← Book details Inda Rai Da Rabo Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 111 OF 198

Sashe 111

Inda Rai Da Rabo Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

A can gidan Abban kuwa Zulfa’u durk’ushe take gaban Iyayen nata Bana Alhaji da Abbah, Baba Alhaji ya kuma gyara zama kana yace “Ke muke saurare Zulfa’u kinyi shiru, shirunki na nufin kin amince da komawa gidan mijinki na fari kenan....”
Abbah yai saurin katsesa da fad’in “A’a Yaya shirun bazaura baya nufin Eh ne, idan baka mance ba ko shari’a cewa tayi Budurwa ce shirunta ke nuni da Eh amma banda bazawara, Yaya karmu mata dole, akwai lokaci, munada nan da wattani biyu gaba idan har tayi shawari ta tantance sai ta sanar damu amma babu batun tilastawa, koda bata tab’a aure ba ma nayi alk’awari bazan kuma tilasta ma d’aya daga cikin yarana ba, ina kuma fata iyaye masu wannan d’abi’a su farga su daina...” Banda uwar harara babu abinda Baba Alhaji ke aika masa... Ala dole ya jinjina kai kana ya dubi Zulfah da kanta ke k’asa tin shigowarta yace “Maza tashi ki shige gida, amma ki sani bazamu zuba miki ido ba kaman yanda Babanki keso mu sakaki gaba muna kallo, kafin wa’adin nan ya cika kizo mana da zance mai dad’i....”
Jinjina kai kurum tai ba tareda cewa komai ba don idan ta bud’e baki tabbas kuka ne zai fito....
Cikeda tausayawa Abbah ke dubanta, cikin muryar mai taushi yaceda ita “Tashi kije mamata.... Allah Ubangiji ya miki albarka ya miki zab’i mafi alkhairi...”
Baba Alhaji ya saki baki yana kallon d’an uwan nasa, k’wafa kurum yai ba tareda cewa komai ba saima karkad’a kai da yake tamkar wani k’adangare....
Zulfah tana shiga gida ta fad’a jikin Mamy sai kuka, haka Mamy taita lallashinta tana nuna mata ko wani bawa da kalan tasa k’addaran a rayuwa ita kuma kalan tata k’addaran kenan....
Koda Sameer yazo ya sami Abbah da batun shikam Abbah mamaki ma abin ya bashi ganin lokaci guda maganan auren yaran nasa ne yaketa kunno kai kaman wad’anda ake ingizawa, da farko Ma’aruf ne da Zulfa’u yanzu kuma ga Nabilah....Shiru yai tamkar mai nazari har lokacin baice komai ba....
Sameer ne ya d’an gyara zamansa had’ida gyaran murya kad’an kana yace “Abbah idan baka shirya tarbansu ba babu matsala ni sai na sanar da Daddyn sai zuwa wani lokacin....”
Girgiza kai kad’an Abbah yai kana yace “Ba nufina ba kenan Ma’aruf, shin tambayan izini zasuzo ko kuwa neman aure zasuzo, idan neman aure zasuzo toh fah dole sai nayi magana da d’iyata, na sani d’anuwan matarka ne kuma babu wani dogon bincike tinda kai ka sansu tare kuka taso amma d’iyata fah? Dole sai anji daga gareta...”
Sameer ya jinjina kai a hankali kana yace “You’re right Abbah...”
Abbah yace “Yauwa yayi kyau daka fahimci hakan, zan sami mahaifiyarta ta tuntub’eta muji nata b’angaren... Idan ta amince tana son D’ansu shikenan sai suzo muyi magana, don burin ko wane uba kenan yaga d’iyarsa data isa munzanin aure a d’akin mijinta... Duk yanda mukayi da mahaifiyarku zan sanar dakai kai kuma saika sanar dashi....”
Sameer ya amsada “Toh Abbah hakan yayi....”
