Sashe 45
Inda Rai Da Rabo Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
“Toh saime don auren naku ya rabu, shi yak’i biyema ra’ayinki na rayuwa babu stress d’in haihuwa da yara sai kece zakici gaba da zama da wanda baisan asalinsa ba balle tushensa sabida kece uwar soyayya koh... Toh ki zauna kinaji kina gani duk wannan sadaukarwar da kike masa a rayuwa abu mai sauk’i ne wataran yayi replacing d’inki da wata lokacin kin zama chus uwar ‘ya’ya kinaji kina gani saidai ki zama ‘yar kallo a gidanki idan dai mazan zamani ne, ga babban misali nan a gidanku... Ni dai shawari nake baki idan kin d’auka don kanki idan kuma baki d’auka ba rayuwarkice kiyi yanda kika so da ita zaki fad’a min watarana....”
Siyama tai shiru tamkar wacce ruwa ya shanye tana sauraren Laila tana kuma auna shawarin Laila dana Amminta, a hankali ta furta “Shikenan k’awata I’ll think about it....”
“You don’t need to think about it, amintaka da soyayyar dake tsakaninmu bazai tab’a sa na cutar dake ko na baki shawari maras kyau ba Siyama, don’t ruin your own life da kanki, ked’in ‘yar asalice ‘yar dangi, mai ilimi kyau da gata kar ki tab’a bari rayuwarki ta gurb’ace kan wani namijin da a gaba bazaiga hakan ba k’awata....”
Siyama da zauciyarta ta gama kwanciya da shawarin Laila a hankali ta shiga jinjina kai tana mai kuma nazarin kan batun, shawarwari Laila taci gaba bata tana d’orata bisa, Laila bata bari sun ida wayar ba har saida ta fahimci Siyama ta zama fully convinced da shawarwarinta kan nan sukai sallama.....
****
A can Kaduna kuwa Ammi gaba d’aya ta d’aukewa Khalid wuta, shi kanshi saida ya fahimci hakan don gaisheta ya shigoyi ciki ciki take amsa masa, bai kawo komai a ransa ba face rashin kula Yesmin da yakene ya saka Ammi fushi dashi haka, dukda abin ya damesa sosai bai d’ago mata zancen ba don yasan Amminsa bata juran fushi dashi zata sauk’one da kanta su sasanta....
Yauma a d’aki ya taddata Yesmin na tayata sorting drawers na jewelries d’inta, kallo d’aya yayiwa Yesmin ya d’auke idanunsa daga b’angaren da take, itakoh nan ta shiga gaisar dashi tana faman kwainane, ya amsa mata a tak’aice fuskarsa babu yabo babu fallasa kaman bashine wanda idan ta gaisar dashi baiko amsawa ba, mamaki da wani irin dad’i suka kama Yesmin, yau ita Khalid ke amsa gaisuwarta har k’wayar idanunsu na hard’ewa, kaman ta buga tsallen murna haka taji, shikaw ba don komai yayi hakan ba saidon Ammi ta amsa nasa gaisuwar ta daina fushi dashi.....
Saman stool ya zauna yana satan kallon Ammin wacce ta had’e gabas da yamma, yau d’inma ciki ciki ta amsa masa gaisuwar tasa...
Ya had’iyi miyau yana mai kai duba gefen bedside yanda takan ije kayan motsa baki wanda ba sai ta buk’ata daga downstairs ba, robar dambun naman kaza ya hango amma saidai kad’an ne ya rage a ciki, ya d’an mik’a hannu ya janyo k’aramar bokatin ya bud’e ya somaci ba wai don son ci d’in yake ba...
Cikeda rawar jiki Yesmin ta mik’e ta nufi k’ofa tana fad’in “Ya Khalid bara na k’aro maka downstairs...”
Kafin ya sami zarafin magana ta fice cikeda rawar jiki ta sauk’a k’asa...
Ammi da kaman jira take Yesmin d’in ta fice ta aje awarwaron hannun had’ida gyara zama tana kuma jefowa Khalid muguwar kallo wanda yai kaman baisan Ammin na jefa masa kallon ba, sai tura dambun naman yake bakinsa...
