← Book details Inda Rai Da Rabo Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 79 OF 198

Sashe 79

Inda Rai Da Rabo Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Khalid ya had’iyi miyau da k’yar kana yace “Daddy hak’uri na dawo na baku, na sani abinda nayi ban kyauta ba... Bazan iya fad’a daku ba cos you’re my parents... I’m sorry Daddy and na yarda na amince zan karb’i zab’inku ma’ana na amince da auren Yesmin....”
Cikeda tsananin mamaki Ammi ta d’ago tana dubansa, shi kansa Daddyn duban mamaki yake masa...
Daddy ya gyara zama sosai kana yace “Ka tabbata da abinda kake fad’i...?”
Khalid yai k’arfin halin jinjina kai kana yace “Eh Daddy na tabbata...”

Alhaji Mainasara yace “Good...” Caraf Ammi ta cab’i zancen da fad’in “Ni dama nasan yarona mai biyayya ne kawai dai wancan watsetsiyar yarinyarce taso brainwashing d’insa...”
Wani duba Khalid ya mata kana yace “Ammi please ki cire Nabilah a batun nan, ku k’yaleta haka tinda nayi abinda kuke so, nima kuyi abinda nakeso ku barta haka kedasu Siyama please...”
Harara ta watsa masa kana ta mik’e cikeda murna tana fad’in dole taje taiwasu Yesmin da Siyama wannan albishir...
Daddy ya bita da kallo har ta fice kafin ya maido da dubansaga Khalid... Gyara zamansa ya kumayi had’ida d’an gyaran murya kana yace “Saifullah ka tabbata zakabi umarninmu...?”

Ya jinjina kai a hankali kana yace “In sha Allah Daddy.... fatana shine ku yafemin d’aga muku murya da bijire maku da nayi a baya....”

Nan ma jinjina kai kana yace “Babu damuwa ni dama nasan kanada biyayya da sannu rana irinta yau zatazo... Na yafe maka tuntuni, Allah ya maka albarka....”
A hankali ya amsada Ameen Daddy, suka d’an tab’a hiran company kad’an Daddy nata k’ok’arin shan cikinsa yaji ko don tak’ura da talauci ne yasa shi ya dawo yayi nadama amma shiru baiji hakan ba... Har saida Khalid d’in ya mik’e zai fice kana ya dakatar dashi da fad’in “You can now have access to your bank accounts... Ga sauran credit cards d’inka a drawer a can ka d’auka.... Sannan zaka iya komawa company office d’inka right away...”

Khalid ya jinjina kai yace “Na gode Daddy....” Ya d’anja fasali kad’an kafin ya dawo da baya ya kuma risinawa yace “Daddy banso ka dubi wannan da wata manufa... But to be honest with you.... I’ll like to resign from the company.... Zan applying neman aiki a wani wajen... Bawai don wani abin ba sai don Kawai inaso na zama independent ne.... I hope you’ll understand me Daddy...”

Shiru Daddy yayi na wasu ‘yan dak’ikai kana ya sauk’e ajiyan zuciya yace “Khalid ban fitar dakai waje karatu don ka dawo kayi aiki ma wasu ba sai don watarana ka zamto ka rik’e abinda zan bar maku koda bani a raye, domin kaw kai zaka gajeni a company d’in... Amma idan haka ka zab’a babu matsala ni zan sama maka aikin in sha Allah....”
Khalid ya d’anyi jim kana yace “Daddy dama dai da so samune na nemi aikin da kaina ba tareda taimakonka ba please.... I hope that’s ok with you...”
Shiru na d’an lokaci kana ya jinjina kai yace “Alright if that’s what you want... Bakada matsala dani, Ubangiji ya taimaka... Amma ka sani ko yaushe kaji kana son dawowa company d’in mahaifinka the door’s always open kaji koh....”
Ya jinjina kai a hankali kafin yayi sallama wa mahaifin nasa ya fice....

