← Book details Inda Rai Da Rabo Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 113 OF 198

Sashe 113

Inda Rai Da Rabo Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Shiru yai had’ida d’aura hab’arsa saman tafukan hannayensa ya shiga tunanin abinda Baba ya sanar dashi gameda karan kansa da k’anwarsa Daula a lokacinda Baban ke jinyarsa ta ajali.....
_Ma’aruf! Ma’aruf!! Shine kalama guda tak da kake fad’i a lokacinda na tsinceku.... Ko an tambayeka sunanka iyakacin abinda kake fad’i kenan, hakan ya bamu tabbacin tashin hankali ne daka tsinci kanka ciki ya shafe maka tinaninka wanda ka mance komai saiko kalmar sunanka da bai fice a kwanyarka ba da kuma saman harshenka... K’asar duwatsu da muk’e tonon zinari a nan na tsinceku kaida yarinya jaririya k’udundune cikin zanin goyo, a lokacin bazaka wuce shekaru shida a duniya ba, ga kuma jaririyar daka rungumeta cikin hannunka... Na tambayeku ya akai kuka kasance a wannan k’ungurumin daji mai cikeda had’ari baka iya cemin komai ba sai kalmar sunanka Ma’aruf da kaketa nanatawa, a lokacin da muka tsinceku nida abokan tafiyata sai naso dank’aku hannun d’aya daga cikin yarana Kafin mu mik’a cigiyarku ga hukuma, amma koda mukazo tafiya sai kayi gudu ka kama k’afata kana fad’in kalmar Baba kuma kak’i kowa ya amshe jaririyar dake hannunka, ganin haka yasa na d’aukoku na kawoku gida wajen iyalina dashike ni a lokacin banida d’a ko k’wara dukda kasancewar nid’in sabon aure ne ban jima da yin aure ba, wani abin mamaki shine sanda na kawokuga Iyalina sai Allah ya jefa k’aunarku a zuciyarta, na sanar da ita yanda na sameku can Mining side k’asar duwatsu na tsinceku, tausayinku ya cika zuciyarta musamman wannan jaririya da aka raba da mahaifiyarta, na sanar da iyalina cewa zaku d’an zauna na kwana biyu likita ya dubaku a maku magani kafin na mik’akuga hukuma, mukai matsaya akan haka nida ita, bayan kwana biyu da shak’uwa ya kuma shiga tsakaninku sai cemin tai itakam bazata iya rabuwa daku ba, ba kaman Daula wacce ita da kanta ta rad’a mata wannan suna, dikda cewa dangina da nata basuso haka ba musamman da sukaga bamuda ‘ya’ya sai ku d’in kawai ga kuma tarin dukiya da mahaifina kedashi wanda ni kad’ai zan gajesa bayan bashi duniya ni kuma kune magadana don tuni nayi hakan a rubuce tinda banida mahaifiya banida yayye ko k’anne saiko dangin nesa dagaku sai iyalina Hafsatu wacce ta rigayemu gidan gaskiya kaman yanda ka sani, ciwon dajin mama shi yai ajalinta...._ Wannan karon Engr goge hawayen da suka siraro masa yai sanda ya tuna Mamarsa mai tsananin k’aunarsu wacce haihuwarsu ne kawai batayi ba amma duk wani kulawa da k’auna da uwa ke baiwa ‘ya’ya tabbas Mama Hafsatu ta basu wannan, Ubangiji yakai rahama makwancinki Mama, da ace mutanen duniya zasu zama irinki da Duniyarmu ta cika da albarka... Ya saki kalla uwar murmushi kafin yaci gaba da tuna jawabin Baba a gareshi...
_Kaman yanda ka sani mahaifina Alhaji Mutallab maiDala shine mammallakin MUTALLAB’S Mining Company... Kamfanin hak’an ma’adanai na k’asa kama daga zinari zuwa duk wasu duwatsu masu daraja, Babana Mutallab Maidala ni kad’ai Allah ya bashi baida kowa sai tarin dukiya, dukiyarda nan gaba zaku gada kaida ‘yaruwarka Daula... Ma’aruf ka rik’e Daula amana ka kula da ita dikda cewa nasan na mik’ata hannun da za’a kula da ita, amma kasa ido akanta dikda haka, Daula itace sanyin idaniyana... Ka kular min da ita.. Sannan Muhibbah..._ Wannan karon nannauyan ajiyan zuciya ya sauk’e kafin yaci gaba da tinanin wasiyayyar Baba gameda Muhibbah a gareshi...
_Muhibbah amanace a gareka kaman yanda ka sani mahaifinta amini ne a gareni, duk cikin d’iyoyinsa ya kasance yafi son Muhibbah, wannan dalili yai mata lak’abi da Muhibbah ya kuma rok’i alfarmata kan nai mata duk abinda takeso bayan bashi a raye ko menene matuk’a baifi k’arfina ba, wannan dalili yasa sanda tace duniyar nan bata son kowa sai kai banyi k’asa a gwiwa ba na aura maka ita, nasan baka sonta biyayya kawai kamin a matsayina na Uba a gareka... Ubangiji ya maka albarka yasa watarana kayi arba da danginka na asali dikda cewa kasha sanar dani cewa kaida Daula baku da iyayen da suka wuce nida Hafsatu, amma ina fata wataran INDA RAI Allah ya sake had’aku da asalin iyayenku... Ma’aruf ka rik’e amanan mutum Biyu Matarka Muhibbah ko mai zata maka da kuma K’anwarka Daula dikda cewa tana gidan aurenta..._
Wad’annan sune wasiyyan Babanshi a gareshi.... Yasa duka tafukan hanbayensa ya share fuskarsa had’ida fuzar da iska mai d’umin gaske, dubansa yakaiga Muhibbah wacce ke baccinta hankali kwance kana ya k’ura mata idanu tamkar mai tinanin wani abin, ya d’au lokaci yana duban nata kaman mai nazarin wani abu har saida ya soma jiyo kiraye kirayen farko na assalatu kana ya muk’e ya nufi bathroom da zummar d’auro alwala... Raka’atanil fajri ya soma gudanarwa a gida wanda dama d’abi’arsa ce duk ranar duniya kafin ya fice masallaci sallan asubahi....
Gaba d’aya yau d’in wane iri yake jinsa....

