Sashe 185
Inda Rai Da Rabo Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Sam Kubura batasan yana tsaye wajen ba taketa zuba yawa an bud’e famfo... Kaikaitowan da zatai ta hangesa k’ame wajen yana sauraren abubuwan da take fad’i, fuskar nan nasa a murtuk’e kuwa... Tashin sense, ai Kubura batasan sanda ta had’iyi wani miyau da ya tokare mata mak’oshi ba... A daburce ta aje aikan data shigo dashi daga wajen Ammi tana mai furta “An Anty Siyama dama dama wannan na kawo... Inji Ammi ne, Wai na Anty Nabila ne...” Ta soma k’ok’arin risinawa tana gaida Khalid da ko kallo bata ishesa ba ya wane had’e rai sosai...Ai a d’ari ta fice k’afafunta har suna hard’ewa.... Siyama tabita da kallo tana dariya take fad’in “Ki dawo ki maimaita dik abinda kikace gabansa...” Ai inaa ko tsayawa Kubura batai ba suna iya jiyo yanda take sauk’a daga matakalan cikin gudu gudu tana mai fad’in ta shiga uku....
Gajeren tsaki Khalid yai kana ya ida shigowa cikin d’akin... Siyama ta dubesa tace “Haba Khalid yarinyar nan tanaji da kai amma kai ko ‘yar gaisuwan nan bata shiga tsakaninku..”
Gajeriyar tsakin ya kumayi kana yace “Toh ni sa’anta ne... Ni bansan mai ya hana Ammi maida wannan mahaukaciyar yarinyar garinsu ba, ta jima a birni amma ta kasa wayewa...”
Siyama ta d’an dara kad’an kana tace “Aiko Ammi da Kubura sai Allah.. Kubura ai ta zama d’iyar Ammi k’anwarka mai bi maka...!” Ta k’arashe teasingly...
Gajeren tsakin ya kumayi yana mai sakala hannayensa cikin aljihu lokaci guda yake jifar Sahibar tasa da wani irin duba ganin tai banza dashi tamkar batasan ya shigo ba...
Siyama ta d’an saci kallon Nabila ta kuma duban yanda Khalid ya kafeta da idanu kana ta bud’e murya tace “Wai wa yace maka ango yana ganin Amarya before akaita... Kaga ka fita kafin na kirawo maka Aunty B....”
Baice komai ba saima tsimewa da ya kumayi, lokaci guda ya kuma duban agogon dake d’aure hannunsa kana yace “Nifa idan bazaku kaita ba ne zan d’auki matata mu tafi...”
Wannan karon baki sake Siyama ke dubansa kana tace “Lallai abu ya girmama, Allah shi huci ran angon teddy bear nai maka na Kubura... Kaga Partner muke jira shi zai kaimu...”
Khalid ya d’an dubeta kad’an kana yace “Sameer fah suna tareda Daddy tuntuni downstairs... Please Siyama ki azalzala masu ku fito ku tafi, ni badon ina jiran Baffah ba da tuni na d’auketa mun tafi, I can’t wait any longer...” Ya k’arashe maganar yana zaro wayarsa cikin aljihu...
Har lokacin nan bakin Siyama a rik’e yake kana ta dubi Nabilah ta ida aika masa harara tace “Toh Nabilah kin dai ji angon naki, Kafin ya bamu kunya gaban sirikai bara naje nacewasu Aunty su fito mu tafi tinda Sameer d’in ya k’araso...”
Ita dai Nabilah batace komai ba saima sadda idanunta k’asa da tai tana mai ci gaba da aika masa harara ta k’asa k’asa....
Aiko Siyama na ficewa ta kuma d’agowa tana mai ci gaba da b’alla masa harara, tana ji yana yiwa Baffah kwatancen gidan.... Saida ya ida wayar ya tsaya yana d’an ci gaba da shafa wayar na wasu dak’ik’ai kana ya kaikaito yana dubanta yanda tasha mur sosai... Murmushi ya saki a hankali kana ya tako kad’an ya k’araso gabanta... Tinda sama har k’asa yake k’are mata kallo yanda lafaya d’in ya zauna sosai jikinta, ya mata kyau sosai tamkar dominta dama aka k’era.... Hannayenta ya kamo yana mai furtawa a hankali “Teddy bear kinyi kyau...!”
