← Book details Inda Rai Da Rabo Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 159 OF 198

Sashe 159

Inda Rai Da Rabo Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Laila ta dubi Sultan... Siyama ta subesu cikeda mamaki dan batai zaton akwai wani abinba kuma iyakaci accident d’in Daddy suka sanar da ita, suka kuma ce zasu rakata wajen Ammi su taimaka mata wajen sanar da Ammin.... Sinkayo muryar Sultan Siyama tai yana ci gaba da fad’in “Already family d’insa sun sani, dan dik suna tare a asibitin ciki harda d’anki Khalid...!!”

Gaban Ammi yai wani irin tsinkewa ya fad’i, ta d’an girgiza kai tana fad’in “Kana nufin kace min Anty Hanne sister ta da Khalid sun sani basu sanar dani ba....?”

Wannan karon mik’ewa tsaye Sultan yai kana yace “Ban tsamman sister d’inki ta sani....”
Daga Ammi har Siyama duban mamaki suke bin Sultan dashi yayinda Laila ta tari zancen da fad’in “Ammi shin kinsan mijinki nada wata mata...?”
Gaban Ammi ya bada Dumm! Dan ta tsani a d’ago labarin mijinta nada wata mata cen k’asar turai dikda ba wani zuwa wajenta sosai yake ba....
Ammi ta tab’e baki kad’an kana tace “Nasan yanada mata Helen, so kuke kuce ita da take daga can America ta rigani sani ko kuwa...?”
Sultan ya girgiza kai a hankali kana yace “Ban tsamman matar mijinki baturiya ce... Dan wannan bahaushiya ce ‘yar k’asar nan kuma musulma sannan harda yara tanada...”
Baikai aya ba Ammi ta katsesa da fad’in “Kai rufe min baki bana son iskanci da rashin kunya... Ku wuce ku fice min a gida idan abinda ya kawoku kenan....!”
Hayaniyar Ammi ya sanya Yesmin dake bacci fitowa babu shiri, Kubura dake kitchen itama ta fito a guje Mama Kaltume mai dafa abinci itama ta nufo parlorn babu shiri jin muryar Uwar gijiyar tasu cikin tsananin tashin hankali....
Siyama data tari zancen kaman wani almara, takowa gaban Sultan tai tana binsa da kallon mamaki lokaci guda take furta “Sultan... Mai keke nufi...? Are you sure of what you’re saying...? Ka ko san mai kake fad’a....? You’re talking about my Dad here Sultan....!”

Jinjina kai Sultan yai alamun tabbatarwa kana yace “I’m quite certain Siyama... Your Dad has another family here in Nigeria... Daga source mai kyau na sami wad’annan information d’in, Nazir aidai kinsan Nazir abokinmu nida Sameer toh shi ya sanar dani komai dan yana d’aya daga cikin likitocin dake rik’eda case d’in Daddy.... Siyama I’m sorry you had to find out like this ... Bansan maiyasa Sameer zai b’oye miki ba, dan idan har na sani toh definitely shima ya sani.... Ace Dad d’inki yana cikin hali irin wannan na rayuwa ko mutuwa bai sanar dake ba... Ko shakka babu maybe akwai abinda yake b’oye miki...!”

Siyama da tuni ta yankin jiki ta zauna gijif cikin kujera girgiza kai take tana fad’in “No Partner bai sani ba, da ace ya sani da ya sanar dani... The only person dake da laifi a nan Khalid ne....”

