← Book details Inda Rai Da Rabo Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 172 OF 198

Sashe 172

Inda Rai Da Rabo Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Haka Siyama ta nufi motarta tana kuka sosai kaman ranta zai fita... Bata tab’a data sanin irin abubuwan da taiwa mijinta Sameer irin yau a rayuwarta ba.... Haka ta kifa kanta saman steering wheel tana kuka sosai, kukan da ko ba’ace ba daga cen k’asar zuciyarta yake fitowa... Wane irin kuka ne da zata iya rantsuwa bata tab’a yin irinsa a rayuwarta ba.... Ta rasa kukan mai take guda d’aya, shin kukan cin amanan da Laila tai mata ne...? Ko kuwa kukan rasa Sameer gaba d’aya da take gab da yi ne...? Ko kuwa dai kukan Partner d’inta yayi aure ne...? Innalillahi wa inna’ilaihi raji’un... Sameer d’inta fah... No no way munafuncin Sultan ne... Partner bazai tab’a auren wata mace bayanta ba... Sameer nata ne ita kad’ai... Su d’in Partners ne babu yanda za’ai wani mutum na Uku ya shigo between them, idan ma hakan zai kasance toh fah saidai d’ansu... Kuma tinda basuda d’ah su d’in dai Sune partners.... Cikin sauri ta Tashi motar ta fice daga asibitin a guje, dole taje ta gani ma idanunta... Inaaa not her Sameer....!! Wata zuciya tace ‘Toh idan shima auren yai irin yanda Daddynki yaima Ammi fah..? Shin zaki iya yafe masa...?’ Zuciyarta ta kuma tsinkewa... Lokaci guda taji zuciyarta na bugawa da sauri da sauri... Ta shiga girgiza kai ita kad’ai tana mai furta “No... No .... no Sameer bazai min haka ba... We made a promise to each other.... Mu biyu zamu rayu har abada... Sameer is mine alone... He’s mine... He’s mine..!!!” Ta k’arashe sabon kuka na kuma kufce mata had’ida danna wata wawiyar birki sakamakon shigewa da tai bama ta lura da traffic light da ya tsaidata ba... Tai saurin kame kanta da duka hannayenta biyu tana mai rintse idanunta.... Allah ya rufa asiri basui karo da motar dake gabanta ba amma kam tasha surutu wajen mutane...
Ita dai bama tabi takansu ba dan tashin hankalin da take ciki yafi k’arfin tinaninsu....

***

A kitchen ya iske Mummy da Raihana suna shirin kwab’a dough na yin chicken bread... hannayensa sakale cikin aljihun wandon jeans d’insa ya d’an karkace yana dubansu yanda suke gudanar da al’amaransu tamkar d’iya da uwa, gwanin ban sha’awa...
Mummy ta mik’o apron ta d’aurawa Raihanah da kanta kana tace “Yauwa d’iyata, toh yanzu kin shigo kitchen... Let’s get started....”
Juyowar da Mummy zatai sukai idanu hud’u dashi ya kame daga jikin k’ofa yanata kallonsu.... Mummy ta sakar masa murmushi kana tace “Son shigo mana... Come and join us...!” Ta k’arashe tana mai bud’e drawer had’ida ciro sauran kayan had’in...

Raihanah kaw tinda taji Mummy ta ambaci Sameer ta nemi natsuwar da take ciki ta rasa, gaba d’aya sai ta daburce, ga k’irjinta daka bugu da sauri da sauri... K’arasowa yai cikin kitchen d’in har lokacin hannayensa sakale cikin aljihu kana ya nufi Mummynsa yana lek’en abinda take k’ok’arin kwab’awa lokaci guda yake satan kallon Raihanah daketa k’ok’arin zira hannayenta cikin gloves na aikin kitchen....
Mummy ta saci kallonsa taga yanda idanunsa suke... Murmushi ta saki kana ta juyo sosai tana dubansa... Saida ta d’anyi gyaran murya kafin ta soma fad’in “You know Son, I think zaifi kyau idan ka zama malamin yau...!” Tai maganar tana mai zame apron d’in dake d’aure jikinta ta shiga k’ok’arin d’aurawa Sameer d’in...
Yayinda Raihanah ta daskare wajen, zuciyarta naci gaba da bugawa... Innalillahi Wai Mummy itada Ya Ma’aruf zata barta... Wai shi zai mata cooking class d’in yau.... Innalillahi Wayyo Allahnta itakam tasan tabbas babu wani abinda zata fahimta yau d’in....

