← Book details Inda Rai Da Rabo Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 150 OF 198

Sashe 150

Inda Rai Da Rabo Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read

Tsaye suke jikin motar Daddy sanda Daddyn yaci gaba da fad’in “You’re a gentleman now Khalid... Soon enough zaka soma aje Iyalai, har kullum wasiyyata a gareka ka kula da family d’inka Khalid... Take care of our family, my family.... Kai hak’uri da mahaifiyarka da kuma ‘yaruwarka Siyama, na sani idan labarin aurenka ya riskesu komai ka iya faruwa, amma a matsayinka na namiji kuma magidanci a halin yanzu... Inaso kabi komai a sannu sannan kai hak’uri da kowa kaji koh....”
Khalid ya jinjina kai a hankali kana yace a sanyaye “Amma Daddy maiyasa shayibun bazai kaika ba, idan yaso ni sai na taho dasu gaba d’aya...”
Daddy ya d’an murmusa kad’an “Banda abinka Khalid idan na tafi da Shayibu ita matar taka ai baza’a rasa wad’anda zasu mata rakiya ba koh... Toh gani ai motar tai maku kad’an, shi Shayibun dai ya zauna ni zan tuk’a kaina kada ka damu kaji koh...”
D’an jim Khalid yai kana yace “Amma Daddy....!”
Katsesa Daddy yai da fad’in “Ya isa Khalid kayi abinda nace kawai... Allah shi maku albarka gaba d’aya....”
Khalid ya amsada “Ameen Daddy, Allah ya tsare ya kiyaye hanya...” Dik jiki a mace yake maganar...
Daddy ma ya amsa mar da Ameen.... Har yasa kai zai shige mota sai ya kuma juyowa ya dubi Khalid....
Lokaci guda ya rubgumesa sosai, saitin kunnensa yake rad’a masa “Take care of my family...!”
Wani irin bugu Khalid yaji k’irjinsa na mai haka kurum... Yanaji yana gani har Daddy ya shige mota yai mata key, kaman wanda aka dasa haka yai tsaye a wajen har saida Daddy ya fice daga gate d’in gidan.... Jiki babu laka Khalid ya furta “Be safe Daddy...!” Jiki a natuk’ar sanyaye ya juya ya komo cikin gida, harta Nabilah saida ta kula da canzawan Khalid d’in... Dikda fushi yake da ita amma sai taji tana son sanin matsalarsa saidai Khalid d’in sam bai bata k’ofar jin damuwar tasa ba, k’arshe ma sallama yai masu ya koma masauk’insa.... Suma dai daga nan gida suka tattafi yayinda Aunty B ta tsare Zulfa’u a d’aki tai mata nasiha sosai mai ratsa zuciya sannan ta k’arada “Idan mijin naki ya iso kafin ku wuce gidanku zai biya dake wajen Abbah kinji koh....”
Tana danne hawayenta take jinjina kai alamun taji, saidai tuni hawayen sun soma zubowa.... Gaba d’aya sai jikin Aunty B d’inma yai sanyi.... Matsowa kusanta tai sosai kana ta kamo hannayenta tace “Zulfa’u d’ago ki dubeni....” kasa d’agowan tai har saida Aunty Bara’atu ta maimaita... Nan ya ta d’ago idanunta masu zuban ruwa tana dubanta... Lokaci guda Aunty B d’in ta rungumeta cikeda tausaya mata, take kukan Zulfah ya k’aru sosai.... Har saida Aunty B ta matse nata k’wallan kana tace “Haba Zulfa’u kukan nan ya isa haka, aure fah bafa mutuwa bace, idan kina haka ita kuma Nabilah tai yaya....? Kukan nan ya isa haka kinji koh....”
