← Book details Inda Rai Da Rabo Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 74 OF 198

Sashe 74

Inda Rai Da Rabo Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Fuzar da iska Muhibbah tai tana mai binsa da kallo kana ta k’ak’aro murmushi, lokaci guda ta kuma takowa ta bayansa kad’an tana mai gyara masa zaman suit d’insa had’ida daidaita masa necktie d’insa.... Fuska a shagwab’e take fad’in “Bazakaje dani ba...?”
“Ba taron mata bane....”
Ya fad’i a tak’aice yana mai matsar da ita gefe had’ida d’aukan turare....
Cikin sauri ta rik’e hannun nasa ta amshi turaren tana k’ok’arin fesa masa cikin salo....
Duk abinda take kallon arziki bata ishesa ba, sauri sauri ya ida abinda yake ya fice ya barta nan tsaye....
A parlor ya tadda yaransa sunyi shirin tafiya makaranta, Najma tana hangosa ta taso a guje ta rungume tana fad’in “Daddy good morning...”
Engr ya rungumeta had’ida manna mata peck a goshi “Morning my princess....” Ya kamo hannunta suka nufi dining table din yanda sauran ‘yan uwan nata suke...
Gaba d’aya yaran gaidasa sukai fuskokinsu fal fari’a... Hakan take kasancewa da mahaifinsu sab’anin mahaifiyarsu da sam babu sabo tsakaninsu da ita....

“Daddy yau kai zaka kaimu sch....?” Hanan mai shekaru shida ta tambaya....
Shafa kanta yayi murmushi bai gushe saman fuskansa ba daidai sanda Murja ta k’araso da lunchboxes din yaran...
“Kunaso na kaiku ne...?”
Gaba d’aya yaran suka had’a baki wajen cewa eh...
Fuskarsa d’aukeda murmushi yake fad’in “Alright kowa ya gama cin abincinsa and Daddy will take you to school today...”
Yaran suka shiga murna suna tsalle musamman k’anana guda biyun, shi babban mai shekaru goma dama magana bawai ya faye yinta bane, haka nan yake tamkar wani miskili....
Harta Murja saida taji dad’i cikin ranta don sosai yaran suke bata tausayi musamman idan ta tuna cewa yaran basu nemi komai sun rasa ba face soyayyar mahaifiya...
Muhibbah kaw daga yanda take tsaye tana dubansu ta cika tayi fam, wato sabida tsaban rainin hankali itace zaice mata sauri yake kada yayi latti amma ga yaransa nan ya sakasu gaba yana biyesu k’arewarta ma cewa yayi da kansa zai kaisu makaranta, dad’i da k’arin takaicinta shine yanda daga Ma’aruf har yaransa ita d’in bata gabansu, yaran ko sallama basu mata ba suka fice wanda ta tabbata da ace ubansu ne bazasu fita basu masa sallama ba, wato ma babu wanda ya d’auketa da wani kima da daraja cikin gidan...
K’wafa tai kana ta haye sama tana neman layin Suby aminiyarta

“Hello Suby.... Nifa na gaji Wllhi na gaji da zama waje guda, kinga masu gidanma ba noticing d’ina suke ba, gaskiya ni na gaji da wannan zaman don wllhi ji nake kaman banida lafiya.....”
Daga d’aya b’angaren wacce ta kirada Suby dariya ta tintsire dashi kana tace “Toh Wai ki fito kiyi mai bayan babu business a k’asa.... Kedai kawai kiyi hak’uri na d’an lokaci ki kuma winning mutumin nan over ta haka ne kurum idan yaci zab’en nan zamu samu kasonmu, kuma kinga business d’inmu ma zata kuma bunk’asa tinda ba lallai yasan tak’amaimen kasuwancin da muke ba...”
Muhibba ta sauk’e nannauyan ajiyan zuciya kana tace “Suby bazaki gane bane akwai matsala....”
Suby ta kuma shek’ewa da dariya kana tace “K’awata nasan matsalarki bazai wuce abin ba, zan turo Jenny ta kawo maki anjima...”
Muhibbah ta murmusa kana sukai sallama...
Ta jima tana tsaye wajen kafin ta nufi bedroom d’inta...
Kai tsaye closet d’inta ta nufa ta janyo wata ‘yar drawer.... Wata ‘yar farar leda mai d’auke da k’waya ta ciro lokaci guda ta saki murmushi.... Hancinta ta toshe da yatsunta guda biyu kafin ta afa k’wayan tana mai rintse idanunta....