Ganin har lokacin kanta kife yake gashi tamau a murtuk’e ya sanyashi saka hannu ya d’an d’ago hab’arta kad’an, bata dubesa ba saima kauda kanta gefe da tai... K’uri yai mata yana dubanta, dan sosai ya hango k’walla tab idanun nata... Ya d’an gyara tsayuwarsa a hankali kana yace “Teddy bear aren’t you excited... Gidanmu fah zamu tafi... Finally Allah ya cika mana burinmu... Baki Farin ciki da hakan Nabeela... Ko na miki wani abu ne...?” Ya k’arashe murya a d’an raunane...
Hannu tasa tana share hawayen da suka d’an gangaro mata kana tace “Mamy nake tinani da Abbah...!”
Ya saki sassanyar murmushi a hankali cikeda tausayinta, kana ya kuma kamo hannayenta yai masu masauk’i saman sofa... Hannayensu ya sakala cikin na juna kana yaci gaba da fad’in “Yanzu ni ne Abbah kuma ni ne Mamy, I’ll take care of you kaman yanda sukeyi koma fiyeda yanda sukeyi...” Ta d’an dubesa kad’an... Jinjina mata kai yai alamun tabbatarwa kana yaci gaba da fad’in “Nasan Mamy bata goyonki toh ni har goyaki zanyi.. Yayi maki..?”
Dariya ya bata wannan karon, ta d’an dara kad’an don tasan k’ok’ari yake ya cheering d’inta up... Shigowansu Aunty Bara’atu da Aunty Daula ne ya sanya shi mik’ewa yana d’an sosa kai, yayinda Nabilar ma tai saurin matsawa Daga kusansa....
Gaisar dasu Khalid Aunty Daula sai zolayarsa take ya biyo sahun matarsa tinda sunk’i kai masa... Murmushi kawai Khalid yake har ya fice Daga d’akin bata daina zolayarsa ba...
Tuni Aunty B ta k’arasaga Nabilah da tuni ganin k’annen mahaifiyar tata ya kuma sanyata kuka... Tare suka zaunarta sukai mata nasiha mai tsuma zuciya musamman duba da iftila’ain da suka fuskanta a rayuwa gashi yau komai ya zama tarihi, Aunty B taci gaba da fad’in tabbas cikin rayuwarsu na baya akwai darasi sosai gameda alfanun hak’uri tinda taga ga yanda yau hak’urinsu ya kawosu... Mahak’urci dama ance mawadaci kuma Allah da kansa yace yana tareda masu hak’uri... Kuma shakka babu hak’uri ta kaisu ga cin nasaran rayuwa... Haka dai sukaita mata nasiha kana sukace zasu tafi su kaita gidan mijinta...
Nabilah ta kuma fashewa da Sabon kuka tana rungumar Aunty Bara’atu tana fad’in “Aunty dan Allah kada ki tafi ni dai ki barni....”
Gaba d’aya sai ta raunana masu zukata suma...
Aunty B ta d’ago fuskarta tana share mata hawayen lokaci guda take furta “Haba Nabila, Kukan nan ya isa haka... Kuma ma banda abinki ga Auntynki Daula kuna nan tare gari guda, gobe da yardar Allah nima zan d’auki hanyar Kano... Kiyi hak’uri Ki zauna kiyi biyayyawa mijinki da sirakanki kinji. Balle ma ke kika mori dangin miji, suna matuk’ar k’aunarki kuma dik auratayya ya riga ya had’a dik an zama tushe guda... Kiga dai yana Siyama ke nan nan dake yanzu daga ita har mahaifiyarta, ki gode da wannan rahama da Ubangijinki yai maki kinji... Kema Ki k’aunacesu yanda suke k’aunarki Ubangiji ya baku zaman lafiya ya azurtaku da zuri’a d’ayyiba... Mamy zatafi kowa Farin ciki idan taji yanda Allah ya sauya zukatan sirakan d’iyarta Daga k’iyayya zuwa soyayya mai tsafta...!” Ta k’arashe murmushi kwance saman fuskarta...
