← Book details Inda Rai Da Rabo Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 125 OF 198

Sashe 125

Inda Rai Da Rabo Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

A yayinda biki ya rage saura sati guda Sawwama da Hafiz suka isa territory d’in gungun ‘yan iskan...Tafiyar kusan awanni uku ya kwashe su daga gari zuwa cikin dajin ...
Sawwama ta juyo ta dubesa kana tace “Ka tabbatar da abinda kake shirin yi...? Ka shirya mu shiga...?”
Jinjina mata kai yai “I was born ready...”
Sawwama ta murmusa kana tace “Wannan itace Fadar Babba Duna... Shugaban duk wani wanda yai k’auri a fannin garkuwa da Bil’adama a k’asar nan, rashin imanin Babbba Duna ya wuce dik yanda kake tunani, cire kan d’an adam a wajensa ba komai bane... Biyoni muje....”
Hafiz dai sai waige waige yake yana duban k’ungurumin dajin da suka shigo had’ida mamakin ina Sawwama tasan irin wad’annan mutane...

SameenaAleeyou📚

*INDA RAI*
_...............DA RABO_

*85*

*©️Sameena Aleeyou...✍🏽*

Wane irin sunk’urumin daji ne da baka jin sautin komai sai kukan tsintsaye, kallo guda zakaiwa Hafiz ka fahimci tsananin tsoro dake tattareda shi, dole ne yai hakan bashida wani zab’i muddin yin hakan zaisa matarsa Zulfa’u ta dawo garesa... Ganin dai bazasu daina kutsa cikin dajin nan ba ya sanyashi janyo hannun Sawwama dake gaba dashi da saurin gaske, cikin k’asa k’asa da murya tamkar mai tsoron kada wani yaji abinda zai fad’i yace “Ke dakata... Wai har yanzu nufinki bamu iso wajen Babba Duna ba, ko kina nufin kice sai munga k’arshen dajin nan ne....? I thought you said mun iso fadarsa... Toh ina Fadar take...”
Murmusawa tai da gefen baki kana tace “Dad’ina dakai saurin karaya saikace ba namiji ba.... Toh banda abinka da nace maka mun iso Fadar Babba Duna ai gabaki d’aya katafarin Dajin nan shi yake mulka... Wai tsaya ka canza zuciyarka ne...? Idan ka canza zuciyarka ne shikenan sai Mu koma....”

Numfasawa Hafiz yai yana mai kame kunkuminsa, shayeda tsananin mamaki yake dubanta “Mamaki nake ina kika san irin wad’annan gaggan ‘yantaddan...?”

