← Book details Inda Rai Da Rabo Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 26 OF 198

Sashe 26

Inda Rai Da Rabo Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Waige waige ta soma tana neman ta yanda zata hangoshi amma ko k’yallin mai kamanninsa bata gani ba, murmushin yak’e tai lokaci guda ta kuma had’e fuska kaman tasan yana kallontan kana tace “Malam ba wani deal tsakanina dakai idan kuma ka matsa sai na biyaka kud’in gyaran motarka nima sai ka biyani kayana da ka b’ata...”

Murmushi maras sauti ya kumayi kana yace “Ki daina wahalan juye juye just turn to your left....”

Waigowa ta kumayi ta direction d’in da ya fad’i nan ta hangi motarsa pake k’asar bishiya....

Sauk’e ajiyan zuciya tai kana tace “Kaga Malam ka k’yaleni ka daina bibiyata....”

Katseta Khalid yayi da fad’in “You haven’t asked about my wound... Ko kinsan cewa har yanzu bai warke ba, har yanzu ina ganin likita a sabida ciwon da kikajimin... To add it to your expenses zaki biya....” Saurin kasteta tai da fad’in “Malam kodai kai d’an 419 ne... Toh idanma kai d’an damfara ne babu abinda zaka samu daga gareni just stop stalking me...”

Wannan karon sosai ta basa dariya amma ya gimtse yace “But you know I can press charges, ciwon dake fuskata is enough evidence kin yarda.....?”

Fuzar da iska tai kafin ta kashe wayar ta nufi yanda motar tasa ke pake kaman zata tashi sama sabida tsananin huci da take....

Su Yusrah kam saidai hango k’allin mayafinta da sukai ta nufi wani wajen, Yusrah na kiran sunanta inaa ko tsayawa batai ba balle ta tankata...

Gaba d’aya suka murmusa suna fad’in “Nabila case ko ya tab’owa kansa kuma sai Allah....”

Yusra ta girgiza kai had’ida tab’e baki tace “K’awata ta kaina, ku k’yaleta zata dawo idan taje ta saita duk abinda ta taro, kaga Safwan ci gaba da ciremu daga ruwa kafin ta dawo tinda ance mutumin nan unannounced test yakeyi...”

Basu kuma bi takanta ba sukaci gaba da abinda suke....

Koda ta iso babban abinda yafi bata takaici shine ta kusan minti uku masu kyau tsaye a wajen Khalid baisan tama iso ba yana kwance cikin motarsa yana shan AC, sarai tasan salon wulak’ancinsa ne yana kallonta itace dai bata ganin sa tinda glass d’in motar mai duhu ne...

Kaman ta shige tai tafiyarta sai kuma ta shiga bubbuga masa glass d’in motar da iyaka k’arfinta....

A hankali ya shiga zuge glass d’in motar....

Lokaci guda ta d’ago idanu tana dubansa fuskarta kaman zata kurma ihu... Wani ni’imtaccen k’amshi ne had’ida tururin AC suka fara mata sallama kafin ta iya d’ago idanu tana dubansa

Kwanceccen murmushi ta hango saman kyakkyawan fuskarsa, idanunta na duban wajen ciwon nasa da yace bai warke ba, bata hango ciwon ba sai d’an sauran alamun tabo alamun ya gama healing, batasan dalili ba amma sai taji zuciyarta ta nastu da ganin ciwon nasa ya warke, tai saurin d’auke idanu daga duban nasa, fuska a tamke tace “Malam wai mai na maka da tsanani kake bibiyata...?”

D’an kauda kansa gefe kad’an yayi kana ya juyo yana kuma dubanta “First one has to say salam before anything else....”

A kaikaice ta kuma dubansa kana tace “Kaga Malam let’s settle this once and for all, Im pretty tired gida nakeson tafiya... You want money... Is that the only thing that matters....?” Tayi maganar cikin tsananin fad’a

Tinda ta soma magana yake dubanta ba tareda ko k’yafta idanu ba, sosai yakeso yaga mace na masifa irin haka, murmushi yayi da gefen bakinsa ba tareda ya katseta ba har ta ida masifan nata kana yace

“Of course not... I just want you to learn how not to go through life hurting beautiful innocent people....”

