← Book details Inda Rai Da Rabo Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 30 OF 198

Sashe 30

Inda Rai Da Rabo Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

Daga yanda yake tsaye yaji shiru shiru bata dawo ba ga kunnuwarsa dake jiyo masa sauti kaman na kuka da hayaniya, gabansa ya fad’i ya yanke kardai dukan yarinyar nan ake...
Bai wata wata ba ya yanke shawarin kutsa kai cikin gidan ceton yarinyar nan....

Hango Mace da yayi sai jibganta take tana ihu ga wasu gefe suna shewa ya sanyashi saurin k’arasawa ya amshe muciyar daga hannun Hajiya yana fad’in “Idan kika kasheta koda ace ‘yarkice sai na maka ki a kotu...!” Yanda yayi maganar gaba d’aya hankulansu ya dawo gareshi..

Ido cikin ido Sameer ke duban Hajiya, wani irin fad’uwan gaba had’ida firgici suka dirar mata lokaci guda... Ta tuna sanda ta toshe bakin Ma’aruf dake tsananin kuka yana kiran Mamynsa da tsumma ta jefashi bayan bus suka bar gari, ta tuna yanda ta damk’ashiwa Aminiyar sirri bayan ta gama azabtar da yaron... K’wayan idanun bazasu iya b’ace mata sabida k’wayan idanu ne masu tsananin wahala ace mutum ya mance, Hajiya ta kasa koda motsawa sannan ta kasa bud’e baki ta furta koda kalma guda ta kuma kasa janye idanunta daga duban wannan mutumi da gani take tamkar d’an marayan azikine Allah ya tayar da abinsa..
A b’angaren Sameer ma kallon fuskar matar yake kaman yanaso ya tuna yanda yasan mai irin fuskar saidai sam ya kasa tunawa, tamkar ya tab’a cin karo da muguwar mata mai tsananin kamanni da wannan matar a can wasu shekarun baya su kuwa su Sahariyya da Najah mutuwar tsaye sukayi suna santin wannan had’edd’en saurayi d’an gayun had’ida mamakin mai ya shigo dashi cikin gidansu....

SameenaAleeyou 📚
*INDA RAI*
_..............DA RABO_

*27*

*©Sameena Aleeyou...✍🏽*

Haule da gaba d’aya gumi ke tsartsafo mata k’ok’arin daidaita kanta tai kana tace “Toooh kaikuma asuwa... Wane uban ne ya baka izinin shigowa kan matan aure...? Bakai zubin masu saida kifi ba da sai nace kaine daduron nata, aikin banza aikin wofi...”

Tinda ta soma magana Sameer ke dubanta, bai tankata ba sai duk’awa k’asa da yayi yana duban Raihana cikeda tausayawa yanda jikinta yayi luhu luhu ya tara jini... Sahariyya ma batasan sanda ta duk’a ba had’ida rafka uban tagumi tanai masa mayen kallo kaman zata lasheshi....

Kasa furta koda kalma yayi saima tsananin tausayin yarinyar da ya kuma rufeshi, d’agowa yayi yana ma Hajiya wani irin kallo mai tsananin firgitata kana ya mik’e tsaye yace “Duk yanda akai ba kece kika haifeta ba.. amma ki sani yatsa guda idan kika sake d’aurawa akanta....”

Hajiya ta katsesa da fad’in “Mai zakayi... Nace mai zakayi... Hukuma zaka kiramin toh kira gwangwani uwar d’amara...”
Bai furta komai ba sai duban da yake mata, ruri da wayarsa ta d’auka ya sanyashi tuna ashe jiranshi ake a asibiti...
Wani kallo ya kuma baiwa Hajiya wanda ya k’irjinta bugu kaman an sauk’e guduma kana yasa kai ya fice daga gidan zuciyarsa bai daina masa wasu irin tunani sarara ba....