Yesmin da bata jima da sauk’owa ba tai karaf tace “Cousin karfa kiga laifin My K laifi na Daddy ne da dik babu wanda yasan da labarin yanada wata mata har saida Allah yasa da asirinsa zai tonu yayi accident koh Ammi...?” Ta k’arashe tana duban Ammi wacce ta koma tamkar bata a wajen sabida yanda duniyar Ke juya mata... Ahmadinta bazai tab’a munafuntarta haka ba... No hakan ba mai yuwu bane... Itafa bata yarda da koda kalma guda bane data gama sauraro daga bakin Sultan da Laila... She needs to go and see it herself... Dole taje ta tabbatarwa idanunta....
Lokaci guda tamkar wacce aka sinkara ta nufi upstairs a d’imauce tamkar zata kifa.... Siyama tabi bayanta a d’ari tana tanbayarta ina zata... Ba tareda ta dubeta ba sai haurawa sama kurum tai ta isa closet ta shiga firfito da kaya tamkar hankalinta bai jikinta....
Siyama tai saurin rik’eta tana tattara kayayyakin da Ammi ke firfito dasu tana watsasu saman gado....
“Ammi please, you need to calm down first.... Ina zaki haka...? Dan Allah Ammi please...!”
Katseta tai da fad’in “Tambayata kike ina zani Siyaam... Are you really asking me that...? After what you’ve just heard..... Har kina tambayata ina zani....? Of course Abuja zan tafi... Right this moment domin na tabbatar ma idanuna gaskiyar abindake faruwa.... First accident sannan kuma ga wata mata da bamu sani ba... Who knows what we’re going to find out next.... Dan haka yanzu babu b’ata lokaci zan tafi Abuja... And don’t you dare think of stopping me....!” Ta k’arashe tana mai kuma jefa kayan fuskar Siyama....
Cikin sauri Siyama ta fice tana mai dokawa Kubura kira, nan take ta umarci Kubura ta hau sama ta shiryama Ammi kayanta zasuyi tafiya yanzu yanzu.... Yesmin tai karaf tace aiko itama zataje tinda ance Khalid na can.... Cikin mintuna k’alilan sukai shirin tafiya Abuja.... Ammi, Siyama, Yesmin saiko Kubura...

Su Laila da Sultan suna ficewa suka kwashe da dariya, Laila tace “Kai amma naji dad’in wannan al’amari... Kai wannan aboki naka yaci kyauta.....”
Sultan yai wata k’asaitacciyar murmushi kana yace “Kinga yanzu Siyama zata kuma zama furious da Sameer, zatace yasan Daddynta yayi accident bai sanar da ita ba, haushinsa zai ninku cikin zuciyarta.... Daga nan mu kuma sai mu executing all of our plans.... Sameer zai rabu da Siyama once and for all, zan mallaketa Ke kuma zaki mallaki Sameer, dan Sameer ba komai ya rasa daga Siyama sai kula, kece zaki bashi wannan kulan Ta yanda zai mance ya tab’a soyayya da wata mai irin sunan Siyama... Kinga daga nan shikenan....”

Laila tai k’asataccen murmushi kana tace “Ka biyani Sultan, gaskiya kwanyarka naja amma baikai na My Sameer ba....!”
Suka kwashe da dariya a tare kana Sultan yaja mota suka wuce yana mai fad’in su jira suji wayan Siyama idan suka isa Abuja suka tarar da abinda suka fad’i masu gaskiya ne...

***

A can Kano kaw koda Jami’an tsaro suka isa gidan Hafiz domin interrogating nasa basu taddashi ba saiko matarsa Sawwama, dikda cewa Sawwama ta razana da ganin jami’an tsaro bata bada wata k’ofa da jami’an zasu fahimci tanada saka hannu a b’acewar Akram d’in ba hasalima sai k’ok’arin implicating Hafiz d’in da ta kumayi tana nuna masu cewa itama zaman hak’uri take dashi dan gaba d’aya ya makance da soyayyar Zulfa’u ko hakkinta na auratayya baya bata a matsayinta na matarsa...
Ta kuma yin raurau da idanu tana ci gaba da fad’in “Officer ku taimaka ku zak’ulo yanda yake wllhi ni kaina tsoro yake bani a halin yanzu... Idan dai akan Zulfa’u ce na yarda mijina zai iya aikata komai....!” Ta k’arashe tana matsan k’wallan k’arya...
D’ansanda guda d’aya yai wasu ‘yan rubuce rubuce jikin wata k’aramar takarda kana ya dubi Sawwama yace “Madam zamu tafi for now, amma muna iya dawowa ko yaushe sannan idan kinji wani abu gameda mijinki, inform us right away kinji koh....”

Jinjina masa kai tai da saurin gaske yawa mutuniyar arziki kana tace “An gama yallab’ai... Na gode fah...!”

