← Book details Inda Rai Da Rabo Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 186 OF 198

Sashe 186

Inda Rai Da Rabo Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Baffah ya dara yana kuma lek’o kansa ta glass d’in mota yake ci gaba da fad’in “Ban isa ba ai Gimbiya Yusrah ta bada sak’o a kawo wa k’awarta kaga dole na tsaya na bada sak’on Sarauniya kada a hukunta ni...”
Darawa kad’an kurum Khalid yai kana sukai sallama, Nabilah kaw mamaki ne tsantsan ya cikat... D’an darawa tai a hankalk ita kad’ai tana mai kuma shan mamaki kana tace “Shegiya Yussy Wato ashe ashe dai soyayya suka k’ulla da Baffah Aiko asubahin fari zan kirawo ‘yar duniya nasha labari...” Jin kaman sautin steps d’insa alamun yana haurowa ya sanyata fad’uwan gaba, tai saurin k’arasawa tana janyo mayafinta... Tsulum ta zauna saman gado had’ida rufa mayafin, sai faman wasa da yastun hannunta take....Tana jin alamun ya shige nasa d’akin ta sauk’e ajiyan zuciya had’ida yaye mayafin... Tinanin Yusrah ya kuma fad’o mata, ai bazata iya jira till tomorrow ba, cikin sauri ta janyo wayarta ta shiga dialing layin Yusra, bata d’aga ba, nan ta kuma bud’e shafin sada zumunta na whatsapp tana magana ma Yusran ta nan... Shiru shiru tana jiran reply d’inta har dai ta soma bin sauran wasu sak’onnin nata da suka shigo wayar yanda ta lek’a group d’insu na makaranta ta tadda tarin congratulations da fatan Alheri da akaita aiko mata.. Murmushi take tana bi d’aya bayan d’aya tana karantawa... Hardai ta soma kaman gyangyad’i... Sam bataji alamun shigowarsa ba sai fitannen k’amshin shower jell had’ida wasu arnan perfumes da sukaima k’ofofin hancinta sallama... Tai saurin ware idanunta sai ganinsa tai duk’e gabanta ya k’ura mata idanu, kyakkyawar murmushi saman fuskarsa da hasken k’wan wuta ya haske tarau... Ta d’an zabura ta tashi zaune tana kuma dubansa, sanye yake cikin silk jallabiya mai ruwan sararin samaniya... Ta shiga murtsuka idanunta da hannayenta biyu... Dariya taso basa kana yace “Wai haka kike bakida wahalan bacci... Oya taso kije kiyo alwala ina jiranki...”
Ya k’arashe yana mai mik’ewa had’ida zama bisa gadon, lokaci guda ya kafe wayarsa da idanu kaman mai tura sak’o...
Kaman mai tsoron sauk’owa daga saman gadon haka ta sakalo k’afafunta k’asa, harga Allah wani irin fad’uwan gaba da nauyinsa takeji... A hankali ta furta “Nifa nayi sallah...!”

Ba tareda ya dubeta ba yace “Na sani zamu sake wani daban ne...”
Idanunsa naga wayar salulansa yai maganar...

A hankali ta mik’e daga saman gadon ta soma tafiya tamkar kazar da k’Wai ya fashema a ciki... Ya saci kallonta yana mai sakin murmushi da gefen bakinsa...

Yana nan zaune wajen ta fito sai faman yarfe hannunta take, neman hijab ta somayi, aka kaw yi sa’a tana bud’e first drawer ta gansu a jere, ta d’auko guda d’aya tazira kana ta k’araso cikin d’akin kanta a k’asa... Khalid da tin fitowarta idanunsa ke kanta mik’ewa yai ya nufota yana mai karantar yanayinta... Saida ya d’anyi gyaran murya kana taga ya shiga janyo hannunta yana fad’in “Let’s go...!”

Ita dai d’aga k’afafunta kawai take tana biye dashi har suka iso d’akin nasa wanda shima ya had’u iyaka had’uwa....

