← Book details Inda Rai Da Rabo Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 140 OF 198

Sashe 140

Inda Rai Da Rabo Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Daidai nan Bara’atu ta cab’i zancen da fad’in “Mun shirya had’uwa dasu a kasuwa yanda na tabbatar masu matar da zan bata Ma’aruf ‘yar k’ungiyar shan jini ce.... Kuma Ma’aruf zai fice a rayuwarsu har abada... Sun yarda dani Sun yarda duk zan aika abinda nace.... A kasuwa na janye hannun Ma’aruf da sauri sanda ake k’ok’arin kawo d’aukiwa Mamy sakamakon haihuwa da yazo mata... A tasha na had’uda Dumba na damk’a mata Ma’aruf sai kuka yake... Nima zuciyata ta karaya... Tsugunawa nai na rungumesa kana nace INDA RAI DA RABON mu sake had’uwa Ma’aruf d’ahna... Na rok’i Dumba kan cewa ta kula dashi da kyau.... Dumba tace dani itama Ma’aruf d’anta ne kuma zatai duk yanda zatai taga ya samu rayuwa mai kyau da inganci... In sha Allahu Allah zai raya Ma’aruf. kuma INDA RAI wata ran zai dawo ya fuskanci kurayen da sukai farautar rayuwarsa a lokacinda basuda k’arfin halak’a shi.... Haka muka rabu da Dumba tana rungume da Ma’aruf da har lokacin kuka yake yana ambaton Mamynsa...”
Ta juyo tana duban Mamy da hawaye suka wanke mata fuska lokaci guda taci gaba da fad’in “Wannan shine dalilin da yasa na d’aukake ahalinki na kuma sadaukar da rayuwata ga ahalinki Mamy... Na sani da zuciya d’aya muka tseratar da Ma’aruf amma daga baya zuciyata ta kasa aminta da cewa hakan ba babban laifi bane... Na kasa saka ma zuciyata hakan ba zalunci bane mai girma .... Shiyasa nai komai dan naga kin kasance cikin Farin ciki... Shiyasa ban tab’a rabuwa dake ba... Sabida girman laifin da na aikata a gareki ‘yaruwata....” Ta k’arashe tana mai duk’awa saman gwiyoyinta gaban Mamy wacce ta kasa tab’uka komai sai hawaye...
Wajen yayi tsit duk wanda yace bai zibda hawaye ba yayi k’arya.... Abbah ma kasa tab’uka komai yai sai jin abubuwan yake tamkar a shirin film, ta ya Mamani zata b’oye wannan babban al’amari a gareshi... Ai girman mahaifiya ta wuce wasa... Ya cancanci yasan wacece mahaifiyarsa ta asali....
Ya Abida ta isa ta d’ago Aunty Bara’atu, hawaye na gangaro mata take girgiza kai tana furta “Idan da mai laifi ba Ke bace Bara’atu... Tabbas nice mai laifi... Shin na aikata haka ne domin ‘yar uwata ta d’and’ani abinda naji na rashin d’ah ko kuwa na aikata hakane dan ina tsoron kada na kuma rasa wani d’a a karo na biyu... Ina tsoron kada watarana makircinsu yai tasiri akan Ma’aruf k’arami... Mariya a yau na rok’eki gafara ki yafe min.... Ki gafarta min ‘yaruwata....!” Ta k’arashe cikin tsananin rawar murya...
Sameer dake gefe ne ya share hawayen da suka jik’a masa fuska kana ya k’araso ya d’ago Aunty B ya kuma kamo hannun Yaya Abida ya had’e dana Mamy ya rungumesu gaba d’aya, lokaci guda yake furta “A naku fahimtar kunyi Hakane ne ba don komai ba sai don ku cire Ma’aruf cikin k’ingurumin daji mai cikeda duhuwa da tarin had’ari... Na gode maku gaba d’aya, Allah ya k’addari bazan girma taredaku ba amma cikin rahamar Sa da buwayarsa sai ya kuma dawo dani kama yanda kukace INDA RAI Da RABON watarana na dawo gareku zan dawo... Abinda nakeson ji yanzu shine shin ina Ma’aruf Babba wanda naci sunanshi shin ya akai ya salwanta... Sannan maiyasa aka d’aura alhakin b’acewarsa kan mahaifiyata....?”