***

Abbah ya gama jin bayanan Aunty B tsaf kana yace “Bara’atu ba nak’i maki bane amma abinda Nabilah ta aikata sam ba daidai bane kuma ba tarbiyan gidan nan bane.... Mai amfanin wayar hannunta da ko mahaifiyarta bazata kira ta sanar da ita taje gidanki ba... Maima zaisa daga makaranta ta shige can gidan naki... Shin makaranta tace zataje kokuwa gidanki...?” Cikin kakkausar harshe yake maganan...
Aunty B ta kuma cewa ai hak’uri Abbah hakan bazata sake faruwa ba in sha Allahu.....
Kan Nabilah na k’asa ta kasa furta komai sai faman rakub’e rakub’e take.... Ita koh Aunty Lami idanunta k’yam kansu don bata yarda iyakacin gaskiyar ba kenan...
Daga parlorn Abbah acan sashen Mamy ma fad’a taitayi, daga Nabilar har Aunty B d’in bata k’yale kowa cikinsu ba....
Ita kaw Aunty Lami sad’ad’awa tai tabi bayansu don jin yanda zasu kaya da Mamy....
Aunty B da taga fad’an tai yawa da alama sosai ran Mamy ya b’aci don har tafi Abban nasu d’aukan zafi...
Gyara murya tai tace “Gidan Yaya Abida na kaita...”

Gaban Mamy ya yanke ya fad’i don rabonta da taji an ambaci wannan suna ta mance.....
Ta d’ago tana duban Aunty B d’in..... Aunty B ta jinjina kai alamun tabbatarwa....
Zulfa’u ma duban Aunty B d’in take lokaci guda k’irjinta na bugawa yayinda Marliya da Nabilah suka rasa gane wacece Yaya Abida.....
Ita kaw Aunty Lami dake lab’e jikin k’yaure dafe k’irjinta tai da duka hannayenta biyu.... Lokaci guda k’afafunta suka d’auki rawa.... Cikin sauri ta shiga jada baya da baya zuciyarta bai daina yankewa ba...

SameenaAleeyou 📚

*INDA RAI*
_................DA RABO_

*64*

*©️Sameena Aleeyou...✍🏼*

Mamy tai shiru ba tareda ta kuma cewa komai ba, Zulfa’u ce ta janyo hannayen k’annenta suka shige suka barwa Mamy da Aunty Bara’atu parlorn domin su tattauna....
Mamy ta kuma duban Aunty B kana tace “Gidan Yaya Abidah... Maiyasa kika kai Nabilah....?”
Aunty Bara’atu tai shiru na wasu dak’ik’ai kana tace “Na fad’a maki dama INDA RAI sai nayi silan k’ulla zumuncin da ya riga ya wargaje a baya, koda hakan zai zama k’arshen abinda zan k’ulla kenan a duniya....”

Nan ma shiru Mamyn tai batace komai ba sai duban Bara’atun da tayi, lokaci guda ta koma ta zauna cikin kujera jikinta a mace....
Ganin haka yasa Aunty B zama daga can kujeran gefenta....

A can d’aki kuwa Nabilah da Marliya ne suka tsare Addarsu Zulfa’u da tambayan wacece Yaya Abidah....
Marliya tace “Dama Mamy tanada wata ‘yaruwa shine bamu santa ba, koda wasa ko a labari bamu tab’a jinta ba....”
Dafata Zulfa’u tai kana tace “Marliya har abada babu sirrin da zai tabbata a rufe, a iya sanina shekarun baya can lokacin nima banida wayo sosai mukanje gidanta da Mamy, rana tsaka muka daina zuwa kuma koda na tambayi Mamy sai cemin tai Yaya Abida ta mutu bata raye, idan nai mata batunta sai tacemin ko sunanta kada na kuma ambata, ni kaina na mance da ita sai yanzu da naji Aunty Bara’atu na cewa gidanta sukaje da Nabilah.... Tabbas ni kaina nawa kan ya d’aure akwai wani sark’akk’iyar al’amari dake faruwa wanda iyayenmu basu fayyace mana ba....”
Marliya ta jinjina kai a hankali kana tace “Toh ko maiyasa Mamy tace ta mutu...? Maiyasa suka datse zumuncinsu...? Maiyasa bamusan da ita ba...?” A tare ta jero duka wad’annan Tambayoyin.....