Abbah ya jinjina kai kana yace “Toh kai ya batun naka auren....?”
Gaban Sameer ya yanke ya fad’i, shi harga Allah mancewa yakeyi da wani aure dake gabansa...
Ganin yayi shiru yasa Abbah cewa “Anya Ma’aruf kana farin ciki da hukuncin da ka yanke...?”
Gaba d’aya sai yaji jikinsa ya masa mugun sanyi da tambayar mahaifin nasa, ta yaya zai sanarda Abbah yana Farin ciki da wannan hukunci da ya yanke ma kansa bayan yasan ba hakan bane, toh amma wannan hukunci ne da ya riga ya yanke ma kansa dukda sanin cewa shi kansa baisan ko zai iya ba...Baikaiga bashi amsa ba sukaji sallama daga k’ofa, Aunty Lami ce ta shigo sai washe baki take tana kod’a Sameer da fad’in “A’ah Kaga ashe ma ga angon a nan... Ango mai tagwayen mata dama nemanka nake....”
Murmushin yak’e kawai Sameer keyi yayinda Abbah ya tsare yana dubanta...
“Sameer yace wani abu ne Aunty...?”
Aunty Lami dake k’ok’arin zama saman kujeran gefen Abbah tace “Dama kan maganan lefe ne, kasan Mamy dai ‘yar kunyace ta d’an fari tsakaninku shine ta wakiltani mu tattauna komai, kama daga kayan lefe zuwa duk wani abu na Al’ada da za’a buk’ata kaga sam bamuda wani sauran lokaci wata biyu ne jal ya rage mana baima cika ba...”
Sameer ya d’an shafa kansa kana yace “Wannan duk babu matsala Aunty, duk abinda ake buk’ata a fad’a mun, kayan lefen kuma zan maki transfer din kud’in zuwa account d’inki idan akwai abinda yayi short sai a sanar dani...”
Aunty Lami ta shiga Washe baki tanaci gaba da kod’asa yayinda Abbah yabi d’an nasa da duban tausai, harga Allah tausayin Sameer yake don yasan wannan aure tilasta ma kansa kurum yayi..... Wayar da ake bugowa Sameer d’in ya sanyashi mik’ewa ya fice don amsa kiran yayinda Aunty Lami taci gaba da kid’inta tana rawarta don sam Abbah bai kulata ba tinda shi ba farin ciki yake da wannan aure ba....
***
Koda Mamy ta tuntub’i Nabilah da batun Khalid bata bata k’wakk’waran amsa kai tsaye ba, ita Nabilar gani take kaman anyi gaggawa, wai ita ake maganar aurenta bayan ga Addah Zulfah yanzu a gida ita kam da dai an bari ba yanzu ba har ta tafi IT, miyema na gaggawan....
Mik’ewa Mamy tai ta dubi Nabilah da har lokacin kanta ke duk’e k’asa kana tace “Idan nima kunyata kikeji ga Addarki nan sai ki sanar da ita, idan baki sonsa kar a b’ata masu lokaci na sanar da mahaifinku....”
Sai sannan ta d’ago tana duban Mamy da idanunta da sukai raurau, ita fah Wai son Khalid bane batayi hasalima bata tab’a soyayya da wani d’ah namiji ba bayan Khalid d’in, amma abinne yazo mata a bazata, sannan sai tana ganin kaman anyi hanzari, bata ce komai ba har Mamy ta fice...
Zulfa’u ta kamo hannayen ‘yar uwarta murmushi kwance saman fuskarta take fad’in “Nabilah karki dubi wai dan gani nan a gida, shi aure ba haka yake ba, koda ace ban tab’a aure ba kowa da lokacinsa, sau nawa k’arama a gida takanyi aure ta bar yayyenta, hakan ba yana nufin laifinsu bane ko gazawarsu ce, a’a lokacinsu ne baiyi ba don shi aure hab’o ne da zaran lokaci yayi toh fah sai anyi, haka nan wasu nasu lokacin a kusane ballantana ke da har kike jami’a da girmanki da hankalinki, nidai a nawa ganin idan har kina sonsa ki basu dama....”