D’an sandan dake sanye cikin bak’ar suit instead of kaki ya jinjina kai shima kana yai mata godiya suka fice sauran biyun na biye dashi...

Suna ficewa ta sauk’e nannauyan ajiyan zuciya kana ta isa ta d’auki wayarta da sauri... Bugu biyu a na uku Babba Duna ya d’aga....
Sawwama taci gaba da fad’in “Babba karkaji komai na riga nayi implicating Hafiz, babu wanda zai zargeni balle kayi tinanin za’a zak’uloka....”

Babba ya kwashe da wata jahilar dariya kana yace “Ke dama kina tinanin ina tsoron wani k’aramin maras kunya mai saka uniform a k’asar nan ne.... Ki k’yalesu su nemi idan zasu iya... Kin kyauta ma kanki da kika zame kanki amma ki sani mijinki ya shigo hannun Babba kenan ya zama namu....”

Sawwama ta fuzar da iska kad’an kana tace “A halin yanzu Hafiz bazaimin wani amfani ba, amma inada sharad’i Babba....”

Babba yace “Ina jinki mecece sharad’in Ki.....?”

Sawwama ta mik’e tsaye sosai kana tace “Kasan a shekarun baya nida mahaifiyata mun baka ‘yandaudu d’ai d’ai d’ai har guda uku kai waqfin daji dasu kai asiri da al’auransu wanda har rana mai kaman ta yau babu su babu dalilinsu, banaso kaima Hafiz wannan mummunar abu... Idan komai ya lafa ka sakeshi ya dawo cikin ‘yanuwansa kafin nan ni kuma nayi tafiyata zuwa waje mai nisa....”

Babba ya kuma fashewa da dariya kana yace “Bakida matsala amma bazan miki alk’awari ba.... Dik abinda ya faru da mijinki shi ya janyo dan ba’a bijire ma Babba.....!” Daga haka bai jira cewarta ba ya katse kiran

Juyowa yai yana duban Hafiz da jini ya b’ata masa fuska sai haki yake, an d’add’aure masa hannaye da k’afafu ga Akram daga gefensa shima a d’aure.... Babba ya shafi fuskar Hafiz yana mai furta “Pretty boy Kaga yanda dik kasa yaran Babba sukaji rauni ma wannan kyakkyawar fuskar taka.... Banso abubuwa suka kasance haka a tsakaninmu ba.... Maiyasa zakace ka juya ma Babba baya kai waye da zaka shigo dajin nan kace zaka bada order alhalin Babba ke mulkinta....?”
Ya kuma murmusawa a hankali kana yace “Wato ka fahimci kaima ka zama loser bari ka taimaki d’an uwanka loser ka fitar dashi daga dajin nan koh...? Toh ka b’ata....”

Hafiz na tananin haki yake furta “Inace ni ne nan na kawoshi, toh nace ku fitar dashi, ku rik’eni instead... Shi hakan bai maku ba....?”

Dariya Babba ya kumayi kana yace “Idan kyawawan maza irinku har guda biyu suka shigo hannun Babba kuna tinanin zaiyi sake su kufce masa ne....? Kashhh! Hakan bamai yuwuwa bane dan dikanku biyu Babba ya yaba daku... Kuma da sannu zaku zama mallakin Babba, hakan yasa ba’a had’aku waje guda da sauran mutanen da muke garkuwa dasu ba..... Ku huta tagwayen amare na...!!!” Ya k’arashe yana mai kuma bankewa da wata irin dariya maras dad’in saurare...

Hafiz ya juyo a hankali yana duban Akram dake tsananin huci yana bin bayan Babba Duna da mugun kallo wanda yaransa suka sanyashi tsakiya suka nufi wajen mutanen da suke garkuwa dasu dan amsar kud’in fansa....

Hafiz yai tsaki a hankali yana mai kuma fincika cikin d’aurin da aka masa.... Akram ya tsaresa da jajayen idanunsa ga tsananin huci da yake.... A zuciye Hafiz yace dashi “What...!? Meye ka wani k’uramin idanu....!!”

Fincika Akram yai yana fad’in “The nerve...! Har kanada bakin daka min tsawa bayan kai ka jefani a wannan bala’ain....!”
Chapter 159 · 0% Book details