← Book details Inda Rai Da Rabo Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 164 OF 198

Sashe 164

Inda Rai Da Rabo Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Muhibbah tana isowa tai parking ta kutsa cikin gidan tagajan magajan tamkar mahaukaciya sabuwar kamu... Gudu gudu ta fad’a cikin gidan tana fad’in a fito mata da yaranta, sauk’in abin yaran duk basu nan sun tafi makaranta.... Zulfah da ida sallan walharta kenan ta soma jiyo wannan hayaniya, ai babu shiri ta mik’e ta shiga linke sallayar kana ta nufo parlor..... Kicib’is sukaida Muhibba dake faman huci tamkar wata zakanya.....Gaban Zulfa’u ya yanke ya fad’i dan sosai ta razana da ganin yanayin matar Engr.... Muhibbah tai birki tana k’are mata kallo daga sama har k’asa... Lokaci guda ta tintsire da dariya tana mai ci gaba da nuna Zulfa’u take fad’in “Ki jibeki... Ke har kin isa Ki jera dani....” Ta kuma yin k’asaitaccen murmushi tana jijjiga lokaci guda take furta “Allah wadan mijina ya rasa macen da zai d’aura idanu a kanta saike...? What a low taste of him...! Bari kiji na fad’a miki bana saudakar da fad’a cikin sauk’i, wllhi sai kinyi da kinsanin auremin miji da kikai... Gayyan matsiyata, ina yarana...!!” Ta k’arashe tana daka tsawa wanda ya sanya Zulfa’u d’an zabura kad’an dan ko iya amsata batai ba tama kasa.... Harga Allah ita bata k’aunan wani tashin hankali a halin yanzu....
Muhibbah ta kuma darara mata tsawa “Nace ina yarana ko bakiji bane... Munafuka algunguma kin wani tsaya kina k’are min kallo.....!”

Muryar Ammah ce ya katsesu da fad’in “Zulfa’u Zo Ki wuce ciki abinki, k’yaleni da ita....”
Zulfah ta d’ago idanunta da sukai raurau tana duban Ammah... Muhibbah kaw gyara tsayuwarta ta kumayi tana mai aikawa Ammah walak’antacciyar kallo....
Ammah ta k’araso gareta tana mai dubanta babu alamun wasa a tattare da ita.... “Ga dikkan alamun baki sami wadatacciyar tarbiya ba.... Allah kad’ai yasan kalan hak’urin da Ma’aruf yai dake...”

Muhibbah dake faman yatsina tana aika mata muguwar kallo tace “Baiwar Allah bakisanni ba so zaifi kyau idan baki katsalandan cikin rayuwata ba... Bar gani kin zama mahaifiyar Ma’aruf rana tsaka ni nan da kike gani nice Ma’aruf, na bashi kulawar da baki ba , dan haka har abada bazaki tab’a zama mahaifiyarsa a idanuna ba.... Dan ko shakka babu k’aryar banza ce wan....!” Batakai aya ba taji sauk’an wata jahilar mari a kumatunta wanda ya haifar mata da d’aukewar ganinta lokaci guda.... Wayoyin kanta gaba d’aya taji suna spark...
Ta saki ihu tana mai kame k’uncinta, lokaci guda ta d’ago tana lalumen waye ya wanketa da irin wannan mari da tsawon rayuwarta babu wanda ya tab’a mata... Ido hud’u sukai da Engr da bai jima da shigowa ba....
“Excellency na kan wannan matar da baka jima da sani ba ka mareni...” Nan ma bata kai aya ba ya kuma wanketa da wata marin maiji da lafiya wanda ya kusa kurmatata...
Muhibbah dake dubansa da tsananin mamaki dafe da k’uncinta take fad’in “Excellency na... Yanzu marina ka kuma yi kan wan.....” Marin ya kuma watso mata Ammah tai saurin rik’e hannunsa banda sakin wani irin huci mai tiriri baya komai....
Ammah taci gaba da fad’in “K’yaleta haka Ma’aruf... Ba halinka bane dukan mace.... Lusarin namiji shike dukan mace....”

Engr dake tsananin turiri ga idanunsa da suka kad’a sukai jazir fad’i yake “Ammah Ki k’yaleni na bata abinda na kasa bata tsawon shekarun nan.....” Ya kuma maida dubansaga Muhibbah dake tsaye sororo dafe da k’uncinta cikin rashin yarda da abinda take gani Wai yau ita Ma’aruf ke mari haka mutumin da tsawa mai tsanani ma bai mata idan ba ta b’aci ba, iyakaci ta b’ata masa rai saidai ya bata space na kwana biyu amma yau shike wanketa da wasu irin bahagwayen tagwayen maruka...
Maidoda dubansaga Muhibbah ya kumayi kana yaci gaba da fad’in “For years ina tolerating d’inki, knowing cewa Ke d’in amanace a hannuna... Muhibbah gaba d’aya shekarun nan nayisu ne ina hak’uri dake ba don komai ba sai dan na cika ma Baba burinsa da kuma alk’awarin da na d’aukar masa... Allah shine shaidana... I’ve never loved you, but na zab’i na zauna dake nai hak’uri da duk wasu halayyanki marassa kyau... Only to get this in return....? How dare you zaki bud’e baki kice zaki aibanta mahaifiyata .... Ke har kin isa...? Dik rashin kunyarki akaina naji nayi tolerating.... But to my own mother... kinyi k’arya.... No Muhibbah baki isa ba.... Kije dik yanda zaki je I’ll not stop you.... Amma abu guda da nakeso ki sani bazaki d’auki d’aya daga cikin yarana ba.... Ki tafi dik yanda zaki tafi... If you like go to hell... Amma bazaki tafi da one of my children ba... Since when ma kika fara k’aunarsu... Stupid Kawai.... Now get out... Get... the... hell out of here!!!” Ya k’arashe cikin tsananin daka tsawa yana mai nuna mata k’ofa hawayen zafin rai na tsartowa daga idanunsa....