***

Basu sha wahalan neman gidansu Khalid ba dashike ba gida ne b’oyayye ba, tinda Nabilah ta d’aga idanu ta kalli gidan gabanta yayi mugun fad’uwa, lallai dole ma su Siyama su nemi datse tsakaninta da Khalid.... Aunty B ta dafata kad’an kana tace “Kina buk’atar na rakaki cikin gidan...?”

Murmushi ta sakarwa Aunty B tana mai girgiza kai kana tace “A’a Aunty, da kika kawoni ma kin gama min komai, this is my war ya kamata na fuskanceta ni kad’ai...”
Aunty B ta jinjina kai a hankali kana tace “Shikenan ina jiranki a nan cikin mota, I know you’re strong enough to do this alone...”

Nabilah ta fuzar da iska tana mai k’arfafawa kanta gwiwa, cikin ranta take furta “I can do this..I know I can...”

***

Fitowarsu daga masallaci Hafiz ya d’auki hanyar gida tamkar wanda ake sinkaransa don ko sallama da Magaji bai sami zarafin yi ba....
Tinda mai babur ya ijesa k’ofar gidan yaji kansa na sara masa, babu abindake azalzalarsa face tsan tsan tsanar matarsa Sawwama, komai ya shiga dawo masa, ya d’aga kai ya kuma duban k’ofar gidan, idanunsa suka sauk’a kan mota k’irar Corolla dake pake k’asar bishiyar delbejiya dake a k’ofar gidan....

***

Kubura ta dubi Nabilah daga sama har k’asa kana tace “Baiwar Allah kikace fah wajen Mai gidan kikazo...?”

Cikin dakewa Nabilah tace “Ko na sake maimaita maki ne...?”

Kubura ta murmusa kana tace “Yo abinne da mamaki wai an baima d’an kura ajiyan nama... Bama kice wajen Hajiya kikazo neman taimako ba sai kice Alhajin d’ungurungum....”

Ammi dake k’ok’arin sauk’owa daga staircase waya manne kunnenta ta katse Kubura da fad’in “ke Kubura Wai keda wayene wajen nan.....?”

Kubura ta bud’e murya tace “Ammi salon bariki nake gani, wannan mai baran Wai wajen Alhaji tazo bama wajenki ba.... Shine abin ya d’aure min kai....”

Ammi taci gaba da sauk’owa daga bene still waya manne kunnenta tana duban yarinyar dake tsaye da Kubura...

Kan Nabilah a k’asa banda bugu babu abinda k’irjinta keyi, batasan idan zata iya d’agowa ta dubi mahaifiyar Khalid ba, batasan idan zata iya ci gaba da abinda ya soma ba.......

SameenaAleeyou📚

*INDA RAI*
_................DA RABO_

61

*©️Sameena Aleeyou...✍🏻*

NOT EDITED

Tin daga sama har k’asa Ammi ke k’are mata kallo, still waya na manne b’angaren kunnenta na dama... Daga d’aya b’angaren shiru Baffah yai yana sauraren sautin maganganun Kubura dake tashi a wajen.....
Ammi ta k’araso har gaban Nabilah a daidai lokacinda Nabilah ta d’ago suna duban juna.....
Gaban Nabilah ya yanke ya fad’i a karo na farko....
Sosai Ammi take dubanta tana k’ok’arin tuno yanda tasan wannan fuska....
“Baiwar Allah lafiya...? Daga ina kike....? Sannan maiyasa kike neman mijina....?” Lokaci guda Ammi ta jero mata wad’annan tambayoyi....

