← Book details Inda Rai Da Rabo Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 163 OF 198

Sashe 163

Inda Rai Da Rabo Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

D’akin da aka kwantar da Ammi ya nufa yanda ya tadda Siyama na zaune gefen gadon da take bisa har lokacin matsan k’walla take..... Daga cen d’an gefe yaja ya tsaya yana duban mahaifiyar tasu cikeda tausayawa... Ya d’an K’araso kusan Siyama hannayensa sakale cikin aljihun wandon jeans d’insa, idanunsa kan Ammi dake bacci yaceda Siyama “How’s she doing...?”

Siyama ta d’ago pale eyes d’inta tana duban Khalid d’in shaye da mamaki, saida ta muskuta kad’an kana tace “Seriously Khalid... Tambayata jikin Ammi kake..? Kana can kai a dole ga mai mata... Look, kalli mahaifiyarmu Khalid.. She’s broken amma ko ajikinka instead ta sami kukawarka kana can kana siding da mak’iyanta...”
Katseta yai da fad’in “Enough please Siyaam..!”
Ta katsesa da fad’in “Don’t call me Siyaam.... This is serious Khalid... Ta ya zakaiwa mahaifiyarka haka....? What kind of a son does that to his very own mother..?”

Khalid ya fuza da huci a hankali kana ya d’an bud’e murya kad’an yace “Will you please stop complicating things Siyama... For crying out loud this isn’t easy for me either... Instead Ki tausasi Ammi sai kuma aza wutan rigima kike... Haba Siyama kina gani Daddy fah har yau unconscious yake... Haba, ya kamata Ki fahimci what’s done has already been done... You can’t change the fact that Aunty Daula is our father’s wife... Kuma...!”

Katsesa tai da fad’in “Don’t play the victim Khalid... So, Tell me... Does Sameer knows.... Shima ya sani bai sanar dani ba....?”

Khalid ya d’an kame naman goshinsa kana yace “Siyama please....”
Ta katsesa da fad’in “ Just tell me idan shima ya sani, no more secrets please Khalid...”

A hankali ya jinjina mata kai kana yace “But ya kamata Ki gane ba hurumin Sameer bane sanar dake about this, kuma shima all of a recent ya sani.....”

A zuciye tace dashi “Don’t you dare cover up for him....”
Tab’e baki yai wannan karon had’ida janyo kujeran dake gefenta ya zauna kusan kan mahaifiyarsu... Lokaci guda ya zaro wayarsa yana shafawa yayinda Siyama taci gaba da b’alla masa harara tana sauk’e k’wafa a jere...
Idanunsa naga wayarsa yace da ita “Kunyi waya da Aunty Hanne ne...?”
A harzuk’e tace dashi “Ban sani ba...!”

Ya kuma tab’e baki alamun ko inkula kana yaci gaba da abinda yake cikin waya.....

Bayan shud’ewan kaman awanni biyu acan d’akin hutu na nurses yanda aka kwantar da Yesmin ta mik’e tana dafe kanta da yai mata nauyi... Lokaci guda ta shiga tuno abubuwan da suka faru... Ta zabura zata sauk’o daga saman gadon nurse guda ta k’araso tanai mata sannu had’ida tambayarta yanda takeji.... Harara ta b’alla masu tana fad’in su bata hanya ta shige uban wa yace masu ita mahaukaciya ce.... Suka kaw bata hanya ta shige tana tangad’i had’ida kame b’angaren kanta guda... Sarai sunsan da hankalinta iskanci ne tsantsan hakan yasa sukai maganinta suka danna mata allurar bacci maras k’arfi... Tana ficewa suka kwashe da dariya had’ida tafe hannu d’ayar tana fad’in “Maganin mai haukar rashin kunya kenan...” suka kuma tafe hannaye....

Yesmin na tafe taci karo da Mahaifiyarta Aunty Hanne Kubura na gaba zatai mata rakiya zuwa d’akin da Ammi Ke kwance.... Aiko Yesmin na gani mahaifiyarta Ta fad’a jikinta tana kuka sosai... “Mummy shikenan na rasashi, na rasa my Kay Mummy....”

Mummy Ta shiga jijjigata tana fad’in “Ke Yesmin lafiyarki... Tashi kimin bayani....”

