Sashe 118
Inda Rai Da Rabo Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Dariya suka kwashe dashi had’ida tafe hannaye, Haule ta mik’a mata hannu suka tafe.... Lami tace “Wato Haule bakida kyau, shikenan yanzu zaki had’asu fad’a ki jefa gaba mafi muni a tsakaninsu....”
Haule na jijjiga tana wani duban Lami take fad’in “A ranar d’aurin auren Sameer Aminiyar Sirri zata bayyana masu... Sannan duniyarsu zata sauya, ‘Ya’yan Mariya gaba d’aya bama Sameer kawai ba sai sun tsaneta, Mariya zatai ido hud’u da Butulci da kuma cin amana mafi muni.... Zamu zamto mu kad’ai muke shanawa... Zaki zamto tauraruwa a idanun ‘ya’yanta da kuma mijinta.... Na fad’a miki Lami idan kika rik’i Haule toh fah har abada bazakiyi kuka ba.... Wata d’aya jal ya rage muga rugujewarsu har k’asa, mu bayyana Aminiyar Sirri a tsakaninsu... Muga yanda fuskokinsu zasu sauya idan suka fahimci ko wacece ita da duk kalan k’uncin data jefasu ciki.... Tabbas zamu koma gefe muna dariya muna shagalin bikinmu....”
Lami ta kwashe da dariya suka kuma tafe hannaye kana tace “Ranar da gidan Biki zai koma tamkar gidan mutuwa a b’angaren wasu... Yayinda a namu b’angaren abin zai kasance mafarin Farin ciki mai dawamma....”
Suka kuma bushewa da dariya suna ci gaba da tafe hannaye....
Naja’atu dake lab’e bakin k’ofa hawaye masu tsananin d’umi suka gangaro mata, ta dubi Hajiya da Aunty Lami yanda suke dariya suna fad’in muguntarsu suna tafe hannaye... Shin ta aikata ne ko ta k’yalesu su cimma burinsu.... Yaya zatai ne...? Ta wane hanya zata b’ullo ganin burin Mahaifanta bai cika ba.....? Ta kuma saka bayan hannunta ta goge hawayenta sanda zuciyarta ke ayyana mata _Do the right thing_ A hankali ta janye jikinta ta shige daga wajen
Tsakar gida ta koma ta rapka uban tagumi had’ida k’urama waje guda idanu, a haka Sahariyya da aminiyar ya Fa’iza suka shigo nik’i nik’i da kayan anko na K’awayen su da suka riga suka bada kud’i...
A gajjiye suka zube saman tabarman da Najah Ke zaune bisa, Sahariyya ta ije crutches d’in da take dogarawa dashi tana watsawa ‘yar uwar tata muguwar duba, a yatsine take tambayarta Hajiya....
“Tana d’aki tareda Aunty Lami...” Ta fad’i sanda take k’ok’arin bari masu wajen, Fa’iza ta bita da dak’ilellen kallo ganin tana nuna mata kalan ankonsu tana tambayar ra’ayinta Naja’atun bata kulata ba....
Fa’iza tace “Tooooh ke kuma fah... Kishi ko hassada...?”
Sahariyya ta amsata da fad’in “K’yale munafuka duka biyu take....”
Daidai lokacinda Hajiya Haule da Aunty Lami suka fito, da alama tafiya Lami d’in zatai...
Lami ta dubi Sahariyya tana Washe baki take fad’in “A’a Kaga amaryar mu...”
Sahariyya harda d’an sanne kanta ita a dole kunyar Aunty Lami ta soma ji.... Suka had’a baki itada Fa’iza suna gaidasu.... Hajiya ta isa ta d’auki yadin material d’in tana fad’in “Kai gaskiya yaran nan kun iya zab’e... “Sai juyawa take tana mannawa jikinta....
Fa’iza kaw cikeda zagwad’i ta d’ago leshin da suka sayowa Hajiyar tana fad’in “Hajiya ya kikaga wanda muka zab’o maki, ai yau tsaf saida muka zagaya Kwari gaba d’ai dan zab’o maki leshin da zaki kece raini uwar Amarya....”
Haule ta kame d’an guntun hancinta ta shiga rangad’a gud’a tana wasa kanta matsayinta na uware Amarya Lami na zigata....