“Wajen Daddy nazo....” Nabilah tace tana mai d’auke idanu daga duban Ammi....
Kubura taci gaba da tafe hannaye tana fad’in “Oh yau ni naga jaraba, Ammi na fad’i maki Yanzu haka irin masu neman taimakon nan ne da Daddy ke taimaka masu shine suka soma biyo shi har gida... Bani umarnin fitar da ita yanzu kiga aiki da cikawa....” Ta k’arashe tana nannad’e hannun riga tamkar wacce zata sunkuce Nabilar....
Sauk’owan Yesmin kenan daga sama cikin shirin fita da alama da Siyama take wayar cak ta tsaya tana duban yanda su Ammi ke tsaye carko carko, mamakin bai ida kama Yesmin ba saida ta hangi fuskar yarinyar dake tsaye bakin k’ofa Kubura ta mata k’ababa....

Da k’arfi Yesmin ta furta “Nabilah..!!”
Daga Ammi har Kubura harma ita kanta Nabilar d’agowa tai tana duban Yesmin dake sauk’owa daga bene... Daga d’aya b’angaren Siyama tace “Mai kikace cousin... wata Nabilah kenan....?”
Yesmin tana mai k’arasowa garesu idanunta kan Nabilah take ci gaba da fad’i cikin wayar “K’warai kuwa Cousin Nabilah’s here she’s right here in front of me.... Da alama duk wulakancin da muka mata bai isheta ba ta kawo kanta....”

Duk maganganun nan a kunnuwan Baffah... A hankali ya furta “Nabilar Khalid....!” Yai saurin bud’e murya yace “Ammi ba damuwa naji kaman kinada bak’i ki gama abinda kike sai muyi magana...”
Ammi tace “Alright Baffah I’ll get back to you...” Ta kashe wayar tana mai duban Yesmin da kyau kana tace “Explain... Wacece ita... A ina kika santa...?”

Yesmin na murmushi mai k’unshe da Allah sarki idanunta kan Nabilah take furta “Ammi wannan itace yarinyar da Khalid ya d’imauce kanta har ya sab’a umarninku for the first time in his life.... “

Ammi tace “Kina nufin kicemin wannan itace yarinyar... Kan wannan abar Khalid ya bijire mana, ya zab’i ganin k’uncinmu sama da farin cikinmu.... No wonder naga kaman nasan fuskar nata ashe a wancan video d’in na santa, yarinyar da ‘yan unguwa suka had’u suna mata wak’an Karuwa...” Ta kuma maido da dubantaga Nabilah wacce ta kasa d’ago idanunta sabida tsananin k’una da k’irjinta ke mata...
Murmushi Ammi ta saki kana taci gaba da fad’in “Aw shine kika biyoshi har gida, kika taso tin daga uwa duniya kika biyo namiji har gidansu... Eh lallai kin cika cikakkiyar kilaki...”

“Ni ba kilaki bace, kuma ni ba wajen Khalid nazo ba, na sani Khalid doesn’t live here anymore...” Ta fad’i cikin tsananin rawar murya....

Kubura ta rangad’a guda tana mai tafe hannaye da salallami take furta “Yau naga salo... Ni nan ina tunanin mijin Ammi aka zo k’wacewa har gida ashe nawa mijin aka biyo.... Toh wllhi kinyi kad’an Karuwan cikin gidan ma sunyi sun k’yalesa ballanta ke da na tabbata a naira goma bazai amsheki ba....!”

Ammi ta saki baki tana duban Kubura shaye da mamaki, lallai ta yarda haukan Kubura ya fara yawa dole a nema mata taimako.... Ganin Ammi na mata wani irin duba yasata saurin yin shiru tana mai furta “Yo Ammi ai gaskiya na fad’i su karuwan cikin gidan sun san kansu....”
Yesmin da tuni ta kufula ta yo kan Kubura tana fad’in “Wa kike kira karuwa....”
“A wacce ta tsargu....” Kubura tace tana watsa mata harara....
Ammi ce ta raba tsakaninsu tana fad’in “Banison shashanci da hauka kuna jina koh....”
“Ammi shiyasa nace Kimin iyaka da wannan lunatic maid d’in....” Yesmin ta fad’i fuska a shagwab’e.....
Chapter 74 · 0% Book details