← Book details Inda Rai Da Rabo Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 31 OF 198

Sashe 31

Inda Rai Da Rabo Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Tinda wannan mutumi ya fice daga gidan Hajiya Najah da Sahariyya ke ci gaba da santinsa suna addu’an Allah dawo dashi,
Najah ta dubi Sahariyya kana tace “Addah wannan guy d’in dai kinsan dani ya dace..”
Banzan kallo Sahariyya ta mata kana tace “Ke Najah ko a gidan giya akwai babba don haka wannan mutumin nawa ne...”
Najah ta tab’e baki tace “Sai mu jira dai muga wace zai zab’a...” Ta k’arashe tana juya idanu had’ida watsa mugun kallo wa Addar tata..
Sahariyya tai k’wafa tana fad’in “Eh lallai yarinyar nan wuyarki ta rik’a da har zanke fad’i kina fad’i...”
Najah ta shiga taku tana juya jiki take fad’in “A duba ko ajiki ansan wacce za’a zab’a ballanta sabbin jini irinmu ake yayi wllhi...”
Sahariyya takai mata jifa da takalmi Najah ta kauce tanaci gaba da taku had’idayuwa Addar tata gwalo...
Duk tattaunawar da suke Raihanah na d’aki na kwance tana saurarensu tana hawaye, gaba d’aya jikinta ciwo yake mata sabida bugun da taci, cikin zuciyarta take addu’ar Allah kawo mata d’auki ya shiryar da Hajiya da ‘yan uwanta idan kuma ba masu shirirya bane Allah ya fitar da ita daga wannan wahala da take ciki...
A b’angaren Hajiya kaw tana can d’aki tana faman safa da marwa tabbas yau taga abinda Lami ta gani....
Ta shiga yarfe gumin dake tsartsafo mata, meke shirin faruwa dasu, sirrin da ya jima a b’oye sama da shekaru 30 yana neman bayyana kanshi..
Ta kuma janyo wayarta hannu na rawa ta shiga neman layin Lami
Bugu biyu a na uku Lami ta d’aga...
Daga yanda Aunty Lami taji muryan Hajiya Laure tasan babu lafiya, aje wuk’ar da take yanka albasa tai kana ta mik’e tsaye tana fad’in “Laure lafiya..?”
Hajiya ta kuma yarfe gumi kana tace “Lami na ganshi wllhi na ganshi yau nayi idanu hud’u da Ma’aruf...”
Aunty Lami ta sauk’e ajiyan zuciya kana tace “Laure ki natsu kimin bayani yanda zan fahimta...”
Cikin sark’ewar murya Hajiya take fad’in “Bayanin kenan Lami Ma’aruf na gani, wannan k’wayan idanu nashi bazan tab’a mancewa ba, shin Lami ya akai yanzu yake neman dawowa rayuwarmu, shin Aminiyar Sirri bata tabbatar mana da mutuwarsa ba, ko kuwa dai mutum na mutuwa ya dawo ne, Lami randa duk Mariya tai idanu hud’u da gudan jininta ina mai tabbatar maki cewa zata ganeshi...”
Aunty Lami tai saurin tura k’ofar kitchen kana tace “Abinda nake sanar dake kenan, dolece ta kama mu wanke k’afafunmu muje mu samu aminiyar sirri don wllhi ko Malam zai tabbata yana fad’i mana abu a duhu baiga komai ba bazan yarda saurayin da na gani ba Ma’aruf bane.....”
Haule ta sauk’e ajiyan zuciya kana tace “Kinga maza maza ki fito mu tafi, ni da kika ganni ko wanka bazanyi ba zan fito sai mun had’u a mahad’a...”
Daga haka katse wayar tayi tana k’ok’arin shiryawa
Aunty Lami ta kashe girkin da take tana tunani, tabbas idan asirinsu ya tonu sai tafi Haule fad’awa uku sabida ta tabbata koda Mamy zata yafe mata Alhaji Usman Mailafiya bazai tab’a yafe mata ba uwa uba jarabebbiyar tsohuwar nan Mamani tabbas sai taga bayanta tsawon shekarun data jefata cikin k’unci....