Sahariyya ta shagwab’e fuska tana fad’iwa Aunty Lami ta taimaka ta rok’ar masu Sameer ayi dinner dan yanda ta samo mijin kece raini cikin k’waye ya kamata ayi dinner ta nuna masu tafisu sa’a.... Aunty Lami ta dafa kafad’arta tace “Kwantar da hankalinki Sahariyya, uban dinner ma sai anyi, don babban buduri zamuyi a Bikin nan.... Babban biki za’ai a Zuri’ar Mahmood Mailafiya, Bikin da ba’a tab’a irinsa ba, Biki Uku kuma za’a had’a.. Ga naki da Ma’aruf, ga na Nabilah da Zulfa’u....”
Batakai aya ba Hafiz da shigowarsa kenan ya tari zancen da fad’in “Wata Zulfa’un....?”
Sahariyya da k’awarta Fa’iza kaw tini suka tattari kayansu suka shige parlorn Hajiya suna kiran k’awayensu suzo su amshi ankonsu...
Aunty Lami ta murmusa da dubi Hafiz kana tace “Afff bakada labari, ai itama an tsaida ranar aurenta rana guda dana k’anwarka Sahariyya, bada jimawa aka kawo tambyar aurenta ba kuma ina mai tabbatar maka an basu ranar buki...”
Tinda ta soma magana yake dunk’ule hannayensa waje guda, Haule na mata ido tai shiru inaa Lami sai zuba take yawa an bud’e famfo....
Take idanun Hafiz da fatarsa suka sauya launi zuwa ja.... Shi kad’ai sai sakin tururi yake.... Baiceda kowa komai ba sai gani sukai ya fice daga gidan....
Haule na kiransa ko saurarenta bai ba yayi ficewarsa... Ta maidoda dubantaga Lami tana mata duban tuhuma....
Lami ta kame baki tace “Yo ni na mance tsohuwar matarsa ce ashe....”
Hajiya Haule tace “Yau kin b’allo mana ruwan teku bamuda jirgin ruwa... Mai tsaida wannan ruwan da kika b’allo sai Allah Lami....”
Aunty Lami tace “Ahap zaiyi ya daina dan ko mutuwa zai wannan yarinya Zulfa’u bazata yarda ta koma gidansa ba... Kece bakiso maida masa matarsa ba Haule...”
Haule ta dubeta da mamaki... “Ni kuma...? Kaman yaya ni....?”
Murmusawa Lami tai kana tace “Ba ko wani makirci kikeda bakin zarenta ba Haule... Keda kikeda Aminiyar Sirri a hannunki...?” Ta k’arashe tana kannare idanu...
Numfasawa Haule tai kana tace “Kuma fah haka... Amma sanin kanki ne mijinki nada kafiya Lami, babu yanda bamuyi ba nida Alhaji ganin ya maidawa Hafiz matarsa amma k’ememe yak’i... Bana tinanin akwai mai iya tank’warasa... K’yale Hafiz nasa mai sauk’i ne... Nidai tinda zamu gwara kawunansu ranan biki hakan yafi min komai dad’i a duniyata....”
Suka kuma tafe hannaye kana Haule tace “Muje na taka miki zuwa waje...”
Haka nan sukaci gaba da tattaunawarsu da tsara yanda zasuga k’uncin Mariya ranan Bikin ‘ya’yansu....
****
Tamkar wani zararre haka ya shiga har cikin ofishin nasu, ana tare shi ana janyoshi hakan bai hanasa kutsa kai cikin gidan radio d’in ba, tsakiyar gidan radio d’in ya tsaya yana k’walla mata kira da iyaka numfasawar shi....
Tana d’akin gudanar da shirye shirye ta sinkayo muryarsa na ambato sunanta cikin wane irin sautin...
Juyawa tai ta dubi Atika wacce itama ita d’in take duba... Babu shiri ta cire headphones d’in dake mak’ale kunnenta ta nufo waje Atika na biyeda ita...
Su Ameer da securities suna ta k’ok’arin fiddashi amma ya doge yace bazai fita ba har sai Zulfa’u tazo....
“Ku k’yaleshi Ameer....” Ta fad’i daga can nesa yanda take tsaye...
