Sashe 165
Inda Rai Da Rabo Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
A can Abuja asibiti kaw dik yanda Khalid yai ya daidaita tsakanin ahalinsa dakeda b’angare biyu a halin yanzu abu yaci tura, shin wanne zai zab’a wanne zai bari... Ga matarsa da matar Babansa b’angarensu guda sannan a d’aya b’angaren ga mahaifiyarsa da ‘yaruwarsa Siyama da kuma nasu tawagan... Ma iya cewa a halin yanzu rashin lafiyan Daddy yafi damun Khalid dasu Aunty Daula, ita kaw Ammi da nata ayarin basuda buri da ya wuce Daddy ya tashi ya warware wannan badak’ala da ya had’a, dan ita Ammi cewa tai ita bata yarda ma Daula matar Daddy bace har sai Daddyn ya tashi ya sanar da ita hakan da bakinsa sannan bata yarda Nabilah matar Khalid bace itama har sai Daddyn da yaje ya d’aura auren ya farka ya k’aryata auren munafuncin da yaje ya k’ullawa d’anta.... Haka ake zamana asibitin kaman zakuna a fagen daga ana hangen juna daga nesa nesa, Aunty Hanne na gefe na ziga Ammi cewa koda wasa kada ta yarda ta amince Daula matar mijinta ne sannan Nabilah matar d’anta ne...
Khalid na daga tsakiya tsakankanin mata shi kad’ai har abin tausayi... Idan ka gansa dole ne ma ka tausaya masa, babu hali ya nufi yanda matarsa da Aunty Daula suke Ammi zata doka masa kira tana fad’in idan ya k’arasa wajen tsinannun can saita d’aga masa nono... Haka badon yaso ba zaka ga ya juya har abin taisai... Shida Nabilah saidai kallo daga nesa har su baka tausai... Gashi ga matarsa amma bai isa ya tink’areta ba itama bata isa ta tink’aresa ba... Yesmin da Kubura kaw hakan ba k’aramin dad’i yai masu ba tamkar su zibda ruwa k’asa su sha.....
Shi kansa Dr Hameed har yana tinanin tink’aro wad’annan family da suke nema su maida masu asibiti filin cecekuce dan ma Allah yasa su Aunty Daula basa biyesu... Dik zafin zuciya irin na Aunty Bara’atu tana k’ok’arin danne kanta dan tasan a halinda ‘yar uwarta ke ciki bata buk’atan tashin hankali....
Dr Hameed ya nufosu da result d’in hoton chest d’in Daddy dan tabbatar da cewa bai sami matsala a heart ba ko wani internal bleading.... Gaba d’aya suka taso ta ko wane b’angaren suka nufosa....
Aunty Daula na hawaye take tambayar Dr Hameed sakamakon result d’in... Kafin yakaiga bada amsa Ammi ta fuzge result d’in tana fad’in “Bak’ar munafuka kin wani taso kina hawaye na munafunci, ni danai shekaru sama da talatin taredashi banyi kuka ba saike... Dan ki nunawa duniya ke kin cika munafuka koh...!”
Aunty Hanne ta tari zancen da fad’in “K’yale munafuka ta nuna ta fiki k’aunar mijinki....!”
Dr Hameed ya d’anyi gyaran murya kana ya soma fad’in “Wato....!” Dakatar dashi Ammi tai da fad’in “Ya isa basai taji halinda mijina ke ciki ba, it doesn’t matter ta sani ko kar ta sani....Dan a idanuna ita ba matar Ahamadi Mainasara bane....Kaga likita shige kaje abinka....!” Ta k’arashe tana mai danna result d’in cikin handbag d’inta....
Khalid da zuciyarsa ke tsananin tafarfasa muguwar kallo kurum yake aikama Aunty Hanne da Ammi.... Lokaci guda yake girgiza kai cikeda takaici....
Jiki a sanyaye Aunty Daula ta juya ta koma yanda ta baro Aunty Bara’atu da Nabilah su Yesmin da Siyama sai faman aika masu wulak’antaccen kallo suke daga nesa.... Daga Aunty Bara’atu har Nabilah k’arfin hali kurum suke amma kam su Siyama sukaisu k’ololuwa...