Murmushi Aunty Daula ma take kana ta k’araso ta rungumesu su duka uku...
Aunty B tace “Oya muje Yayanki Ma’aruf na k’asa yana jiranmu...”
Jiki a matuk’ar sanyaye Nabilah ta mik’e tabi bayan iyayen nata kanta a k’asa...
A nan parlorn k’asan suka taddasu Daddy Ammi da Kuma Sameer d’in...
Daddy ya kumayiwa Nabilah nasiha da wasilci da hak’uri sannan yace shi d’in kaman Abbanta ne babu wani surkunta, ita dasu Siyama su Ijlaal duk d’aya suke wajensa kaman yanda Sameer yake wajensa... Haka Daddy yai masu addu’a da fatan alheri Ammi ma Ta tofa nata albarkacin da fatan alheri, harda rungumar Nabilah tai mata rakiya har mota tana kuma jadadda mata dik Khalid yai mata wani abin waya kawai zata d’aga ta kirata ta sanar da ita... Su dai su Aunty Daula sai dariya suke ganin yanda Ammi ta hak’ik’ance cewa idan Khalid yaima Nabila wani abin ta kirata right away Ta sanar da ita zatai maganinsa ne... (Wayaga su Ammi mai sirka an tuba... Lol)....
Siyama na gaba, Sameer Ke driving saiko su Aunty Daula da Aunty Bara’atu da suka saka Nabila a tsakiya...
Koda suka isa gidan Aunty D da Siyama ne suka haura da suitcases d’inta sama, suka shirya mata kayan tsaf cikin sip, suka kuma gyara gidan dikda a gyaren yake.. Ko ina very need and beautiful.... Aunty B da Sameer kaw suna k’asa suna kuma yiwa Nabilah nasiha da bata hak’uri.... Sameer ya kamo hannayenta cikin nasa kana yaci gaba da fad’in “Khalid mutumin kirki ne, and he loves you very much... After all, you deserve all the happiness in this world...little sis, come here give me a hug....” Ya k’arashe yana bud’e hannayensa, cikin sauri ta k’arasa ta rungume d’an uwan nata tana hawaye...
Siyama da sauk’owarta kenan tai tsaye tana dubansu, jikinta a matuk’ar sanyaye take taji hawaye na gangaro mata... Ta d’an saka bayan hannunta ta goge hawayen... Lokaci guda Aunty Daula ta k’araso, ta isa ta d’an rik’o hannun Siyama, murmushi Siyama ta sakar mata had’ida d’aura kanta bisa kafad’ar Aunty Daula...
Idan kaga wannan ahali a halin yanzu dole su birgeka su kuma baka sha’awa... Haka suka tafi suka bar Nabilah da kewa... Ta mik’e tana bin tsarin d’akin da kallo dan kafin su tafi saida Siyama da Aunty Daula suka rakota har nata d’akin... Komai gwanin ban sha’awa... Taji wani irin sanyi mai cikeda ni’ima na ratsa dik wani k’ofa na zuciyarta... Tana nan tsaye tana faman k’arewa d’akin kallo taji alamun tsayuwar mota... Cikin sauri ta isa ta janye labulen window d’in tana lek’e... Khalid ta hango tareda Baffah.. Baffan ne yai dropping nasa dan tana ji Khalid d’in na cewa bazai shigo ba... Baffah yace a’a dare yayi gobe kafin ya wuce dai zai tsaya tinda dama mak’asudin zuwansa duba jikin Daddy ne kuma yayi abinda ya kawosa...
Khalid yai k’wafa a hankali kana yace “Dama kanada mutunci ne... Idan kaga dama goben ma kai tafiyarka kada ka tsaya dan Allah...”