Hafiz ya juyo yana mata wani irin duba... Lokaci guda yake takowa gabanta...
Hawaye ta hango kwance saman fuskarsa yana mai k’arasowa gareta...
“Da gaske ne.... Aure zakiyi... Ki fad’a min da bakinki... Da gaske ne abinda nakeji....?” Ya k’arashe idanunsa suna kuma yin jazir...
A hankali ta jinjina masa kai “K’warai da gaskene abinda kaji Ya Hafiz, wata guda ya rage aurena....”
Murmushin data tafi kama data rainin hankali Hafiz yai kana yace “You must be kidding Zulfa’u.... Gidan duniyar nan bakida mini sai ni Hafiz... Na miki imani a wannan ranar saidai a maida aurenmu amma wllhi tallahi muddin ina numfashi bazaki auri wani bayan ni ba....”
“Ya Hafiz, please don’t make a sin here... Ka tafi dan Allah...” Tai maganar tana mai nuna masa hanya....
Jinjina kansa yai yana mai tab’e fuska, lokaci guda yake ci gaba da fad’in “You don’t know what I’m capable of, idan har da gaske kina sonshi kuma kin damu dashi, toh kiyi gaggawan bashi shawari ya fasa aurenki da yake yunk’urin yi, dan idan ba haka ba....” Murmushi yai ga hawaye dake gangarowa daga idanunsa lokaci guda yaci gaba da furta “Rayuka da dukiya zasu iya salwanta ta dalilin hakan, Babu Wanda ya isa ya mallakeki matuk’a ni Hafiz ina numfashi a doron k’asa.......” Daga haka sa hannu yai ya share hawayen da suka wanke masa Fuska kana yasa kai ya fice cikin sauri...
Hawayen da take k’ok’arin maidawa suka shiga ambaliya a fuskarta.... Atika ta k’araso da sauri ta rungumeta...
Sosai Zulfa’u Ke kuka tana fad’in “Atika what if yaje yayiwa Akram wani abin....?”
Atika na lallashinta take fad’in “Bai isa ya masa komai ba Zulfah, Hafiz bai isa yiwa Akram abinda Allah bai masa ba, kurari ne kawai da cika baki dan kice kin janye auren Akram... Karma ki bari zuciyarki ta raya miki wani abin... Ci gaba da fawwala wa Allah lamuranki...”
A hankali ta lumshe idanunta wasu hawayen masu d’umi suka kuma gangaro mata.... Atika ta janyo hannunta suka shige studio
Saidai gaba d’aya kasa gudanar da shirin tai, dole Ameer ya canjeta... D’akin hutu ta shige dan gaba d’aya batajin kanta daidai...
Tana isa d’akin ta tadda wayarta dake chaji jikin socket tana faman ruri... Mutumin nata ne mai kira.... Ta k’urama wayar idanu tamkar bazata d’aga ba... Sai kuma ta tsinci kanta da son d’aga kiran... Ta d’aga cikin rawar murya irinta mai kuka.... Yau d’in daga sallama bata iya cewa komai ba sai busting cikin kuka da tai had’ida saurin katse kiran....
Kaman kullum sak’on ya shigo mata...
_Kuka bata kamaci kyakkyawar muryarki mai dad’in sauraro ba...Ita murya mai kaman sarewa tafi dad’in a saurareta a matsayin abin nishad’antarwa da d’ebe kewa ga mai saurarenta, Ina fata kalamaina su sanyaki murmushi su kuma gusarda damuwarki koda na k’ank’anin lokaci ne..._
Ta samu kanta tana mai sakin murmushi bayan ta ida karance sak’on, haka kurum taji wani irin sanyi na ratsa cikin zuciyarta, tana fatan Allah ya nuna mata wannan bawan Allah koda sau d’aya ne tak a rayuwarta... Shin waye shi...?
Sauk’e ajiyan zuciya tai tana mai kuma karance sak’on...
****
Murmushi Sawwama tai mai cikeda ma’anoni tana mai duban mijin nata da tin dawowarta gidan maganar arziki bai shiga tsakaninsu ba.... Saida ta kuma mik’ewa tsaye kana tace “Sharad’in shine zaka dawo gareni bazaka kuma juya min baya ba...”