Jin yanda Ammi ta ambaci sunansa yasa k’iris dmbun baibi masa wata hanyar ba...
“Khalid..!!”
Ala dole ya kasa had’iyar abindake bakinsa yai shiru yana saurarenta...
“Kana jina wllhi bazaka maidani mutuniyar banza ka janyo min abin fad’i a duniya ba, tun wuri tun dare bai maka ba gwara ka sake tunanin kaji na fad’a maka...”
Ya had’iyi dambun dake bakinsa ya janyo bottle water dake gefe ya bud’e ya d’an kurb’a kana yace “Ammi mai nayi kuma fisabilillahi, tinda na dawo daga Kano kike fushi dani, what have I done kuma...?”
Ta kafesa da idanu tanai masa duban eh lallai ka cika...
Jinjina kai tai a hankali kana tace “Kadaka nemi rainamin hankali, uban mai ke kaika Kano...?”
Ya d’an dubeta cikeda mamakin tambayar da ta masa kana ya d’an kauda kai gefe yace “Ammi how many times do I have to answer this question... Ammi for goodness sakes aiki ke kaini....”
Baikai aya ba ta katse shi da fad’in “Uban aiki... nace uban aiki, wato kama maidani shashasha bansan mai nake ba, toh Siyama ta sanar dani komai, dama wannan uban rawar k’afar dakake hanyar Kano bazai wuce akan mace ba, toh wllhi ka saurareni da kyau, ni bazan bari kaci mutuncina ka kawo min ko wacce irin shirgi ba, idan da gaske auren zakai ga matarka nan gida tana jiranka....”
Khalid ya murmusa a hankali kana yace “Ammi I thought alhakin zab’ar macen da nake son ta kasance lifetime Partner d’ina a hannuna yake, dan Allah kar mu sake maganar nan Ammi...”
Ya k’arashe yana k’ok’arin mik’ewa a daidai sanda Yesmin tai tsaye bakin k’ofa da tray d’inta k’arama ta dambu a hannunta hawaye na neman gangarowa daga idanunta...
Cikin saurin Ammi ta katsesa da fad’in “Khalid karka fice a d’akin nan, ban gama magana da kai ba...”
Cak ya tsaya yana saurarenta ba tareda ya juyo ba hannayensa skale cikin aljihun wandonsa...
“Tell me who she’s, su waye iyayenta, meye sana’arsu idan ma’aikatan gwabnati ne wani mataki suka taka, idan masu mulki ne wace sarauta garesu.... ina saurarenka.....” Ta k’arashe tana mai takowa yanda yake...
Sai lokacin ya d’ago yanaiwa mahaifiyar tasa wani irin duba cikin rashin yarda da kalaman dake fitowa daga bakinta...
“Kai nake saurare Khalid....” Ammi ta kuma katse shi...
Idnuwanshi sunyi jazir cikin wane irin yanayi yake furta “Is that what really matters Ammi... Is that what matters to you...?”
“K’warai kuwa, a matsayinka na tilon d’anah namiji dole na bukaci sanin duk abinda na jero gameda macen da kake son kasancewa da ita....”
Khalid ya kuma dubanta cikeda mamaki kana yace “I thought zaki tambayeni if I really love her, if I’ll be happy with her....?”
Cikeda karaji tace “Farin cikinka kenan nake nema maka Khalid, farin cikinka shine namu kuma ba kowa bace farin cikinka illa Yesmin, yarinyar dake sonka tsakaninta da Allah....”
“Well! I don’t love her Ammi....!” Ya kasteta cikin d’an d’aga murya idanunsa na firfitowa waje...
Ammi bata daina huci ba take fad’in “Then learn, learn how to love her... Sabida itace matar dana zab’a maka and no one else...!”
