← Book details Inda Rai Da Rabo Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 6 OF 198

Sashe 6

Inda Rai Da Rabo Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Sauk’e ajiyan zuciya Sameer yayi kana yace “Sultan I don’t know how to break the news to her, sanin kanka ne I only have a week left here, to be honest with you banason transfer d’in nan domin hakan na nufin rayuwata tana shirin canzawa completely....”

Murmushi Sultan yayi had’ida girgiza kai kana yace “Nasan haka zai faru abokina, bazaka iya tafiya kabar Partner ba koh...?”

Murmushi Sameer yayi da gefen bakinsa kana yace “Ka sani kuma kake tambaya.... Sultan wannan transfer d’in is a disaster to me....” Ya k’arashe yana kurb’an coffee d’insa....

Sultan ya kuma murmusawa kana yace “So tari nakanyi tunanin wane irin so kakewa Siyama... Anya kuwa Sameer wannan nuna soyayya da kulawa taka batai yawa....?”

D’ago idanu Sameer yayi yana duban Sultan kana yace “I love her with all my heart... Bazaka fahimci mai nake fad’i ba sai ka had’u da wacce kake so irin haka....”

Sultan yayi tak’aitaccen murmushi kana yace “Banji akwai wacce zan mata irin wannan soyayyan Sameer, nifah a ra’ayina soyayya duk k’aryace kuma ina maka tsoron watarana da zaka yarda da maganata cewa babu komai cikinta face k’arya da yaudara....”

K’uri Sameer ya masa kafin ya girgiza kai yace “Nida Partner hakan bazai tab’a faruwa damu ba cos we’re Magnets shiyasa nake tunanin transfer d’in nan ka iya kawo tashin hankali ma rayuwata...”

Sauk’e ajiyan zuciya Sultan yayi kana yace “Dr kenan, kai bama tunanin iyayenka da basuda wani d’a kake ba sai Siyama... Besides Kano da Kaduna ai bakida hanci ne idan kaga dama duk bayan kwana biyu kana hanya...”

Girgiza kai Sameer yayi kana yace “Ba kaman idan ina nan ko yaushe ba, nidai gaskiyar magana bud’e sabon asibitin k’una da gwamnatin tarayya tayi a jihar Kano baimin ba...”

Dariya ya kufcewa Sultan kana yace “Haba Sameer nasanka da son taimakon al’umma wannan asibiti da aka bud’e ai sabida al’umma aka bud’eta kuma wayasan d’imbin burn victims da zaka taimaka a jihar Kano, tun had’uwata dakai nasanka mutum ne mai k’aunar aikinsa ba don komai ba sai don ganin ka taimaki al’umma so please kar ka bari wannan k’udirin naka ya gushe akan soyayyar da kakewa matarka don na tabbata itama bazataso hakan ba....”

A hankali Sameer ya sauk’e ajiyan zuciya had’ida fuzar da iska kafin wata speaker ta soma announcing ana neman Dr Sultan da Dr Sameer sakamakon kawo wata budurwa da akayi k’unan wuta ya mata babu dad’i....

Cikin sauri suka mik’e suka nufi bakin aikinsu don ceton ran wannan budurwa....

****

*Kano*

Shi kad’ai sai wani cika yake yana batsewa, tun bayan gaisuwarta da ya amsa bai kuma bi takanta balle karin kummalon data had’a masa, kallon arziki bata ishesa ba ya k’arashe saka cuff links d’insa, sanin ba magana zai mata ba ko zasu kwana a haka ya sanyata bud’e baki tace “Fita zakayi baka karya ba...?”

Da wutsiyar idanu ya dubi sashen da take kana ya kuma kauda kansa, wani k’atutun bak’in ciki ya tokari k’ahon zuciyar Zulfa’u, wato shiru ma amsa ne.....

K’ok’arin shanye wannan bak’in cikin tayi kana ta kuma yin k’asa da murya tace “Abban Khausar magana fah nake maka...”

A hasale ya maidoda dubansa gareta yana mai darara mata tsawa “Wai meyasa bakida hankaline Zulfah, idan zanci sai nace miki zanci ne, idan nayi ra’ayin ci basai kinmin tuni ba, ko kinfi son cikina ne...? Abincinki ne yau banyi ra’ayin cinsa ba, sai ki ajiye kiyita cinsa har dare don bazan lamunci ayita min almubazzaranci da abincin gida ba....”