Sauk’e ajiyan zuciya Zulfa’u tai kana tace “Mamy ce kawai zata iya bamu wad’annan amsoshin......” Tai maganar tana mai lulawa duniyar tunani...
Itakaw Nabilah gaba d’aya ba saurarensu take ba, hankalinta yafi karkata kan halin data baro Khalid ciki... Shikenan sun rabu rabuwa ta har abada....Anya tayi adalci ma kanta..? Anya hukuncin data yanke tai daidai ma zuciyarta da ruhinta...? Toh amma hakan shine daidaima Khalid, hanyar daya d’auka a baya bamai b’ullewa bane, ta gwammaci ta sadaukar da farin cikinta kan taga rayuwar mutum guda tak data tab’a so ya tagayyara.... Ta lumshe idanunta a hankali had’ida jingine kanta da ya mata nauyi jikin gado....

***
Mamy taci gaba da fad’in “Maiyasa kika d’auki Nabilah kika kaita wajen matar da kinsan cewa ta jima da mutuwa a babin rayuwata da iyalaina.... Maiyasa kike son tono abinda ya jima a rufe... Bara’atu maiyasa kike son dawowa da jiya yau....” Cikin tsananin rawar murya tai maganar...

Aunty B na hawaye ta taso ta durk’usa gaban Mamy had’ida rik’e hannayenta lokaci guda take furta “Wasu sirrikan suke bud’e kansu... Wasu sirrikan basu yarda su dawwama a rufe.... Ki sani’yar uwata ina sonki, ina k’aunarki ko mai zaije yazo, and I’ll forever be here for you.....” Ta k’arashe cikin tsananin rawar murya.... Lokaci guda suka rungume juna suna hawaye... Suna a haka wayar Mamy ya d’auki ruri, Sameer ne mai kirant, gaisawa sukai yanda Mamyn ta jisa a d’an birkice, tana tambayarsa ko zai shigo gidan ne kafin ya shige can gidansa sai ce mata yayi “A’a Mamy, ina asibiti dai tukuna...”

Mamy tasa yatsa tana goge hawayen da suka mak’ale mata had’ida gyara zama sosai kana tace “Toh... Lafiya amma...?”

Sameer ya d’an shafi sumarsa yace “Mamy Hafiz muka kawo asibiti ya d’an sami had’arin mota... But he’s out of danger now.. Amma dai bai farfad’o ba...”
Mamy ta mik’e tana furta “Subhanallahi, wani asibitin kuke Sameer.... Ka kira su can gidansu Hajiyar tasa...?”

Sameer ya sanar da ita asibitin da suke kana ya k’arada “A’a ban kirasu ba kece kawai na kira...”
“Toh shikenan, gamu nan zuwa zan sanar da Abban naka yanzu, zai kira Alhajin ya sanar dashi...”
Sameer ya amsada “Ok Mamy sai kunzo....” Sukai sallama kana ya katse kiran yana mai duban Shamsu da ya tallafi fuska da hannaye bibbiyu yana dubansa...

Jin Mamy tana fad’i ma Aunty B yanda sukaida Sameer d’in cewa Hafiz ne babu lafiya ya sami had’arin mota yana can asibiti yasa gaban Zulfa’u mugun fad’uwa... Cikin sauri ta d’aga labulen d’akin ta fito, fuska d’aukeda tashin hankali take ceda Mamy zata asibitin itama...

Aunty B ta galla mata harara kana tace “Kije ina...? Kije ki masa mai... Iyakaci addu’ace ince...? Toh ki masa ita daga nan....”
Idanun Zulfa’u sukai raurau... Ta kasa furta komai sai sadda idanun nata k’asa da tai....
Tuni Mamy ta fice sashen Abbah Aunty B ta mara mata baya... Aka bar Zulfah tsaye wajen tana kokonton halinda Hafiz ka iya kasancewa ciki... Marliya ta dafata kad’an kana ta kamo hannunta ta zaunar saman kujera, har lokacin Zulfah bata dawo daidai ba, mutuwar Kausar ya dawo mata sabo... Gani take kaman shima Hafiz d’in mutuwa zaiyi... Shikenan duk sun tafi sun barta... Bazatace ga abinda takeji gameda Hafiz ba amma can k’asan zuciyarta tanajin wani irin rauni had’ida tausayin kanta... Ta lumshe idanunta a hankali sanda ta tsinci zuciyarta na addu’an samun sauk’iga Hafiz... Mutumin da ya d’aid’aita mata rayuwa ya tagayyara....

***
Chapter 79 · 0% Book details