← Book details Inda Rai Da Rabo Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 137 OF 198

Sashe 137

Inda Rai Da Rabo Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

A hankali Bara’atu ta jinjina kai kana ta fice cikin sauri....
Juyowa Mamy tai tana duban Ma’aruf da har lokacin yak’i yin shiru sai kukan a sai masa mota yake.... A hankali ta dafasa tace “Ma’aruf... Mota kake so...?”
Ya jinjina mata kai cikin sauri....
D’an fuzar da iska tai a hankali dikda bayanta da takeji kaman abu na mintsilinta, bata fatan Mamani ta shigo ta taddasu hakan tasan abun bazai kyau ba, dan idan Mamani tai mata tatas Bara’atu ba shiru zatai ba sabida fad’a irin nata itama, ita kuma bata fatan abinda zai d’aga hankalinta dana mijinta tinda mahaifiyarsa ce, idan kaji Mamy ta samu sab’ani da mijinta toh fah ka tabbata akan mahaifiyarsa ce kuma kan an tab’a tilon jikanta Ma’aruf ne... Hakan yasa Mamy ya zaro mayafi tace “Muje bakin kasuwan na sai maka....”
Tiryan tiryan suka d’au hanyar kasuwa tana rik’eda hannun d’anta ga zungureren ciki da ya sauk’a k’asa sosai... Sun isa kasuwa ana cikin mota abu kaman wasa ta soma jin ciwo na k’aruwa, sam bata kawo haihuwa zatai ba, aiko ashe dai haihuwarce tazo, azaba yasa ta saki hannun Ma’aruf tana kame mararta da cikinta... Kan kace me matan da suke kasuwar sun rufu akanta ana k’ok’arin bata d’auki na gaggawa... Tana iya jiyo sautin kukan Ma’aruf yana ambato sunanta “Mamy! Mamy!! Mamy!!!....”
Itama d’in ambato sunansa take “D’ah na, ku agazamin akwai d’ahna a wajen nan... Ma’aruf!!!” Inaaa tuni sarkin kasuwa ya iso da mota matan nan sun saka Mamy ciki an nufi asibitin general da iya dan babu wanda ya saurari cewa da take d’anta d’anta duk a zatonsu d’an cikinta take nufi....
Mamy ta numfasa kana taci gaba da fad’in “Daga wannan lokaci ban sake jin d’uriyan d’ah na Ma’aruf ba.... Farkawa nai na ganni kwance a gadon asibiti ga kuma jinjira a gabana nad’e cikin showel, abinda na fara fad’iwa nurses d’in shine “Ina D’ah nah... Ina Ma’aruf...? !!”
Nurse ta kusa dani ta d’auko jinjirar da na haifa ta mik’a min tana mai fad’in “Ba yaro kika haifa ba yarinya ce Gata nan....”
Cikin wane irin k’ara nake furta tare nake da d’ah na su bani d’ah na... Nurses sukace su basuga wani yaro ba ni kad’ai aka kawo ni.... Haka na dinga kuka ina fad’in su bani d’ah na, har saida suka min alluran bacci sannan dan ko jinjirar da na haifa na kasa d’auka....
Ko bayan dana dawo hayyacina na tadda labarin haihuwata ya isa ga ‘yanuwan mijina, Haka Mamani tamin chaaa a asibiti tace bataji ba bata gani ba sai na nemo mata jikanta Ma’aruf da ganganci na d’aukesa na tafi dashi kasuwa na salwantar dashi, wannan dalili yasa k’iyayyata data d’iyata Zulfa’u yai tasiri a zuciyar Mamani a cewarta ganganci na ne yasa na tafi dashi dikda ansan tsautsayi sannan ita kuma Zulfa’u itace mai farar k’afa yasa ranan da zatazo duniya d’an uwanta ya b’ace... A b’angaren mijina ma ban sami wani sauk’i ba domin kaw shima da hukuncin mahaifiyarsa yake aiki.... Bara’atu......” Birki ta d’anja sanda ta ambaci sunan Bara’atu kana ta d’ago kod’add’un idanunta a hankali tana dubanta....
Mamy ta sa hannayenta biyu ta share fuskarta kana taci gaba da fad’in “Bara’atu ‘yar uwata ita kad’ai ce bata gujeni ba... Kuma bata juya min baya ba... Tana nan taredani tsawon shakarun nan... Dan harta aure data tashi yi saida naita bata baki nace bazai yuwu ta k’are rayuwarta a kula dani da kuma yarana ba... Bara’atu ta sadaukarda lokutanta dukiyarta soyayyarta da duk wani abinda ta mallaka a gareni da ahalina... Dikda cewa mijinta ba mazauni bane, bata zab’i ta bishi ba, ta zab’i ta zauna dani a nan ta kula dani da kuma ahalina.... Bara’atu itace komai nawa tsawon shekarun nan wacce nake gani naji sanyi, wacce take d’ebe min kewa da soyayyarta mai tsafta, wacce take nuna min hanya a lokacinda na tassama b’acewa, K’anwa data zamto tamkar uwa a gareni... Shin ta yaya matar da muka aminta da ita nida ahalina zata mana haka..? Shin ta yaya zuciyata zata aminta da hakan ....’”” Ta k’arashe cikin tsananin rawar murya hawaye na gangaro mata...