Nan ta tadda har darduma ya shimfid’a masu, gidan gaba da’aya sai k’amshi yake dan su Siyama saida suka tirara gidan da turarruka masu k’amshi kafin su tafi... Nan Khalid yajasu sallah raka’a biyu... Ya jima yana addu’o’i da mik’a godiyarsa ga Rabbil Izzah da ya nuna masa wannan rana mafi kyau cikin rayuwarsa... Tana jin sanda ya juyo ya d’aura hannunsa na dama saman goshinta ya karanto addu’o’in sabbin aure kaman yanda yazo a shari’a... Nan yai mata ‘yan tambayoyi gameda addini musamman abinda ya shafi fiqhu, ita har mamaki ma abin yaso bata ganin yanda yake zayyano mata tambayoyi gameda addini sam batai zaton yanda yake d’an gayun nan yasan addini har haka ba....

K’uri yai mata yana kallon yanda tai relaxing jikin bedcover da ya sauk’o ya rufe jikin gadon Daga k’asa... Ya d’an labgab’e kai kad’an kana yace “Ya naga kina lumshe idanu badai bacci kikeji ba...”
Gajeren murmushi tai ba tareda cewa komai ba...
“Wait, you can’t go to bed without eating anything... I’ll be right back...” Bai jira cewarta ba ya fice...

Ta samu daman k’arema d’akin nasa kallo... A ranta take cewa Wato shi fah wannan andai yi d’an gayun gaske, ta kuma tab’e baki kad’an kana ta isa gefen tv dake a cikin d’akin tana bin cd plates na TV games dake zube wajen da kallo... A ranta tace oh shi kuma k’ato dashi Wai game yake bugawa... Nan ya taddata tsaye tana duba plates d’in...
Ya isa saman rug ya aje gasasshiyar chicken da yoghurt d’in dake hannunsa, bata ankara ba sai jin jikinta tai cikin nasa ya mata rumfa Ta baya, hannayensa ya mik’o ya d’aurasu saman nata yanda tai rik’eda gidan cd plate d’in ya shiga juyawa tareda hannunta, tamkar mai rad’a saitin kunnenta yake furta “Do you want to play...?”

Nabilah da gaba d’aya a daburce take d’an girgiza kai tai kana tace “Besides I don’t know how to play TV games...” Dagajin yanda take maganar kasan da k’yar take....
Idanunsa a lumshe still hab’arsa saman wuyarta yake furta “Don’t worry I can teach you... Besides indai muna tare dole ki iya playing... Come let’s eat first...!” Ya k’arashe yana mai janyo hannunta yai masu masauk’i saman rug d’in...
Ya soma k’ok’arin bata a baki ta d’an mak’e kafad’a tana fad’in ita ta k’oshi...

Wannan karon mur yasha sosai kana yace “No teddy bear you must eat something...Oya open your mouth..!”
Ganin yanayinsa babu alamun wasa ciki ya sanyata bud’e baki babu shiri... Haka yaita bata idan tak’i bud’ewa ya d’aure fuska sosai har dai saida ta saka masa kuka tana fad’in ita ta k’oshi kana ya K’yaleta... Janyota jikinsa yai yana lallashinta kana yace suje su buga TV game... Haka Khalid yai mata matashi cikin jikinta dikda cewa har yanzu d’ard’ar take dashi... Suna nan a haka suna buga game d’in har Ta soma dariya ganin sai lallasa mata yake dan ita bawai ta iya bane, sai gashi kaman zai barta taci sai kuma yaci wasan... K’arshe jifa tai da control path d’in ta shiga kai masa duka tana fad’in that was cheating....
Sosai yake dariya yana kare dukan har dai ya janyota ta fad’o saman k’irjinsa....K’irjinta ya tsananta fad’uwa, Khalid yana iya jiyo yanda zuciyarta Ke bugawa da sauri da sauri, tsoro ya nuna sosai saman fuskarta, tai k’ok’arin yunk’ura zata tashi amma saiji tai ya kuma rik’ota sosai....Daga nan ne wasan nasu ya canza salo daga TV game, wasanda k’wak’walwrta da tinaninta suka gaza d’auka, gaba d’aya yau d’in bear d’in nata ya canza mata...(Nima dai k’wak’walwata ta gaza d’aika dan haka na janyo masu k’ofa na fito.. Lol)...
***
A hankali ya bud’e idanunsa ya sauk’esu kan kyakkyawar fuskarta, da gani kasan baccin tsoro da azaba kawai take, ga ragowar hawaye yanda suka bushe saman fuskar nata... Abubuwan da suka faru daren jiyan sukaita dawo masa... Tausayinta da soyayyarta na kuma ratsa duk wasu k’ofofi na zuciyarsa... A hankali ya sumbaci saman lumsassun idanunta yana mai furta “Thank you for last night teddy bear... Thank you for making me the most happiest man on earth....I love you so much... So much..!” Ya k’arashe cikin sigan rad’a yana mai kuma sunbatan labb’anta a hankali....
Tana jin sanda ya bar saman gadon wasu hawayen suka kuma gangaro mata, ta bud’e lumsassun idanunta a hankali sanda ta tabbata ya shiga bathroom tana yunk’urin tashi da k’yar, amma mai? Ji tai kaman an dadd’ure gab’ob’in jikinta... Ta kuma lumshe idanunta a hankali ita kad’ai tasan mai takeji, da k’yar ta iya tattaro duk wani strength d’inta ta mik’e da bin bango ta bar d’akin dan bazata iya zama ya fito ya taddata ba...

