← Book details Inda Rai Da Rabo Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 40 OF 198

Sashe 40

Inda Rai Da Rabo Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Murmushin k’arfin hali Abbah yai kana yace “Da ace yana raye da ya dawo garemu... Mun nemeshi a duk yanda ya dace mu sameshi amma bamu sameshi ba... Ma’aruf ya jima da mutuwa....” Ya k’arashe yana k’ok’arin mik’ewa tsaye saidai jiri ya kusan dawo dashi k’asa...
Sameer yai saurin tallafo shi yana fad’in “Sannu Baba, are you alright...? Muje barin kaika gida...”

Abbah ya girgiza kai yace “A’a kar ka damu zan iya tafiya....”

Girgiza masa kai Sameer ma yayi kana yace “A’a muje na kaika....” Ya k’arashe yana rik’edashi...
Murmushi Abbah yayi kana yace “Na gode...” Cikin zuciyarsa yana ayyana farin ciki da iyayen Sameer suke kasancewa ciki samun nagartaccen d’ah tamkar Sameer....
A haka suka fito har haraban masallacin, Sameer ya gyarawa Abbah takalmansa ya saka suna tafe yana tambayar Abbah ko yana shan maganin hawan jininshi da kyau abinka da likita.....

A haka suka k’araso gida hannun Sameer rungume da kafad’un Abbah yana taimaka mashi, Aunty Lami dake tacan baya wajen famfo tana tattare wasu kaya a igiyan shanya ta hangi Abbah da wannan matashi wanda ta masa suna da Ma’aruf suna tafe rungumeda juna tamkar asalin d’ah da mahaifi....
K’irjinta yayi wani irin bugawa tamkar an ijiye mata guduma akai, jikinta ya d’auki karkarwa batasan sanda tai watsi da kayan dake hannunta ba, tabisu da kallo har suka b’acewa ganinta....
A fujajan ta koma d’aki ta shiga zagayawa gumi na karyo mata, shikenan ta faru ta k’are, kar dai wad’annan bayin Allah sun fahimci junansu ne....? Kardai hasashensu ya zamto gaskiya ne....? A kullum k’ara kusanci suke da juna, tabbas idan basuyi wani hobb’asa ba sunaji suna gani da gaske Ma’aruf zai dawo cikin rayuwarsu...
Lami ta had’i wata miyau mai d’ankaren azaba kana ta shiga neman layin Haule jikinta har wani k’yarma yake sabida tsananin tsoro....

A kusan k’ofan sashen Abbah suka had’u da Marliya zata shige, nan ta tsaya tana gaidasu had’ida shiga damuwa ganin mahaifinta an tallafo shi...
A d’an daburce tace “Abbah lafiya... Maike damunka...?”

Sameer ne yace “Karki damu ba wani abu bane, da zaran ya kwanta ya sami hutu zai warware...”
Abbah ya k’arada “Kiramin mahaifiyarki...”

Cikin sauri fuska d’aukeda damuwa Marliya tace “Toh Abbah...” Nan take ta nufi sashen Mamy..
A yanda Mamy ta ganta ta tabbata babu lafiya....
Mamy tai saurin aje ludayin damun fura dake hannunta don tinda Aunty Lami ta bata shawrin ta sassautawa kanta da tunanin cewa Ma’aruf ka iya dawowa take k’ok’arin d’aukar shawarin dukda cewa can k’asar zuciyarta tanajin bazata iya ba domin kaw abune mai matuk’ar wahala... Matsar da langar tai kana tace “Marliya lafiya na ganki haka...?”

Marliya ta d’an share k’wallan da suka ciko idanunta tace “Mamy Abbah ne...”
Mamy ta mik’e zumbur cikeda tashin hankali take furta “Mai ya sami Abbanki...?”

“Mamy Abbah baida lafiya, yana sashen shi... Yace kije...”

Marliya bata ida fad’i ba Mamy ta fice a fujajan ta nufi sashen mijinta....