Duban Ammi kurum yake idanunsa na kuma kad’awa... Zuciyarsa cikeda k’una yake girgiza kai bai iya furta komai ba sai ficewa da yayi cikin sauri, k’iris ya rage basuci karo ba shida Yesmin dake tsaye bakin k’ofar kaman an dasata hawaye na gangaro mata alamun taji komai gaba d’aya tattaunawarsa da mahaifiyar sa, tsaye yayi yana k’are mata kallo ga tray a hannunta, itakoh Yesmin tuni ta sadda nata idanun k’asa hawaye naci gaba da kwaranyo mata....
For the first time da yarinyar ta bashi tausayi, baisan mai zai furta mata ba don haka d’an girgiza kai kurum yai yasa kai ya sauk’a k’asar benen cikin sassarfa....
Yesmin tabi bayanshi da kallo hawayenta na k’aruwa, itakoh Kubura dake lab’e k’asan staircase dad’i kaman ya karta ganin yanda Khalid ya gwale Yesmin dake rawar k’afar kai masa dambu... Sosai dad’i ya kama Kubura ta gama amintawa zuciyarta cewa Khalid ba abinda zaiyi da Yesmin, ko shakka babu shid’in rabonta ne...
A hanakali tana mai sakin murmushi take furta “KubsyKhal....” Tai Wani murmushi domin kaw had’in sunayen nasu ya mata, ta lumshe idanu a hankali ta lula duniyar tunani tana hango kalan soyayyar da zasuyi a gidansu, k’aurin k’unan abinci da hancinta ya jiyo mata daga kitchen ya sanyata zabura ta nufi kitchen d’in a guje...
A haka sati ya shud’e Yesmin na tunanin mafita, taji komai taji akwai yarinyar dake neman mata katanga da Khalid, saidai ba garin take ba balle ta tink’areta, menene abinyi...? Take tunanin Siyama ya fad’o mata, gidan Siyama kawai zata tafi tayi zamanta bazata dawo ba har sai ta saita ko wacce shegiya ce ke neman rabata da Khalid d’inta, ta kuwa sami Ammi da batun, Ammi tace tayi dai dai hakan shine mafita, tuni ta saka driver yakai Yesmin har garin Kano, ita kanta Yesmin tasha mamakin gidan da Siyama ke zaune cikinsa, idan ance mata Siyama zata iya zaman irin wannan gidan sai tayi musu...
Jiki a sanyaye ganin yanayin Siyamar Yesmin ta zauna had’ida kamo hannayenta tana kuma k’arema gidan kallo...
“Cousin ya haka.... Wannan ne gidan naku...?”
Siyama ta sauk’e ajiyan zuciya had’ida tab’e baki kana tace “Wai fah... Nidai dan Allah kada ki fad’awa Ammi don wllhi nasan kina fad’a mata aurena da Sameer ya k’are... Ni ban san uwar mai unguwar ke tsinana masa ba, kin gannin tinda nazo unguwar nan ko k’ofa ban tab’a lek’awa ba balle nasan kalan mutanen cikinta, bama zan iya adopting halayyansu da d’abi’unsu ba, daga kallo sai wayata idan ya fice asibiti...”
Yesmin ta jinjina kai a hankali kana tace “Aiko nima bazanso aurenki da Ya Sameer ya k’are ba banci uwar yarinyar da Khalid ke b’ata lokaci kanta ba, saidai fah Cousin zaman gida yanzu bai kamaki ba domin kaw dole ki taimaka min mu samo gidansu yarinyar nan mu saka mata layi...”
Siyama tai dariya a hankali kana tace “Bansanki da tashin hankali ba Yesmin, kodai Ammi ce ta ingizoki...”
Yesmin ta fuzar da iska a hankali tace “Akan My Khalid babu abinda bazanyi ba cousin aidai kinsan yanda nake k’aunarsa, promise kawai you’ll help me...”
Siyama ta kuma murmusawa kana tace “Kar ki damu I got your back ....” Yesmin ta murmusa cikeda jin dad’i kana suka mik’e Siyama na tayata d’aukan kaya zasu kai d’aya d’akin da ba kwana suke ciki ba....
***