Sashe 15
Inda Rai Da Rabo Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Duk bala’i irin na Aunty B saida taji jikinta ya mata sanyi tausayin Zulfah da Kausar ya kuma kamata, sai tanaji sam bata kyauta ba donji take tamkar ita ta kashe ma Zulfa’u aure don koda Nabilah zatai magana Auntyn ita ta kwab’eta suka rungume ‘yar uwarsu suka fice....
***
Dubansa Shamsu ya kuma a karo na biyu yanda ko tab’a abincin dake bisa dinning table d’in baiyi ba har ya sauk’o daga sama wajen Mama, tasowa yayi daga parlorn ya dawo dining area d’in had’ida jan kujeran gefen Sameer ya zauna....
Dafasa Shamsu yayi kana yace “Still thinking about her, kodai zamuje Kaduna gobe ne, karka damu I’ll drive...”
Girgiza kai Sameer yayi had’ida fuzar da iska kana yace “I don’t know I don’t know Shamsu,so many things on my mind.... can k’asan zuciyana inaji Partner is not ok, inajin kaman wani abin ya sameta, sannan a nan kuma Ina ganin abubuwa wanda suke min tamkar na sansu wani wajen, I don’t know bansan meke faruwa ba Shamsu....”
Zuru Shamsu ya masa kana ya d’an sauk’e ajiyan zuciya yace “Toh ko dai bakason zaman unguwar ne...?”
Cikin sauri ya girgiza kai had’ida fad’in “No no no, in fact this is the best.... Har ina tunanin randa Mama zata gaji da zamana a nan....”
Shamsu ya d’an dara kana yace “Kasan Mama bazata tab’a damuwa ba In fact hakan sai yafi mata dad’i.... Kasan mai za’ayi tashi mu d’an fita...”
Babu musu Sameer ya mik’e suka fice ko zai refreshing....
***
Ko k’afafunta ta kasa motsawa sai faman tamke idanu take ga tsananin jiwa dake shirin kada ita... Dole Laila ce tai driving d’insu zuwa gida....
Siyama ta kasa fitowa daga mota nan ma saida Laila ta taimaka mata, a bakin k’ofar parlor suka lab’e kana Siyama ta umarci Laila ta lek’a mata idan Ammi da magulmatan ma’aikatanta basa downstairs sai su wuce cikin sauri gudun kada Ammi ta d’ago komai.....
Hakan kuwa akayi, Laila na na rik’eda ita har suka haura sama d’akin Siyama...
Sauk’e nannauyan ajiyan zuciya Siyama tai kana ta fad’a toilet don kuma kimtsa kanta....
Tsayuwa tai gaban madubi dake barhroom d’in tana duban kanta, b’angare na zuiyarta ta tambayarta _Siyama kin tabbata abinda kikai kinyi dadidai...?_
Take d’aya b’angaren ya shiga raya mata hakan shine daidai Siyama domin kuwa haihuwa yana nufin canza rayuwarki ne gaba d’aya, komai naki zai canza kama daga suffar jikinki zuwa hidiman kulada yara, ke kuwa baki shiryama wannan ba hasalima shi kanshi mijin naki haihuwa bata damesa ba domin kuwa ko a d’an irin tad’i da kuke na soyayya bai tab’a sako miki batun haihuwa ciki ba baima tab’a hasashoki da juna biyu ba balle yara, kin yanke hukunci mai kyau....
Sauk’e nannauyan ajiyan zuciya tai sanda ta jiyo Laila na k’wank’wansa mata k’ofar bayin tana fad’in me takene haka a bathroom tai sauri ta fito ta sha maganinta kafin lokaci ya wuce...
Cikin wahalcecciyar murya tace “I’m coming,...”
B’alle magingunan Laila taci gaba dayi tana aje matasu su zama ready... Tamkar wacce aka jefota saiga Ammi a d’akin ta shigo....
Gaban Laila ya yanke ya fad’i don bata mance gamuwarsu da Ammi ba sanda tai k’ok’arin raba k’awancensu da Siyama, don a cewar Ammi sam hankalinta bai kwanta da Laila ba gashi ita kuwa Siyama duniya batada k’awa sai Laila....
Gaisar da Ammi tai ta amsa a tak’aice kana tace “Ina Siyamar....?”
Laila tace “Tana bayi...”