Hawaye suka ciko idanunta, tayi k’ok’arin maidasu kana ta bisa da “A dawo lafiya....”

Nan ma bai amsata ba yasa kai ya shige, har ya fice ya dawo da baya yace “Ki tabbata kinje kin baiwa Hajiya hak’uri kafin na dawo....”

Cikin hawaye ta jinjina masa kai yana ficewa kuwa ta fashe da wani irin kuka mai tsuma zuciya domin kuwa tanajin sanda wayarsa tayi k’ara ya d’aga yana sanar da budurwarsa gashi nan tafe a ajiye masa favorite d’insa... Da shike budurwar tasa d’iyar Hajiya Magajiya ce wata mai restaurant a can bayan layinsu, babu yanda Zulfah batayi ba ya rabu da Sawwama d’iyar Magajiya tinda kowa yasan halinta shashasha ce ballagaza maras kamun kai amma yak’i saurarenta, k’arshema mugun kashedi ya kafa mata akan alak’arsa da Sawwama, takai ta kawo Sawwama har nunata suke suna dariya idan tazo zata wuce bakin shagon mahaifiyarta...

Babu yanda Nabilah bataida Zulfah ba kan ta bartada Sawwama zatai maganinta amma fir Zulfah ta hanata shiga maganar, hakan bashike hana Nabilah yab’a masu magana ba muddin tazo wuce k’ofar restaurant d’in....

***

Hajiya na zaune saman tabarma a faranda Khausar na kwance gefenta tana bacci don tunda Raihanah ta goyata take bacci, zab’en safe da ake a gidan radio k’arfe goma shad’aya take sauraro Zulfa’u tayi sallama....

Da gangan Hajiya ta k’ure sautin radio d’inta, jin ba’a amsata ba ya sata k’ara d’an bud’e murya tana kuma sallaman haba nan fah Hajiya ta hayyayak’ota da ruwan masifa don dama ta d’ago muryar nata... “Shegen iyayi da munfurcin banza, an amsa miki bawai ba’a masa ba amma sai nanatawa kike yawa biya karatu... Munafuncin banza kawai...”

Hayaniyar Hajiya ya d’aga Khausar....

Tinda ta soma bala’i kan Zulfah na k’asa, da k’yar ta iya furta “Kiyi hak’uri Hajiya....”

Aiko Khausar najin muryar mahaifiyarta ta nufeta a guje tana mai ci gaba da kuka saidai kafin ta isa Zulfah dake duban d’iyar tata cikin shauk’i da bege tuni Sahariyya da fitowarta kenan daga d’aki don ayi da ita dashike taji zuwan Zulfah, tuni tayi tsalle ta sure Khausar dake kuka tana fad’in “Bazakije ba anan ake koyamiki munafunci.....”

Zulfa’u batasan sanda ta mik’e ta nufi Sahariyya ba sabida tsananin k’una da rad’ad’i da zuciyarta ke mata.... Fincike d’iyarta tayi tana mai furta “Sahariyya kinyi kad’an ki rabani da d’iyata.... Zan lamunci duk wani cin zarafi da zaku min amma banda d’iyata....”

Khausar kuwa tuni ta kwanta cikin jikin Mamanta tana shan zuciya a hankali....

Hajiya da tuni ta saki baki tana kallon ikon Allah mik’ewa tayi had’ida rangad’a gud’a “Eh lallai Zulfa’u kin rik’a kin cika cikakkiya, bari kiji na fad’a miki idan kin mance, Sahariyya tafiki iko da yarinyar nan tunda k’anwar Ubantace, yo aurenki ko mutuwa yayi ba baki Khausar za’ayi ba Sahariyya kuwa za’a mallaka mata Khausar domin kuwa Ubanta ma ita yasha nono ya sake.... Ke Sahariyya karb’i yarinyar nan idan ta cika ta kuma fizgeta.....” Hajiya ta k’arashe tana dukan k’irji alamun fad’a...

