← Book details Inda Rai Da Rabo Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 151 OF 198

Sashe 151

Inda Rai Da Rabo Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ya d’ago yana duban Najma yanda tai kwance lif jikin Zulfa’u.... Murmushi ya saki a hankali kana yace “Princess ba oyoyo wa Daddy ne...?”
Sai sannan ta tashi ta nufoshi da gudu ta rungumeshi... Zulfah ta saki murmushi tana mai gaidashi....
Fuska a sake shima ya amsa mata, a zatonta fita zai dan harga Allah tinaninta ya biyo sahun yaransa ne... Amma ga tsananin mamakinta sai gani tai ya zauna daga saman kujera mai kallon gadon da take zaune bisa had’ida d’aura d’iyarsa saman cinyar sa dake ta faman zuba masa shagwab’a yana kan biyeta... Itakaw Zulfah k’uri ta masu dan harga Allah sosai suka birgeta... Sosai ta shagala da kallonsu har saida ta jiyo muryarsa yana fad’in taje taiwa Aunty goodnight kiss itama... A guje ta taho taima Zulfah peck a kumatu tana fad’in “Goodnight Aunty...!”
Zulfah ta Shafa kanta tace “Goodnight Princess...!” Daga haka ficewa yarinya tai cikin d’an tsalle da gudu irin na yara... Gaba d’aya suka bita da kallo murmushi saman fuskokinsu Engr na fad’in “Watch your steps baby...Be careful... I love you...!”
Maido da dubansaga Zulfah yai wacce har yanzu bata daina bin k’ofar da kallo tana murmushi ba, ya zuba mata kyawawan idanunsa yana dubanta, har saida taji bugun zuciyarta na k’aruwa... Tai saurin waigowa aiko nan idanunsu suka sark’e waje guda.... Tai saurin sadda nata k’asa dan bazata iya juran duban cikin idanunsa ba....
Engr ya d’an gyara zamansa kad’an yace “Amarya har kukan ya k’are ne.... Ko don bakiga an tafi dake gidan naki bane tinda har yanzu gidan Mamanki kike....” Yanda yai maganar dole ya baka dariya, dan dagaji had’o kalaman kawai yake amma bawai ya saba da surutun bane....
D’an murmusawa tai kad’an ba tareda tace komai ba, shiru ne na ‘yan wasu dak’ik’ai ya raba tsakani.... Kowa da abinda yake sak’awa cikin zuciyarsa... A b’angaren Zulfah ma iya cewa tambayar kanta take ta faman yi shin mai ya zaunar da bawan Allahn nan a d’akin... Idan sawun yaransa ya biyo ai sun tafi... Toh mai kuma yakeyi...? Batakaiga samo amsar ba ta sinkayo muryarsa mai cikeda charisma yana fad’in “Emmm... Munyi magana da Ammah zaki zauna a nan for the meantime before a ida gyaran naki sashen.... Idan akwai dik wani abinda kike buk’ata Ammah ba sirkarki bace mamarki ce... Ko mai kike so don’t hesitate to tell her kinji koh...”
A’a gaba d’aya kan Zulfah fah ya k’ulle Wai meke faruwa ne....? Batakaiga samo amsar ba ta kuma sinkayo muryarsa naci gaba da fad’in “Nasan you might be a little confused, but karki damu... Ga wannan Ki karanta, idan kin gama karantawa anjima kad’an zan shigo nai maki bayanin komai... But for now read this first...” Ya k’arashe yana mai aje mata takardan da Akram ya bariwa Yusuf ya bata saman gado....
Innalillahi wa inna’ilaihi raji’un... What’s all this... Wai meke faruwa ne...? Meye wannan yake faruwa yanzu da ita...? Gaba d’aya jikinta ya koma sanyi k’alau... Itafah bata fahimci komai ba... Wai me hakan yake nufi ne...? Ta k’arashe tinanin tana mai bin bayan Engr da ya fice yana amsa waya da kallo....
