← Book details Inda Rai Da Rabo Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 188 OF 198

Sashe 188

Inda Rai Da Rabo Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Suna haurawa sama wanka yai yayinda Siyama ta fito masa da jallabiya sabuwa k’ar ruwan silver, ita taketa k’ok’arin taimaka masa wajen shiryawa abin sai mamaki yake basa, kallo guda zakai mata kasan k’arfin hali ne kawai take... Ta kuma d’auko perfumes tana fesa masa harda d’auko su hairbrush tana taje masa sumar... Yanda take abu kazar kazar zaka fahimci tsananin dauriyace kawai... Shi kaw Sameer k’uri yai mata cikeda tausayinta... “Partner...!” Ya ambato sunanta a hankali bata amsa ba....Ya saka kira nan ma bata amsa ba bata kuma dubesa ba saima ci gaba da abinda take da tai.... “Partner..!!” Ya d’an k’ara fad’i da k’arfi had’ida rik’e hannunta da take amfanida wajen fesa masa turaren.... Cak ta tsaya ba tareda taci gaba da abinda take ba....
Sameer yaci gaba da fad’in “Partner look up.... Kalleni...!”
Da k’yar Siyama ta d’ago idanunta siririyar hawaye na gangaro mata....
Bai tab’a jin zuciyarsa ta mugun karaya irinta yau a rayuwarsa ba, a hankali ya furta “Siyama... Are you sure about this..?”

Ta k’ak’aro murmushi tana mai goge hawayen da suka gangaro mata kana tace “Dik abinda zai saka ka Farin ciki nima ina son wannan abin Partner....This is how much I love you...!”
Tausayinta ya kuma kamasa... Lips d’inta ya sumbata a hankali yana mai furta “Ban tab’a gani ko jin labarin mace irinki ba Siyama... You’re one in a million... Kinada zuciya mai kyau...!”
Mumusawa Ta kumayi kana tace “Don’t make me blush partner... oya shall we..!”
Ta k’arashe tana mik’o masa hannu... Murmushi ya saki kana ya kamo hannun nata suka nufi k’ofa....
Har k’ofan d’akin Raihanah Siyama ta mar rakiya, Sameer ya tsaya cak bakin k’ofar yana dubanta cikeda tsananin tausayi...
Siyama dake sakin murmushin k’arfin hali hannunsa ta kamo ganin yai sakare yana dubanta kana tace “Partner don’t worry I’ll be fine... Good night... you take care..!” Ta k’arashe tana mai k’ok’arin juyawa wani irin kuka na zuwa mata.... Takowa yai kad’an yanda take kana ya rungumeta Ta baya “I love you Partner..!” Ya fad’i idanunsa a lumshe...
Hawayen da take ta k’ok’arin dannewa suka zubo mata....
Tana jin sanda ya saketa ya nufi d’akin Raihanah.... Durk’ushewa Siyama tai a wajen had’ida k’unshe bakinta tana cazgan kuka mai tsuma zuciyar mai sauraro.... It is not easy at all... Saida ta koma d’aki tai kuka mai isanta kafin ta dawo k’asa ta d’auki Ijlaal yanda ta samu tuni har tai bacci tana kallo... Siyama ta k’arashi tattare wajen kana ta d’auki Ijlaal suka nufi d’aki...
Sauk’inta ga Ijlaal tareda ita amma kam da batasan yanda daren zai kaya mata ba, dan haka taita juyi tana ganin time sam yak’i tafiya, zata iya cewa bata tab’a ganin dare mai tsawo irin wannan a rayuwarta ba...

