Sashe 190
Inda Rai Da Rabo Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Akram ya d’an murmusa kad’an kana yace “Wllhi kaikam dai, yanzu ma silalewa nai na fice suna can mak’il suna jirana... Gashi shima Excellency sam hidimar court case d’in matarsa ya kasa masa hankali, abin ba’a cewa komai...”
Hafiz ya d’an jinjina kai kad’an kana yace “Wllhi Akram Bawan Allahn nan tausai yake bani, ya had’uda iftila’i da dama na rayuwa daga shi har Zulfa’u sun cancanci Farin ciki...!”
Akram ya jinjina kai a hankali kana yace “Excellency Al’umma ne a ranshi mutum ne mai k’ok’arin kawo buk’atun al’umma farko kafin nashi....Kuma dikda yanda yakeda d’inbin magoya baya daidai da rana guda bai tab’a sakawa ransa cewa shi zai lashe zab’en nan ba, a kullum maganar sa Allah shi mamu zab’in Alkhairi...”
Hafiz ya d’an jinjina kai yana mai furta “Allah sarki alamun adalan shuwagabanni kenan... Allah ya bashi ikon k’watanta adalci idan har ya nufesa da rik’on kujerar...”
Akram ya amsada Ameen a daidai sanda Naja’atu tai sallama tana fad’in “Ya Hafiz time din shan maganinka yayi...” sam batasan yanada bak’o ba... D’an jada baya tai tana k’ok’arin gaida Akram da tuni yai mutuwar zaune yana dubanta...
Bata kuma duban yanda Akram yake ba, kanta a k’asa ta k’arasa ta ijiyewa Hafiz maganin gabanshi ta b’abb’alla masa had’ida zuba masa ruwa, Hafiz yai mata godiya yana mai tambayarta ko Hajiya ta komo daga islamiya...?
Najah ta amsa masa da a’a basu dawo ba tukuna, da shike Hajiya da Sahariyya sun shiga islamiyar matan aure dake bayan layinsu...
Hafiz yace “Shikenan jeki abinki, na gode...!” Ta jinjina kai tana mai ficewa kanta a k’asa...
Akram ya kuma binta da kallo har saida Hafiz ya d’anyi gyaran murya kafin ya janye idanunsa daga barin duban k’ofar... Cikeda da d’an jin nauyi Akram ke shafa kansa kana yaceda Hafiz “Toh Abokina Inaga nikam zan koma kafin su fara nema na...”
Hafiz ya d’an mik’e zaune kad’an yana mai godiyawa Akram d’in, harda d’an tasowarsa yai masa rakiya zuwa k’ofa yana kuma masu add’uan nasara a forthcoming election d’in....
Haka Akram ya tafi fuskar Naj’atu bai daina masa gizo ba....
Tafiyar Akram da kad’an su Hajiya kaw suka dawo, nan Hafiz ke shaidawa Hajiyan Akram har yazo ya tafi, Hajiya Haule tace “Allah Sarki Aiko ba rabon mu gaisa ba...”
Hafiz yace “Zaku gaisa ne wataran Hajiya tinda dik ana tare yanzu....”
Haule tace “Haka ne... Ai wannan yaro Akram shida mijin Zulfa’u babu abinda zamu iya saka masu dashi saidai addu’ar Akhairi.... Musamman mijin Zulfa’u... Allah dai ya basa nasaran abinda ya saka gaba... Oh Duniya yanzu Zulfa’u ce muke cin albarkacinta a rayuwa... Kai Allah ka dad’a rufa mana asiri ka kuma tsaremu da aikin dana sani....”
Hafiz ya amsada “Ameen Hajiya jiki a matuk’ar sanyaye, dan kokaci guda yaita tina rayuwar aurensu da Zulfah....
D’an muskutawa yai kad’an kana yace “Waini Hajiya ya labarin shiga kotun su Baba Alhaji ne...?”
Nan da annurin fuskar Haule ya d’auke... Ta d’an muskuta kad’an kana tace “Yo ni ina zan sani.... Ai tsuntsun da ya janyo ruwa shi ruwa Ke bugu... Kuma babban abin kunya gayacan d’an uwan nasa da yaita k’ulla masa k’ulleliya shi yai tsaye kan case d’in nasa... Abban ku Usman shiketa d’awainiya dashi Nidai kam nayi rantsuwa ko zaman shari’ar bazan halarta ba...” Ta k’arashe cikeda k’unan zuciya...