Baki sake take dubansa yanda yayi maganar babu ko alamun wasa tattareda shi...

Murmushin yak’e tai kana tace “I think that’s what you’ve to learn.... I came because you scared me... I’ve to see your wound...” Ta k’arashe murya can k’asan mak’oshi....

Da mamaki yake subanta kana ya fito da kanshi sosai yana kuma dubanta, murya a hankali ya furta “Just my wound...?” Yayi tambayar idanunsa a kanne sihirtaccen murmushi kwance saman fuskarsa...

Ganin irin duban da yake mata ya sanyata d’an daburcewa, a hasle ta kuma cewa dashi “Eh.. eh mana sabida na tabbatar ba 419 kazo kamin ba... If you don’t have more to say ni zan tafi friends d’ina na jirana....”

Tasa kai zata wuce tajiyo sautin muryarsa na ambaton sunanta a karo na biyu bayan kiran sunanta da yayi randa suka soma had’uwa....

“Nabeelah.....!”

Cak ta tsaya na wasu ‘yan dak’ik’ai kafin ta juyo a hasale tace “What again...!!!”

“We haven’t finished talking yet, idan da gaske kin gaji kuma gida kike son tafiya toh ki shigo na kaiki...”

Galala take dubansa kafin ta dawo da baya ta point kanta tana mai furta “Ni.. Na shiga wannan motar taka... Allah ya sawwak’e mun... Wait what do you think of me...?” Ta k’arashe tana mai d’aura hannu saman kunkumi...

Khalid ya kauda kai gefe had’ida rausayar da idanu bai tab’a zaton akwai macen da zatai ta gaya masa maganganu baijin zafinsu ba sai wannan yarinya mai d’an uban masifan....

Dawo da dubansa gareta yayi kana yace “Idan kinaso naje na sami Abbah ne fine kinsan har parlornsa na sani...” Ya k’arashe murya babu alamun wasa...

Cuno baki gaba tai tanaji kaman ta rufesa da duka don har yau batasan meye alak’ansa da mahaifinta ba gashi kuma har parlorn Abbah ta ganshi yana cin abinci...

Wannan karon murya k’asa k’asa tai maganar “Kaga an hanani shiga motar strangers idan kanaso mu k’arasa maganar nan kowama ya huta ka fito daga motarka mu k’arasa...

Yanda tai maganar cikin kwantar da murya sai ya masa banbarak’wai, da gefen bakinsa ya kuma murmusawa kana yace “No... Really, I’m scared of people ban saba da irin universities d’inku na nan ba...”

Baki sake take dubansa, lallai wannan babban d’an rainin hankali ne... A fili ta furta “You’re unbelievable....” Tasa kai abinta tayi wucewarta cikin sauri... Tuni shima ya tada motar ya shiga bin bayanta, A hanya suka had’uda Yusra ta gaji da jiranta don harsu Safwan sun wuce hostel...

Yusrah taga hamshak’iyar motar sai bin k’awarta take, kafin Yusrah tai magana Nabilah ta finciko hannunta tana fad’in “Kar kice komai wuce mu tafi...”

Yusrah na waige take fad’in “Ke dilla ki tsaya muga waye, why is he following you... Dan Allah Naby ki tsaya mu....”

Bata kai aya ba Khalid ya kuma shan gabansu da motar, Nabilah tazo wuya sabida tsananin k’uluwa ji take kaman ta d’au dutse ta kuma fasa masa gilashin mota....

Yusrah bata kuma sumewan tsaye ba saida ya shiga zuge gilashin motar ta hango matuk’un motar wanda har yafi motar had’uwa...

Fuska babu alamun wasa yace “Shige muje.....”

Harara kurum take galla masa kana tace “Too bad ban shiga...”

Yusra ta kalli wannan ta kalli wannan, nan ta shiga mintsilin Nabila tana fad’in “Kiyiwa Allah ki cecemu mu shiga motar nan...”