Washe gari kaw sassafe Ijlaal ce ta tada ita da k’iriniyarta, nan sukai wanka suka shirya had’ida d’an tattare waje kana suka nufo downstairs, ta jima tana kallon k’ofan d’akin Sameer kana ta sauk’e nannuyan ajiyan zuciya sanda ta jiyo muryar Ijlaal daga k’asa tana faman kwand’ara mata kira... Murmushi ta saki ita kanta tasan Ijlaal kyautace a gareta daga Allah...
Tai saurin nufan k’asa tana fad’in “Coming Princess...!”
Tare suka fad’a kitchen Siyama na k’ok’arin had’a masu breakfast dikda kitchen ba wajen warginta bane amma tana kan k’ok’arinta wajen ganin ta had’a abinda kowa zai iya ci.... Ijlaal na gefenta suna faman kwab’e kwab’ensu gwanin ban sha’awa, idan sunyi abu yai kyau sai Kaga Sun tafe hannaye cikeda murna... Sameer dake tsaye jikin k’ofan kitchen yana dubansu murmushi bai bar saman fuskarsa ba, kasancewa cikakkiyar matar gida da zama uwa ta gari sosai yaiwa Siyama kyau... Ijlaal ce ta soma hangosa yanda ya hard’e hannaye yana dubansu, ta isa gareshi da gudu tanai masa good morning... Bugun zuciyar Siyama ya k’aru, batasan da wasu idanu zata dubi Sameer ba, bayan kalan abubuwan da taji jiyan.... Dan haka ci gaba da soya pancakes taci gaba da yi ba tareda ta dubesu ba... Shiko Sameer idonsa na kanta dikda surutu da Ijlaal Ke zuba masa....Nan tace ya k’arasa yai tasting pancakes d’in da sukai itada Aunty Siyama.... Ya mik’e yana furta bara ya tab’a yaji.... Gefen Siyama ya tsaya yana duban yanda tai k’urima abinda take... Ya gutsiri pancake guda da fork d’in da Ijlaal ta mik’a masa kana ya saka a baki ya soma taunawa yana mai dubansu su duka biyu....
K’uri sukai masa suna jiran suji response d’insa, Ijlaal tai saurin cewa “So, how does it taste...?” Tai maganar tana mai alama da hannu... Kaman bazaice komai ba dan harta Siyama tsaye tai itama tana jira taji mai zaice....
Lokaci guda sukaga ya lumshe idanu yana mai furta “This is... Delicious... I love it...!”
Tsalle Ijlaal tai had’ida mik’awa Siyama hannu suka tafe cikeda jin dad’in Sameer ya yabi abincinsu...
Siyama ce ta d’an dafa Ijlaal kana tace “Princess take those to dining table, Can you..?” Jinjina mata kai yarinyar tai tana fad’in “Of course I can...” Ta k’arashe tana mai tattare set of plates zuwa dining table...

Sameer dake tsaye gefenta hannayensa ya kuma sakalewa cikin aljihu kana ya d’anyi gyaran murya yana mai furta “Partner... Good morning...!”
K’ok’arin saita kanta take cikin zuciyarta tana mai furta you can do this Siyama, lokaci guda ta kaikaito tana dubansa kana tace “Morning Partner... How was your night...?”
Bai amsata ba sai k’ura mata idanu da yai murmushi saman fuskarsa...
Lokaci guda ta d’an murmusa mai kamada yak’e kana tace “Great I guess..”

Murmushi yai kad’an kana ya jinjina mata kai.... Ta d’an murmusa itama kana tace “Naji dad’i since you are happy... Ya Amarya...?”
Murmusawa ya kumayi kad’an kana yace “Ya K’anwarki zaki ce...”
Ta d’an murmusa kad’an itama kana tace “Toh Ya k’anwata...!”

D’an murmusawa Sameer yai kana yace “Partner I never thought you can cook like this...”
Murmusawa ta d’an kuma yi kana tace “Ai na fad’a maka na canza gaba d’aya... Em dama inaso nace maka zamuje gidan Mummy nida Ijlaal anjima kad’an daga nan zamu wuce shopping... So we don’t have to disturb you kaida Amarya, oh k’anwata...!” Ta k’arashe tana mai goge hannunta da kitchen towel...
Girgiza kai yai kad’an kana yace “No Partner you don’t have to go anywhere... Besides I love to see my beautiful women beside me... Ba sai kinje ko ina ba...”

Ta murmusa a hankali kana tace “Please Partner I insist... Besides I want to take Ijlaal out.... Please say yes kaji Partner...!” Ta k’arashe tamkar mai shirin kuka...