Hafiz yai jigum yana saurarenta kana yace “Hajiya hannunka baya rub’ewa ka yanke ka yar, karki mance dukkaninmu masu laifi ne amma aka yafe mana... Kuma Baba Alhaji sharrin Magajiya ya had’udashi...”
Haule ta katsesa da fad’in “Kada ka sake ambato min sunan wannan tsinanniyar matar.... Taje can ta k’arata daga ita har d’iyarta dashi Alhajin da ya jefa kansa cikin uku....” Ta k’arashe tamkar mai shirin kuka....
Kaman daga sama sukaga Sahariyya, Naja’atu da kuma Raihanah da bata jima da shigowa ba sun shigo sun duk’a gaban Yayansu Hafiz....
Hajiya Haule dake k’ok’arin maida hawayenta, da gani kasan k’arfin hali kurum take amma tana kewar mijin nata itama, bud’e baki tai tana fad’in “Ku kuma meye haka kuka wani tasa shi a gaba haka... Lafiya...? Ke Raiha yaushe kika shigo...?”
Raihanah tace “Ban jima da shigowa ba Hajiya, ina yini...”
Haule ta amsa da sakin fuska harda tambayarta mai gidanta dikda cewa shekaran jiya tare suka shigo da Sameer d’in...Nan Raihanar Ke gaida Hafiz tana masa sannu da jiki...
Daga Hafiz har Haule k’uri sukai masu ganin sunyi jigum jigum... Hajiya ta kuma fad’in “Kunyi jigum jigum ku muke sauraro....
Najah da Raihanah harmada Sahariyya duban juna suke suna zullumin ta yanda zasu soma sanar da Hafiz da kuma Hajiya buk’atarsu....
Haule tai tsuka a hankali kana tace “Raiha nasan kinfisu hankali fad’a min meye kuka tasamu gaba haka kaman masu karb’an bashi...”
Raihanah ta d’an muskuta kana tace “Hajiya dama kan batun Baba ne.... Jiya Ya Ma’aruf ke sanar dani yanda Lauyan Baba sukai da Abbah... Muddin anaso Baba Alhaji ya kub’uta shaida k’wakk’awara za’a kawo cewa baida tarayya dasu Magajiya... Kuma sauran shaidar da akeda hope akai guda d’aya ne....”
Haule ta d’an muskuta kana tace “Toh mu ina zamu samo shaidar tinda bai shawari damu ba....!”
Duban Hafiz Raihanah tai yanda taga idanunsa sun kad’a sosai fuskarsa tai jazir, sai faman murza zanin gadon dake bisa yake, da gani kasan ransa k’una kurum take....
Sahariyya taci gaba da fad’in “Hajiya Ya Hafiz shine k’arshen shaidar Baba, shi kad’aine zai bada shaida gaban Alk’ali cewa Baba baida saka hannu a ta’addancin su Magajiya....”
Murmushi da tafi kama da yak’e Haule tai kana tace “Aiko idan sai Hafiz yaje ya bada shaida saidai a yanke masa hukuncin koma menene, mutumin da aka had’a baki dashi wajen ganin bayan Hafiz d’in... Aiko ko ya amince zaije ni ban amince ba ehe...!” Ta k’arashe jikinta na tsananin tsuma...
Naja’atu da Raihana suka dubi Hafiz da ya b’ace shiru tamkar bashi a wajen kana Raihana ta soma fad’in “Ya Hafiz please do this for our father... Dan Allah ka yafe mishi... Bamuda wanda yafishi Babanmu ne dik yanda akaje akazo.... Kuma kai shaida ne sharrin Magajiya ne tinda kaima ka auka wa sharrin Sawwama before... Dan Allah save our father, he can’t go to prison... Kaga yanzu hakanma ance inmates d’in da suke tare sun masa duka har hak’ori Sun cire masa... Shin haka zamu zuba idanu muga mahaifinmu... Muma fah duka ‘yan adam ne masu kure...!” Ta k’arashe cikin tsananin rawar murya...
Sahariyya da Naja’atu suka had’a baki suma suna rok’on d’an uwan nasu yayinda hawaye suka ci gaba da gangaroma Haule... Gaba d’ayansu ma hawayen suke....
