min d’aki haka balle har kiyi tunanin zama kusa dani... Tashi ki fice nace kafin na watsar maki da hak’wara....!!”
Ya k’arashe cikin daka tsawa....

K’walla tab idanunta take dubansa....
“Leave I said...!!!”
Chapter 83 · 0% Book details