Aunty B da kukanta ya tsananta durk’usawa tai gaban Mamy hannayenta biyu had’e waje guda lokaci guda take furta “Ki yafeni Mamy... Ki yafeni ‘yar uwata....!!” Ta kasa ci gaba da magana sai kuka.... Wajen yai tsit sai sautin kuka kawai da kakeji...
Haule ta tako tazo tsakiyarsu tana mai sakin shewa kana tace “Toh Mariya kin daiji wacece Aminiyar Sirri kuma tsawon shekarun nan har bayan bayyanar d’anki Ma’aruf bamu daina Aminci da AMINIYAR SIRRI ba..... Ba mijina bane kawai maci amanan d’an uwansa k’anwarki itace gasunk’umar maciyiya amana... Hasalima mu taimakon Ma’aruf muka tasamma yi wannan munafukar k’anwar taki itace tazo da shawarin a salwantar dashi... Itace AMINIYAR SIRRI...”

Wata Murya sukaji daga bayansu tana fad’in “Idan kunyi tunanin Bara’atu itace AMINIYAR SIRRI kunyi babban kuskure... AMINIYAR SIRRI ta rayu ne a tsakaninku cikin jikin Bara’atu..... A yau d’in zaku bud’e bakunan ku da kanku ku fad’i duk irin bak’in aikin da kuka aikata......”

Gabaki d’aya suka juya suna duban k’ofa.. Matar da babu wanda ya tsammaci ganinta a waje irin wannan.....

“Ni ce nan AMINIYAR SIRRI... Sirrikan zasu ci gaba da hak’o kansu... Wasu sirrika ne da wasu mutane suka jima da binnewa... Wasu sirrika ne da aka jima da aza masu k’asa... Kyawawan ayyuka sukan tafiyar da munana... Saidai wasu sirrikan basu yarda su b’oye kansu... Sukan bayyana kansu domin hakan ya zamto izna ga al’umman da zasuzo a baya....!” Ta k’arashe tana isa gaban Mamani da tai mutuwar zaune tana jin kalaman nata.... Yayinda gwaggwanayen Kazaure suka mik’e zumbur, Mamy da Aunty Bara’atu sukai mutuwar zaune suna kallonta....
Wani irin bugu k’irjin Engr yai saida ya dafe garundake gefensa sakamakon ganin fuskar wannan mata da yai.... Take k’wak’walwarsa ta shiga tina wasu abubuwa da suka faru shekaru masu tsawo... Haka ya dinga hango hotunan abin cikin k’wayar idanunsa tin sanda Mamy ta soma kwararo bayananta bugu da k’ari bayyanar wannan matar cikin k’wayan idanunsa... Dikda girma da ya kamata fuska ne da ya jima yana masa gizo a kwanyarsa da k’wayan idanunsa......