K’asaitaccen murmushi Sawwama tai tana mai aika masa duban kama rainani kana tace “Wai da da nace maka inada makullin cin nasararka a hannuna ka zaci wasa nake...?”
Girgiza kai Hafiz yai kaman d’alibi gaban malaminsa kana yace “Ni duk a tunanina ‘Yaniskan cikin gari kike magana ba manyan ‘yan fashi da makami ba....”
Ta kuma murmusawa had’ida gyara tsayuwarta “Bana huld’a da k’anan ‘yan iska.... Biyoni muje...”
Fuzar da iska yai yana mai kuma bin dajin da kallo lokaci guda yake biyeda ita, wasu mutane guda biyu suka soma hangowa jikin wata bishiyar gamji mai tsananin duhuwa ko wannen su rungume da manya manyan bindigogi, murtuk’a murtuk’an mutane bak’ak’e k’irin dasu, haka nan k’wayan idanunsu jajazir babu alamun annuri ko rahama a tattaredasu....
Daga can gefe gefe tsinta tsinta suna hango mutane jifa jifa suma duka rik’e suke da makaman yak’i... Hafiz ya had’iyi miyau da k’yar dan shi zai iya rantsuwa bai tab’a ganin bindiga ido da ido tsirarta ba sai yau da Sawwama ta kawosa wannan waje.... Abinda yake gani a finafinai gashi na faruwa a karan kansa...
Koda suka iso saida mutum guda ya cajesu tsaf kafin ya nuna masu saman wata Dutse yace su jira acan... Babu musu suka k’arasa suka zauna, hankalin Hafiz dai dik ba’a kwance ba yayinda Sawwama ko ajikinta saima taunar chewing gum d’inta take...
Hafiz banda Uwar harara bai aika mata komai, yana ayyanawa cikin zuciyarsa lallai babban kilaki ya aura a matsayin mata... D’an dubansa tai taga yana faman watsa mata muguwar kallo....
Tab’e baki tai kad’an kana tace “Ya dai lafiya ko wani abin ka gani...?”
Girgiza kai Hafiz yai yana mai kuma dubanta kana yace “Ke yanzu tashancin naki bai tsaya a Alhazan gari ba harda ‘yan fashi da makami da masu garkuwa da mutane kike bi... Tell me Sawwama maza nawa kikai huld’a dasu kafin ni..!!!” Yai maganar yana faman bubbud’e k’irji da hanci saikace bashine ya gama rakub’e rakub’e ba....
Tintsirewa da Dariya Sawwama tai tana dubansa...
Ya kuma harzuk’a “Au dariya ma na baki... Ke ko kunya bakiji ba...”
Dakatar dashi tai da fad’in “A’a Kaga Malam daina min ihu aka, ni nan taimaka maka nake ka samu ka kuma mallakar Matarka Zulfa’u a karo na biyu... Idan kuma kace zaka kawo min rainin hankali wllhi kaji na rantse saidai a maidama Hajiya k’ok’on Kan d’anta dan idan naso sai ai gunduwa gunduwa dakai yanzu a wajen nan...!!” Cikin karaji tai maganar tana kallon yanda alamun tsoro da tashin hankali suka kasa b’oye kansu a fuskar Hafiz dikda k’ok’arin b’oyesu da yake...
Lokaci guda ya kuma tintsirewa da dariya ta shiga shafa fuskarsa tana fad’in “Relax mijina... Karka damu ni d’in har yanzu mai k’aunarka ce so ka kwantar da hankalinka... Kuma da kake cewa har mazan daji Ina bi toh kai kuskure domin kaw babu mata a tsarin Babba Duna... Dama idan kace akasin mata Wato Ina nufin maza...” Tana maganar tana yawo da ‘yar yatsarta a sassan jikin Hafiz had’ida kashe murya irinta gogaggun kilaki....
A firgice Hafiz yajada baya yana mai girgiza kai had’ida duban Sawwama da tsananin mamaki wanda bai tab’a irinta ba....
“Sawwama so kike kice abinda kika kawo ni ayi dani kenan... Sawwama wata irin biladama ce ke.... Ki d’auko mijinki na sunnah ki damk’asa ma ‘yanluwad’i....!”
Bai kai aya ba ta katsesa da fad’in “Kaga Hafiz nifa ka isheni... Idan bakaso burinka ya cika ka dawo da Zulfa’u sai ka tashi ka tafi is not a big deal...”
A zuciye ya mik’e yana aika mata muguwar kallo yake fad’in “I was so stupid da na yarda dake... Na yarda notin kaina sun kwance da har na yarda Ke d’in zaki taimaka min na dawo da matata.... Kafurci na baikai nan ba, bazan aikata wannan laifin ba Sawwama kinga tafiyata....”
Juyawan da zaiyi sai cin karo da bakin bindiga yai an saita k’irjinsa...
K’iris ya rage Hafiz bai saki fitsari ba sabida tsananin firgita, abinda yake gani a fina finai na neman aukuwa dashi....
Mik’ewa Sawwama tai tana mai murmusawa kana tace “Hafizi na kenan... Hafizi na Sawamma haka kuma angon Zulfa’u... Ka kwantar da hankalinka Ina mai tabbatar maka babu abinda zai faru dakai.... Ai ni na maka alk’awari kuma ya zama dole na cika maka.... Babba Duna owes me big time, akwai bashina akansa sabida haka aikin da zai mana baida buk’atan biyan reward ka fahimta....” Ta k’arashe tana sakin murmushi, lokaci guda tai alama ma d’aya daga cikin yaran Babba Duna da yai pointing bindiga a k’irjin Hafiz da ya janye bindigar....
Basu jima ba wasu k’artai biyu da wani d’an tsakurkurin mutumi tsakiyarsu suka nufo yanda suke daga can k’asa da wajensa suke....
Sawwama ta mik’e tana sakarma d’an tsakurkurin mutumin da murtuk’a murtuk’an mutanen nan Ke tsaronsa murmushi....
Daga can tsakurkurin mutumin nan da bai wuce a hure ba ya shiga maida mata maetanin murmushinta yana bud’e hannaye alamun sannu da zuwa yake furta “Barkada zuwa Fadan Babba Duniya... Kyakkyawa mai kyawawan ‘yandaudu..... Fad’i dik abinda kike babu b’ata lokaci za’ai miki... Ki fad’i duk Uban da kikeso a saco miki shi a fad’in k’asar nan.... Idan barikin Soji ne yake yawo dashi matsayin masu tsaronsa Ina mai tabbatar miki sai mun sace miki shi.... Babba Duna bai tab’a saka abu a gabanshi yaga gazawa ba....” Ya k’arashe yana k’ek’yata dariya....

