← Book details Inda Rai Da Rabo Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 41 OF 198

Sashe 41

Inda Rai Da Rabo Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ko wacce ta rik’e ‘ya’yan calbi d’aid’ai a hannunta suna jiran cewar Malam dake faman zanen k’asa yana motsa baki a hankali...
Bayan wasu ‘yan lokuta Malam ya amshi cazbahan dake hannayensu dai dai yanda suka rik’e....
Duba ya shiga binsu dashi d’aya bayan d’aya kana yai gyaran murya yace “Abune da kamar wuya....”

Suka kalli juna su duka biyun kana suka maida dubansu ga Malam...
Hajiya Haule ta gyara zama sosai kana tace “Malam ban fahimceka ba, kaman yaya abune mai kamar wuya, b’atar da Ma’aruf a karo na biyu kake nufi ko kuwa salwantar da rayuwarsa....? Kai mana bayani yanda zamu fahimta...”
Ta k’arashe k’irjinta na tsananin bugu...

Dubansu yaci gaba dayi kana ya kuma gyaran murya yace “Abinda nake nufi duka biyu abune mai matuk’ar wahala, kasancewar kun riga da kunci galaba shekaru talatin baya zai wuya ku kuma cin galaba akan Ma’aruf, da ace kunyi amfani da damar da kuka samu tuntuni da yanzu kun wuce babin Ma’aruf amma baku kashe shi ba tun wancen lokacin hakan na nunida mai yuwa Allah ya k’addara masa rayuwa mai tsawo nan gaba.... Watak’ila ku kuma tonan asirinku ne yazo shiyasa Ma’aruf ke bibiyan tsakaninku...”

Baikai aya ba Haule ta dakatar dashi da fad’in “Kai dalla can rufe man baki, yo har akwai wanda ya isa yaja damu wllhi k’aryarsa tasha k’arya, kai wannan dama da ganinka baza’ai abin arziki dakai ba, ke Lami tashi mu tafi kinji gidan Malamai da bokaye fad’i garesu har yaushe zamu tsaya wannan shashashan yana d’ura mana ruwa a ciki, yanda mukaci galaba kan Mariya shekaru talatin baya haka zamu sakeci....” Ta k’arashe tana mik’ewa tsaye had’ida mak’ale posa d’inta a hammata, bata daina sababi tana zagin bokan nasu ba cewa baisan komai ba...
Malamin nasu ya murmusa kana yace “Kuje duk yanda zakuje a fad’in duniya saidai a fad’a maku abu guda domin kaw wannan dalili yasa na sanya ko wacce cikinku d’aukan k’waran cazbaha kuma kun d’auka kun d’auki k’addararku da yatsunku don haka ku k’ara gaba kar bala’inku ta shafeni...”

Haba nan fah Haule taci gaba da sababi tana fad’in “K’arya kake mak’aryacin banza da wofi bala’i saidai ta k’are maka kuma k’addararmu ba hannunka take ba hannun Allah take ehe don haka nasara na garemu da izinin Allah...”

Malam ya katseta da fad’in “Da ace kinsan k’addarar taku da gaske hannun Allah take da baki b’ata k’afarki tun fari kinzo nan ba, idan baki daina kumfan baki kin fice min a gida ba wllhi saidai ki bar gidan nan da shenyenyyun k’afafu...”

Jin haka yasa Aunty Lami saurin janyo Haule dakeci gaba da kumfan baki suka fice a d’ari Lami naci gaba da kwab’arta....
Suna tsaye bakin layin suna neman adaidaita Lami ke ci gaba da fad’in “Kinga Hajiya Haule karma ki d’aurawa Malamin nan laifi, idan akwai wacce zamu d’aurwa laifi bai wuce tsinanniyar matar can ba....”

“AMINIYAR SIRRI...!” Haule tace tana sakin huci, lokaci guda taci gaba da fad’in “Yo Makirar Sirri dai... Amma matar nan ta cucemu da har ta bari muka amince da ita....”

Aunty Lami tace “Ba abin mu tona mata asiri ba mu tono asirin kanmu...”
“Babu batun tone tonen asiri amma sai mun gunsura mata rashin mutunci inkaw ba hakaba ba sunana Haulatu ba....” Ta k’arashe tana mai sakin k’wafa sanda suka sakawa Adaidaita hannu...