Shiko Khalid cikin sauri yai k’ok’arin takewa Dr Hameed baya, sai sinkayo muryar Ammi yai tana fad’in “Khalid koda wasa wllhi karma kai tinanin zaka bisa Office ya sanar dakai ka zago ka fad’a ma wannan shu’umar yarinyar da a haife na haifeta.... Idan kuma ka sanar da ita condition d’in Daddyn Siyaam ban yafe maka ba...!”
Aunty Hanne dake gefe ta shiga jinjina kai tana fad’in “Kinyi daidai Farida...!”
Khalid ya juyo yana duban mahaifiyar tasa cikeda takaici... Takowa yai zuwa gabanta kana yace cikin tsananin k’unan rai “Really Ammi....? Wai dan Allah mai kike so ne.... Mai kike so ai yanzu dan Allah ki daina dik wad’annan abubuwan... Do you want me to beg on my knees..!” Yai maganar yana mai kai gwiwoyinsa k’asa... Lokaci guda ya had’e hannayensa duka biyu waje guda yana mai ci gaba da furta “Ammi please... Stop all this, please put an end to this ko dan halinda Daddy yake ciki... Dan ki k’yale Aunty Daula haka nan... Ta cancanci tasan halinda mijinta Ke ciki itama... Ammi na rok’i arzikinki ki sauk’e dik wani fushin da kike da Daddy akaina... Amma Ki k’yale Aunty Daula haka nan... Tanada zuciya mai kyau...”
“Kai dalla cen rufe min baki...! Sun baka a ruwa kasha... Toh kaima ka sani bawai na gama dakai bane da wannan kwashesshen auren naka... Jira nake shi wanda ya had’a wannan Auren shiriritar ya tashi ya kwanceta dan wllhi kaji nai maka rantsuwa ina numfashi baka isa kai zaman aure da yarinyar nan ba...!”
Aunty Hanne Ta k’arashe da fad’in “Yauwa fad’a masa dai yaji da kyau.. Matarsa guda d’aya ce nan gidan Duniyar k’anwarsa Yesmin...!”
Wani irin muguwar kallo Khalid ya watsa mata kana ya mik’e yana bug’e gwiwar wandon jeans d’insa yanda ya duk’a lokaci guda yake furta “Amma dai Aunty ya kamata a d’an ringa dubawa ana kama girma....”
Aunty Hanne ta shiga sallalami tana kame baki “Saifullahi ni kake maida ma martani... Eh lallai na yarda ba haka kawai suka Barka ba....!”
Ammi tai k’wafa kana tace “Nan gaba bama maida martani ba had’emu zai gaba d’aya yace zai zane sabida an tab’a danginsa na asali, matarsa da uwarta... Yayi Khalid... Ya maka kyau... Toh ka dakemu mana kawai sai nasan ka cika...!”
Shidai bai kuma tofawa ga tsananin zafi da k’irjinsa ke masa, tsakaniga Allah he’s tired of all this... Bai kuma cewa komai sai sa kai da yai ya fice gaba d’ai daga cikin asibitin dan hakan ne kawai yafi masa sauk’i a halin yanzu...
***
KANO
Tagumi Haule ta rapka tana duban ‘yandaudu dake baje tsakiyar gidan nasu suna buga lido da karta ga k’aurin hayak’i da ya kaure gidan gaba d’ai....
Dr Awwab ya ida duba jikin Sahariyya ya bata dik wasu magunguna da take buk’ata kana ya dubi Haule yace “Jikin nata da sauk’i sosai k’unan is not that deep so basai an kaita asibiti ba, with the help of these prescriptions zata sami sauk’i cikin yardar Allah....”
Haule ta sauk’e ajiyan zuciya kana tace “Likita mun gode sosai...”
Awwab yace “Kuyi godiya ma Allah dan shi ya kiyaye sannan kuyi godiya ma Sameer dan shi ya turoni na dubata....” Yai maganar yana had’e kit d’insa...