Jinjina kansa yai kad’an kana yace “Alright fine... just because you insist...”
Murmusawa tai kad’an kana tace “Thank you Partner... I’ll go check on Amarya...” Ta k’arashe tana nuni da hanya...
Murmushi yai yana mai jinjina mata kai kana ya nufo dining area wajen Ijlaal...

Yinin ranar dai su Siyama basa nan Sun baiwa Ango Sameer sarari yanda zai kula da amaryar sa sosai, soyayya mai tsafta yake nuna mata wanda ita bama tai zaton irin soyayyar na existing a gaske ba, dik a zatonta sai a littafan soyayya da finafinan India hakan ke faruwa ashe dai anayi da gaske, ko dan ta taso cikin kyara da tsangwama ne a gidan Haule shisa take ganin hakan...? Koda shike tana iya hango tsananin k’aunarta a k’wayan idanunsa dikda cewa har yanzu d’in bata wani dake dashi ba musamman idan ta tina abinda ya riga ya ratsa tsakaninsu, harga Allah wane irin nauyi da kunyarsa takeji...

Bayan sun dawo ne Sameer ya fice ya nufi gidan Iyayen nasa su Mummy dan gaidasu, nan ne Siyama da Raihana suka d’an samu daman zama tare sabo mai tsafta na k’ok’arin shiga tsakaninsu, harta tsaraban shopping saida Siyama ta kawowa Raihanar nata...Siyama ta sanar da ita ta kwantar da hankalinta ta d’auketa tamkar yaya su taru su farantawa mijinsu, dama a b’angaren Raihanah kam babu wannan matsalar, harta su shiga ruwan zafi akai akai saida Siyama ta nusar da ita din ta kula abokiyar zaman nata yarinya ce sosai... Sam bazakace wannan Siyama bace, gaba d’aya lokaci guda Allah ya canzata... Suna nan a haka Laila ta kirata tana tambayarta ko ta dawo daga Abuja dan taji k’ishin k’ishin Sameer yayo mata kishiya k’aramar yarinya....
Siyama tace tana zuwa zata kirata later dan dole tai tinanin abinda zatacewa Laila bayan abubuwan da taji daga garesu itada Sultan...
Raihanah ta d’an dubeta kana tace “Aunty Siyama wani abin ne Ke damunki....?” Dan gaba d’aya ta kula tinda Siyama ta ida wayar yanayinta ya canza....
D’an dubanta Siyama tai kana tace “Bansan ya zan sanar dake ba Raihanah.... Laila aminiyata ce da na d’auki dikkan yardana na bata amma taci amanata...” Take dai Siyama ta labarta mata dik yanda sukai dasu Laila...
Raihanah ta numfasa cikeda tausayin Siyama kana tace “Aunty Siyama kin had’u da sharrin muguwar k’awa... Amma itace a rana, abinda zakiyi ki k’yaleta tazota sai ki nuna mata tamkar bakisan da zancen ba ko kuma kin sani kina neman shawarinta kiji mai zatace, daga nan ne Ke kuma sai exposing d’inta Ki nuna mata kin San komai kinsan ko ita wacece hakan sai yafi mata ciwo... If possible mu had’a plan d’in harda Ya Ma’aruf shima ya kirawo Sultan yace dashi yazo gidansa yana neman shawarinsa gameda yanda zai sanar dake batun k’arin aurensa... Kinga daga nan sai a exposing munafukai....”
Siyama ta kuma dubanta cikeda mamakin hikima irinta Raihanah kana tace “Perfect... Wannan shawari naki yayi Raihanah... Zamuga yanda fuskokin munafukai zai sauya...” Ta k’arashe cikeda murna tana fad’in “Kinga bara na kira Partner yanzun nan and tell him about our plan...” Lokaci guda Siyama ta mik’e ta nufi upstairs a guje d’auko wayarta tana mai kuma godiya wa Raihana....
Murmushi kurum Raihanah keyi tana duban yanda Siyama ke farin ciki...

***
Kaman yanda suka tsaran haka kaw akai, Sameer ya kirawo Sultan yayinda Siyama ta kirawo Laila tai inviting d’inta itama....
Chapter 188 · 0% Book details