← Book details Inda Rai Da Rabo Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 133 OF 198

Sashe 133

Inda Rai Da Rabo Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Kaman daga sama ta soma jiyo k’awayenta su Hameeda dasu Barakah coursemates d’insu k’alilan da suka gayyata suna lek’en window suna fad’in “Ga ango ga ango...” Dumm!!! Sautin da k’irjinta ya bada, tana jiyo muryan maza da dama daga window yanda suke gaisawa da mutane... Tuni Aunty B tasa akai masauk’i a parlor... Babu yanda ba’ai da Nabilah taje su gaisa ba fir tak’i saima sabon kukan da ta fashe dashi... Khalid kaw jin ance tak’i zuwa tanata kuka ya sanyasa mik’ewa tsam ya nufi d’akin yana mai neman izini wajen Aunty Bara’atu... Aunty tace yaje shi ai daga ita amaryar ce saiko k’awayenta... Khalid kaman zai kifa haka ya nufi d’akin... Tanajin su Hameeda na gaidashi bugun zuciyarta ya k’aru, ga k’amshin nan nasa na cikin motarsa da sam ya kasa b’acewa daga hancinta yana tashi cikin d’akin...
Sai faman shan zuciya take sanda ya isa saman gadon ya zauna a gefenta... Bugun zuciyarta ya ninku.... K’uri yai mata yana kallon yanda ta tak’ure waje guda ta kasa koda d’ago kanta ne... A hankali ya d’an kwanto da kansa saitin fuskarta dake kife “Teddy bear.... Look up... D’ago ki kalleni....Kinada labarin ke d’in matata ce yanzu.... Teddy bear yau anyi aurenmu... Mu d’in ma’aurata ne yanzu...” Yanda yake maganar ya kuma sanyata sakin kukan... Kukan da sam baijin dad’in sautinsu cikin kunnuwarsa da zuciyarsa...
D’an gimtsewa yai kad’an kana yace “Nasan maiyasa kikak’i d’ago kai ki dubeni, kika kuma k’i ki daina kuka... You’re still mad at me... Oya tashi ki scolding d’ina yanda kike so kinji koh...” Yai maganar yana k’ok’arin yaye mayafin data kifa kanta ciki...
Janye jikinta tai tana fad’in “Ni ka k’yaleni... Ba kai ne... Ba kai ne ba....” Ta kasa ci gaba da maganan sai Sabon kuka... Wannan karon rungumota yai cikin k’irjinsa yana fad’in “I know teddy bear, ni d’in mai laifi ne... I’m sorry please forgive your Bear... Daga yanzu bazan sake barinki ba, zamu kasance tare har k’arshen rayuwar mu... Your bear is here with you... Hash now...!”
Cikin sigan lallashi mai cikeda kulawa yake maganar yayinda Nabilah ta kasa turesa daga jikinta saima cukwikuye fuskarta da tai cikin babbar rigarsa ga sautin ajiyan zuciyarta dake tashi, zukatansu suna bugawa lokaci guda... Haba su Hameeda sun shagala da kallon irin wannan soyayya, wannan ta tab’a wannan wancan ta tab’a wancan... Barakah harda saita wayarta a sace tana masu video a cewarta wannan soyayya bata gani ita kad’ai ba dole takai gaba....
Khalid dai da k’yar ya lallab’o amaryarsa ta fito parlor da rakiyarsu Yusrah suka gaisa dasu Baffah... Sai zolayan Ango suke suna dariyar yanda gaban rigarsa ya b’aci da kwalliyan Amarya danginsu janbaki da gazal... Ko ba’ace ba kasan Amarya taci kuka a gaban babban garen ango..
Shiko Khalid d’in sai wani tsimewa yake yana b’allawasu Baffah harara...
***
A can gidan Abbah kuwa gama d’aurin auren da kad’an Sameer ya iso, Shamsu ne ya d’aukosa daga can airport, fitowar safe yai dan ya riga ya gama abinda zai a Lagos d’in, baisan daliliba amma sosai yaji zuciyarsa ta karkata zuwa Gida.... Sanda ya isa ya tadda mutane ‘yan d’aurin aure Sun watse saiko d’aid’aiku dake parlorn Abbah suma d’in su Daddy ne saiko Engr da suka tsaya tattaunawa lamarin...
Gaisawa dasu kawai yai kana ya nufi can gidansa dan kintsawa, har wannan lokaci baida labarin wainar da ake tuk’awa, saidai Abbah ya sanar dashi yayi farin ciki da dawowarsa dan akwai muhimmin abinda ya kamata ya sani...