***

Sawwama dake make gaban motar saurayinta Alhaji Liti sai aikin taunar chewing gum take tana juya idanu mayafi a kafad’a... A d’an yatsine tace dashi Alhajin Shagali a nan bakin layi zaka ajeni zan k’arasa....”

Alhaji Liti ya washe baki yana wani kanne idanu da hularsa dake karkace gefen goshi ya kai hannu ya d’an shafi cinyarta yace “Haba sahiba bazaki bari a k’arasa dake ba yanda yau kika farantan rai ya kamata na kaiki har makwancinki da mota basai kin taka k’asa ba....”

Ta wani murmusa had’ida juya idanu tana mai gyara zaman rigarta take fad’in “Karka damu aljihuna daka cikamin yafimin komai, kaga idan ka k’arasa dani cikin layin za’a sami matsala....”

Ya washe baki cikeda jin dad’i kana yace “Yanzu sai yaushe kinsan dai bazan jure rashinki na tsawon kwanaki ba...”

Sawwama ta kuma taune chewing gum tace “Alhaji kenan, kar ka damu idan don wannan ne aljihuna nayin k’asa zakajini...”
Alhaji na matsowa kusanta yake furta “Anya kuwa zan iya..?”
Ta murmusa tace “Zaka iya Alhaji.. Sai ka jini...” Ta k’arashe tana bud’e marfin motar had’ida d’aukar ledar kaji da ya sai mata... Harda hura masa iska a fuska kafin ta fice, Alhaji ya saki murmushi yana mai washe dargajejjiyar bakinsa cikeda fatan su kuma had’uwa bada jimawa ba...

Tana tafe tana kad’a jiki kaman yanda ta saba tana taunar chewing gum, nan ta hangi dandatson mutane sai faman jajantawa mijinta suke, tai saurin k’arasowa tana son jin abindake faruwa, durk’ushe ta tadda Hafiz ya rapka uban tagumi tsananin damuwa kwance saman fuskarsa....
Tana tambayar sababi Hafiz bai iya amsata ba sai duban da ya bita dashi yana mamakin ina ta fito haka, mutanen dake wajen ne suka koro mata bayani had’ida jajanta mata...
Halin ko inkula ta nuna kana ta tallafo Hafiz tana fad’in “Yo sai mai zaka sami fin haka Habibi tashi mu shige ga kaji na kawo mana...”

Tamkar rak’umi da akala haka Hafiz ya mik’e yabi Sawwama dake rik’eda hannunsa, yana son tambayarta yanda ta fito amma wani mugun shakkanta yake, suka isa parlor tana basa baki sanda take kwab’e mayafinta, k’amshin turaren maza da ya daki hancinsa shi ya sanyashi kuma d’agowa yanai mata wani irin duba, saida turarruka sana’arce don haka yasan k’amshin turare da dama kuma zai iya banbance maka turaren mace da na namiji...

Zama gefensa tai ta bud’e k’ullin kajinta ba tareda ta masa tayi ba ta sanayasa gaba tana yagan kaji tana fad’in “Tsautsayi ne Habibi, kawai kaje ka sami Alhaji da batun ya sai maka wata tinda dai kaga kayan wancan shashashar matar taka sun k’are da an d’aga ko gado ne an saida ni na cika maka ka sai sabo...” Ta k’arashe tana gwigwiyan k’ashi da bakinta...
Tinda ta soma magana banda binta da kallo baya komai, shi tinda yake bai tab’a ganin d’an Adam mai cin abinci irin Sawwama ba, idan ta aje kwanon abinci a gabanta saita mak’erin kwanon uwa uba ta samu kaza, kaza ko nawa ne zata iya b’addawa, shi da yake namiji quarter d’in abincin da Sawwama ke ci bazai iya ci ba, tinda ya aurota komai na gidan baya yakeyi, gashi yanzu ba wadataccen ciniki yake samu ba, nan da nan kayan abinci ya k’are yanda kasan a rumbu ake zubawa kuma shi gashi ba bashi abincin ake yaci ya k’oshi ba wani jik’on sai ya dangana da gidan Hajiya, kasancewar cinikinsa yaja baya a dole ya shiga saida wasu kayayyakin Zulfah dake rufe d’aki yana wasu hidiman da kud’ad’en ballantana yanda Sawwama ke son kaji ba’a kwana biyu sai an sai kaji kuma ba’a sayan d’aya don d’aya ya kasa mata... Kan ya ankara Sawwama ta d’age ledar kajin dake gabanta ta shiga saki masa gyatsa tana tanne hannaye...

