← Book details Inda Rai Da Rabo Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 52 OF 198

Sashe 52

Inda Rai Da Rabo Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Cikin tsnanin tashin hankali Marliya da Raihanah suka shiga janye Nabilah wacce ta koma tamkar mutum mutumi suka nufi cikin gida da ita, da k’yar Nabilah ke iya d’aga k’afafunta ga mutane sunyi chaa kuma babu wanda yayi yunk’urin hana yaran abinda suke... Abu mai kaman wuya kaga kukan Nabilah saigashi k’walla sun ciko idanun nata, ta d’ago idanunta da k’yar tana duban mutane a daidai lokacinda ta hangi Siyama da Yesmin zaune cikin motar Siyamar suna faman sakin murmushin cin nasara lokacin guda suna d’aukar tozarcin da akewa Nabilah cikin wayoyinsu, hakan yayi daidai da zubowan k’wallan da suka mak’ale cikin idanun Nabilah, tinda take ba’a tab’a mata cin zarafi irinta yau ba, kalmar karuwa da aka kirata dashi yafi komai d’aga mata hankali, ji tayi duk duniya babu wanda ta tsana irin Khalid, domin kuwa shi ya janyo mata wannan wulak’ancin, da ace bai shigo rayuwarta ba su Yesmin bazasu san da zamanta ba balle su aibatata su mata sharri da b’atanci ga sunanta wanda yafi komai d’aga mata hankali....
Koda suka shiga gida ma d’aki ta fad’a ta kulle kanta ta kifa kanta ta shiga rusa kukanta son ranta, Raiha da Marliya duk jikkunansu yayi sanyi, yau d’in abubuwa ne da dama kekan faruwa cikin ahalin gidansu, haka sukai jigum jigum sunma mance aike suka dawo gidan, tsnanin tausayin Nabilah na d’awainiya dasu....

****

Shamsu ya dubi Sameer a karo na biyu kana yace “Sameer are you sure of what you’re doing....?”

A kaikaice Sameer d’in ya d’an dubesa hannayensa duka biyu rungume da fuskarsa kana ya jinjina masa kai ba tareda ya furta koda kalma guda ba...
Lokaci guda ya mik’e ya suri car keys d’insa, yakai dubansaga Shamsu da raunannun idanunsa kana yace “Da zaran result ya fito, idan har ya tabbata mutanen nan iyayenane zanje can gida Kaduna na tambayi su Mummy gaskiyar al’amari.... I’m confused Shamsu... Abubuwa da dama sun shige min duhu, ina buk’atar haske cikin rayuwata....” Ya k’arashe siririyar hawaye na gangaro masa....

Jiki a sanyaye Shamsu ya k’araso ya d’an dafa Sameer cikeda tausayawa, cikin tausashesshiyar murya yake fad’in “Sameer kar ka damu everything will be alright in sha Allah, komai zai bayyana maka da yardar Allah, na sani is not easy but ka k’ara hak’uri da sannu komai zai wuce....”

Sameer ya d’an dubeshi kana ya jinjina kai yace “Na gode brother....” Daga haka k’ok’arin sa kai ya soma zai shige Shamsu ya take masa baya....

****

KADUNA

Yana kishingid’e saman kujera gefen Ammi tanaci gaba da masa sannu don baijin dad’i kwana biyun, zazzab’i yake fama dashi...
Kubura ta shigo d’auke da bowl na fruit salad ta ije saman stool d’in dake gefensa tana satan kallon yanda ya fad’a ya kuma yin haske a d’an rashin lafiyan kwana biyu da yayi, gaba d’aya tausayinsa ya rufe Kubura, cikin zuciyarta take ayyana inama sunyi aurene da ita ke jinyar kayanta ba Ammi ba, sai faman zuba shagwab’awa Ammi yake ana tambayarsa mai yake sonci yana basarwa, inama ma ita yake wannan shagwab’ar itakaw taita riritatasa kaman jinjirin goye...
Duk wannan tunani da Kubura keyi tsaye take kansa k’ik’am shiko sai faman shafa wayarsa yake baimasan tana tsaye wajen ba...
Ammi ta saki baki tana kallon ikon Allah, har saida ta dakawa Kubura tsawa kafin ta dawo hayyacinta...
“Ke! Lafiyarki kikayiwa mutane tsaye aka....? Badai kin aje abinda ya kawoki ba... Toh tsayuwar kuma ta minene...?”