Mummy ta gama d’aura masa har lokacin bai daina satan kallon Raihana da gaba d’aya ta koma sukuku da ita ba... Mummy ta d’an ja chicks d’insa da duka hannayenta biyu kana tace “You behave... I leave you in charge.... Kuma a kular min da d’alibata dan yau d’in ta zama d’alibarka...”
Murmushi Sameer yai yana duban Mummy cikeda so da k’aunarta kana yace “But Mummy I hope kin fad’awa d’alibar taki I’ve my own kitchen rules, and one must abide those rules...!” Ya k’arashe yana mai duban Raihanah with a straight face wanda har saida ya d’an sanyata zabura... Ta lab’e a bayan mummy tana lek’ensa a hankali....

Murmushi Mummy tai had’ida jan hancinsa kad’an tace “Na maka alk’awari d’alibata tafi Ta kowa kula....Kuma koda wasa kada ka razana min ita.... Amana na baka...”
Wannan karon murmusawa yai kad’an had’ida jinjina mata kai... Mummy ma Ta murmusa kana ta dafa Raihanah kad’an tace “Daughter idan yai miki wani abin Ki kwand’ara min kira kinji zanzo na samesa ne....” Ita dai Raihanah batace komai ba saima sanne kai da take... Mummy ta fice tana kiran mai aikinta Larai....