Koda ta shirya a nata d’akin lamo ta kumayi saman gado abubuwan da suka faru daren jiya suna kuma dawowa kwanyarta kaman wani a mafarki, wasu abin ta d’an saki murmushi dan ita da kanta sai yanzu take baiwa kanta dariya, wasu abin kaw saidai ta d’an rintse idanunta had’ida rufe fuskarta da tafukan hannu alamun taji kunya... Tana jin k’aran tab’a k’ofarsa alamun zai fito ya sanyata saurin lumshe idanunta tamkar wata mai bacci...

K’amshinta ne ya soma masa sallama kana ya hangeta kwance saman gado, tana sanye cikin atampa mai laushin gaske d’inkin riga da skirt wanda ya zauna d’amas a jikinta, ya saki murmushi a hankali had’ida takowa cikin d’akin gefenta ya zauna yanda fuskanta yake kallo, bugun k’irjinta ya k’aru musamman da taji k’amshin nasa yana ratsa k’ofofin hancinta... K’uri yai mata yanda idanunta Ke rawa alamun ba bacci take ba, ya kuma murmusawa da gefen baki kana yakai hannu ya d’an shafi fuskarta yana fad’in “Teddy bear I know ba bacci kike ba, oya bud’e idanunki mu gaisa...”
Shiru tak’i bud’ewa saima damk’e idanun da ta kumayi... Ya kuma murmusawa a hankali yana mai furta “Toh shikenan idan bazaki bud’e ba zamu kuma playing TV game yanzun n....”
Ai Baikai aya ba ta bud’e tana mai shirin saka masa kuka....
Sosai ta basa dariya ganin yanda dik ta wani birkice, a ranshi yace ko ina tsiwan da masifan yau suka tafi....? Janyota yai cikin jikinsa yana mai k’unshe dariyarsa yake fad’in “Is ok teddy bear wasa nake miki...Tv game ya huta abinshi... Wai haka kikeda tsoro kaman farar kura teddy bear..!”
Baikai aya ba suka soma jiyo horn daga gate... D’aga idanunsa yai yana duban agogon bango dake mak’ale jikin garun d’akin ya nuna k’arfe 10:15am... A hankali ya furta “who could that be..?”
Ya mik’e a hankali yana mai furta Bara ya duba, ita dai jinjina masa kai kurum tai had’ida bin bayansa da kallo, sai yanzu ta samu ta k’are masa kallo, sanye yake cikin lallausar yadi navy blue anyi mata d’inkin half jampa mai gajeren hannu, yayi kyau sosai da ka gansa kaga sabon ango...

Kafin ya k’araso k’asa har security ya bud’e masu gate, Siyama ce rik’eda hannun Ijlaal sanda Khalid d’in ya bud’e masu k’ofa.. Ijlaal ta fad’a jikinsa a guje abinka da d’anuwa.. Nan ta shiga zuba masa zance tana tambayarsa Aunt Beels... Ya d’auketa ya aza a kafad’a suka nufi cikin parlorn suna gaisawa da Siyama...
Chapter 186 · 0% Book details