Kubura ta d’an zabura kad’an tana k’ak’aro murmushi take fad’in “A’a Ammi wai dama nace ko akwai abinda yake buk’ata kuma...”
Girgiza kai kurum Ammi tayi domin ita kanta ta soma fahimtar take taken Kubura kana tace “Jeki idan ya nemi wani abin na kiraki...”

Kai a k’asa Kubura ta amsa tana mai satan kallon Khalid da kacaukam hankalinsa kega wayarsa, da alama sam baima saurari tattaunawarsu da Ammi ba... Ficewa tayi cikin zuciyarta tanai masa fatan samun lafiya...
Shiko Khalid dialing layinta yaketa k’ok’arin yi amma bai shiga, ya d’an saki garen tsuka a hankali had’ida lumshe dogayen idanunsa...
Ammi tace “Saif ka tashi ka sha fruits d’in ko kad’an ne, jibi duk yanda ka rame ina magani zai maka amfani baka cin komai, ko nima so kake ciwon damuwa ya kamani ne...?” Ta k’arashe cikin raunin murya...

D’an duban Ammi yai daga kishingid’en da yake, tausayinta yaji ganin duk yanda itama ta shiga damuwa, a hankali ya mik’e zaune, Ammi tai saurin nufosa zata taimaka masa yana murmushi yace “Haba Ammi zan iya zama fah....”

Ta d’an hararesa kana tace “Don dai bakaga yanda ka rame bane...” Tai maganan tana zuba masa fruits d’in cikin k’aramar bowl ta d’auko d’an spoon d’in tana k’ok’arin bashi a baki...
Nan ma murmushin ya kumayi yana mai girgiza kai had’ida jinjina irin k’aunar da mahaifiyarsa ke masa...
Amsa yai yana fad’in “Haba Ammi stop treating me like a kid again, I’m all grown fah....”
Nanma hararan ta d’an jefa masa kana tace “Toh maza ci na gani....”

Haka ta tasa Khalid a gaba yana tura fruits d’in, saida ta tabbata yaci sosai kafin ta k’yalesa, ya d’anji k’arfin jikin nasa kam ya kuma sami d’an appetite...
Remote d’in dstv ya janyo yana k’ok’arin kamo tashan ball yaji k’aran shigowar sak’onni cikin wayarsa...
A hankali ya mik’a hannu ya janyo wayar yana k’ok’arin dubawa, Whatsapp d’insa ya shiga bud’ewa don ta nan ne aka aiko masa sak’on... Ganin bak’uwar lamba yasa yaji kaman bazai bud’e ba sai kuma ya bud’e yana k’ok’arin dubawa..
Video ce da alama tuni ta bud’e da shike auto download ne wayar tasa...
Sosai ya mik’e ya gyara zama yana kuma kallon video d’in, bai gama tabbatarda abinda yaran ke fad’i ba saida ya hangota tsaye tamkar mutum mutumi ana jifanta ana watsa mata k’asa, sannan duk wajen an rasa mai hana yaran... Yana ganin sanda hawaye suka gangaro mata ‘yanmata guda biyu wanda shakka babu ‘yan uwanta ne suna k’ok’arin janyeta.....
Wani irin mummunar fad’uwan gaba ne ya sauk’arwa Khalid, take ya nemi zazzab’in da yake ya rasa, gaba d’aya ji yayi duniyar na neman juye masa, What’s all this... Ya fad’i a zuciyarsa, ya kuma duban wayar tasa yana jujjuyawa cikin rashin yarda da abinda ya gani... Teddy bear ake kira karuwa...? Karuwa fah....? Khalid ya dafe kansa da ya kuma masa nauyi a hankali, yama rasa tunanin mai zaiyi....
Lambar da aka turo masa video d’in yai k’ok’arin kira saidai bata zuwa... Ya kuma kaiwa kan lambar Nabilah kaman zai dialing sai kuma yaji bazai iya ba, ji yai Kano kawai yake son tafiya...
Kaman wanda aka zabura dukda cewa yamma ce lis hakan bai hanasa tunanin hawa kwalta a daidai lokacin ba....
Sashensa ya nufa ya hau shiryawa gadan gadan...
Ammi da ta fito tana tambayar ko za’a kawo masa fish pepper soup na ta tarar babu Khalid a parlorn...
Tai mamakin daga d’an tashinta har ya sami k’arfin ficewa a parlorn.... K’ila sashensa ya koma ta fad’i hakan cikin zuciyarta had’ida zama cikin sofa tana canza tashan k’wallo da Khalid yakai, ga magungunansa da wayarsa duka a wajen ya bari....