***

KADUNA

Babu abinda Ammi ta fasa na shirye shiryen Bikin Khalid da Yesmin, ko Daddy bai tsaida Rana ba a cewarta ita zata tsayar saidai dik abinda zai faru ya faru, yauma sun ida waya kenan da Aunty Mahaifiyar Yesmin Don Yesmin d’in ta matsa mata ita zata dawo taga Khalid d’inta ta gaji da zamar Abuja, Ammi tace ta dawo kayanta ai duka gida ne da Abujan da Kadunan tinda mahaifiya takema Yesmin...
Khalid na kishingid’e d’akinsa yana duban hotunan Nabilah da ya sata a dp d’inta shi kad’ai sai sakin murmushi yake yana tina farkon had’uwarsu da kalan tsiwar da tai masa gashi tin jiya yake neman wayarta ya kasa samu, ji yake kaman yai tsuntsuwa ya gansa a Kano, kaman daga sama sai ganin hamshak’an Gezna yai farare da kaloli Ammi ta watsa saman rug tana fad’in “Gasu nan tinda kai bakasan kai shiri ma kanka ba....”
Da tsananin mamaki ya tashi ya zauna sosai... “Ammi wad’annan fah... Na menene... Kinsan dai banson saka kayan da daga nesa za’ai noticing d’ina, banson saka kaya masu haske da d’aukan ido ni ba wani basarake ba...” Baikai aya ba ta katsesa da fad’in “Kai tafi can ka rufewa mutane baki, wane ango ne ka tab’a ganinsa babu kwalliya ranan bikinsa...”
Sai yanzu ya fahimci kayan na menene.... Ammi taci gaba da fad’in “Sai ka zab’i color d’in da zaku saka ranan dinnner shisa na had’o maka da Golden brown da kuma Royal blue tinda nasan ranan d’aurin aure White zaku saka... Amma inaga dai ka zab’i golden brown d’in tinda naji Yesmin d’in ma Momynta na cewa tafi son golden d’in akan blue d’in, tinda dukanku farare ne sosai zai haskaku... Gameda huluna kuma munyi magana da Maman Falmata ita take sak’ama akasarin gwamnoni da manyan ‘yan siyasa zata turo kalolin designs sai ka zab’a, hula ne masu kyau sak’ar Maiduguri, ai dai zanna kake sakawa inji...”Tinda ta soma magana ya rafka uban tagumi yana dubanta....
“Inata magana ka zuba mun ta mujiya, kaga bazan zauna na zuba maku idanu kaida Babanka ba, na biye nashi sam bazai maganar auren nan yanzu ba...”