Marliya data kawo mata aike daga wajen Mamy tsaye kawai tayi tana maimaita sunan da taji Aunty Lami na ambata “Ma’aruf” shi kad’aine abinda ta iya jiyowa sai kuma taji muryar tata tai k’asa... Tsaye kurum tai tana tunani tabbas idan bata mance ba wannan sunan Yayansu ne da ya b’ace shekaru masu yawa hasalima saidai a hoto suka sanshi yana k’arami d’an shekaru uku....A haka Aunty Lami ta bud’e k’ofar kitchen ta tadda Marliya tayi tsaye tamkar gunki tana aikin tunani, k’iris ya rage Aunty Lami bata dungura k’asa ba sabida tsananin tsoro da taji, ganin Marliya ce ya sanyata sakin murmushin yak’e tana fad’i cikin sark’ewar murya “A’a Marlili kin..kin jima ne a nan..?”
Murmushin Marliya ma tai mata kana ta girgiza kai tace “A’a Aunty isowata kenan... Ga wannan inji Mamy...” Ta k’arashe tana mik’a mata flask d’in hannunta
Aunty Lami tai k’ok’arin saita kanta ta amsa dukda rawa da hannunta keyi, zata bud’e Marliya tace “Kunun nono ne bata jima dayi ba...”
Nanma murmushin yak’e Aunty Lami tai kana tace “Ayya Mamy bata gajjiya tasan abinda nake so kice da ita na gode...”
Marliya ta jinjina kai kana ta fice cikin sanyin jiki...
Nabilah na kwance tana kallon shirin _Crush of the week_ Marliya ta shigo jiki a sanyaye ta zauna..
Nabilah nata mata labarin yanda ake gudanar da shirin tana kora kununta nan ta lura hankalin Marliya baya tareda ita..
Mik’ewa tai sosai ta zauna tana duban ‘yar uwar tata don da wuya kaganta cikin yanayi irin haka kana ta d’au throw pillow ta jifa mata tace “Ke meye haka, tunanin mai kike...?”
Marliya ta sauk’e ajiyan zuciya kana tace “Addah Nabilah shin Ma’aruf bashine sunan Yaya da ya b’ace ba years back....”
Nabilah ta jinjina kai kana tace “Toh sai akayi yaya, ko kin samo wa Mamy shine..?”
Marliya ta sauk’e ajiyan zuciya kana tace “Kinga yanzu da na kaiwa Aunty Lami kunun nan.... I overheard her talking on the phone kaman sunan take ambata kuma wayar nata kaman na sirri kaman bataso wani yaji...”
Nabilah ta gyara zamanta sosai
“Ma’aruf kawai kikaji ta ambata bakiji komai ba..” Nabilah ta tambaya
Marliya ta jinjina kai kana tace “Addah Nabilah I don’t want to believe this, ban sani ba meyasa zuciyata tak’i aminta da wayar da Aunty keyi... Is like she’s hiding something... Oho I don’t know...”
Jinjina kai Nabila tai tana hura hanci kana tace “Shiyasa na tsani matar nan tuntuni, something about her is fishy, tayita nunawa Mamy soyayya kuma bayan da ba haka take ba, who knows wayasani maybe she has something to do with our brother’s disappearance....”
Girgiza kai Marliya tai kana tace “A’a kada kice haka, Allah shine masanin gaskiyar lamarin tinda banji komai ba bayan suna da naji ta ambata ta yuwu wani Ma’aruf d’in ne.. And please kar kicewa Mamy komai kada mu d’ago mata gyambon dake zuciyarta mu maidasa sabo...”
Jinjina kai Nabilah tai kana tace “Idanma tana b’oye wani abin I’ll find out, kuma wllhi idan na fahimci cewa itace silar k’uncin Mamy sai yanda k’arfina ya k’are...” Ta k’arashe tana mai tsananin huci....

A b’angaren Sameer kuwa tinda ya isa asibitin yake jinsa wani iri, abubuwan da suke faruwa dashi a Kano sun d’aure mai kai, ji yake tamkar wasu memories ne da suka faru lokaci mai tsawo, shin kodai iyayenshi sun zauna a garin ne particularly wannan unguwar da a yanzu yake zaune cikinta, shin kafin suyi zaman Amurka k’ila nan ne garin da suka fara zama idan ba haka ba meyasa yakejin wani abu gameda environment d’in da mutanen cikinta... A hankali ya sauk’e ajiyan zuciya can wata b’angare na zuciyarsa na tuna masa yarinyar nan Raihan da halin da ya barta ciki...
Agogon hannunsa ya kuma dubawa ko lokacin sallah tayi sabida yanada wani surgery da rana, wani tunani ne ya fad’o masa kana ya suri makullensa ya fice...