Sameer na k’ok’arin zaunar da Abbah had’ida jingina mashi bayanshi jikin cushion Mamy ta sako kai parlorn.....
Take k’irjinta ya shiga bugawa da sauri da sauri...
Ta kasa ci gaba da tafiya ta tsaya cak tana kallon ikon Allah...
K’wayan idanunta suka sauya lokaci guda sanda ta tsinci kanta tana mai ci gaba da takawa a hankali har ta isa garesu....
A dai-dai lokacinda Sameer ya d’ago k’wayar idanunsu suka sark’e waje guda....
Wani irin yanayi maras fasaltuwa suka tsinci kawunansu ciki.... Su duka biyu sunaima juna wani irin duba mai cikeda shauk’e, abubuwa da dama suke iya hangowa cikin idanun junansu...
Abbah dake daga kishingid’e ya kafesu da idanu yana kallon duban da sukema juna zuciyarsa na harbawa....
Abbah ne ya katse shirun da fad’in “Na gode likita....”
Sameer yai saurin dawowa cikin hankalinsa yai k’ok’arin k’ak’aro murmushi yace “Babu komai Baba...” Lokaci guda ya shiga gaisheda matar da bayyanarta gabanshi yai tsananin jefasa cikin wani yanayi maras fasaltuwa....

A b’angaren Mamy ma k’arfin hali tai kana tai k’ok’arin saita kanta ta amsa masa da sakin fuska bata daina mashi wani irin duba mai nuni da wani babban al’amari ba...
Abbah ya fahimci halin da Mamy ta tsinci kanta ciki, domin kuwa yanayi ne wanda ya tsinci kanshi ciki a lokacinda ya soma had’uwada Sameer, baiso taci gaba da wahala tana sakama ranta Ma’aruf zai dawo garesu tunda Sameer ya tabbatar mashi yanada nashi iyayen hasalima aiki ya kawo shi nan sannan babu ta yanda za’ai Sameer ya kasance d’ansu Ma’aruf wanda ya jima da b’acewa, watak’ila dai yanayi da kamanni ne yakedashi irinta Ma’aruf d’insu, a halin yanzu bai k’aunar matarshi uwar ‘ya’ayanshi ta kuma kasancewa cikin k’unci, zai k’ok’arin kawar mata da duk wasu k’unci data kasance ciki a baya wannan shine kawai hanyar da zaibi ya mayewa matarsa gurbin tarin bak’in cikin da ya jefata ciki a baya....

Mamy ce ta katse shirun da fad’in “Abbah meke faruwa, Marliya tace min bakada lafiya....” Ta k’arashe tana matsowa kusanshi...

Abbah ya sakar mata murmushi mai taushin gaske kana yace “Kar ki d’aga hankalinki Mariya, is a good thing wannan yaro Sameer yana wajen, bugu da k’ari k’wararren likita ne....”

Mamy ta jinjina kai fuska fal fari’a tana mai furta “Allah sarki... Sannu bawan Allah...”

Sameer ya d’ago ya dubeta fuskarsa d’aukeda murmushi yace “Babu komai Hajiya.... Ammm ni zan wuce, sai a kula da shan maganin BP d’inshi sannan ya rage yawan tunani...” Ya d’an juyo ya dubi Abbah kana yace “Baba a kula...”

Abbah ya jinjina kai yace “In sha Allah Sameer... Na gode k’warai...”

“A’a Baba ka daina godiya a gareni dan Allah an riga an zama d’aya....”
Abbah ya jinjina kai cikeda jin dad’i daga shi har Mamy duban Sameer suke tamkar yaci gaba da zama haka a gabansu suna dubansa suna murmushi....
Ganin da gaske tafiya yakeda niyyanyi yasa Mamy saurin mik’ewa tana fad’in “A’a ka tsaya a kawo maka abinci...”

Sameer yace “A’a Mama na gode...”
Mamy tabisa da kallo jin ya kiratada Mama...
Ta d’an murmusa tace “A’a zakaci wani abu dan Allah... Koda fura ne ka tsaya ka sha yanzu na damata ban jima da had’ata ba...”

Take murmushin Sameer ya fad’ad’a ya koma ya zauna yana mai furta “Aiko inason damun fura sosai tun tasowata...”

Gaban Mamy ya kuma fad’uwa, jikinta ya kuma yin sanyi tana mai duban Sameer d’in... A hankali ta mik’e ta nufi sashenta jiki a sanyaye ta had’o masa damun fura da kindirmo...
Sameer kaw gyara zama sosai saman darduma yana sha yana santi don dama rabonsa da abinci mai k’wari tun daren shekaran jiya....
Abbah da Mamy sukai masa k’uri suna dubansa zukatansu nai masu wani irin dad’i, su duka biyun Ma’aruf suke hanga zaune wajen...