SameenaAleeyou📚

*INDA RAI*
_................DA RABO_

*91*

*©️Sameena Aleeyou...✍🏽*

Wannan ya kalli wannan wancan ya kalli wancan, hakance ta kasance... Wata sabuwa ana wata ga wata... Sameer da kansa gabaki d’aya ya k’ulle bud’e baki yai yace “Wai meke faruwa ne a nan... Wacece ke kuma...?!”
Matar ta maida dubantaga Sameer kana tace “Ni ce Aminiyar Sirri.. Nima kuma nayi tarayya ne da wata Aminiyar ta Sirri a yayinda na tura wata Aminiyar ta Sirri ta wakilceni tsakaninsu.....!!”
Haule da Lami harma da Baba Alhaji da mugun mamaki suke kallon matar nan... Wato ita Lami bama tasan mijin Haule nada babban kaso cikin zunubin da sukai tarayya ba sai yanzu.... Ita dik a nata zaton su uku suka k’ulla wannan sharri... Daga ita sai Haule saiko Aminiyarsu ta Sirri... Toh yanzu ga wasu batu suna fitowa daga baya... Lami kanta abin ya soma bata tsoro... Take ta tina jawabin Malaminsu na taubbu da ya tab’a sanar dasu muddin basuyi aikin da kyau ba Toh fah bazasu tab’a fahimtar komai ba, Abu a duhu ne zaita bayyana masu... Eh lallai ta yarda da batun Malam na cewa Abu a duhu... Ta yarda aikin had’aka akai wajen kawar da Ma’aruf tinda ga wasu fuskoki da batasan dasu ba cikin aikin suna kan bayyana...

Yanzu kam kan kowa ya kwance.... Wane irin al’amari ne wannan...??
Take Sameer ya shiga girgiza kai yana huci lokaci guda yake furta “Aminiyar Sirri Aminiyar Sirri..! Aminiyar Sirri....!!Shin Wai menene wannan Kalmar...? Maiyasa har yanzu magana k’wakk’wara ya kasa bayyana...? Maiyasa har yanzu gaskiya guda d’aya ta kasa fitowa... What’s all this..??”
Abbah ne ya nufi Sameer yana furta “Mu fice a nan d’ahnah, muje ka huta...”
Girgiza kai Sameer yake cikeda rud’ani yana furta “No Abbah I need to know everything, every single thing....I need to get to the bottom of this...!”
Baikai aya ba Ya Abida ta katsesa da fad’in “Babu wanda zai bar wajen nan sai an gama warware komai...!” Usman akwai abinda ya kamata kaima ka sani....!!”
Abbah da k’irjinsa ya buga kuma dubanta yai kana ya d’an girgiza kai yace “Ya Abidah kin jima kina shan magani na cutar damuwa (depression) inaga har yanzu baki ida warkewa ba... Ya kamata duk mu watse, duk wanda ya zalinci wani mu fawwala ma Allah komai, a b’angarena nida iyalina na tabbata bamuda matsalar yafiya....”
Matar da ya kirada Ya Abidah ta katsesa da fad’in “Usman ni d’in na jimada warkewa... Sannan akwai wasu sirrika da basu tab’a yardane su binne kansu... Ko Mamani...??”
Mamani da tuni idanunta sun kad’a girgiza kai ta soma tana k’ok’arin mik’ewa take fad’in “Kinga Abidah.... Maza ki fice mana a gida, magana ya riga ya k’are... Yanzu dai ga Ma’aruf Allah ya bayyana mana shi kuma in sha Allah dik muguntar mugu da k’ullin mai k’ulli bazai sake kama jikana ba... Jeki ki tafi can da k’uncin rayuwarki ki....”
Batakai aya ba Ya Abidah ta katseta da fad’in “Dama muguntarsu bai tab’a tasiri akan Ma’aruf ba ko sau d’aya ne kaman yanda sukai tunanin yayi... Kaman yanda sukai tunanin ya tafi tafiya ta har abada da bazai kuma dawowa ba.... Sannan sirrin da kikeso ki ci gaba da b’oyewa d’anki Usman bazai tab’a b’oyuwa ba muddin za’a warware wannan al’amari....”
Mamaki ya cika illahirin jama’an dake wajen idan ka d’auke Engr da har yanzu bai dawo daga duniyar tinanin da yai nisa ciki ba, memory d’insa ne kawai take flashing back... Hotunan abubuwa sunata dawowa kwanyarsa...
Chapter 137 · 0% Book details