Nabila ta aika mata mugun kallo kana tace “Idan kin matsu kya shiga yakaiki daga nan yayi kud’i da kanki...” Ta kuma sa kai zata shige yace “Idan kinaso mu gama deal d’in once and for all kowa ya kama gabansa kina iya shiga motar, idan kuma yankan kai kike tsoro kaman yanda kikace har cikin gidan naku zan iya shiga...”

Kaman zata kurma ihu haka take dubansa, rai b’ace ta finciki marfin motar tayi shigewarta baya “You better keep your word..” , Yusrah ma sim sim ta shige d’aya side d’in tana mamakin ina Nabilah ta samo wannan had’edd’en guy d’in babu ko labari...

Kashe motar mai gaba d’aya yayi alamun idan ta dawo fronts eat zasu tafi....

A hasale ta kuma fincikar marfin motar ta koma gaba tasan idan bata dawo gaban ba haka zasuci gaba da tsayuwa gashi tuni la’asar ta shige....

Yusrah ta d’an kanne murya tana gaisheshi, tinda ya amsa a tak’ice bai kuma cewa komai ba, saima wayarsa data d’auki ruri, Siyama ce mai kiransa... Kaman bazai d’aga ba sai kuma ya d’aga, hannunsa guda na rik’eda waya guda kuma naga steering wheel...

Kaman baison maganar yace “Yes Siyaam....”

Daga d’aya b’angaren Siyama tace “Khalid we need to talk, is about Yesmin...”

Saida ya d’an fuzar da iska yana jiran traffic ya basu hannu kana yace “I’m busy right now.... We talk later...”

Yusrah kam tana daga baya tana k’arewa wannan miskili kallo da gani za’asha fama dashi, itakaw Nabila tinda taji ya ambaci sunan mace tabada k’eya tana duban window ko ba’a fad’i mata ba ta sani da budurwarsa yake waya, tayi k’wafa cikin zuciyarta tana mamakin duk wanda ta kasance budurwan wannan d’an rainin hankalin, don dagajin yanda yake maganawa budurwar ma ba dad’insa takeji ba, ta kuma tab’e baki ita kad’ai tana ayyanawa cikin zuciyarta ko maza sun k’are bazata tsaya da wannan d’an rainin sense d’in ba....

Tafiya kawai suke a motar babu mai cewa komai sai sassanyar music dake tashi cikin radio d’in motar, Yusrah dai tuni ta shiga shafa wayarta ana zuwa layin gidansu ta sanar dashi ga yanda zata sauk’a, ga mamakinta kaw harda sallama Khalid ya mata ya saci kallon Nabila dake sallama da k’awarta tana sanar da ita ta turo mata assignment question d’in Dr Man....

Bayan Yusrah ta fice Khalid yace “Mai ya hanaki kwafa a class sai ta waya za’a turo miki...?” Yayi maganar idanunsa naga kwalta

Da gefen idanu ta dubesa kafin ta kuma kawda kai tace “Ra’ayina ne...”

“Ba tareda ya dubeta ba shima yace “Ra’ayinki kokuma kina jira ayi solving a turo miki ba...”

A kufule take dubansa kafin ta kauda kai ba tareda ta kuma cewa komai ba don ta lura shi wannan zaman lafiya ne sam baiso a rayuwarsa tanson tambayarsa yanda ya sami lambarta da yanda akai yasan sch d’insu amma tasan bazataji mai dad’i ba kuma bazatai hak’uri bata rama ba kawai ta fasa tambayan nashi, ana isowa layinsu ta hangi ‘yan islamiya nakan faman tafiya bata k’aunan suyi artabo da magulmatan ‘yan gidansu don tasan idan suka ganta motar wani shikenan zance ya karad’a gidan har ya isa ga Abbanta...

Aiko suna tana fitowa daga motar ta hangi su Basma zasu tafi islamiya kuma sarai tasan sun ganta sai juyo suke ta danna masu harara suka wuce sim sim... Kotakan Khalid bata kuma bi ba tasa kai ta shige...
Chapter 26 · 0% Book details