← Book details Inda Rai Da Rabo Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 112 OF 198

Sashe 112

Inda Rai Da Rabo Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

K’uri Muhibbah ta masa sanda yake ci gaba da feshe jikinsa da tiraren, kaman wacce ta tina wani abu ta mik’e ta amshi turaren tana mai ci gaba da fesa masa, hannu ya mik’a ya d’auki hukarsa dake saman drawer a nan closet d’in, tai saurin amsa tana k’ok’arin saka masa, tsaf ya sauk’e kyawawan idanunsa saman fuskarta, kana iya hango tsananin damuwa da tashin hankali cikin fuskar tata....
Hannunta ya kamo duka biyu har lokacin idanunsa na tsareda ita, ta d’ago idanunta da sukai rau rau, tai saurin sadda idanun nata k’asa yawa mutumiyar arziki... Hannu yasa ya tallafi hab’arta, ya d’ago,
A hankali ya furta “Kuka...?”
Kaman wacce akace nan hawaye suka soma zarya a fuskarta....Cikin murya irinta mai kuka take furta “What do you expect...? Aure fah zaka tafi nema.. Ba dole nayi kuka ba...” Ta k’arashe cikin salo na ban tausai....
Murmushi ya sakar mata kana yasa tafukan hannayensa duka biyu ya tallafi fuskarta “Ki kwantar da hankalinki neman aure zan tafi amma ba nawa bane wannan karon, rakiya zanyi wannan karon....”
D’an turo baki tai kana tace “But still naka na zuwa...”
Da gefen bakinsa ya d’an murmusa kana yace “I thought we’ve already talked about that...”
Jinjina masa kai tai kana tace “Haka ne Excellency na, and you’ve no idea how happy I’m daka zama pure and transparent baka b’oye mun komai ba, farin cikinka shine nawa mijina... You’ve my unconditional support ba’a siyasarka kawai ba harta a neman aurenka muddin zaka kasance cikin farin ciki.... Burina na faranta maka mijina...” Ta k’arashe cikin salo na kashe murya had’ida shafar fuskarsa...
K’uri kurum ya mata kaman mai son fahimtar wani abu.... Gajeren murmushi ya sakar mata kana ya shafi fuskarta kad’an yana mai duba agogon da bai jimada d’aurawa a tsintsiyar hannunsa ba.... “Suna jirana... Sai na dawo koh....” Ya k’arashe yana mai gyara zaman hularsa da tasha tangaran sai k’yalli take....

Karkace kai Muhibbah tai tana dubansa, shu’umin murmushi saman fuskarta take furta “A dawo lafiya Excellency na, you take care....”

Yana ficewa dariya ta tintsire dashi had’ida fad’awa kan gado da baya, a fili take furta “Ma’aruf kenan, lallai iska na wahal da mai kayan kara, kayi kuskure da ka amince nid’in zan zuba maka ta mujiya ka kawomin wata ‘yariska gidan nan da sunan amarya....”
Ta k’arashe tana mai kuma tintsirewa da dariya....
Wayarta dake gefen gado ta janyo ta shiga neman layin Akram....

SameenaAleeyou📚

*INDA RAI*
_................DA RABO_

*80*

*©️Sameena Aleeyou...✍🏽*

Shiru Akram yai yana saurarenta daga d’aya b’angaren, shi kansa baisan ina suka dosa ba shida Boss d’in nasa balle yace mata ga yanda suka nufa.. Fitowar Engr yasa Akram katse kiran yana mai sanar da ita zasuyi magana...
Cikin saurin ya fito da niyyan bud’e masa front seat, kaman ko yaushe jama’ansa suka nufosa, masu kawo koke da matsaloli nayi masu gaisuwa nayi... Gaba d’aya hak’uri ya basu kasancewar baiso ya makara dan yanda zaijesa nada matuk’ar mahimmanci, ya dubi Akram yace dashi ya tsaya yaji matsalar kowa ya kuma rubuta ya aje masa....
Akram ya d’an sosa kai kana yace “Your Excellency fitar namu fah....? Sannan waye zai tuk’aka, ko na kira Jalo ne...?”
Gyara zaman babban garensa yai kana yace “Karka damu zan driving da kaina, just stay here ka saurari matsololinsu....” Ya k’arashe yana mai nad’e babban rigar tasa sanda yake shiga mazaunin matuk’i.....
Jinjina kai Akram yai ba tareda zuciyarsa ta sami natsuwa ba, shi kansa baisan dalilin hakan ba... Har Engr ya fice daga gidan Akram bai koma daidai ba, zamewa yai daga cikin mutanen ya nufi sashen Muhibbah yana mai dialing wayarta....