Zulfah naci gaba da goge fuska cikin muryar kuka take fad’in “Aunty shin meye makomar aurena a karo na biyu... Shin iftila’in dana fuskanta a gidan aurena na fari shi zan kuma fuskanta... Aunty ina mijina...? Baisan an d’aura mana aure bane... Maiyasa ya kasa koda kirana a waya balle na sakashi a idanuna.... Aunty tsoro nake kada na kuma tarar da rayuwa irin wacce nayi a gidan tsohon mijina... Ni kuma kalan nawa jarabawar kenan Aunty...?” Ta k’arashe cikin tsananin rawar murya...
Ga tsananin mamakinta murmushi taga Aunty Bara’atu tai wannan karon kana ta kuma kamo hannayenta kad’an tace “In sha Allah kin baro wancan rayuwar kenan, rabuwa ta har abada... In sha Allahu zaki tadda Farin ciki da haske mai wanzuwa a sabuwar rayuwar da kika tsinci kanki ciki.... Ki kwantar da hankalinki kuma ki karb’i zab’inda Allah yai maki dan a koda Yaushe zab’insa shine mafi alkhairi a garemu kinji koh...!”
Jikinta ya kuma yin sanyi sosai kana ta shiga jinjina mata kai a hankali... Sallama suka kumayi Aunty Bara’atu ta nufi wajen ‘yar uwarta Ya Abida suka kuma yin sallama....
Atika ma dai mik’ewa tai tana fad’in “Toh amarsu ta ango, yanzu kam sai munyi talaho kuma....”
Shaye da mamaki Zulfa’u Ke dubanta kana tace “Wai tsaya kina nufin kema tafiyar zakiyi ne....?”
Atika dake sab’a mayafi tace “Sake tambayata, mai kuma zan zauna na miki bayan ango yanzu zai shigo....”
Zulfah ta girgiza kai cikin rashin yarda kana tace “Kina nufin bazakimin rakiya ba kenan....?”
D’an darawa kad’an Atika tai kana tace “Yo rakiya na nawa kuma bayan wanda nai maki, ko so kike ango ya fatattakeni kam, ai sai na hau masa kai... Kinga kedai zamuyi waya kawai, daga baya kuma mazo ganin d’aki taredasu Aunty Zilai....”
Zulfah tai k’wafa ganin dai da gaske Atika ma tafiyarta zatai, gashi sai shak’iyanci take mata tana fad’in ta wanke idanunta da kyau dan ango shigowar bazata zai mata... Dik wannan hannunka mai sanda da Atika Ke tai mata itafah bata fahimci komai ba, hasalima bata kawo komai a ranta ba, suna a haka yaran Engr suka shigo a guje har suna rige rigen mik’awa Zulfah sabuwar hijabi da cazabaha Ammah ta basu su kawo mata... Ta amsa fuska fal fari’a had’ida yi masu godiya, ta ije saman abin sallah dake linke gefe...K’aramar ta d’auka ta d’aurata bisa cinya tana kuma tambayarsu sunayensu... Nan da na yaran suka saki jiki suna zuba mata zance musamman Najma da take jinta Tamkar d’iyarta Khausar... Suna a haka suka jiyo sallaman babansu, gabanta ya yanke ya fad’i... Tai saurin gyara zaman mayafinta had’ida amsa sallaman.... A guje yaran suka tafi suka rungume Babansu idan ka d’auke Najma da tak’i matsawa daga jikin Zulfah....
Yaran suka shiga zuba masa shagwab’a yana biyesu, Samha fad’i take “Daddy ni dai nafi son gidan Ammah please Daddy banso na koma gida... Shima Irfaan hakan yace baiso ya koma gida wajen Mummy....”
Shafa kansu yai kana yace “Alright za’a kawo maku uniforms d’inku sai kuyi kwana biyu ma granny ko...” Gaba d’aya tsalle suke suna murna harda rungumesa suna fad’in we love you Daddy.... Shima ya rungumesu yana kissing kansu... Abin sosai ya baiwa Zulfah sha’awa ganin yanda Engr Ma’aruf keda kyakkyawan alak’a da yaransa yanda ake so ko wane uba ya kasance da yaransa.... Ficewa yaran sukai suka nufi sashen Ammah dan sanar da ita Daddynsu yace zasu zauna a gidanta...
Chapter 150 · 0% Book details