A can cikin gida kaw tinda Mamy tai tozali da Daula hankalinta ya gaza kwanciya, bugun zuciyarta ya ninku babu shiri ta d’aga waya ta sanar da ‘yar uwarta Bara’atu cewa maza tazo taga wannan abin al’ajabi da take gani na faruwa a idanunta... Aiko babu shiri Aunty Bara’atu ta fito ta nufi gidan Mamy afujajan...

A can gidan Baba Alhaji kaw Haule na tsaka da tik’an rawa Lami ta kira wayarta cikin d’imauta da tashin hankali.... Da k’yar ta iya d’aga wayar dan bata fatan abinda zai katse mata wannan farin ciki da annashuwa da take ciki....
Jin muryar Lami d’in a birkice yasa Haule saita kanta kad’an kana tace “Lami ki natsu ki sanar dani meke faruwa.... Mufa yau ranar farin cikinmu ne an d’aura auren Ma’aruf....”
Lami tace “K’warai an d’aura auren Ma’aruf amma fah abu ne a duhu...!”
Gaban Haule ya bada Dumm! Domin kaw ta tsani wannan kalmar *Abu a duhu* kaman yanda bokansu yaita fad’a masu gameda b’acewar Ma’aruf d’in...
“Ban gane abu a duhu ba Lami...? Wane irin abu a duhu..? Shin ba’a d’aura auren Ma’aruf d’in bane....?”

Aunty Lami ya katse zufan da take ya tsartsafo a goshinta kana tace “Haule k’warai abu a duhu domin kaw babu tak’amaimen wanda zaki tambaya yace miki ga matar da aka d’aura mata aure da Ma’aruf saidai kowa yanada tabbacin ba Sahariyya bace matar...”
Tashin hankali gobarar gemu...!!!
Take Haule ta soma gani bibbiyu... Mai kid’a yana kuma k’ure speaker Haule ta malmalo ashariya ta watsa masa... Tamkar wata zararriya take fad’in “K’arya kenan... Wllhi k’arya kenan... Babu ubanda ya isa yaga bayana ni Haule.... Lami bakiji da kyau ba... Wayyo wayyo Wayyo na shiga Uku..!!!” Duniya ta shiga juya ma Haule upside down, Haule ta warware d’aurin kanta tai d’amara tana kururuwa... Haba nan fah mata aka soma kame baki ana ‘yar k’us k’us abin nema ya samu...
Sahariyya kaw ihu take bataji bata gani, ... A haka Baba Alhaji ya shigo yana washe baki tamkar Sabon Ango saidai tashin hankalin da ya tadda gidan nashi ne ya bala’in tada masa hankali domin kaw zani a hannu yaga Haule sai ihu take tsakar gida tana tsalle had’ida kururuwa....

Suna a haka Sahariyya ta fito daga d’aki tamkar zararriya tana kilan Basmah data kawo mata rahoton anyi auren Yaya Ma’aruf amma ba ita bace Amarya.... Bugunta kurum Sahariyya take da sandar crutches d’inta tana fad’in “Dan uwarki sai na halak’aki... Mai mugun alkaba’iri.... Yau sai na cire miki son gulma da munafunci.....Ku barni na karta shegiya mai mummunan fata...!!!” Haba nan fah jama’a akai kan Sahariyya ana k’ok’arin rik’ota had’ida ceton Basmah da take shan duka da sandar k’arfe hannun Sahariyyar...
Naja’atu ce ta k’araso ta fincike sandar hannun Sahariyya... Lokaci guda tana huci take fad’in “K’warai Addah Sahariyya Ya Ma’aruf bai cancanceki ba, kuma idan da wacce zaki daka nice nan ba Basmah...!!”