Ammi ta jinjina kai kana ba tareda ta amsa ba.... Duban d’akin taci gaba da yi tanason gano wani abin....
Duban Laila ta kumayi a kaikaice kana tace “Idan ta fito kice Ina nemanta....”
Babu musu Laila ta jinjina mata kai tana ficewa ta kwaikwayi maganarta had’ida buga tsuka....
***
Koda suka tafi can gidan Zulfan suka d’ebo ‘yan wasu kayayyakin sakawanta ba gida suka wuce ba kai tsaye gidan Aunty B suka wuce don Aunty B d’in tafiso da safe ta kaita wajen mahaifan nata tayi bayanin komai.....
Koda Nabilah zata tafi na saida Aunty B ta kwab’eta cewa kada tacema Mamy komai tukuna...
Haka Zulfa’u tai kusan kwana tana hawaye, abubuwa da dama sun cika mata kwanyarta da zuciyarta, uwa uba mutuwan aurenta, ga musiban da zataje can gida ta tarar wajen Abbah, wajen Mamy ma tasan bazata samu da sauk’i ba, ga d’iyarta can hannun Hajiya da d’iyoyinta wanda tasan sai abinda sukaga dama zasu mata tunda dai tasan tsanar da suka mata ya shafi d’iyarta.....
A hankali ta rintse idanunta hawaye masu d’umi suka gangaro mata, cikin tsananin sanyi jiki ta mik’e ta nufi bathroom d’auro alwala.....
***
Tinda ya isa gidan yaji gidan ya masa sarari da yawa, yakai dubansa ga kujeran da kullum idan ya dawo a wajen yake hangota kodai tana bacci ko kallo ko kuwa karatu... Ya jima sosai yana duban wajen kafin ya d’an tab’e baki ya k’araso ya zauna cikin kujera had’ida dafe kansa kad’an, kana ganin sa zaka fahimci yana cikin damuwa, ga Sawwama na tsananin fushi dashi sabida amanartarda sukaci shida aminiyarta ga matarsa bata nan.....
Ya jima a parlorn har baisan sanda bacci yayi gaba dashi ba yana nan rik’eda waya yana jiran ko kiran Sawwama zai shigo....
Bashi ya farka ba saida gari yayi haske sallah yayi kana ya shirya cikin sauri ya nufi gidan Abbah kafin Abbah ya tafi Kasuwa....
Ya kuwa taki sa’a Abban bai fice ba, Mamy ya tadda da Nabilah na tayata shirya kayan karin kumallo saman darduman Abban wanda yake cin abinci bisa....
Nabila tana ganinshi haka yaci uban wanka harda hula gabanta ya yanke ya fad’i domin kuwa sam bataso Ya Hafiz ya fara zuwa ba, bataso a soma jin zancen ta bakinsa don tasan yanzu sai ya iya canza zancen...
SameenaAleeyou 📚
[10/01, 19:22] +234 703 745 3539: *INDA RAI*
_...............DA RABO_
*16*
*©Sameena Aleeyou...✍🏽*
Abbah bai daina bambamiba yana fad’in rashin kunya irinta yaran zamani da sam basu ganin girman dattijai....
Maganganun mutumin ya sanya Sameer saurin fitowa daga motar da niyyar basa hak’uri domin kuwa sam ba d’abi’arsa bace cin zarafin d’anadam ballantana har dattijo kaman wannan, sosai yake ganin girman nasa iyayen da bazaiso wani ya wulak’antasu ba don haka shima bazai wulak’anta tsohon wani ba...
“Baba dan Allah kayi hak’uri bada nufi nake maka horn ba kayi hak’uri don Allah......”
Wani irin bugu k’irjin Sameer yayi a sakwanni sanda sukayi eye contact da mutumin nan, a b’angaren Abbah ma babu sauk’i take yaji bugun zuciyarsa na harbawa da sauri da sauri, wannan k’wayan idanu tabbas yasan irinsu, wannan fuska tabbas yasan makamancinsa, tamkar an tsunduma a fridge haka jikin Abbah yayi sanyi, Sameer bai daina duban mutumin ba yanajin wani irin yanayi maras fasaltuwa a tattaredashi....
Ganin mutumin ma bai daina dubansa ba ya sanyashi matsawa baya a hankali ko zai samu sauk’in bugun zuciyarsa kayi... K’aran wayan salulan Sameer ne ya dawo dasu duniyar da tunaninsu ya barota....