Kitchen ya rage saura su biyu... Gaba d’aya motsi k’wakk’wara ta kasa, sai k’ok’arin gyara gloves d’in hannunta take... Sameer ya kafeta da idanu murmushi na k’ok’arin kufce masa... Lokaci guda ya d’an sha mur kana yace “Rule number 1: No wearing of gloves in my kitchen....”
Ta d’ago da sauri tana dubansa... Gani tai babu alamun wasa a tattare dashi ya had’e fuska sosai... Ta had’iyi miyau da k’yar kana tace cikin sanyin murya “But Mummy tace yana daga cikin tsafta na kitc...”
Katseta yai da fad’in “Rule number 2:Dik tsarin da na bayar shi kawai ake amfani da a kitchen d’ina and no but....!”
Raihanah ta had’iyi sauran maganan nata had’ida kifa kanta k’asa...
Murmusawa yai a hankali kana ya tako kusanta a hankali... K’irjinta sai bugawa yake ganin na kwantowa kusanta sosai... Ta ware idanunta sosai ganin da gaske kusanta yake matsowa... Lokaci guda ta rintse idanunta tana mai karanto dik addu’an da yazo bakinta... Bata ankara ba saijin zuban ruwa tai Daga famfon sink... Nan taga ashe hannayensa yake wankewa kuma daf jikin sink d’in take tsaye dama... Saida har ya gama wankewa kana ya janyo towel ya goge hannayen nasa dashi....
Sauk’e ajiyan zuciya tai had’ida d’an kaucewa kad’an kana ta shiga k’ok’arin d’auko bowl d’in da flour d’in Ke ciki... Amma mai..? Muryarsa ta sinkayo yana fad’in “Rule number3...”
Raihanah tai saurin tsayawa cak tana jiran taji rule number 3... K’arasowa yai cikin taku irin nasa kana ya dubi bowl d’in ya dubeta... Hannunsa ya mik’a kaman zai amsa bowl d’in ya d’aura hannayensa saman nata, yana iya jiyo yanda hannayen nata ke rawa sosai... A hankali ya matso da bakinsa saitin kunnenta kana yace “Rule number 3 a cire wannan tsorona d’in a ajiye gefe dan ba asibiti muke ba, kuma ba allura a hannuna....!”
Wane irin ajiyan zuciya ta sauk’e still idanunta suna lumshe... Tana jin sanda ya amshi bowl d’in yace ta mik’a masa flour kaman bashine ya gama rad’a mata magana a kunne ba... Cikin ‘yar dabuwrcewa ta mik’a masa flour d’in.... Ya d’ago ya d’an dubeta kad’an sanda zai soma kwab’awa... Ai kafin yai magana Raihana tai saurin cewa “Rule number 4...!”
Dariya taso basa ya d’an gimtse kad’an kana yace “Yes rule number 4: student must pay attention and.... she must participate in everything... Oya coma...” Ya k’arashe yana jada baya kad’an had’ida mata alama da idanunsa kan tazo ta tsaya a gabansa...
Wani irin bugu k’irjin Raihanah yai.. Innalillahi itakam anya bata yafe classes d’in yau ba... Wayyo Allah ta ina zata tsaya gabansa....Batakaiga samo amsa ba ta sinkayo muryarsa wannan karon a dake yana fad’in “Rule number 5, I don’t repeat myself...!”
Cikin sauri ta matso had’ida yin yanda yace, jikinta sai karkarwa yake... Ganin haka yasa Sameer d’an kwanto da kansa daga yanda yake tsaye a bayanta, saitin kunnenta yake rad’a mata “I said rule number 5, I don’t repeat myself... Ko kin mance mai na fad’i maki a rule number 3 ne....?”
Cikin ‘yar daburcewa ta shiga jinjina kai tana fad’in “Kace baka son tsoro...!”
Murmusawa yai kana yace “Good kin tuna.... Lokaci guda taji hannayensa saman nata bata ankara ba saiji tai ya saka hannayen nasu waje guda suna kwab’in dough d’in... Tana iya jiyo yanda yake murza ‘yan yatsun hannunta a hankali cikin flour d’in... Tai saurin rintse idanunta dan yanayi ne da zatace bata tab’a tsintar kanta ciki ba... Gashi gaba d’aya runfa yai mata daga yanda yake tsaye bayanta... Tamkar ta kurma ihu ko zai k’yaleta haka nan taji... Sarai ta gane wannan dalilin nasa ne yasa ya hanata saka gloves... Gaba d’aya Raihanah ji take tamkar k’afafuwarta zasu gaza d’aukarta badon Allah yasa na tsaye bayanta ba tabbas tasan da k’asa zata zube... A haka aka ida kwab’a fulawar.... Ta saki wani irin ajiyan zuciya a hankali sanda taji ya zame hannayensa... Addu’a take Allah kawo Mummy kitchen d’in tace ta fasa class d’in yau... Kaman daga sama sukaji wayarsa ta soma ringing... Dan wanke hannayensa yai ya goge yana k’ok’arin amsa kiran lokaci guda ya nufi back door daka kitchen d’in.. Nan dabara Ta fad’o mata, kawai gwara ta sad’ad’a ta fice daga kitchen d’in kafin ya ida wayar da yake...
Cikin sand’a tamkar wata munafuka ta soma tiptoeing tana d’an lek’en k’ofar da yake tsaye.... Har ta kusan kaiwa k’ofar fita Ta sinkayo muryarsa yana fad’in “Rule number 6: Ba’a fita daga kitchen until we’re done...!”
Rintse idanunta kurum tai had’ida tsayawa cak yanda take... Bai kuma bi takanta ba ya koma ga abinda suka baro.... Muryarsa ta sinkayo yana fad’in “Looks like kin mance rule number 4..!”
Kaman zata kurma ihu haka ta dawo jiki a sanyaye tamkar wata mai shirin yin kuka... Ya saci kallonta da gefen idanu... Kauda fuskarsa yai had’ida sakin murmushi a hankali... Ta tsaya gefensa sai kuma taga ya matsa baya alamun tazo ta tsaya a wajenta na d’azu... Zatai magana Ta sinkayo muryarsa yana fad’in “Rule number 7: No asking questions..!!”
Chapter 172 · 0% Book details