Tamkar wacce aka zabura tai wuf ta d’au takardan tana juyawa k’irjinta bai daina bugu ba.... Sosai hannayentake rawa sanda ta soma warware takardan.... Taji jiri na neman d’ibanta.... Ta mik’e zumbur zuciyarta naci gaba da wani irin tsinkewa... Shin abinda take gani gaskiya ne koko akasinsa... Shin dama Engr Mutallab shine mutumin da ya soma furta yana sonta, ashe Akram da fari ba kanshi ya kawo ba Ubangidansa ya kawo.... Zuciyarta taci gaba da tsinkewa sanda take ci gaba da karanta wasik’ar... Wasu irin hawaye taji suna gangaro mata d’aya bai jiran d’aya.... A hankali ta lumshe idanunta da suka jik’e shakaf da hawaye sanda takai k’arshen rubutun... Ta zauna gijif saman gado har lokacin takardan na rik’e hannunta.... Ita harga Allah tama rasa mai takeji... Wane irin al’amari ne wannan, abu saikace a film... Ji tai kukanta na k’aruwa sosai lokaci guda.... Bata ankara ba sai jinta tai cikin k’irjinsa ya mata runfa had’ida rungumeta.... Wani sabon fad’uwan gaba ta tsinci kanta ciki... Cak ta nemi kukan da take ta rasa sai bugu da k’irjinta yaci gaba dayi... Ita tsoro ma abin ya soma bata, sai yanzu abubuwan da suka faru sukaita dawo mata, hannunka mai sanda da Atika ta dinga mata, Aunty Bara’atu da tace mijin da Allah ya zab’ar mata shi ta aura... Ashe wannan shine nufinsu... Engr Mutallab mai neman takaran kujeran governor kuma Yayanta Ma’aruf shi ne mijinta.... Ya Salaam taji zuciyarta tamkar zillo yake cikin k’irjinta... Lokaci guda ta rintse idanunta dan gaba d’aya ta kasa katab’us cikin k’irjinsa... Jin tai tsit tamkar an d’auke ruwa ya sanyashi d’an sakinta kad’an yana mai dubanta.. Zulfah kaw jin ya saketa ya sanyata janye jikinta a hankali zuciyarta bai daina bugu ba... Yanada tabbacin koda bai bud’e baki ya sanar da ita cewa shid’in ne mijinta yanzu ta fahimci hakan... Ganin tana k’ok’arin ci gaba da janye jiki daga kusansa ya sanyashi d’aura hannunsa guda saman nata ya d’an rik’eta kad’an hakan ya hanata ci gaba da janye jikinta.... Jikinta yaci gaba da rawa sosai dan har yanzu bata dawo daidai ba... Ganin yanayin nata ya sanyashi d’an sakar mata hannun kana yai gayran murya kad’an yace “Ki huta idan Allah ya kaimu da safe zamuyi magana koh... Goodnight...!” Ya k’arashe yana mai mik’ewa tsaye had’ida ficewa daga d’akin...
Innalillahi wa inna’ilaihi raji’un... Ai yana ficewa Zulfah data koma tamkar mutum mutumi a d’ari ta mik’e ta nufi dressing mirror tana duban kanta... Itace matar shi Wai.... Wai shid’in shine mijin da aka aura mata... Shisa babu wanda ya damu dikda cewa babu wanda yaga idanun Akram...Ta lumshe idanunta a hankali wani irin abu na fizgar mata a zuciya... Motsi kad’an tai kaw sai taji har yanzu tamkar cikin k’irjinsa take... Tai saurin ware idanunta ta shiga lalumen wayanta... Atika dake zaune parlorn mahaifiyarta tana labarta mata yanda Al’amarin Allah ya juye sai ganin kiran Zulfa’u tai, ta d’aga tana darawa dan tasan by now k’awar tata tasan dawan garin....
Jin yanda Atika ke k’ek’yata dariya ya sanya Zulfan kuma kufula... “Kin kyauta ma kanki... Ya miki kyau...!” Ta fad’i a hasale....
Daga d’aya b’angaren Atika na dariya tace “Da nayi mai....? Ango shi zai breaking news d’in wa amaryarsa kinga laifina da ban fad’a miki ba...”
K’wafa Zulfa’u tai kana tace “Allah zan kamaki ne zaki sani....”
Atika ta kuma darawa kana tace “Haba ta His Excellency ni Ki rufamin asiri kafin kisa Excellency yaji na b’atawa amaryarsa rai a hanani shiga gidan gwamnati..”
Tsuka tai a hankali kana tace “Ke kika san wannan kuma maras m kawai...”
Atika ta kuma darawa kana tace “Ta Excellency kinga kashe wayar nan kafin ango ya shigo yace wannan k’awar taki ta faye gulma... Saida safe asha love lafiya....” Ko jiran amsar Zulfah batai ba ta katse kiran tana mai ci gaba da darawa....
Zulfah tai k’wafa kurum kana ta silale jiki ta kwanta kan gado, ko zarafin mik’ewa tai alwalwan shafa’i da wuturi ta kasa, tana jin Najma ta turo k’ofan ta shigo tana fad’in ita wajenta zata kwana, hakan sai yaima Zulfa’u dad’i sosai dan da batasan yanda zata kaya da tinanin nan da ya tsaya mata a rai ba, ko banza Najma zata d’ibe mata kewa.... Tuni ta rungumo yarinyar suka haye gado tanajinta tamkar d’iyarta...