Cikin sanyin jiki Sameer ya d’aga wayar yana satan kallon mutumin da ya kasa daina dubansa...
“Yes, yes gani nan zuwa In sha Allah....” Daga gani daga asibiti aka kirasa...
A hankali yasa kai zai koma ya shige motarsa Abbah yayi saurin k’arasawa ya damk’o kafad’ar Sameer guda.....
Shock d’in da Sameer ya tsinci kansa ciki har yafi na ganin Abbah da yayi....
A hankali yake kaikaito da kansa har ya sauk’e k’wayan idanunsa kan hannun Abbah yanda ya masa wani irin damk’a....
“Saurayi nan gaba ka dinga kula idan kana tuk’i....”. Cewar Abbah cikin dakewan murya...
A hankali Sameer ya jinjina kai kana yace “Na gode Baba...”
Daga haka cikin sauri yasa kai ya nufi motarsa Abbah bai daina duban yanayin tafiyarsa ba....
Har ya tada mota sai kuma ya juyo ya hangi mutumin nan dai na nan na kallonsa suka kuma had’a idanu....
Kashe motar Sameer yayi ya kuma fitowa ya nufi mutumin, ganin haka yasa Abbah saurin juyawa ya nufi motarsa data kasa tashi don dubata....
Yana tsaye jikin bonnet d’in motar Sameer ya k’araso ya tsaya dab gefensa, Abbah saiji yayi hannun saurayin nan saman nasa yana k’ok’arin amsar abin gyaran....
Abbah ya d’ago idanu ya dubi kafad’unsu yanda ya tsaya dai dai tsawonsu dai dai babu wanda ya d’ara wani, gabansa ya kuma yankewa ya fad’i babu wanda yazo zuciyarsa face d’ansa Ma’aruf, da ace yana raye da yana around shekarun wannan matashin ne, ya tuna Ma’aruf na yaro wani rana sun fita tun a lokacin Abbah yana caring and loving father kafin ya zamto abinda yake a yanzu, Ma’aruf na tsalle a wuyan Abbah yana furta “Abbah watarana zan kamoka tsayi idan na girma...?”
Abbah yaja hancinsa had’ida manna masa sunba a kumatu kana yace “K’warai kuwa masoyina, zaka kamoni tsayi harma ka k’etarani.... Amma bazaka k’etarani ba sai na tsufa sosai na koma tafiya a durk’ushe idan Allah ya ara mana kwana...”
Ma’aruf ya rungume mahaifinsa yana fad’in “Abbah na bazai tab’a tsufa ba...”
Abbah ya rungumeshi cikeda so da k’auna yanai masa shillo.....
K’aran tashin motarsa ce ya dawo dashi daga duniyar tunanin da ya tafi, Sameer ya sakar masa murmushi yana fad’in “Ta tashi Baba zaka iya tafiya yanzu....”
Abbah da tun b’acewar d’ansa ba kasafai yake murmushi ba sai gashi ya murmusa a hankali yana duban Sameer, k’arasowa yai zai shige motar kana yace “Na gode saurayi...”
Sameer ya jinjina kai yana furta babu komai Baba kana ya nufi nasa motar cikin sauri don yasan shi kad’ai ake jira a asibiti...
Har saida motarsa ta rab’a ta gefen na Abbah kafin ta shige ya kuma yin horn had’ida d’aga hannuwa Abbah shima Abban ya d’aga masa hannu yana mai bin motar tasa da kallo sai sannan Abbah ya tuna bai tambayeshi sunanshi ba....
Abbah ya kwanta jikin car seat had’ida lumshe idanu yana mai gargad’iwa zuciyarsa cewa wannan bazai tab’a zama Ma’aruf ba domin kuwa d’ansa Ma’aruf ya jima da mutuwa shi ya sani ya kumaji hakan a jikinsa, zuciyarsa ce dai mai neman kawo masa rud’ani yanda yake gab da shekarun girma..... Kasuwar da bai iya zuwa ba kenan a dole ya koma gida ya kwanta a d’akinsa...
Aunty Lami da fitowarta kenan daga kitchen nan ta hangi tamkar wucewar mutum sashen Abbah bacin tasan tuni Abbah ya fice kasuwa....