Kallon mamaki take binsa dashi kana tace “Ma’aruf ni kake kora daga rayuwarka kamar wata bola... Ma’aruf ni Muhibbah amanar Baba kake kora... Ma’aruf Rana d’aya ka watsar da dik shekarun da mukai tare ka zab’e mutanen da ka sansu rana tsaka..”
A zuciye ya kuma cewa “Ki fita nace before I lost control..!!!!”

Tsawan da saida ya sanya Muhibbah jada baya cikeda firgici... Ita kanta Zulfa’u dake rakub’e daga baya saida ta firgita da ganin wannan yanayi nasa, cikin ranta take ayyana lallai b’acin ransa baida kyau....

Muhibbah na hawaye tasa kai Ta fice cikin sauri tamkar zata kife k’asa, lokaci guda ta juyo tana dubansu gaba d’aya kana ta murmusa tace “This isn’t over Ma’aruf... This is far from over... Wllhi wllhi I’ll ruin you.... I’ll take you down to the ground... Mark my words...!!” Daga haka sa kai tai ta fice a guje tana kuma cazgan kuka mai tsuma zuciya....

Engr kaw tsuka ya buga cikeda b’acin rai yake furta “Pesky Idiot...!!” Lokaci guda ya zaro wayarsa ya d’an fice ya shiga neman layin makarantar yaransa dan ya sanar dasu koda wasa kar su bada yaransa ma wannan mahaukaciyar ko taje d’aukansu....

Zulfah Ta K’araso da sauri ta kama Ammah had’ida zaunarta saman kujera, tai saurin nufan dispense ta taro mata ruwa ta kawo mata... Ammah ta amsa tana mai saka mata albarka.... Jim kad’an Engr ya shigo dik ransa a Jagule yake, Zulfah ta d’an saci kallonsa kana ta mik’e ta basu waje shida mahaifiyarsa... Kallo ya bita dashi har ta shige kafin ya maidoda hankalinsa ga mahaifiyarsa....
Murya can k’asa ya soma fad’in “Ammah kiyi hak’uri dan Allah... Wllhi da ace nasan Muhibbah zatazo har cikin gidan nan ta aibataki da na jima da rabuwa da ita tin kafin zuwan wannan rana....”

Girgiza kai kad’an tai kana tace “Kada ka bata takarda Ma’aruf... Kai hak’uri zafin kishi ne kawai ya sanyata yin hakan amma zata sauk’o zata shiryu in sha Allahu... Ko dan albarkacin yaranta kai mata afuwa...”

Da tsananin mamaki yake duban mahaifiyar tasa kana yace “Ammah ta ya zan iya ci gaba da zama da matarda batasan darajan iyayena ba... Ta ya zanci gaba da zama da matarda bata baiwa mahaifiyata kimanta da darajanta ba... Ammah darajarki da kimarki ya wuce haka a gareni....”

Ammah ya kuma jinjina kai kana tace “Sanin inada wannan daraja da kima a wajenka yasa nace kai hak’uri karka bata takarda, da sauk’o da kanta dik yanda zataje kaji koh... Kai hak’uri Ma’aruf... Ka k’ara akan wanda kake... Idan zuciya ya b’aci ba’a yanke hukunci cikin b’acin rai kaji koh..”
A hankali yake jinjina kai yana amsa mahaifiyar tasa dikda zuciyarsa dake matuk’ar masa zafi...
Ammah tace “Allah shi maka Albarka ya shiga lamuranka...!”
Ya amsa da Ameen Ammah... A hankali...
Shiru ne ya d’an ratsa tsakani kana Engr ya d’anyi gyaran murya yace “Ni kaw Ammah ina son tambayarki dangin Abbah na... Naga babu wanda ya tab’a koda lek’owa....”

Sauk’e ajiyan zuciya tai kana tace “Tin lokacin da mahaifinka ya rasu suka kwashe dukiyarsa sukai tafiyarsu ban kuma ganinsu ba, a cewarsu ni nai ajalinsa na kuma salwantar dakai dan naci dukiyarsa.... Basu kuma waiwayata ba har rana mai kaman ta yau...!” Ta k’arashe tana mai goge hawayen da suka d’igo mata...
Engr ya d’an matso kusanta kad’an had’ida kamo hannayenta, cikeda tausayin qalubalen rayuwa da mahaifiyar tasa ta fuskanta yake furta “You’ve went through a lot Ammah na.....!”
Ta saki murmushin k’arfin hali tana mai dafe fuskarsa take furta “Dik ya zama labari yanzun... Allah ya maido min dakai abinda yafi duk wata dukiya da zasu d’iba.... Kuma da ya tashi dawo min dakai sai ya dawo min harda dik wasu ahalina da na rasa a baya kuma kaima har ka hayyafa kayi Naka ahalin....Na gode ma Ubangiji na da wannan rahama a gareni...!”

Ya saki murmushi a hankali zuciyarsa nai masa sanyi kana yace “Haka ne Ammah na... Ahali shine gaba da komai... Ubangiji ya kuma had’e kawunanmu da alkhairi...!” Ammah ta amsada Ameen sassanyar murmushi saman fuskarta.... Daga wajen Ammah mik’ewa yai ya nufi d’akin Zulfa’u dan itama Amman kitchen ta shige duba Hajjah wacce take tamkar K’awa a gareta....

****
Chapter 164 · 0% Book details