***

Hafiz bashi ya tashi sai wajajen k’arfe goma na hantsi, ya yunk’ura zai motsa yaji k’ashin bayansa na amsawa, banda sarawa babu abinda kansa keyi...
Tsaye ya hangi Sawwama da kwaskwon turaren wuta sai zagaya gidan dashi take tana ‘yar wak’enta, hammar yunwa ya kuma saki ga k’amshin turaren sam bai masa ba, yayi k’arfin halin mik’ewa ya nufi band’aki, jim kad’an ya fito ya taddata a parlor tana kunna kayan kallo k’afa guda akan guda sai taunar chewing gum k’araras....
Zaune yayi gefenta yanata faman jira ta gaisheshi amma shiru baiji alamun zata gaishe shi d’inba....
Shafe goshinsa ya kumayi kana yace “Ba’a kawo breakfast bane...?”
Idanunta naga kayan kallonta tace dashi “Sun kawo amma nace su maida...”
Hafiz ya bita da kallon mamaki kana yace “Ban gane kince a maida ba, toh mai zanci... kokuwa kin dafa ne...”
Galala take dubansa kana ta murmusa a hankali had’ida kuma tauna chewing gum d’inta tace “Aidai kai shaidane ko kantin abincin Mamata kaje kayan dad’i ake cika maka tumbi dashi don haka babu abinda zaisa a nannagomin k’osai da uwar safiya safiyarma na amarcina naci nayita tusa, bazai saku ba...” Ta k’arashe tana watsa masa mugun kallo had’ida maida idanunta ga kallon da take....
Jinjina kai yayi yana dubanta kana ya furta “Yayi kyau...”
Jiki babu k’wari ya mik’e ya shige d’aki ya d’auko makullin abin hannunsa yasa kai zai fice..
Tsaye Sawwama tai a gabansa tanai masa kallon tambaya “Ina zakaje...”
Ya bata wani mugun kallo kana yace “Ki matsa min a hanya...”
Murmushi ta sakar masa kafin ta marairaice fuska tanai masa salo take fad’in “Haba Habibi duka duka fah jiya aka kawoni yau kuma zaka fita so kake ‘yan bak’in ciki su mana dariya...?” Ta k’arashe tana wasa da ‘yan yaysunta saman fuskarsa..
Samun kansa yayi da kasa mata musu saima d’an dubanta da yayi ta kuma kashe masa idanu...
Wannan karon saida ya d’an fuzar da iska kafin yace “Sawwama yunwa nakeji...”
Hannu ta d’ora saman k’irjinsa tanayi kaman tana d’an gyara masa kwalar rigar kana tace “Kar ka damu idan dai abinci ne yanzu za’a kawo maiji da lafiya kaji koh, haba karfa ka mance kantin abinci garemu...”
Ya d’anyi k’arfin halin sakin murmushi kana yace “Toh Amarya a barni naje na gaida Hajiya...”
Wasu salon take kuma masa had’ida langab’e kai tace “Hajiya ta ganka a wannan lokaci ai zatace ba lafiya muke zaune ba, kaga yau gaba d’aya bai kamata ka fice ba a gida ya kamata ka zauna muci soyayyarmu... Muje na wankeka...” Ta k’arashe tana k’ok’arin b’alle masa boturan riga..
Hafiz ya zaro idanu waje ga k’irjinsa da yayi mugun bugawa yanajin yanda har yanzu tin daga gadon bayansa yayi kwankwasonsa zuwa cinyoyinsa gaba d’aya ciwo suke masa a firgice yace “Ki wanki wa...? A’a Sawwama wanka kuma ai saidai na gobe...”
Sawwama ta d’an murmusa kana tace “Nafa sani bakai wankan sabulu ba Habibi muje na cud’eka ta shiga turasa cikin d’akin yana turjewa...
“Sanyi nakeji nida tab’a ruwa bacin alwala sai gobe ke alwalan ma rik’eta zanyi ya k’arashe yana k’watan kwalan rigarsa daga hannunta...
Sawwama bata daina abinda tayi niyya ba take fad’in “A’a a yau a k’alla kayi wanka sau biyar... Kaga muje dan Allah....”
Ya kuma zaro idanu waje ganin abinta da gaske take musamman data dannashi cikin d’aki...
Banda innalillahi da salati baya iya komai, dafe kansa yayi gumi na keto masa, zata hauro saman gadon ya shiga matsawa baya yana fad’in “Kiyiwa Allah ki bani abinci first Sawwama tun jiya da rana babu abinda naci wllhi banida k’arfi....”
Sallaman da sukajiyo daga bakin baranda ya ceci Hafiz, jin abokansa ne ya sanya Sawwama jan tsuka ba tareda ta amsa ba, masu sallama suka soma fad’in kodai babu kowa gidan ne.. D’aya yace kokuma basu tashi ba dai, k’ila mun masu sammako...

A d’ari Hafiz ya mik’e dukda ciwo da jikinsa ke masa yana lek’e ta window yake fad’in “Wa’alaikumussalam... Magaji ku dawo karku tafi... Mun tashi...”
Yana fad’i Sawwama na k’ok’arin janyosa amma tuni ya mak’ale jikin window tamkar wani d’an biri yana fad’iwa abokan su dawo, yanda kasan mai kiran azo a ceci rayuwarsa..

Suna dawowa da baya Hafiz yaji wata relief cikin sauri ya shiga kintsa kansa yana fad’in “Bani waje bani waje inada bak’i....” Sauri sauri yake komai
Sawwama ta bisa da kallo sanda ya fice kana tai k’wafa tace “Bakai kace ka iya kai mace hotel ba har nice zaka rainama hankali ka nemi k’awata, kad’an ka soma gani wllhi wllhi sai na cire maka kwad’ayin duk wata mace... Sawwama nake...” Ta k’arashe tanayin k’wafa a hankali kafin ta fito parlor ta tadda abokan mijin nata sai gwad’ata suke amarya baki laifi
A gefe guda kuwa sam basu gane kan abokin nasu ba kaman ba ango ba, suna ango kasha mai saidai ya kauda kai gefe yana sauk’e haki a hankali..

***
Chapter 30 · 0% Book details