← Book details Inda Rai Da Rabo Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 191 OF 198

Sashe 191

Inda Rai Da Rabo Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Sai dare su Zulfah suka tafi suka barsu da kewa, Raihanah ce kawai kwance d’akin Mamy, Ta ida sallan isha ta d’an mik’e wajen... Marliya nacan k’ofan Baffah Ado sashen su Sakina yayinda Mamy ke sashen Abbah....

Kaman daga sama ta jiyo sallamarsa, da alama dawowarsa kenan daga asibiti... Ta mik’e zumbur tana k’ok’arin amsa masa sallamar, saidai kafin takaiga amsawa har ya shigo cikin d’akin yana mai tsareta da idanu...
Sannu da zuwa tai masa tana k’ok’arin linke abin sallahn.. Ya amsa yana mai kuma tsareta da idanu tamkar mai jiran wani abin... Itafah harga Allah har yau nauyinsa takeji gashi ya iya tsareta da wannan idanun nasa... Muryarsa ta sinkaya yana fad’in “Haka akewa miji sannu da zuwa...?”

Ta d’an d’ago tana dubansa, gani tai ya tsime sosai....
Ta d’an kauda fuska tana k’ok’arin shanye murmushinta dan idan da Sabo ta soma sabawa da wannan tsimewar tasa wanda ta lura d’abi’arsa ce yanzu zakaga yana murmushi yanzu zakaga ya tsime...
A hankali ta furta “Toh ya akeyi Yaya...?” Tai maganar tamkar mai koyon magana...
Hannayensa ya bud’e mata ba tareda cewa komai ba, ta gane mai yake nufi dan haka a hankali take takowa zuwa gareshi, saida ta k’araso dab kusansa kana ta d’an saci kallon k’ofa tamkar mai tsoron kada wani ya shigo... Ya gane nufinta gani take d’akin Mamy ne she can’t hug him in here... A hankali shi ya tako ya k’araso gareta had’ida rungumarta.... Ta kuwa yi lamo cikin k’irjinsa, saitin kunnenta yake rad’a mata “This is my sannu da zuwa...from now on... Kinji koh...!”
A hankali ta jinjina masa kai tana mai k’ok’arin janye jikinta, ya kuma rik’eta kana yace “Are you ready....Kin shirya mu tafi...?”
Da mamaki take dubansa kana ta d’an sadda kai tace “Yaya ina zamu...?”
“Gidanmu zamu tafi, kwana a nan d’in ya isa haka, I want my wife beside me...!” Ya k’arashe yana mai shafar bayanta a hankali tamkar mai lallshi...
Ta d’anyi still cikin k’irjin nasa sai kuma tace “Amma ai Mamy batace ba fah....!” Tai maganar tamkar mai shirin sakin kuka...
“Mamy da kanta ta buk’aci hakan... Bakida labari....?”
Ta kuma d’agowa tana dubansa...
Jinjina mata kai yai alamun tabbatarwa kana yace “Should I help you park your things...?”
D’an Jim ta d’anyi kana tace “Toh amma idan Mamy taga ina parking Kaya ni mai zance mata...?” Tai maganar tana turo baki gaba...

Bata ankara ba sai ji tai ya sumbaci bakin a hankali yana mai furta “Kice mata zakibi mijinki zaku ci gaba da cooking classes d’inku...”
K’walalo idanuwa waje tai tana dubansa cikin sauri, lokaci guda kuma ta sadda nata idanun k’asa tana fad’in “Ni dai wllhi kunya nakeji Yaya dan Allah kawai ma ka barni a nan kaji...!” Tamkar mai shirin kuka haka tai maganar...
Sameer ya d’an sha mur kad’an kana yace “Bakiso ki ci gaba da classes d’inki ne... Ke ‘yar gata da miji ne ma ke koya miki... Or have you ever heard of matar da mijinta Ke koya mata girki.....?”
Ta d’Anyi Jim tana dubansa sai kuma ta girgiza kai alamun a’a... Sameer ya jinjina kai yace “See....!Kinga Ke mai sa’ a ce...”
D’an gyaran murya tai kana tace “Yaya Wai Maiyasa kake girki, wannan ai aikin mata ne su aka sani da shiga kitchen...”

Yanda ta jefo masa tambayar ya sanyasa kafeta da idanu... Murmusawa yai kad’an kana yace “Lokacin da mukai zaman US nakan shiga kitchen na taya Mummy a nan na koya... Daga nan ya zama one of my hubby...”
D’an jinjina kai tai kad’an kana tace “Toh mai kenan matarka zatai ta birgeka if you can cook better than her...?”
Murmusawa ya kumayi kana yace “Naki sai yafi nawa, idan kinyi musamman domin ni sai yafi birgeni, and one more thing... Matarka is your companion, your friend and your partner... She’s not your maid nor your slave....So babu wani aibu dan once in a while ka girka mata abinci... One mistake da nai da Siyama shine na nuna mata nid’in zankeyi shiyasa batayi... Amma yanzu she changed her ways, kuma haka yafi komai min dad’i....”

D’an murmusawa tai kad’an kana tace “You really love her..!”
Ya jinjina mata kai yana mai furta “So much....” Lokaci guda ya kuma kamo yatsun hannunta kana yace “I love you both....!”