Gabaki d’aya kallo ya dawo kan Naja’atu....

SameenaAleeyou📚

*INDA RAI*
_................DA RABO_

*89*

*©️Sameena Aleeyou...✍🏽*

Haule da bataji batun da kyau ba, matsawa kusan Naja’atu tai tana k’are mata kallo shaye da tsananin mamaki “Ke mai kikace....? Maimaita naji dan uwarki....”

Naja’atu dake rungumeda Basmah wacce har lokacin matsan hawaye take tace “Hajiya nasan kinji mai nace, kuma kinfi kowa sanin cewa Ya Ma’aruf bai cancanci zama mijin Addah Sahariyya ba....” Batakai aya ba Hajiya ta shiga salallami tana tafe hannaye “Kice bak’in ciki kike da ‘yaruwarki ta jini Naja’atu... Na shiga uku ni Haule, yanzu Najah sabida tsaban hassada da k’eta kawai dan shi Ma’aruf d’in bai zab’eki ba shine sabida kutungwila irin taki saida kika shiga kika fita kika hana auren ‘yaruwarki yuwa... Haba ai biri yayi kama da mutum kenan dake aka d’aura auren... Toh kaw baki isa ba, idan mutuwa kike sai an kwance an d’aura da Addarki dan mu ba Ke muka bashi ba ehe....!”
Tinda ta soma magana Naja’atu Ke girgiza kai tama rasa abin fad’i ta yarda mahaifiyarta ta gama yin nisa bazataji kira ba... Sahariyya dake tsaye tana huci tamkar zakanya a d’ari tai kan Naja’atu ta shiga fincikarta tana kai mata bugu ta ko ina tana fad’in “Wllhi yau koni ko ke a gidan nan... Munafuka mahassadiya makira annamimiya....!!” Tuni su Fa’iza sukai kan Sahariyya suna k’ok’arin janyeta, ihu kawai Sahariyya take tana bugun dik yanda hannunta ya sauk’a koma wanene, bataji bata gani tamkar sabuwar kamun hauka....
Baba Alhaji kaw tuni ya janyo hannun Haule suka keb’e dan ko takan d’iyarsa Sahariyya baibi ba...
Kwab’e babbar rigarsa yai had’ida maida hular kansa baya, ya dubi Haule data kame kunkumi tana girgiza tana huci...
“Ke Haule Wai meke faruwa ne...? Meye na tadda na faruwa a gidan nan... wane batu nakeji cewa an canza auren Sahariyya...?”

Sororo Haule Ke dubansa kana tace “Shin nada kai waye yafi cancanta ya amsa wad’annan tambayoyin...? Kaida kake wajen bukin d’aurin auren ina ka makara har aka maka wasan kura da yaranka... Idan har kana wajen d’aurin auren ta yaya duk haka ya faru....?”
Gaban Baba Alhaji ya bada Dumm! Tabbas baya wajen aka d’aura auren...

Haule datai sakare tana dubansa jikinta na kuma yin sanyi, gyara tsayuwarta ta kumayi kana tace “Alhaji ina saurarenka, a gidan uwar wa ka makara hakan takasance... Shin ba cemin kai ka fice d’aurin aure ba... Toh idan ba auren ‘ya’yanka ka tafi ba auren uwar waye ka tafi....? Ko kana shirya wani abin ne ba tareda sanina ba...?” Ta k’arashe tana tsattsaresa da idanunta da tuni kwalliyan da akai mata ya soma zazzgowa ya b’ata mata fuska kaman ‘yar wasan tashe...

Tinda ta soma magana yake aika mata muguwar kallo... Cikeda borin kunya yake fad’in “Yanzu ba lokacin nuna yatsaga juna bane, kamata yai mu tafi gidan Usman muji uban waye ya bashi daman yai mana wasan k’wallon kondo da yara...!” Ya k’arashe yana kuma rarumar babbar rigarsa....
Chapter 133 · 0% Book details