***

“Ma’aruf d’an siyasa....” Daddy ya fad’i bayan sun gaisa....
Murmushi saman fuskar Engr Ma’aruf yake fad’in “Ya zamuyi Ya Engr mutane sun zab’omu sunce mu tsaya masu, kuma tinda ku manyanmu kunk’i ku tsaya...”Yai maganar yana mai d’an murmusawa kad’an...
Jinjina kai Daddy yai shima k’aramar dariyarce saman fuskarsa, lokaci guda yake furta “Da mahaifinka nada rai tabbas da yayi matuk’ar alfahari dakai....”
Wannan karon k’aramar murmushi ya d’an saki yana mai tuna Babanshi, mutuminda ya maidasu ‘ya’ya a lokacinda suka rasa iyaye, mutuminda ya maidasu masu galiho a lokacinda suka rasa gata, mutuminda ya masu sutura a lokacinda suturarsu ta yaye... Tabbas dole yaji hud’ubar Baba ya rik’e Muhibbah kaman yanda yai masa alk’awarin rik’eta amana da kuma yin hak’uri da ita.... Babanshi shine musabbabbin aurensa da Muhibbah kuma alk’awari ya masa wanda ya zama dole a gareshi ya cika muddin yana son gamawada duniya lafiya....
Jikin Daddy ya d’anyi sanyi ganin yanayin Engr d’in ya d’an canza....
Gyara zamansa ya d’anyi had’ida yin gyaran murya kad’an “Babanka mutumin kirkine Ma’aruf, har gobe shi d’in babban Yaya ne kuma uba ne a gareni, duk wani matsayi da na taka a yau ta dalilinsa ne, cikin k’udurar Ubangiji, banida abinda zan biyasa dashi bacin na rik’e masa amanar tilon d’iyarsa Daula, bazan tab’a bari wani ya muzgunawa Daula ba muddin ina numfashi a doron k’asa domin ita d’in amanace a gareni.. (Wannan na d’aya daga cikin abinda yasa Daddy ya kasa sanar da Matarsa Farida labarin aurensa na biyu..) Abubuwanda Babanka yaima mutane na alkhairi basa k’irguwa Ma’aruf, ko shakka banayi footsteps d’insa kake bi.... Ubangiji ya dafa maka ya kuma baka nasaran abinda ka sa gaba....”
Engr ya amsada “Ameen Yaya Engr,....” (Haka nan Ma’aruf ke kiran Daddy Ya Engr kasancewar shima Daddy d’in civil engineer ne)
Sallaman Sameer ne ya katse hiran tasu, Daddy ya mik’e yana fad’in “A’a Sameer ka iso...?”
K’arasowa cikin parlorn yai yana mai risinawa had’ida mik’awa Daddy hannu dan musabaha yake furta “Eh Daddy na iso, aiki ne ya d’an rik’eni a asibiti...”
“A’a babu komai, his Excellency d’inma gashi nan ya iso, ai sai mu d’au mik’ati koh...” Ya k’arashe yana mai d’aukan agogonsa saman center table had’ida d’aurawa a hannunsa na hagu...
Sameer ya k’arasa ga mutuminda tin shigowarsa suka kasa janye idanunsu daga barin duban junansu.... Hannu ya mik’awa Engr alamun musabaha... Shid’inma hannun ya mik’o masa har lokacin duban juna suke ido cikin ido, wani yanayine da su kansu bazasu iya cewa abinda sukeji ba.... Sanda hannunsu ya had’e waje guda haka nan ta mik’e tsaye tamkar wacce aka sinkaya, Hajja mai kulada gidanta na amana da tin bayan mutuwar mijinta take gidan take kuma kula da ita dubanta tai ganin yau d’in ta fito har yanda bata iya fitowa cikin gidan tin bayan mutuwar maigidan.... Cikin sauri ta k’arasa gareta kana tace “Hajiya akwai abinda kike buk’ata ne...?”
Dubanta tai da idanunta da kullum suke a kod’e kaman ta maras lafiya kana tace “Ma’aruf..!” Tana fad’in haka kuma sai ta juya ta koma cikin gida tamkar kazar da k’wai ya fashe mata a ciki....
Idan da sabo Hajjah ta saba da hakan, d’an fuzar da iska tai had’ida girgiza kai kana taci gaba da abinda take...