Ta murmusa tana mai kwantar da kanta cikin k’irjinsa, sallaman Mamy ya sanyasu janye jikkunansu daga cikin na juna....

***

Masha Allahu, Allah shi ke bada Mulki ga wanda yaso ya kuma hana wanda yaso domin ya jarabci bayinsa... Anyi Election lafiya, sakamako ya fito a Washe gari, yanda aka bayyana Engr Ma’aruf Mutallab a matsayin wanda lashe zab’en ... Gari ya cikada rally da murna, dik yanda ka shiga shagalin murna kawai zakaga anayi, masu adaidaita da masu babura babu yasu... Toh saidai muce Allah shi tayasa rik’o ya basa ikon kwatanta adalci....
Harta gidan mahaifiyarsa saida jama’a suka cika mak’il sai zuwa masu san Barka ake... Su Marliya da Raihanah ma can suka yini sai dare Sameer ya biya ya d’aukesu dan shima yana tare da Engr d’in through out the day... Aunty Bara’atu ma nan gidan Ammahn ta yini suna tayasu amsar bak’i ‘yan murna...

A gajjiye lik’is ya shigo gidan danma da k’yar ya samu ya janye jikinsa daga wajensu party chairman da sauran masu muk’amai a jamk’iyar tasu, ga kuma mutane da tuni Sun soma tururuwar kawo masu barka...

Wajajen k’arfe goma ya shigo gidan yanda ya taddata da Ammah sunata kallon labaru ana hasko zab’en da kuma wanda yai nasaran... Kaman ta mik’e ta haye jikinsa haka taji dan murna amma bazata iya yin hakan ba kasancewar da mahaifiyarsa zaune wajen....

Samha da batai bacci ba tana nan zaune tareda ita ake kallon yana shigowa ta tafi da gudu ta haye jikinsa tana fad’in “Daddy congratulations... I saw it on the news, you won the election....!”Cab’eta yai yana mai furta “Na gode baby... Addu’a zaki min kinji Allah yamin jagoranci...” Ta jinjina masa kai su Ammah da Zulfah na amsawa da Ameen..

Daga nan ya k’arasoga mahaifiyarsa yana satan kallon Zulfah suke gaisawa da mahaifiyar tasa tana mai kuma masa Barka da fatan alheri had’ida ‘yan nasihu dangane da hidiman da ya shafi Al’umma....
Bayan ta d’an masa ‘yan nasihohi ne ta mik’e tana fad’in zata shiga ta kwanta dama isowar nasa take jira... Samha ma mik’ewan tai da niyyan tafiya sai kuma ta d’an juyo tana duban mahaifin nata....
Engr ya d’an bud’e murya yace “Princess akwai abinda kike so ne...?”

K’arasowa kusansa tai kana tace “Dad we’re missing our mum... When are we going to see her... Why isn’t she here with us.... Ba kaci election ba..? She should be here celebrating with us... What happened to our mum....?!”Ta k’arashe cikeda nuna damuwa...

Zuciyarsa Ta tsinke lokaci guda, anzo wajen yanda zai breaking wannan labari mai nauyi ga yaransa... Harta Zulfah dake gefe saida zuciyarta Ta yanke... Engr ya d’an kaikaito yana duban Zulfah dan baisan mai zaicewa yarinyar ba....
K’uri yaiwa yarinyar yana k’ok’arin nemo abinda zai fad’i mata sai ganin hannun Zulfa’u yai ta dafa Samha, lokaci guda take furta “Sweetheart your Dad has something very important to tell you....Amma ba yanzu ba Coz he’s a a little bit tired now... Kuma kema ya kamata kije kwanta sabida ki tashi da wuri ko kin manta we have plans for tomorrow...?” Ta k’arshe tana kashe mata idanu guda....

Saurin jinjina kai tai cikeda murna tana fad’in Ta tina, lokaci guda ta manna masu peck a kumatu tana mai masu saida safe....

Zulfah ta bitada kallo har ta shige murmushi saman fuskarta....
Engr kaw sauk’e ajiyan zuciya yai a hankali yana mai sauk’e gajiyayyun idanunsa kan Zulfa’u... Lokaci guda soyayyarta na kuma ratsa ko wace kafa ta zuciyarsa.... Juyowa tai taga ya tsareta da idanu... Ta d’an sadda kanta tana murmushi.... Hannunta ya janyo yana mai fad’in ta k’araso cikin jikinsa....
Ta matso cikeda d’an jin nauyinsa.... Nan yai mata masauk’i cikin jikin nasa yana mai lumshe idanu.... Lokaci guda yake furta “Everything is stressing out.... All I need right now, is to be with you....!” Ya k’arashe yana mai bud’e idanun nasa had’ida sauk’esu saman fuskarta....
Ta d’an murmusa kad’an ga k’irjinta dake tsananin bugu....

Tallafo fuskarta yai yana kuma dubanta cikin idanu kana yace “I don’t think I can take half of this without you...Thnk you for taking care of my family, my mum and my children....Thank you for being here... Thank you for everything, my number 1...”

Murmushi saman fuskarta take furt “Dan Allah ka daina min godiya saika naji kaman wani abin nayi... Yaranka yarana ne... Sannan Ammah ko baka aurena she’s still my mum, itada Mamy basuda maraba wajena....!”
Chapter 191 · 0% Book details