Wannan karon Mamy ce ta dubesa kana tace “Ni ce zan baka wannan labarin Ma’aruf domin kaw a hannuna Ma’aruf ya b’ace ko nace ‘yan ta’addan suka kashesu shida Fatima....”
“Wacece Fatima..?”
Sameer ya tambaya
Mamy ta numfasa kana taci gaba da fad’in “Fatima itace d’iyar mahaifiyarmu k’arama, kaman yanda na sanar dakai a baya cewa mahaifinsu Soja ne zuwansa Mali ya auro mahaifiyarmu, nida Yaya Abidah acan k’asar Mali aka haifemu bayan mun dawo Nigeria aka haifi Bara’atu da Kuma fatima... Sanda mahaifiyarmu ta haifi Fatima girma ya soma kamata dan lokacin har Yaya Abida tai aure a nan Kano ya auri wani Alhaji Abbas Maidubabe kuma har Allah ya albarkaceta da d’anta k’wara d’aya mai suna Ma’aruf sannan Ma’aruf har ya soma girma dan yakai kusan shekaru shida zuwa bakwai a k’alla... Mahaifin Ma’aruf Alhaji Abbas Maidubabe attajiri ne sannan yana yawan tafiye tafiye na kasuwanci zuwa mak’wabtan k’asashe a wancan lokacin.... Mukan taho nan Kano hutu wa Ya Abida daga can Jada garin mahaifinmu.. Wata rana munzo mata hutu ta daga zata bimu Jada taga gida sannan takai Ma’aruf ma yaga garin mahaifiyarsa, dad’ida k’ari ga mahaifiyarmu data kusa haihuwa ko yau ko gobe... Da k’yar Alhaji Abbas ya amince kan cewa ta tafi taredamu musamman da shike harda d’ansa Ma’aruf a tafiyar, yaron da ya k’wallafa ransa akanshi sabida shi kad’ai Allah ya bashi ga girma da ya soma kamashi... Ma’aruf shine magajin shi shine sanyin ianiyarshi shine yake d’aga ido ya kalla yaji sanyin cewa ya haye gorin ‘yanuwansa da suka addabeshi a baya cewa shid’in shine bai haihuwa dan dik matar data aureshi k’arshe tafiya take ta k’yalesa muddin tana son haihuwa. Ashe RABON shi na tareda Ya Abida... Wani zuwan shi Jada sunkai kaya ya ganta ya aureta har Allah ya azirtasu da Ma’aruf, kuma tin daga kan Ma’aruf shikenan ko b’atan wata bata sake ba.... Kaman yanda na fad’a maku cewa mahaifinmu Soja ne, yayi yak’i yasha fama sosai da miyagun ‘yan ta’adda, ashe suna yunk’urin kafawa mahaifin mu tarko ganin shid’in jajirtacce ne akan aikinsa.. Ya kafa masu k’ahon zuk’a ya hanasu sakat... A ranar da muka iso gida Washe gari suka shigo har cikin gidanmu suka kashe mahaifinmu, ga mahaifiyarmu da tsohon ciki... Haka muka fita a fujajan Muna neman hanyar tsira ganin muma sun nufomu suna yunk’urin kashemu... Da k’yar muka samu muka b’uya basu ganmu ba, dan dama koda sukazo kashe mahaifinmu saida ya tabbata yayi yanda zamu samu tsira tinda yasan shi suke farauta.... Tashin hankali maras misaltuwa muka shiga, da k’yar muka samu muka isa asibiti sabida mahaifiyarmu da har ta soma zuban jini... Kan kace mai akace saidai ai mata aiki a cire abindake cikinta... Hakan kuwa akai... Koda mahaifiyarmu ta farka sunan mahaifinmu kawai take kira tana fad’in sun kasheshi, ganin mahaifiyarmu haka ya kuma karyar mana da zuciya.... tashin hankali dai da ba’a saka mata rana., A haka mahaifiyarmu ta barwa Yayarmu Abidah Wasiya cewa ta kula damu ko bayan babu ita dan tanaji bazata tashi ba... Haka Ya Abidah taita kuka tana sanar da ita cewa in sha Allahu zata tashi kuma zamu tsira gaba d’aya... Ita dai mahaifiyarmu bata daina cewa ta kula damu ba.... Ta tabbata mun tsira daga hannun wad’ancan azzaluman... Kud’in asibiti ya k’are mana ga mahaifiyarmu kwance babu lafiya ga shi k’anin mahaifinmu da ya rage mana shima ba wani k’arfine dashi ba, uwa uba a wancan lokacin babu hanyoyin sadarwa masu sauk’i na zamani balle Ya Abidah ta sanar da maigidanta halnda ake ciki... Gashi k’wakk’waran motsi bamu isayi ba dan idon ‘yanta’addan akanmu yake... A haka Allah yaima mahaifiyarmu cikawa..!!” Wannan karon kowa ya tsane hawayen da ya gangaro masa, Mamy taci gaba da fad’in “Toh daga wannan lokaci Baffah Kawure yace mu tafi muyi nesa da ahalinsa kada laifin d’anuwansa ya shafesa... Dan da k’yar ya yarda ya amince suka tsaya shida Ya Abida dan ganin anyiwa mahaifiyarmu sitira an kaita makwancinta na gaskiya... Sanin cewa nemanmu ake ruwa a jallo yasa nace Yaya ta bari mud’in mu fara gaba nida Dumba da kuma yaran gaba d’ai Bara’atu, Ma’aruf saiko ‘yar jaririyar k’anwarmu, sosai Yaya Abida tamin kashedin cewa na kulada Ma’aruf da Fatima... Nai mata alk’awarin cewa zan kula dasu da yardar Allah kuma bazan bari wani abin ya samesu ba... Muka fito a fujajan muka nufi tashan mota jaririyar tana goye bayana yayinda hannuna ke rik’eda Ma’aruf... Ashe basu bar unguwar ba akan idonsu muka fito zamu gudu, ganin haka yasa naceda Dumba mu raba hanya dan mu b’atar da tinaninsu, Dumba ta rik’e Bara’atu suka soma gudu yayinda nima na rik’i Ma’aruf muka d’au wata hanyar ga jaririya Fatima a bayana... Da k’yar muka samu muka isa tashar mota... Bayan motoci sun tashi ashe suna biyedamu saida mukai nisa da tafiya kana suka tsaida motar da muke ciki, nan na hangesu sai lek’en motoci suke suna neman mace mai goyo da yaro.... Ganin haka yasa na razana sosai, na kwance Fatima na mik’ata hannun Ma’aruf nace su b’oye k’asan kujera kunsan manyan motoci irin na da har sai mutum ya zauna k’asan seat ma... Yayinda suka umarce duk wani wanda Ke cikin motar ya fito.......suka turamu daji da alama basu gane ina d’aya daga cikin mutanen da suke nema ba kuma basuga yaro da goyo a tare dani ba... Babban tashin hankalin da na tadda bayan sun sakomu daga dajin shine babu Ma’aruf babu Fatima a mab’oyar dana b’oyesu....Ta k’arashe cikin wane irin sauti mai ban tausayi...
“Jama’an dake wajen suka tabbatar min ‘yanta’addan sunyi awon gaba da wasu tsirarun mutane dake cikin motar kuma ga dikkan alamu sun kashesu.... Hakan na nufin iftila’in ya ritsa da Ma’aruf da kuma Fatima...”