Haule da Sahariyya suka dubi juna cikeda al’ajabi... Haule tace kana nufin kace Sameer d’in shine ya turoka ka duba Shariyyar...?”
Awwab ya jinjina kai kana yace “Eh Hajiya Dr Sameer shi ya turoni...”
Wasu sabbin hawaye suka ciko idanun Haule babu shiri....Tasa bakin zaninta tana gogewa.. Lokaci guda take ceda Awwab “Mun gode Ubangiji ya saka da alkhairi... Zamu nemi kud’in aikinka mu biyaka daga baya...!”
Awwab yace “Sameer ya wuce haka a wajena... Magunguna da treatment dik kyauta ne kuma in sha Allah zanke lek’owa ina duba yanayin jikin nata.. Allah shi k’ara afuwa....!” Ya k’arashe yana mai masu sallama kana yai ficewarsa ‘yandaudu na d’aga masa yatsa ko takansu baibi ba....
Sahariyya da Haule suka dubi juna suna mamakin ya akai Sameer ya sani har ya turo abokinsa duba Sahariyya... Najah da shigowarta kenan tace “Ni ce nan na kira Raiha na sanar da ita halinda Addah Sahariyya ke ciki gashi ko tasin kaita asibiti a duba lafiyarta babu ga Baba Alhaji dai yanzu bama gabansa dan ‘yandaudu ma sunfimu ‘yanci yanzu a gidan nan shisa na yanke shawarin sanar da Raiha ita kuma ta sanar da Ya Ma’aruf... Ku gode ma Raihana ku godema Ya Ma’aruf dan bayan dik tilin abubuwan da kukai masu sunada zuciya mai kyau zuciyar yafiya.... Basu k’ullaceku a zukatansu ba....”
Haule da jikinta ya kuma matuk’ar yin sanyi share hawayen idanunta ta kumayi kana tace “Hak’ik’a duniya makaranta ce... Mugunta hassada da k’iyayya ba komai zasu kaika ba sai tarin danasani da d’inbin madama.... Yau ga Ma’aruf yaron da naso salwantarwa tin yana k’arami ya taimaki d’iyata bai k’yaleta ta rub’e a kwance ba, bai k’yaleta ta salwanta kaman yanda naso salwantar dashi ba... Sannan Raihanah yarinyar da tin tasowarta batasan komai daga gareni ba face gallazawa da azabtarwa daga gareni da kuma ita kanta Sahariyya... Sahariyya ita ta k’ona Raihana ta kuma so sake k’onata a karo na biyu Allah ya maida mata mugun nufinta kanta... Gashi yau Raihana Ta taimaketa... Kaicon wannan rayuwa mai cikeda tarin danasani....!” Ta k’arashe tana mai fashewa da kuka...
Sahariyya ma kuka take tana furta “Tabbas wannan hakki ne... Hakkin Kausar da kuma Raiha shine ya bini.... Inama Kausar tana raye na rok’eta gafara... Inama na kasance mutuniyar arziki... Kaicon wannan rayuwa...” Ta k’arashe tana kuka mai tsuma zuciya itama.... Naja’atu dake faman share nata k’wallan itama cikeda tausayin mahaifiyarta da ‘yar uwarta Ta shige tsakankaninsu ta had’esu ta rungume suna kuka mai tsuma zuciya...
A haka Lami ta shigo ta taddasu d’aukeda jakkan kayanta... Haule ta shiga goge hawayenta tana fad’in “Lami lafiya na ganki haka... Ina zaki da jakkan kaya...?”
Aunty Lami ta kuma goge ragowar hawayen idanunta dan itama daga gani taci kuka harta gode Allah... Maimakon ta baiwa Haule amsa sai cewa tai “Haule haka gidanki ya koma matattaran ashararru....? Haule haka rayuwa ta juya mana...?”
Haule ta kuma share hawayenta kana tace “Lami abinda muka shuka ne... Yau ga sakamako muna girba.... Ina zakije da kaya...?” Ta k’arashe cikin tsananin rawar murya...