***

Gaba d’aya hankalinsa gaza kwanciya yai, ga wasu irin mafarkai da yake gameda mahaifinsa... Ya kuma kiran wayan Daddy ya jita a kashe har yanzu... Innalillahi wa inna’ilaihi raji’un kurum zuciyar Khalid Ke nanata masa, haka kawai yake jin tamkar wani abu ya sami mahaifin nasa.... Time ya duba jikin wayarsa yaga lokacin sallan asuba ya kusa... Bathroom kurum ya fad’a ya d’auro alwala ga kansa dake matsanancin masa ciwo sakamon samun rashin wadataccen bacci da baiba daren jiyan.....

Raka’atanil fajir ya soma gabatarwa kafin ya fice masallaci kwatsam yaji wayarsa na ruri.... Gabansa ya yanke ya kuma fad’uwa.... Cikin sauri ya janyo wayar yana dubawa, bak’uwar lamba ce mai kiran nasa... Ya sauk’e ajiyan zuciya a hankali had’ida tattaro duk wani k’arfin halinsa ya d’aga kira..... Daga d’aya b’angaren aka soma tambayarsa “Am I speaking to Architect Khalid Mainasara...?”
Khalid ya jinjina kai yace “Yes speaking... How may I help you...?”
Mutumin yaci gaba da fad’in “I am calling from the National hospital here in Abuja... Your father Engr Mainasara had a terrible car accident a yammacin jiya.... And he was rushed.....”
Baikai aya ba Khalid ya mik’e a birkice yana fad’in “How’s my father doing... Tell me, ina mahaifina.... Talk to me....!” Ya k’arashe cikin tsananin d’imauta...
Mutumin yace “Try to calm down Sir, a yanzu haka Babanka yana ICU namu yana samun kulawa na gaggawa... Muna fatan cikin yardar Allah ya tashi kafad’unsa...” Daga haka katse kiran mutumin yai yana mai kuma baiwa Khalid baki had’ida kalaman k’arfafa gwiwa dikda cewa Khalid baima yarda mahaifinsa na raye ba sabida wane irin crack da yakeji zuciyarsa nayi tin daga can k’asa.... Take yaji k’afafunsa sun gaza d’aukansa... Ya zame ya zauna gijif saman kujera yana mai d’aura hannayensa saman bakinsa... Innalillahi wa inna’ilaihi raji’un, abinda yaji zuciyarsa na nanata masa kenan... Lokaci guda yake girgiza kai yana mai furta “A’a Daddy na yana raye... Zai tashi yaga burinsa ya cika... Family d’insa sun had’e waje guda.... My Dad is alive.... Yana nan da rai.... I’m sure of it... Na sani...” Ire iren sumbatu da Khalid keyi kenan... Lokaci guda yaji wani irin kukan da yaketa dannewa na k’ok’arin faso k’irjinsa.... Allah sarki haka Khalid ya kifa kansa ya dinga kuka yana fad’in mahaifinsa na nan da rai, ida ka gansa dole ne ma ya baka tausai... A b’angaren Nabilah haka kurum taji tamkar wani abu na faruwa da Khalid d’in musamman da taga ta kira wayarsa har sau uku bai d’aga ba, tasan dik fushin da zai da ita bazai k’i d’aga kiranta haka kawai har sau uku ba... Take taji zuciyarta ya karaya sosai, tana son sanin halinda mijinta Ke ciki... Baccin data kasa komawa kenan itama taita jero sallolinta....
Chapter 151 · 0% Book details