Itakaw Kubura dama tana shak’e da haushin Nabilah dan ta hango k’iris ya rage Khalid bai sumbaceta ba, yanzu kuma ga wannan shashasha mahaikaciyar na kukan Ta rasashi... Ji tai tamkar takai mata naushi ko ta huce haushinta....

Yesmin na kuka jikin mahaifiyarta take fad’in “Mummy my Kay fah auran kucakar nan yayi... Kuma Mummy d’azu harda marina tai ta kuma k’ala min sharrin hauka aka cazgwad’a min injection na mahaukata amma ko a jikinsa... Mummy Wllhi tsafesa tai I’m sure of it..!!” Ta k’arashe tana mai kuma fashewa da kuka...
Dariyar Kubura kawai suka sinkaya dan dikda haushin da take ciki saida taji dariya tazo mata amma Wllhi malaman asibitin nan sun bala’ain birgeta da suka tabbatarma wannan shashashar cewa ita mahaukaciya ce mai son wanda bai k’aunanta....

Mummy da Yesmin suka watsa mata harara a tare kana Mummy tace “Kikace Khalid yayi aure...? Kuma shashashar inane Ke da zaki tsaya k’aramar yarinya Ta tsinka maki mari baki tattaleta da maruka masu kayu ba....?”

Yesmin Ta jinjina kai tana kuma matsan k’walla.... Ai tuni Aunty Hanne Ta shiga janyo hannun Yesmin tana fad’in “Muje naji uban da ya tsaya masa ya auri wata ba Ke ba.....”

Yesmin Ta shiga share hawaye tana fad’in “Yauwa Mummy na shisa nake son Ki.......”
Suka d’unguma suka nufi d’akin Ammi.....

Khalid yana ganin sun shigo ya d’auke kansa tamkar bashi a wajen, yanaji Siyama na gaisawa da Aunty Hanne tana maida mata ba’asi... Mik’ewa ma yai yana dialing layin matarsa lokaci guda yake k’ok’arin gaida Aunty Hanne.... Ta amsa da k’yar had’ida rakasa da mugun kallo....
“Kai Saifullahi ina zaka kuma...?” Ta tambaya tana dubansa...
Waya mak’ale kunnensa yake furta “Aunty ina zuwa.... Kuyi a hankali please Dr yace a bar Ammi ya d’an sami baccin....”
Daga haka bai tsaya sauraren kowa ba yai ficewarsa yana waya da habibiyarsa....

Daga Yesmin har Kubura mayen kallo suka bisa dashi har ya b’ace masu..... Aunty Hanne kaw ta dubi Siyama tace “Wai haka Saifullahin ya zama ne....?”

Siyama tace “Anty ya wuce haka ma... Zauna ga waje...”
Ta k’arashe tana tura mata kujera...
Tattauna lamarin suka dinga yi har dai Ammi ta farka ta taddasu suna zancen nan Siyama ta fice ta nufi kiran likita....

***

KANO

Washe gari sassafe ta tashi ta soma had’e kayanta waje guda... Tanayi tana kuka, ita a ganinta cin mutuncinta kawai mijinta yai niyyan yi... Kuma tasan harda munafuncin wannan uwar tasa amma bacin haka tayi imani Excellency d’inta yafi k’arfin ajin wannan yarinyar, dama ita tinda taji Wai ya sami danginsa tasan sai an d’ago wani kutungwilar, dan munafunci za’ace ‘yaruwarsa ce.... Ta goge hawayen da suka zubo mata, tana huci ta nufi d’akin yaranta yanda tasa Murja Ta had’a mata kayan yaranta a cewarta zata biya gidan munafukar uwar Engr Ta kwashi yaranta.... Murja hankali tashe take fad’in “Hajiya dan Allah Ki hak’uri..”

Wani uban tsawa Muhibbah ta darara mata... “Ke kiyi abinda na sakaki banson shegen felek’e....!!”
Jiki har ba rawa Murja taci gaba da had’a kayan....

Yana daga parlorn k’asa dake cikin sashen nata yana sinkayo masifar da takewa Murja.... Ya sauk’e ajiyan zuciya a hankali yayinda hankalinsa ya karkata kan labarun da ake has kowa wasu yara ‘yan mata ‘yan makarantar sakandare aji biyar sunyi drugs over dose sun mutu har guda uku... Cikin tsananin tashin hankali Engr ke kallon labarun....