Zulfah tanaji tana gani Sahariyya ta fincike Khausar daga hannunta, yarinyar sai kuka take sabida tsananin tsoron Sahariyya da take tamkar zata shid’e lokaci guda kuwa Sahariyyan ke darara mata tsawa wai tayi shiru gaban mahaifiyarta....

Wasu irin hawaye masu d’umi su suka shiga gangarowa Zulfah, batasan sanda ta cukwikuye fuskarta gaba d’aya da hijabinta ba ta fice tana mai jiyo sautin kukan Khausar har cikin k’ahon zuciyarta da yanda Sahariyya ke darara mata tsawa tana fad’in kalaman b’atacin akan Zulfah....

Raiha dake kitchen tana girki ta window take duban Aunty Zulfah har ta fice ga kukan Khausar na tashi, tuni Raiha taji hawaye na gangaro mata, kaman wanda aka turo Hajiya kitchen d’in nan ta hangi Raiha na kuka ga abinci bisa murhu da alama tayi nisa cikin kukan ta bar abinci har ya soma k’auri....

Bata ankara ba batasan da shigowar Hajiya ba sai sauk’an Dundu masu ji da lafiya har guda uku dataji a bayanta....

Raiha ya mik’e a d’ari tana kurma ihu.... Hajiya ta rarumo muciya tana fad’in “Dan ubanki sai na dakeki kiyi kukan da dalili, shegiya munafuka wato salon akai abincin nawa Kasuwa ma Alhaji aji babu dad’i koh... Munafuka algunguma... Wuce ki duba min girki kafin nayi k’asa k’asa dake a nan.....”

Raiha ya shige tana hawaye, Sahariyya dake tsaye bakin kitchen fad’i take “Ai Hajiya da buga mata muciyar kikayi sai ta fad’i uwar da aka mata take kuka...”

Hajiya tace “An b’ata ran uwarta Zulfa’u ta fice tana kuka mana, basu ragema juna komai ba tsinannu munafukai...”

Sahariyya ta k’arada “Wllhi kuwa Hajiya ni dama har kama suke min....”

Jifa Hajiya tayi da muciyar tana mai ci gaba da sababi, Sahariyya ta take mata baya.....

***

Kaman daga sama Sawwama da k’awayenta suka hango Zulfah na tafe fuskarta duk ta dauje alamun taci kuka, idanunta a kod’e...

Sawwama tayi shewa tana jiran k’arasowarta duk a tunaninta akan Hafiz take kukan da shike bai jima da barin Kantinsu ba...

Sawwama ta tab’a k’awayenta suka nufi Zulfah

SameenaAleeyou📚
[25/11, 16:43] +234 703 745 3539: *INDA RAI*
_................DA RABO_

*06*

*©Sameena Aleeyou...✍🏽*

Kallo guda Zulfah ta masu ta watsar, lokaci guda taji wani k’arfin zuciya yazo mata, tabbas batada lokacin Sawwama balle na k’awayenta, kai tsaye tasa kai zata rab’a ta gefensu ta shige dashike tuni sun tare gabanta...

A tare Sawwama da k’awayenta Sailuba da Zabba’u suka kuma shan gaban Zulfah, sai faman cika Sawwama take tana wani batsewa....

K’ak’aro murmushin k’arfin hali Zulfah tayi kana tace “Bansan kuna biyo mutane har titi ku sanyasu sayen abincinku na dole ba tunda dai naga wannan hanyar wucewace ba kantinku na nufa ba....”

A tare su Sawwama suka kwashe da wata irin shewa had’ida tafe hannaye kana Sailuba tace “Ai munfi k’arfin mu taro mutane saidai su kawo kansu tinda mijin wata ya kawo kansa.....”

Zabba’u tace “Fad’a mata dai k’awata....”

Itako uwar gayyar sai faman jijjiga take tana famkan fankam....

Har cikin ranta taji zafin kalaman Sailuba amma sai ta daure ta murmusa don bataso su gano lagonta... A fili kuwa cewa tayi “Alama ta nuna haka, ko shakka babu mijin wata ku kuka rok’eshi yaci abinci a kantinku amma ba ra’ayinsa bane, sannan ko kad’an banga laifinku ba don kun ara kun yafa domin kuwa abinci kuke nema ku saka a bakin salati wanda baku samu gidan iyaye ba....”
Chapter 6 · 0% Book details