← Book details Inda Rai Da Rabo Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 189 OF 198

Sashe 189

Inda Rai Da Rabo Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Laila ta kuma gyara zama tana fad’in “Ai wllhi k’awata kada kika yarda, wannan ai rainin wayo ne ma, ke kinfi k’arfin wani d’ah namiji ya had’aki da wata mace Siyama... Wllhi ajinki ya wuce nan... Na sha sanar daki girman class d’inki amma baki ganewa... Wllhi kada kika yarda ai mai yuwa ya zab’a ko ke ko kucakiyar yarinyar..” Ta k’arashe tana wani karkad’a k’afafu had’ida kurb’an drink dake bisa center table...
Siyama ta numafasa kana tace “Allah ko k’awata...”
Laila ta kuma jinjina kai tana mai fad’in “K’warai kuwa... Ai nasha mamaki dama har yanzu bakisan da matar ba, tana can gidan uwarsa ya b’oyeta...”
Jinjina kai Siyama ta kumayi kana tace “Ina zuwa k’awata...!”

Mik’ewar Siyama da kad’an Sultan ya shigo kaman yanda Sameer ya sanar dashi ya shige kawai parlorn na bud’e tinda Siyama dai bata nan baisan ta yanda zai soma sanar da ita zancen aurensa ba balle yai maganar dawo da ita....
Sultan ya turo k’ofa ya shigo sai faman muzurai yake.. Kaman daga sama ya hangi Laila zaune saman d’aya daga cikin kujerun da sukaima parlorn k’awanya... Wani irin wawan birki yaja yana watsawa Lailar muguwar kallo... Itama Laila a d’ari ta mik’e tana binsa da kallon mamaki....
Sultan na nunata da d’an yatsa yake fad’in “Ke Uban mai kike gidan nan, shu’uma Wato kin kasa hak’ura da abokina shine bari ki biyosa har Gida koh.....!” Ya k’arashe kaman zai shak’ota....

Dariya Laila tai tana nunasa da d’an yatsa itama kana tace “Ji wannan kwarton mai bin matan mutane ai kai zan tambaya uban mai kake gidan nan.... Kai ko kunya bakaji kana bibiyar matar abokinka... Kai wllhi tir da aboki irinka Sultan....!”

Sultan ya kuma takowa cikin parlorn yana mai furta “Shut your trap you filthy witch... Ga babban abin kunya tattareda Ke kina k’ok’arin snatching mijin aminiyarki... Kuma ma har sau nawa zan miki iyaka da Siyama... Ke wata irin mayyace Laila...!”

Murmusawa Laila tai kana tace “Siyama ta gayyatoni gidan nan dan na k’wata mata ‘yancinta wajen Sameer kasan she cant do without me....!” Ta k’arashe tana jijjiga...

Sultan da mamaki ya cikasa saurin cewa yai “K’arya kike munafuka, Sameer kika biyo sabida kinsan Siyama bata nan shine bari kiyi amfani da wannan daman cos Sameer invited me here....!”

A’a Laila fah ta soma shan jinin jikinta... A d’an daburce tace kana nufin Sameer ne ya gayyatoka...?
Kafin Sultan ya bata amsa Sameer ya turo k’ofar parlorn yana mai fad’in k’warai ni na gayyatosa....
Laila da Sultan suka dubi juna cikeda firgici had’ida tsoro....
Inda inda suka soma suna nuni da juna daidai sanda Siyama ke sauk’owa daga stirs tana mai tafe hannayenta lokaci guda take furta “Well well well.... Wai akace K’ARAHEN MUNAFUKI JIN KUNYA... Tin daga nan duniya munafuki zai soma girban kayan kunya a idon duniya har a isa k’iyama yanda zai girbi babban abin kunya mafi muni sannan ai masa masauk’i a k’asar jahannama dan dama nan ne fadan munafukai.... Laila kinji jiki wllhi kin bani kunya... Muguwa azzaluma mai datse sinnan ma’aiki.... Wannan zaki tashi bomb a gari wllhi... Kinji kunya munafukar banza....!” Ta k’arashe tana mai dungurin Laila da tuni jikinta ya soma karkarwa....
Dikda sanyin AC dake tashi a parlorn bai hana Laila rawar d’ari tana fad’in “Wllhi wllhi Siyama bazan miki haka ba, wllhi sharrin Sultan ne... Ki yarda dani k’awata...!”

“Yimin shiru munafukar banza da wofi....Babu wani k’arya da zaki kuma min dan naji komai dik abinda kuka tattauna a office d’in wannan babban munafuki kwarton banzan.... Dan haka babu ni babu Ke...Ke Billahillazim ko hanyar da nake bi na kuma ganinki sai na baki mamakin da baki tab’a shan irinsa ba tsawon rayuwarki.... Banza kucaka wllhi ko a layi babu abinda mijina zai dake...!” Ta juyoga Sultan dake muzurai cikeda kunya... Kafin tai magana Sameer ya katseta da fad’in “No k’yalesa Partner namu dashi ne... Babu mai fita a gidan nan kekam...!” Ya k’arashe yana mai jefa wayarsa cikin aljihu had’ida k’urama agogo idanu tamkar mai jiran sak’o....

Sultan sai faman yarfe zufan dake kuma keto masa yake, ko duban idanun Sameer ya kasa... Yayinda Sameer d’in ya kafe agogo da idanu yana k’irga dak’ik’ai...
Laila tazo zata shige kai a k’Asa tana cazgan kuka, Siyama tai saurin tare gabanta tana fad’in “Kije ina... Ai Babu yanda zakije sai naga k’arshen munafuncinki.... Laila na hawaye ta durk’usa tana rok’on Siyama gafara, Siyama ta finciki skirt d’inta tana fad’in “Ni karki tab’ani bak’ar ashana... Karki tab’ani balle ki shafa min zunubin annamimanci...!”