Ji yayi bakinsa ya bud’e ya soma kwararo bayanai tin daga lokacinda ta b’oyesu k’asan kujerar motar hannunsa rungume da jaririyar... Cikin tsananin mamaki da al’ajabi had’ida rud’ani illahrin jama’an dake wajen suka maida dubansu gareshi....
Idaniyansa sunaci gaba da zuban ruwa yaci gaba da fad’in “A lokacin da kika tabbatar Ma’aruf da Fatima sun samu mab’oya mai kyau tsoro da firgici had’ida tashin hankali ya sanya Ma’aruf ya fice a guje rungume da Fatima, babu wanda yaga wulk’awarsa sai gudu da yake falflawa cikin k’ungurumin daji rungume da jaririyar... Ma’aruf bai tsaya ko ina ba sai tsakankanin wasu duwatsu da yake tinanin Sun tsira kenan daga azzaluman mutanen.... A wannan tsakankanin duwatsu wani bawan Allah ya tsincesu har suka zama ‘ya’ya a gareshi...!” Yana ida fad’in haka ya d’ago fuskarsa da ya jik’e sharkaf da zufa ya kuma gauraye da hawaye yana mai bin illahirin mutanen dake wajen da kallo d’aya bayan d’aya har saida idanunsa suka sauk’a kan matar da ta kasa daina takowa izuwa gabansa cikin wane irin yanayi mai ban tausayi....

SameenaAleeyou📚

*INDA RAI*
_................DA RABO_

*92*

*©️Sameena Aleeyou....✍🏽*

*Beautiful Comments everywhere.... Masha Allah😍🥰 Sameena na maku fatan alkhairi a dik yanda kuke....🤝*
Chapter 140 · 0% Book details