Dai-dai k’ofar gate d’in yayi parking yana neman yaron da zai aika cikin gidan... Can saiga wani yaro yazo shigewa Sameer ya tare shi da niyyar aikanshi...
Wata leda ya ciro cikin motarsa ya mik’awa yaron yace “Kaga nan gidan...” Ya masa nunida gidan Alhaji Sani mahaifinsu Raihanah...
Yaron ya jinjina kai yace “Eh.. nasan gidan a unguwar nan nake..”
Sameer yace “Good, ka shiga ka bada wannan sak’on wa Raihan...”
Yaron ya d’an subeshi sai kuma yace “Raihan kuma nasan dai akwai Raihanah a gidan, ba ‘yar Hajiya bace shiyasa kullum Hajiya ke bugunta Mamarta ta jima da rasuwa tun tana yarinya shiyasa ta girma hannun Hajiya... Amma tafi kowa kirki a gidan..”
Tinda yaron ya soma zuba Sameer ke dubansa yana jinjina lamarin, tabbas biri yayi kama da mutum, no wonder matar nan take jibgan yarinyar tamkar ba biladama ba ashe ba d’iyarta bace, wani tausayi ya kuma taso masa.. Duban yaron yayi yace “Maigidan na raye...?”
Yaron ya jinjina kai yace “Yana nan saidai baya iyayin komai a gidanshi...”
Shiru yayi na d’an lokaci yana tunanin abubuwan da yaji daga bakin wannan yaro mai yawan magana, tabbas zaiso ya had’uda maigidan nan dukda cewa ba huruminsa bane amma zuciyarsa sosai ta aminta da ya sadu da maigidan nan..
Yaron yana shigewa Sameer ya shiga motarsa ya wuce..
Sahariyya ya tadda tsakar gidan kwance saman tabarma da pillow tana karanta littafi yayinda Raihanah ke kwance har lokacin a d’aki...
Sallama yaron yayi Sahariyya ta amsa mashi a dak’ile ta k’arada “Wajen waye kazo...?” tana maganar tana duban ledar hannunsa...
Yaron yace “Wani mutumi ne yace a bada wannan ma Raihanah...”
Jin an ambato sunanta ya sanya gabanta mugun fad’uwa tana tunanin kardai mutumin can ne ya dawo...
Sahariyya ta aje littafin hannunta had’ida mik’ewa zaune tana mai gyara d’aurin k’irjinta taceda yaron “Kawo nan..”
Yaron ya d’an doje yace “Nifah ma Raihanah akace na bada...”
Sahariyya ta mik’e sosai tana fad’in “Kai banson iskanci kada ka bari na tashi... Waye ma ya aikoka...?”
Yaron ya k’araso ya dangwala mata ledar kana yace “Wani mutumi ne mai kyau had’ida mota mai kyau...”
Ai Sahariyya batasan sanda ta mik’e tsaye ba tana fad’in “Ina yake... Gudu jeka ka taremin shi...”
Yaron ya mata wani kallo kana yace “Ai ya tafi.... Saidai kiyi hak’uri...”
Harara ta watsawa yaron kana tace “Toh uwar mai kake jira kaikuma da bazaka fice daga gidan ba.....”
Yaron na k’unk’unin shima Raihanah akace ya bada aiken ya fice, Sahariyya sai danna masa ashariya take..
Tai saurin bud’e ledar tana zazzagewa abubuwan ciki suna fitowa...
Magunguna ne da na sha da na shafawa danginsu pain reliever...
Take ta kuma yin kicin kicin da fuska kana ta shiga k’wallawa Raiha kira..
Jiki a sanyaye Raihanah ta fito ta tadda Sahariyya
Wani kallo Sahariyya ke watsa mata kana tace “Munafuka duk salon yaudarar namiji kin iyashi k’arama dake, toh kaw kinaji kina gani maganin nan hanyar ruwa zan watsasu bazaki amfana dashi ba, b’ace min da gani anammimiya...”
Hawayen da suka zubo mata ta kuma gogewa kafin ta koma d’aki cikin tafiya da yafi kama da d’ingishi...
Sahariyya ta rakata da mugun kallo...

***
Chapter 31 · 0% Book details