Jim kad’an ana kiraye kirayen sallan magrib Khalid ya fito cikin shiri sai zuba k’amshi yake, Ammi ta saki baki tana kallon majinyaci ya ware lokaci guda...
“Saif masallaci aka nufa ne...?” Ta tambaya tana mai sakar masa murmushi....
Ba tareda ya dubeta ba yana mai ci gaba da d’aura agogon hannunsa yace “Kano zanje Ammi....” Ya k’arashe yana mai d’aukar wayar salulansa dake bisa center table...
Tamkar wacce aka zabura haka ta d’ago tana dubansa...
“Kano...?” Ta maimaita...
Ba tareda ya dubeta ba yana mai ci gaba da abinda yake ya jinjina mata kai alamun eh... Tuni yasa kai yana fad’in “Sai munyi waya Ammi....”

Ai a d’ari ta mik’e ta sha gabansa tana huci take aika masa mugun kallo... Khalid ya tsaya cak yana duban mahaifiyar tasa...
“Wllhi kaji na rantse bazakaje ba....”

Khalid ya d’ago a hankali ya kuma dubanta.... “Amm.....”
Bata bari ya k’arasa ba tace “Na riga na rantse, kan wancan matsiyaciyar yarinyar zaka d’ibi k’afafu ka d’ale kwalta ba isasshen lafiya ne dakai ba ni kuma kawai sabida gani shashasha sai na k’yaleka koh...? Toh bazakaje ba.... Wayasan uwar mai ta sanya maka kaci ka koma haka, tinda ka dawo ma kake rashin lafiya, wayasan kalan asirin data maka.... Toh wllhi wllhi bazakaje ba, sabida tsaban jarbar asirinta a daren nan zata kiraka ka tafi, idan asirinta yayi tasiri akanka ni bazaiyi akaina ba... Ban yarda ka fita a gidan nan da sunan barin gari ba kaji na fad’a maka....” Tana k’arashe fad’in haka tasa kai ta nufi staircase....
A hankali ya lumshe idanunsa ga zuciuarsa dake tsnanin masa zogi da rad’ad’i, a halin yanzu babu abinda yake sonji kaman yaji gaskiyar lamarin nan daga bakin Teddy Bear wanda, maganar tafi k’arfin waya a’a face to face baki da baki yakeson jin komai....
Da k’yar ya iya jan k’afafunsa ya nufi masallaci...
Kubura dake lab’e ta gama jiyo komai duk abinda Ammi ke fad’i dafe k’irji tai tana fad’in “Na shiga uku ni Kubura, wato ashedai ba Yesmin bace kawai ke neman hana burina cika ashe akwai wata can... Harma asirce shi tayi... Tab! Aiko wllhi da sakel, ina nan ina tunanin wannan k’aramar alhakin Yesmin ashe akwai wata gogeggiya mai bin bokaye da malamai.... Toh wllhi bazata saku ba, Khalid nawa ne ni kad’ai sai na nuna mata malumanta sunyi kad’an, abinda banyi a baya ba yanzu zanyi.... Wllhi sai na mallaki Khalid...!” Ta k’arashe tana d’aga yatsa guda sama had’ida juya yatsar cikin salo na juya idanu....

***

KANO

Hajiya ta cika tayi fam tana kuma hararan mijin nata....
“Toh yanzu sai ka baro masu Raihanan....? Kaga Alhaji gidan nan dai babu mai girki idan ba Raiha ba babu mai iyawa da d’awainiyar gidan nan, kawai makasu a kotu zakai dole a baka d’iyarka tinda babu uban da ya haifa maka ita ehe....!” Ta k’arashe tana sakin huci....

Cire hulansa Baba Alhaji yayi yana shafa kansa kana yace “Haule Mamani fah kike nufi nayi k’aranta a kotu....”
Chapter 52 · 0% Book details