Hafiz da tinda wannan tsakurkuri mai wani irin siffa kaman ba d’an adam ba ya soma magana ya b’oye Bayan Sawwama sai rarraba idanu yake, shi dik a zatonsa zaiga Babba Duna murjeje ne sai yaga wannan k’aramin alhakin.... Amma yayi kama da tsagerun shed’nu matuk’a sannan kallo guda zaka masa ka fahimci shekaru sun fara kamashi ma’ana tsufa ya sauk’o masa, da gani kasan wannan ya jima yana kafurci a duniya....

“Na gode Babba da wannan karramawa taka gareni.... Mijina na kawo, ai masa aiki....” Ta k’arashe tana janyo Hafiz daketa k’ok’arin b’oyewa bayanta...
Babba ya kafe Hafiz da idanu kana yace “Mai ake so ai maka Pretty boy....?”
Hafiz ya kuma hard’e rai jin Babba yana admiring d’insa....
Sawwama ta d’an mintsileshi alamun yai magana...
Babba ya bud’e murya yace “Kar ka damu pretty boy ka fad’i duk abinda za’a maka idan dai a k’ark’ashin alfarman Sawwama ne, bakada matsala... Fad’i ko mai kake so...”
Hafiz ya gyara tsayuwarsa yana hango tsakiyar kan Babba kana ya zaro wayarsa a aljihu ya shafa... Lokaci guda yai taku kad’an zuwa gaban Babba ya nuna masa hoton dake bisa screen d’in....
Babba ya amshi wayar ya k’urama hoton idanu kana wayar ta shiga zaga hannun yaransa, wannan ya kalla ya mik’ama wannan har ta dawo hannun Babba....
“Mai kake so ai masa... Wasu sassa na jikinsa akeso a ciro maka...?”
Saurin girgiza kai Hafiz yai kana yace “Ajiyanshi kawai nakeso na baku na wani d’an lokaci...”
Babba ya murmusa irinta basawa kana yace “Na maka alk’awarin ko tandu nan ya barni wajen iya ajiya.... Amma ina mai tabbatar maka idan ajiyan ya kuskuri kufcewa komai ka iya faruwa....”
Hafiz ya dubi Sawwama, itama d’in shi ta duba kana ta murmusa tace “Wuk’a da nama na hannunka Babba....”
Babba Duna ya jinjina kai kana yace “Yaushe ajiyar taku zata soma aiki...?”
Hafiz yai karaf yace “Nan da kwanaki biyar....”
Babba Duna ya d’aga ‘yan yatsun hannunsa tamkar mai lissafi kana yace “An gama pretty boy angon mai ‘yandaudu....”
Hafiz ya kuma dubansa kana yace “Banaso ya escape...Bana so kuma a samu failure...”
Chapter 125 · 0% Book details