Ya d’an kauda kai gefe had’ida yin k’wafa kana yace “Wai ke bakisan abu ya sami mijinki ki kwantar masa da hankali ba saidai ki baje ledar kaji kinaci, haba Sawwama wace irin mata ce ke..?” Ya k’arashe cikin taushesahiyar murya...

Tsegege take dubansa kana ta yatsina fuska tace “Toh kuka kakeso na sanyaka gaba inayi ko kuwa don kana cikin damuwa sai akace kar naci abinci... Kaga Hafiz karma mu soma wannan wasar dakai, kai da anzo kusanka sai ka soma jada baya kanajin tsoro kaman wanda za’a yanki naman jikinka toh ya kake so nayi dakai... A’a wllhi kar ka tak’urama rayuwata...” Ta k’arashe tana kad’a masa mazaunai had’ida ficewa ta nufi kitchen don neman abinsha wanda zai kwantar da kajin da ta nad’a...

Yai k’wafa had’ida sauk’e ajiyan zuciya kafin ya nufi yanda ta aje mayafinta yana faman shinshinawa don tabbatarwa hancinsa abinda yake jiyowa... Yanajin motsinta alamun tana k’ok’arin shigowa yai saurin aje mayafin ya koma wajen zamansa... Tabisa da kallo a kaikaice kana ta d’auki mayafinta da handbag d’inta ta shige d’aki...
Hafiz ya dafe kansa abubuwa da dama k’unshe cikin zuciyarsa....

***

Basmah jikarta d’iyar Baffah Ado ne ke rik’eda hannunta guda zasu tsallake kwalta sun fito gidan bikin jikar k’awarta, sai faman sababi take tana fad’i Basmah ta kula da hanya kar taja a bigesu...
Basmah ta d’an b’ata fuska tace “Allah Mamani shiyasa duk yanda zakije babu mai maki rakiya, fisabilillahi wani irin kula ne banayi...?”

Mamani ta katseta da fad’in “Ke rufe min baki banason salon rashin kunya da kuka sha a nonon iyayenku mata, iyayenku basuda aiki sai aifo mana mata a zuri’a wanda ba tallafa mana zasuyi ba saidai su cinye mana gara, yo da ace inada jikoki maza ai da ba haka ba nima ‘yar Hajjin nan da duk shekara sai na koma duk azumi kuwa na tafi umarah amma tinda naje sau d’aya ban koma ba, yanzu duba jikan Yayale yanda yayi bajinta a bikin nan ko uban yarinyar baiyi ba... Ke d’iyar Ado ce koh...?” Ta k’arashe tana duban Basmar wacce tazo wuya don takaici, tsaban jikokin basa gabanta bama ta tantance d’iyar waye cikin yarantan ba..
Jin Basmah tai mata banza ya sanyata d’ago ‘yar sandarta zata kwad’a mata tana fad’in “Ke koh ubanki bai isa na masa magana yamin banza ba... Nace ke d’in d’iyar waye...”

Cikeda k’unk’uni Basmah tace “Baffah Ado mana autanki Mamani...”

Mamani ta yab’e baki tace “Ai kaji gashi shi Adamu gaba d’ayama kaman baizo duniyar a sa’a ba, shi ba k’wakk’waran sana’a ba shi ba haihuwan yara maza wanda zasu taimaka masa a gaba yake ba ga matan nasa yawa agwagi kullum gasar haihuwar nan suke ga ba abinda akeso suke haifowa ba... Oh ni Halimatu...”

Basmah data gaza hak’uri tace “Amma ai Mamani ‘ya’ya mata rahama ne baki zuwa islamiyya da kinji falala da yara mata ke k’unshe dashi ba, wllhi kekam inaga ko aji guda bakije ba a islamiyya yanda kasan zamanin jahiliya aka d’aukoki...”
Chapter 41 · 0% Book details