“Toh wai Ammi saurin mi akene....? Kuma ma banda abinki Ammi Daddy ai shine mai karb’a min auren koh... Mu jira muga gudun ruwansa tinda shine wakilina....”
Tinda ya soma magana take aika masa muguwar kallo, k’wafa tai kana tace “Ai bakinku d’aya dakai dashi, idanma wani abin kuke b’oye mun Allah zai kamaku, dik abinda kuke k’ullawa Allah zai tonosa..” Tasa kai zata fice Khalid dake k’unshe murmushinsa don yanzu abin Ammin dariya ya soma basa ya bud’e murya yace “Kayan fah Ammi, na biyoki dasune....?”
Harara ta galla masa kana tace “Ka tattara ka kaisu d’inki ban janye k’udirina ba...”
Yai murmushi yana mai bin mahaifiyar nasa da kallo, dukda hali irin nata haka nan yake k’aunarta baida ya ita, tausayinta ya kamasa sanda ya tuna tabbas akwai gagarumin tashin hankalin dik randa tasan Daddy nada wata matar harda Yara... Khalid ya dafe fuskarsa da tafukan hannayensa biyu yana tunanin ko ba dad’e ko ba jima wannan ranan tana nan zuwa, ranan da Ammi zatasan wannan batu... Baisan mecece makomar family d’insu ba dik randa wannan labari ya fito fili... A hankali ya sauk’e siririyar ajiyan zuciya, murmushi kwance saman fuskarsa sanda ya tuna ‘yan k’annensa haka kurum yaji yana son magana dasu, lokaci guda ya shiga neman layin Aunty Daula....

***

ABUJA

Suna tsaka da batun auren Khalid d’in wayarsa ta shigo mata, nuna masa screen d’in tai murmushi saman fuskarta take furta “Kaga ango na kira ana batun shi....”
Daddy ya murmusa kad’an kana yace “Ai naga alama yanzu Khalid yafi ji dake sama dani, d’auka amma karki sanar dashi shirina, ba yanzu ba....”
Jinjina kai tai kana ta d’au wayar da sallama... Gaisawa sukai cikeda barkwanci kana ya tambayi k’annensa, Aunty Daula tace dama tasan kiran nasu ne, tuni ta mik’e ta nufi playground tana k’walla kiransu tana fad’in ga yayansu on the phone, ai har suna rige rigen amsar wayar suna zuba masa shagwab’an yaushe zaizo shi...
Daddy dai murmushi kurum yake zuciyarsa na masa wani irin sanyi...
Aunty Daula ta dubi Daddy tace “Toh ya maganan su lefe da sauransu fah...?”
Daddy ya jinjina kai yace “Wannan wuk’a da nama na hannunki uwar ango... Ke zaki shiga kasuwa kiyi komai...”
Aunty Daula ta jinjina kai tace “An gama rankashi dad’e... Amma nidai gani nake da an sanar da Khalid don shima yai nasa wasu ‘yan shirye shiryen k’asan aure fah ba wasa bane, maganan lifetime commitment ake...”
Jinjina kai yai a hankali kana yace “Nasan da wannan, abinda yasa banso maganar ya isa kunnen Khalid yanzu, nasan zai iya sanar da Farida tinda mahaifiyarsa ce, zaiji sam bai kyauta ba dole ya sanar da ita, itakuma zatai amfani da k’arfin ikon da take dashi akansa a matsayinta na mahaifiyarsa ta b’ata komai ta hanashi Farin cikinsa, I’m doing this for my son, b’oye masa da nayi ba komai bane face sabida cikan burinsa... Daula INDA RAI zan cika burin d’ahna Khalid da izinin Allah....”
Murmushi ta saki mai taushin gaske ta saki had’ida d’aura kanta bisa kafad’ar mijin nata tana mai lumshe kyawawan idanunta....
Chapter 113 · 0% Book details