← Book details Inda Rai Da Rabo Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 126 OF 198

Sashe 126

Inda Rai Da Rabo Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Babba Duna ya tako gabansa kad’an yana mai k’arewa Hafiz duba lokaci guda yake furta “A wannan daji babu wanda ya isa ya fice bada izinin Babba Duna ba muddin ya riga ya shigo fadar Babba toh fah saida amincewarsa ya fice, zaman daji saida shiri pretty boy...”
Tin bayan shigowarsu dajin sai sannan Hafiz ya saki murmushi, tabbas yanaji har cikin ransa Zulfah ta dawo gareshi an gama babu wanda zai kuma shan gabansa....
Koda sukazo ficewa rasa hanya sukai kaman yanda Babba Duna yace, har saida akai masu jagora suka sami hanya,... Wannan dalili yasa suke lak’abi wa Dajin da Fadar Babba Duna,domin kaw dajin kewaye take da shirinsa, hakan yasa ba’a iya kamashi tsawon shekarun da yai yana ta’addanci... Sannan hakan yasa yai k’aurin suna ya shahara a fannin garkuwa da d’anadam....
(Ya Allah ka kawo mana k’arshen wannan ta’addanci ya addabi k’asarmu ya zamto ruwan dare, Allah karka barmu da wayonmu Allah ka kawo mana d’auki Albarkan Annabi d’an gatanka ya Allah) Ameen thumma Ameen..!
***

Muhibbah dake zaune tsakiyar parlor sai faman murmushi take tana ayyanawa cikin zuciyarta yanda Engr zaiji idan yaji labarin auren masoyiyarsa da Babban yaronsa Akram.... Dole ma itace zatai masa breaking wannan news d’in taga kalan reaction d’insa... Babu boka babu Malam babu tashin hankali auren mijinta bazai yuwu ba... Ta kuma murmusawa tana juya glass cup d’in dake hannunta wanda a ido juice ne amma a zahirin gaskiya k’wayoyin maye ne a ciki....
Lokaci guda ya mik’e tana jin kanta a sararin samaniya duniyar na mata dad’i... Takawa ta dingayi har ta isa jikin tapkeken hoton Engr, a hankali ta shiga shafwa tana mai murmusawa “I can’t wait to see your face idan labarin cin amanarda amintaccenka yai maka ya riskeka..... Wannan kyakkyawan murmushi dake bisa fuskarka nasan zai gushe... Sannan babu mai kuma dawo maka da wannan murmushi sai ni Muhibbah... Your one and only wife... You must accept the fact that your home is right here with me...!!!” Ta k’arashe tana mai kuma tintsirewa da dariya tamkar mai tab’in hankali... Cikin tafiya datafi kama da tangad’i take takowa har ta zube saman kujera.. Nan bacci yai gaba da ita... A haka yaran nata suka shigo dawowarsu kenan daga islamiyya suka tadda Mahaifiyarsu nan kwance, idan da sabo hakan yabi jikinsu kasancewar dama tin can basa samun kulawa daga wajenta sunma fi sabo da Murja wacce duk wani d’awainiya da mahaifiya kema d’anta ita take masu...
Murja ta k’urama yaran idanu cikeda tausayawa yanda sukai tsaye suna duban mahaifiyarsu, waima gwamma yanzu suna iya ganin nata, a baya sai su shafe kwanaki basu sakata idanunsu ba, Murja ta k’arasa ta rik’o yaran tana mai saka murmushi saman fuskarta take fad’in “Muje ku canza kayan makaranta kunga Mummy na bacci...” Yaran basu ce komai ba Irfaan ya soma shigewa yayinda Samha ta take masa baya, tabbas murja k’ok’arinta kawai take amma ta sani izuwa wannan lokaci yaran sun soma gane abu tinda sun soma girma... Haka sanda sukaje Abuja gidan Aunty Daula kwanakin baya kaman kar su dawo yanda Aunty Daula Ke nuna masu zallan k’auna irin wanda basu samu daga mahaifiyarsu ba, dan ma Allah yasa mahaifinsu na matuk’ar nuna masu k’auna da kulawa...