Sultan ya d’ago da k’yar kaman zai magana sai kuma suka jiyo ana danna bell.... Da tsananin mamaki Sultan ke duban Sameer da tuni ya nufi k’ofa fuska a murtuke kaman bai tab’a dariya ba ga wani irin duba da yake watsawa Sultan d’in wanda Ke kuma gigita Sa.....
Sultan bai ida mamaki ba saida yaga ‘yansanda biyu sun shigo Sameer na nuni da Sultan d’in yana fad’in “Gashi nan officers ku tattare shi.... Kwarto ne mai bin matan mutane....!” Ya k’arashe yana mai ci gaba da watsawa Sultan d’in k’azamin kallo....

Sultan da polisawa Ke k’ok’arin cuffing d’insa fad’i yake cikin daburcewa.... No no Sameer... No Sameer you can’t do this to me...!” Ya kuma duban officers yana fad’in “No no officers you can’t just arrest me.... Wai mai nai ne... Sameer what is this... Sameer let’s talk sensibly, you can’t do this to me... Haba abokina...!”
Cikin tsananin fuci Sameer ya k’araso gabansa yana furta “Did you just call me your friend...? Lallai na yarda bakada kunya Sultan.... Amma tarbiyan da baka samu ba ina mai tabbatar maka zaka samu yanzu... Officers take him away...!” Ya k’arashe yana mai watsa masa knazamin kallo...

Laila ta yunk’ura zata tashi ganin ba’a had’a da ita ba... Lokaci guda Siyama ta janyota ta shiga zuba mata dundu daga yanda take durk’ushe tana k’wallawa Raihana kira ta mik’o mata muciya a kitchen....
Laila sai ihu take tana neman agaji dan wani ikon Allah ta kasa katab’us.... Da k’yar Laila ta samu ta zille daga bugun da Siyama ke mata tako ina... D’an kwali a hannu Ta fice a guje haka takalma sai ihu take yayinda Raihanah da Ijlaal dake mak’ale jikin staircase sukaita k’yak’yata dariya....

Laila kaw tana ficewa wasu karnukan bakin layin suka kuma rakota sun ganta tamkar wata mahaukaciya sabuwar kamu.....

*****

KANO

Two weeks After

Abubuwa da dama ne suka faru a d’an wannan tsakani, su Sameer da Raihanah sun taho Kano yayinda suka baro Siyama da Ijlaal can Kaduna, cikin abubuwan da suka faru tsakanin harda shiga kotu, ga shari’ar su Baba Alhaji ga kuma na Muhibbah daga b’angaren Engr, gaba d’aya Engr d’in bai samu ya zauna ba, ga kuma zab’ensu da tuni ya kunno kai dan har anyi na shugaban k’asa da ‘yan majalisun tarayya saiko sauran Gwamnoni da ‘yan majalisun jihohi.. Uwa uba ga Ammah a ‘yan kwanakin bata gane jikinta hakan yasa Zulfa’u da yaran sukaci gaba da zama nan gidan Amman dan bama su sami natsuwar komawa can gidan Engr ba..
Tuni Engr ya yowa mahaifiyarsa da matarsa visa dan da zaran anyi election kawai ya yanke shawarin tattaransu gaba d’aya harda yaran nasa dan suje k’asa mai tsarki a duba jikin Ammah daga cen suma su samu suyi aikin umrah....
Saidai har yanzu ko labarin hakan Zulfa’u bata samu ba, toh inama ya zauna balle ta sakashi idanunta, tinda aka soma election d’in nan sai su kusan kwanaki biyu basu sakashi idanunsu ba kullum cikin meeting da sabgogi yake, ita har tausayi yake bata ga trial d’in Muhibbah da shima yai tsayin daka akai dan sam hidimar siyasarsa baisa yayi neglecting Muhibbah ba dik randa za’a shiga kotu sai yai squeezing ya halarci zaman dikda cewa Muhibbah nunawa take bata buk’atarsa, k’arshe dai har ta soma saduda dan satin sama satin zab’ensu Engr Kotu zatai deciding makomar su musamman data fahimci cewa basuda wani k’wakk’waran shaida da zai wankesu gaban Alk’ali daga ita har accomplices d’inta su Bash...

A b’angaren su Hafiz kaw.....

SameenaAleeyou📚

*INDA RAI*
_................DA RABO_

*111*

*©️Sameena Aleeyou...✍🏽*

A b’angaren Hafiz ya samu sauk’i sosai har an sallamesa ya komo gida yanda yake ci gaba da samun sauk’i a hankali, yau d’in babban bak’onsa ne ya kawo masa ziyara wato Akram....
Hafiz na kishingid’e Akram na daga gefe saman sofa suka kuma k’yak’yata dariya sanda Akram d’in ya d’ago masu zancen dajin Babba Duna.... Hafiz yace “Gashi yau kaman ba’ayi shi ba, toh haka Duniyar ma take gaba d’aya... Wataran sai a wayi gari babu kowa an shafe kowa an kuma shafe komai...!”
Akram ya jinjina kai yana mai furta “Wannan haka ne, Ubangiji yasa mu dace...”
Hafiz ya amsa da Ameen kana ya k’arada “Ya labarin election..? Kasan da har nayi fushi dakai sai kuma na tina yanzu zama bai ganku ba tinda aski ya taho gaban goshi...”
Chapter 189 · 0% Book details