D’ago idanu tai tana duban Zulfa’un kana tace “Nifah Addah Zulfah bawai son Khalid bane banayi, hasalima kinsanni banida wani saurayi tun tasowata idan bashi ba sabida no one stands me, fad’ata kawai ta ishesu shid’in dai shine nake tunanin fad’an nawa ne yafi komai birgesa, kuma Addah danginsa fah basa k’aunata especially wannan matar Ya Ma’aruf d’in meyasa all of a sudden zasu amince ya aureni, something doesn’t add up gaskiya....”
Girgiza kai Zulfah tai kana tace “A lokacin da basu k’aunarki basu san wacece ke ba, kumama banda abinki Siyama ai matar Yayanki ne so na tabbata abubuwan data miki da bazata miki yanzu ba indai har tana k’aunar d’an uwanki toh ko shakka babu kema zata k’aunceki, duk bama wannan ba, shi uban gayyan tinda yana sonki ai an gama komai tinda dashi zaki zauna badasu ba...”
Dubanta kurum Nabilah keyi kana tace “Amma Addah ke kinsan illar ace dangin miji basa k’aunarka tinda ya faru dake dasu Hajiyar Ya Hafiz da yaranta...”
Zulfah ta d’an murmusa kad’an had’ida girgiza kai “Wannan yasha bambam da nawa Nabilah, shi Khalid mutumin k’warai ne kuma shi ya nuna yana k’aunarki ni kuma Ya Hafiz dole aka mana kuma bai k’aunata shiyasa ya kasa karb’a mun mutuncina wajen ‘yanuwansa, na tabbata Khalid bazai bari wani nasa ya muzguna miki ba ko ya tozartaki, kuma kema shaidace akan hakan... Amma zab’i na gareki k’anwata, abinda kikeso muma shi muke so... Allah ya miki zab’i na alkhairi kinji koh....”
Nabilah na murmushi ta rungume ‘yar uwar nata tana fad’in “Allah ya shiga al’amranmu gaba d’aya Addah ta....”
Zulfa’u da ce ta sanarda Mamy yanda sukai da Nabilah, tabbas Khalid baida wani aibu idan ka cire mahaifiyarsa da ‘yaruwarsa Siyama, kuma ko wane aure dole yazo da kalan nasa tangard’an tinda abu ne wanda shaid’an bai k’aunar yaga anyishi, babban abinda ake buk’ata shine ma’arautan su kasance masoyan juna ne duk soyayyar wani daban akan iya samu daga baya, tabbas Abbah ya cika alk’awarinsa na baiwa yaransa dama wajen zab’en abokan zamansu...
Bayan kwana biyu ya sami Sameer da batun don bai kamata abar babban mutum irin Daddy yaita jiran tsammani ba, Abbah ya tabbatarwa Sameer sirkinsa Daddy ka iya zuwa neman auren d’iyarsa Nabilah ga d’ansa Khalid, dikda cewa har yanzu Sameer d’in bai shiryada Siyama ba sosai yaji dad’in wannan had’ida za’a kumayi Don ko babu komai Khalid d’an uwane a wajensa koda bai auren Siyama, tare suka taso k’aramin k’ani ne a wajenshi they’re practically brothers... Baiyi k’asa a gwiwa ba ya sami Daddy da batun.... Sosai Daddy yaji dad’in martanin da ya samu daga iyayen Sameer d’in tuni ya shirya ranan tunk’aran mahaifin Sameer da batun, mutum biyu ya wakilta tare dashi shine cikon na ukun, mutane biyun kuwa duka sirakansa ne, Mijin d’iyarsa Siyama Wato Sameer saiko Yayan matarsa Wato Engr Ma’aruf....
***
Chapter 111 · 0% Book details