***

A can gidan Aunty Bara’atu ake gyaran amaren, sanda Bikin ya rage saura sati biyu dama ta tafi dasu can gidan nata, tuni Zulfa’u ta d’auki hutun wajen aiki yayinda Nabila ce kawai ke ficewa makaranta itama sabida exam ne da suke rubutawa wanda daga shi sai tafiya Industrial training da muke saka ran zatai a garin mijinta da yardar Allah... Sam Aunty Bara’atu bata barinta ta fice ba tareda makarin rufe fuska ba nik’ab, idan Kaga amaren dole Kaso sake kallonsu yanda sukai kyau fatarsu ta kuma murjewa tai santsi alamun suna samun gyara da kulawa na musamman, yaran Aunty Bara’atu kenan, aima dole susha gyara ciki da waje, gyara mai tsafta da babu cutarwa cikinta babu kuma algus...
Yauma dai wani dahuwar kazar Aunty Bara’atu ta shigowa Zulfa’u dashi sanda aka ida mata halawa, sai faman ture turen baki take tana fad’in ita ta gaji da wannan tsirface tsirfacen abubuwan da ko a auren fari ba’ai mata su ba....
Aunty dai jinjina kai tai tace “Na dai ji amma sai kin cinye tas kin shanye roman nan, kinsan ance idan kanada kyau k’ara da wanka...”
Atika na gefe sai k’ek’yata dariyarsu take tana fad’in “Allah dai ya bar mana ke Auntynmu....”
Zulfah kaw saidai ta gallawa Atika harara dan ita ke ziga Aunty Bara’atu a cewarta....
Aunty ta dubi Atika dake gefe tana darawa kana tace “Ki tabbata ta cinye bara naje Ina zuwa...”
Batakai aya ba Atika ta bata amsada “An gama Auntynmu...”
Zulfah ta galla mata harara had’ida yin k’wafa...
Matsowa kusanta Atika tai tana kuma k’ek’yata dariya take fad’in “Aaa gaskiya dole Yaya na Akram ya k’aro sadaki Anty ta gama masa komai....”
Duka Zulfah ta d’aka mata a cinya tana fad’in “Kedai Allah ya shiryaki... Mutum abinda ya iya kenan jin baki...”
Atika ta kuma darawa tace “Allah huci ran amaryar yayana Akrami....” Murmusawa kurum Zulfah tai amma ita kanta batasan meke damunta ba dan gaba d’aya ji take maraban auren da aurenta na fari k’alilan ne, dan idan tace tana k’aunar Akram tayi k’arya, tsakani da Allah bata tab’a jin sonsa a ranta ba saidai batasan dalilin da yasa ta amsa ma auren nasa ba, k’ila sabida azalzalawa da Baba Alhaji da d’ansa Hafiz sukai mata ne... Sauk’e nannauyan ajiyan zuciya tai tana bin sangalalin k’afafunta da kallo yanda suketa faman shek’i da d’aukan idanu alamun sunsha dilka da halawa... A hanakli ta furta “Allah kaine masanin maiyasa abubuwa suke faruwa yanda suke faruwa, Ya Allah lamurana suna hannunka... Ya ka zamto majib’incinsu...” lokaci guda taji ta samu natsuwa da wannan addu’a.... Gama addu’anta keda wuya wayarta dake jikin socket yai alamun k’aran shigowar sak’o... Hakan ya haifar mata da fad’uwan gaba ba kowa ya fad’o ranta ba illa Mr Unknown....
***
A can makaranta kaw su Nabilah suna fitowa daga exams aka dami Yusrah da kira, gashi dai da alama bata son amsa kiran ne gaban Nabilar... Nabila ta fahimci hakan dan tin fitowarsu a first paper kafin su shiga second paper Yusra Ke k’usk’us a waya... Har suka isa masallaci kira ake Yusrah na sakata a silent.... Nabila kaw yi tai tamkar bata a wajen saima duba question paper d’in jarabawar da suka fito take... Sanda Yusrah ta tafi alwala ta bar wayar saman jakanta gefen Nabilar kasancewar ita Nabilar ba sallar zatai ba shisa ta zauna daga gefen masallacin tana kuma duba takardanta, kaman daga sama wayar Yusrah ya kuma ruri... Kai dubantaga jakan tai lokaci guda ta janyo jakan zata d’au wayar... A d’ari Yusrah ta k’araso ta fuzge jakanta tana fad’in “Nifa banson sa ido...”
Harara kurum Nabilah Ke galla mata kana tai k’wafa tace “Kici gaba, ce miki akai bana lura dake ne a ‘yan kwanakin nan... Sarai nasan akwai abinda kike b’oyemin, kema hardake a shirye shiryen wannan auren munafuncin da ake shiryawa koh... Toh kici gaba Allah ya baki sa’a, dan Allah karki fasa...”
Yusrah na darawa kad’an take fad’in “Haba tawan kema kinsan bazan miki haka ba, dik abinda zai faranta miki shi nakeyi... Haba amaryar oga Bear..”
“Mtsww.. Ke kika sani kuma...” Ta fad’i tana mai aika mata muguwar kallo...
Yusrah ya dara had’ida mik’ewa tana mai ci gaba da fad’in “A daina cika mana baki dai munsan anaso ana kaiwa kasuwa....”
Ko tankata Nabilah bata sami zarafin yi ba, har yanzu ta kasa daina tinanin Wai Khalid baiko kirata ba har wayarta ta lalace ta kuma gyara duk bai nemeta ba... Anya wannan aure mai yuwa ne kuwa... Anya ba ramuwar wulak’anci data masa Farin had’uwarsu yai niyyan mata ba, idan ba haka ba ita ko a wasan kwaikwayo bata tab’ajin labarin ango irin Khalid ba... Takaicin kanta dana Khalid d’in ya kuma cika mata zuciya...
Batai wani gayya ba itakam, harta coursemates d’insu ma ba ita ta basu katin gayyata ba Yusrah ce duk tai wannan, suma ba duka ta bari Yusran ta gayyata ba, daga su Safwan da Al’amin saiko tsiraru cikin matan wad’anda suke mutunci....

***

Yusuf ya mik’e tsaye yana duban mamakiwa abokin nasa....
“Ban gane ba Akram... Toh Wai kana nufin har yanzu invitation card bai isa hannun his Excellency ba...?”
Chapter 126 · 0% Book details