Introducing junansu Daddy yai kana suka d’auki hanyar gidan Abbah...
Tinda suka iso unguwar yakejin wani abu na tsargar masa, yakanzo unguwar sau tari yakan shige unguwar sau tari a matsayinsa na cikakken d’an siyasa mai neman takaran kujeran gwamna, amma wannan zuwan yanaji wani al’amari ne da baisan ya zai fasalta shi ba, tin bayan had’uwarsa da wannan matashi Sameer d’in yakejin wannan yanayi a tattaredashi, ji yake tamkar dik shekarun da yai a garin kaman akwai wani abu mai girma na rayuwarsa da ya rasa, sunan yayi rakiya ne amma sam hankalinsa bai jikinsa... Ji yake tamkar wani babban al’amari ne ke shirin faruwa dashi, wasu irin tunani yake tamkar wanda yake yunk’urin tina wani abu a shekaru masu tsawo.... Take kansa ya shiga mugun sara masa, bazaice ga maganganun da akai wajen neman auren ba, iyakacin abinda ya sani shine yayi rakiya amma duk wasu tattaunawa da akai da sunayen mutanen da aka ambata a wajen bazaice gasu nan ba, baisan kalan yanayin da yakeji ba, wasu irin tunani yake wad’anda kaman yana ganinsu a mafarkansa lokacinda yake k’uruciya, fuskar matar da ya hanga gittawarta a cikin gidan bai b’ace daga kwanyarsa da k’wayan idanunsa ba, kaman ya tab’a sanin mata mai irin fuskar a can baya wasu shekaru masu tsayi, saidai fuskar da ya sani tafi wannan yarinta da k’uruciya... Meke shirin faruwa dashi...? A ina yasan mai irin fuskar matar can...? Dafe kansa dake tsananin sarawa yai yana mai rintse idanunsa, lokaci guda ya mik’e ya shiga zagaye tapkeken parlorn nasa thoughts d’in bai k’yalesa ba har wannan lokaci, ji yake wasu abubuwa da suka faru dashi in his past suna yunk’urin dawo masa, ji yake bayansa na kiransa... Ji yake akwai wani babban gurbi na rayuwarsa da tsawon shekarun nan yake a bud’e yana yunk’urin cika kansa.... Yanda yaga rana haka yaga dare, wad’annan tunani sun kasa barinsa, kama daga had’uwarsa da Sameer izuwa zuwansa wancan gidan nemawa Khalid aure... Haka kurum yaji k’aunar Sameer ya shigesa har cikin ransa, zaiso su k’ulla alak’a da Sameer d’in don ko babu komai yanaji through Sameer zai sami amsoshin tambayoyin da suka k’ulle masa kai a halinda yake ciki... Harta Muhibbah bata gane kansa ba, dan koda ta tambayesa ya al’amarin ya kasance mai ya faru... Sam Engr bai iya bata amsa ba, ko bindiga za’a saka masa bazaice ga yanda al’amarin neman auren ta kaya ba, wad’annan tunani sunfi komai yawo a kwanyarsa, ya k’udiri niyyan binciko musabbabin abinda ya faru dashi da kuma k’anwarsa shekarun baya koda ace mutumin da ya kasance ya d’aukesu matsayin ‘ya’ya bai raye.....
Chapter 112 · 0% Book details