SameenaAleeyou 📚

*INDA RAI*
_................DA RABO_

*101*

*©️Sameena Aleeyou...✍🏽*

NOT EDITED

Kota kansa bataiba tasa kai zata fice ya bud’e murya had’ida doka mata kira.... Muhibbah taja ta tsaya tana sauk’e huci a hankali...... Lokaci guda ta juyo tana yamutsa fuska.... Engr ya tako gabanta kad’an “Ina zakije...?”
Yanda yai mata tambayar ya sanyata dubansa tsegege kana tace “Mai ya dameka da yanda zanje... Inada sauran amfani a gidan nan ne... Mai kuma zan zauna nai maka...?”
Jinjina kai yai a hankali kana yace “Kinsan yanayin da jiya kika dawo gidan nan cikinta....?”

Ta kuma dubansa dan harga Allah bata iya tina tayi wani b’aran b’arama ba, tabbas tasan Shamzy ce ta dawo da ita gida dan bazata iya driving a halinda take ciki ba... Shan mur tai sosai kana tace “Koma a wane irin hali na dawo laifinka ne... Kuma Wllhi bara na kuma jaddada maka, bazan bar yarana ma wancan kucakar ba... I’m leaving with them.....”

Jinjina kai yai a hankali kana ya shiga nuna mata tv da remote d’in dake rik’e hannunsa... “Look... Ki kalla da idanunki Muhibbah, ki kalli yara k’anana yanda miyagun k’wayoyi yai masu illa... Shin ya zakiji yau idan akace Samha na d’aya daga cikin yaran nan....? Tell me how would you feel idan kikaga d’iyarki cikin irin wannan yanayi...? Ba a shan k’wayoyi kawai kika tsaya ba Muhibbah har safaransu kike...? Shin kinsan rayuwaka nawa suka salwanta a dalilin haramtacciyar business d’inki...? Shin kinsan yara nawa suka haukace wasu suka mutu dik a dalilin wannan mummunar kasuwanci kuma haramtacciya...? Hibbah do you really know how many lives are ruined dik a dalilin san zuciya irin naki....?Why mai na rageki dashi.... Menene bana miki...? Maiyasa kika zab’i wannan hanya.... Drug trafficking Muhibbah....??” Ya k’arashe cikin tsananin tashin hankali wanda ya sauya launin idanunsa....

Tinda ya soma magana idanunta Ke k’asa k’irjinta na bugawa... Ya akai yasan hakan... Lallai ko shakka babu she messed up big time yesterday.... Muryarsa cikin tsawa ya kuma katseta “Answer me..!! Why mai yasa kika jefa kanki kika jefamu da yaranmu cikin halak’a... Answer me Muhibbah....??!!”

A harzik’e wannan karon ta d’ago tana hawaye “Eh... Yes sana’ata kenan, dan kar kowa ya zargeni nakeda manyan stores na kayan k’arau.... Kuma sabida rana irinta yau na fad’a business d’in da zai kawo min kud’i nan take... Nafi k’arfin nai relying akan dukiyar miji... Kuma na wuce miji yamin gori inada nawa arzikin wanda zai isheni da ‘ya’yana harma da jikokina... And let me remind you this, wllhi wllhi babu kai babu yarana... Yanzu ba sai anjima ba zan kwashesu mu tafi....!!”
Ta k’arashe tana mai goge hawayen idanunta kana tasa kai ta wuce fuuu yanda Murja ta fidda mata suitcases d’inta....
Cikin rashin yarda da abinda yakeji yake dubanta... Da gaske dai sana’ar muggan k’wayoyi matarsa keyi... Cikin sauri ya take mata baya yana doka mata kira amma inaaa tuni ta shige mota.... Engr yana fad’in kada securities su bud’e mata gate amma Muhibbah tai kansu tamkar zata d’agasu sama dole suka hangame mata gate had’ida kaucewa kada ta had’e dasu....
Babu shiri ya nufi car park yana dokawa Patrick kira... Patrick na tambayarsa ina zasu ko tsayawa saurarensa Engr baiba ya amshe car keys d’in dake hannun Patrick ya nufi mota guda ya shige ya tada... Take shima ya fice daga gidan da d’an karan gudu yabi bayan motarta.... Su Murja dasu Patrick da sauran Securities sukai tsaye suna kallon ikon Allah hankulansu dik a tashe ganin yanda masu gidan suka fice.....
Chapter 163 · 0% Book details