Aunty Lami dake lab’e jikin k’ofa zuciyarta sai faman harbawa take musamman da taga yanda wannan matashi ke shan kindirmon, jikinta ya kuma tabbatar mata cewa lallai wannan Ma’aruf ne, dole su b’adda wannan mutumi a doron k’asa kafin ya dawo cikin rayuwarsu dumu dumu... Farin cikin da Mariya ta rasa shekaru talatin baya bazai kuma dawo mata ba...
Tai k’wafa a hankali kafin tasa kai ta juya sashenta, sauri sauri ta soma shirin fita....
Nabila da shigowarta kenan ta tadda Aunty Lami a kid’ime na shirin fita...
“Aunty fita ne zakiyi...?” Nabila ta tambaya sanda take zama bisa sofa...

Aunty Lami da gaba d’aya ba’a hayyacinta take ba tace “Eh..eh a’a dama gidan k’anwata Zubaidah zanje yanzu akamin waya akemin bataji dad’i ba...”

Nabila ta tsareta da idanu kana tace “Laa toh Aunty bara naje na fad’iwa Mamy zan maki rakiya...”

Aunty Lami tai saurin d’agowa tana dubanta kana tace “A’a Nabilah kiyi zamanki kawai aima ba jimawa zanyi ba...”

Nabilah ta murmusa tace “Allah babu komai Aunty bara na d’auko hijab d’ina....”

Tasa kai zata fice Aunty Lami da k’atutun bak’in ciki ya tokare mata mak’oshi saurin dakatar da Nabilah tai da fad’in “A’a... um aima inaga bazan samu fita yanzu ba don ban sanar da Alhaji ba, ko zuwa gobe idan na sanar mashi sai muje kinji koh....” Ta k’arashe tana kwab’e mayafinta...

Nabilah tai mata k’uri tana karantar ta kana ta murmusa tace “Shikenan Aunty yanda kikace....”

Lami ta sakar mata murmushi wacce iyakanta fatar baki cikin zuciyarta banda tsinewa Nabilah bata komai domin kaw ta b’ata mata plan d’inta...

***

A parlorn sashensu ya tadda Shamsu na kallon tashan ball as usual, shi kad’ai sai sakin murmushi yake zuciyarsa na masa wani irin sanyi....
Shamsu ya bishi da kallo cikeda mamaki sanin cewa k’unsheda tarin damuwa da bak’in ciki ya dawo garin, amma gashi daga d’an fitarshi ya dawo yalwace da fari’a....
Shamsu ya gyara zama had’ida ‘yar gyaran murya yace “Abokina wannan murmushin fah...?”

Sameer ya kuma murmusawa yana mai zama cikin kujera ya dubi Shamsu kana yace “You know Friend.... I feel we’re connected somehow... Like something very strong connects us... I don’t know, but deep down inaji wani babban al’amari ya had’amu....”

Shamsu gyara zama sosai yana dubansa kana yace “Wa kenan...?”

Sameer yace “Alhaji Usman Mailafiya da iyalinsa....”

K’uri Shamsu ya mashi kana yace “Wane irin connection kake tunanin zai iya kasancewa tsakaninku besides babu abinda ya had’aka da garin Kano....”

Sameer ya sauk’e nannauyan ajiyan zuciya kana yace “I don’t know how... But I can feel it....”

Jinjina kai Shamsu yai yana nazarin abin kana yace “By the way... You’ve a guest... A very special one...”

Sameer ya d’an kaikaito yana masa duba mai nuna alamun tambaya “Guest... Wa kenan...?”

“Your wife of course...”

Take annurin fuskarsa ya d’auke...

SameenaAleeyou 📚
*INDA RAI*
_...............DA RABO_

*34*

*©Sameena Aleeyou...✍🏽*

Hafiz ya shiga mutsuka idanunsa da duka hannayensa biyu yana mai kai duba wajen da ya tabbata nan ya aje babur d’insa, lokaci guda yake ci gaba da sauraren muryan mutanen suna fad’in “Wllhi d’an banza ya arce da babur d’in babu irin binshi da gudu da bamuyi ba amma yayi nasaran arcewa da ita... Waima babur d’in waye...?”

Hafiz bai iya amsawa ba sai silalewa da yayi a wajen had’ida dafe hannuwa biyu aka yana furta innalillahi, hankalin mutane ya dawo gareshi sukayo kanshi sunai jajanta mashi abinda ya faru...

***
Chapter 40 · 0% Book details