Siririyar hawaye ta gangarowa Hafiz.... Kauda kansa gefe yai kad’an yana mai share hawayen dake ci gaba da zubo masa... Lokaci guda ya juyo yana duban ‘yanuwan nasa masu zuban hawaye.... “Please ku tashi ku fita zanyi bacci....!” Yai maganar yana mai d’aura kansa bisa pillow... Hawaye basu daina zubo masa ba idanunsa a lumshe...
Duban juna sukai Najah zata kuma magana Raihanah ta girgiza mata kai alamun ta k’yalesa....
Jikkuna a sanyaye suka mik’e suka fito Daga d’akin....
Raihana Ta dubi ‘yan uwanta Sahariyya da Naja’atu kana ta kamo hannayensu tace “Akwai sauran ranaku kafin shiga kotun, in sha Allahu da sannu zamu shawo kan Yaya yaje ya bada testimony d’insa a kotu... In sha Allah Baba will be set free.... Our family will be whole again..”
A tare Sahariyya da Naja’atu suka rungume Raihana sunai mata godiya wajen jajicewarta ganin Babansu ya kub’uta...
Haule dake rakub’e Daga k’ofa tana dubansu tausayinsu ya kamata, babu kaman Raihanah da idan ta tina abubuwan da tai mata a baya sai taji kaman a maida lokaci baya ta gyara amma saidai hakan ba mai yuwa bane... Tana ganin yanda suka rik’i hannayen juna suka nufi cikin parlorn...
Sai yamma Raihanah ta koma gida yanda ta tadda Zulfa’u da yaran mijinta can gidan Mamyn... Abinka da an kwana biyu ba’a had’u ba nan suka b’ige da murna gwanin dad’i, Marliya kaw cewa tai dole ta kira Nabila suyi video call taga dik an hallara babu ita... Hakan kaw akai Marliya ta kirawo Nabila dik suka gaisa Nabila kaman tai kuka ganin Raihana a Kano ga Addah Zulfah ma dik an had’u a gida babu ita..
Khalid dake gefenta harda lek’owa suka gaisada Marliya yana mai sanar da ita soon Nabilar ma zatazo... Nabila ta d’an b’alla masa hararan wasa tana fad’in ya tafi ya k’yaleta su gaisa da ‘yanuwanta... Aiko bai tafin ba hardai Marliya dake d’an jin nauyinsa tai masu sallama...
Nabila ta turo baki gaba tana harararsa, janyota jikinsa yai yana fad’in “Wai dik wannan fushin kan tafiya Kano ne...?”
Turo bakin ta kumayi kana tace “Toh bakai bane ka k’yale mutum ya gaisa da ‘yanuwansa ka wani mana k’ebebe shisa Marliya ta katse kiran... Allah Ammi zan kira na fad’a ma...”
Khalid ya murmusa kad’an kana yace “Da sauk’i tinda ba Kadunan zaki tafi Ki kai k’aran nawa wajen Ammi ba...”. Yai maganar yana wasa da yatsun hannunsa cikin sumarta da yasha gyara sai k’amshi yake....
Gyaran kwanciyarta tai cikin jikinsa tana fad’in “Ni dan Allah yaushe zanje Kano wllhi inason ganin Mamy, Kaga ko vid call d’in nan da mukai Mamy batabi takaina ba...”
Ya murmusa kad’an yana mai fad’in “Ai Mamy ce maganinki, idan kika dameni da batun zuwa Kano ita zan kirawo na kai k’ararki... Keda Kano sai kin haihu shima tare zamuje...!”
Zabura ta d’anyi tana dubansa da idanunta da sukai rau rau.... Khalid ya kuma kwanto da fuskarsa saitin nata had’ida d’aga mata gira guda... Lokaci guda yake kuma matseta jikinsa yana mai fad’i cikin sigan rad’a “Teddy bear don’t you think lokaci yayi da zamu samo Baby bears...!” Ya k’arashe yana rikirkitata da salonsa...
K’ok’arin k’watan kanta take tana fad’in “What’s that smell kaji k’aurin abinci na k’onewa, please ka k’yaleni naje na duba....”
Bai saketan ba yake fad’in “Then we cook another one teddy bear...” Haka ya kuma janyota tanata k’ok’arin k’watan kanta, da k’yar ta samu ta cire jikinta daga na Khalid ta nufi kitchen a guje tanai masa gwalo dan idan ta biye na Khalid tabbas abincin zai k’one... Zaune yai yana binta da kallo da rikitatattun idanunsa yana mai fad’in zai kamata ne....
Nabila dai kitchen ta shige tana dariya...
***