← Book details Inda Rai Da Rabo Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 136 OF 198

Sashe 136

Inda Rai Da Rabo Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Innnalillahi wa inna’ilaihi raji’un... Allahumma ajirni fi musibati wa aklifli khairan minha.... Kalaman da zuciyar Mamy Ke iya nanatawa kenan, k’ololuwar tashin hankain data tsinci kanta ciki bazai misaltu ba, ta ya za’ace ‘yaruwarta ta jini zata mata haka... Ta ya za’ace ‘yaruwarta da ta aminta da ita zata mata wannan babban butulci... Kai gaba d’aya jama’an dake wajen kansu ya k’ulle... Harta su Abbah dasu Mamani saida tashin hankali ya nuna sosai a tattaredasu, tashin hankalin da zasu iya cewa tun bayan b’acewar Ma’aruf basu sake fuskantar irinta ba.... Wato Aminai uku da sukai yunk’urin Salwantar da Ma’aruf kaman yanda Dumba ta fad’i Haule ce da Lami had’ida Bara’atu... Kai wannan irin butulci da mai yai kama, Ke duniya mecece cikin ki bacin tarin maciya amana da azzalumai....
Dik yanda Engr yaso ya fice a wajen ya basu privacy tinda yaga rikici ne na family amma ya kasa, ji yake bazai iya tafiya ba har sai yaga k’arshen al’amarin nan, ji yake can k’asar zuciyarsa tamkar ya tab’a rayuwa a wata duniya irin tasu....Tausayin mahaifiyar Sameer ya cika zuciyarsa, ga wani shauk’i da yakeji tinda yaji an ambaci Sameer da suna Ma’aruf, wani ikon Allah ashe sunansu d’aya gashi labarinsu yaso yayi shige tinda shima Sameer ba a gaban iyayensa ya girma ba shima rabasa da nasa iyayen akai... Tabbas labarin rayuwarsu yaso yai shige....

Kasa furta komai Mamy tai, ta kasa tab’uka komai, saiko tsayuwa sororo da tai gaban Aunty Bara’atu... Sameer yasa duka hannayensa biyu ya tallafi mahaifiyarsa ganin tayi rauni sosai, shin waye ma bazai rauni ba da jin irin wannan labari mai tsananin tashin hankli....
Girgiza kai Mamy taci gaba da yi tana duban Aunty B sa kanta ke kife k’asa, tabbas da ace k’asa zai gsaga ta shige ciki da hakan ya fiye mata sauk’i... Ta ya zata iya d’ago idanu ta dubi ‘yar uwarta...? Ta yaya, bayan wannan babban al’amari dake faruwa dasu....

Murya a matuk’ar sanyaye Mamy Ke fad’in “Bara’atu d’ago fuskarki ki k’aryatasu... Nasan hakan sam ba mai yuwu bane... D’ago kice min K’arya suke ‘yar uwata... Kinji, Dan Allah d’ago ki k’aryata wannan mummunar sharri da suke jifanki da ita... Bara’atu kice min k’arya suke ba kece Aminiyar Sirri ba... Kinji ‘yar uwata...!!” Ta k’arashe tana mai jijjiga Aunty Bara’atu da har lokacin fuskarta Ke kife k’asa....Haule da Lami suka dubi juna suna masu aikama juna makiran murmushi....
A haka Mamy taci gaba da jijjiga Aunty B da iayaka k’arfinta, wannan karon zaka iya hango tsananin tafasa da zuciyarta keyi sabida yanda fuskarta ta rine zuwa jajazir haka nan k’wayan idanunta... Fad’i take “Bara’atu ki k’aruatasu nace... Ki k’aryatasu ‘yaruwata, bazaki tab’a min haka ba ni na sani... A lokacinda na rasa Ma’aruf kina taredani.... Baki tab’a k’yaleni ba daidai da dak’ik’a guda... Dik kalan tashin hankalinda na shiga, taredake nai overcoming d’insu, a lokacinda kowa ya juya min baya ked’in kina taredani ‘yaruwata... Abinda suke fad’i bazai tab’a yuwa ba.... Ki cemin k’arya suke Bara’atu..!!!”
Aunty B da itama kanta ahesshek’ar kuka take, a zuciye ta fincika ta d’ago tana duban Mamy lokaci guda take furta “Eh... Eh Ya Mariya ni ce Aminiyarsu ta Sirri.... Taredani suka shirya komai... Na taimaka masu sun cika burinsu na kawarda Ma’aruf gaban iyayensa.... Kuma ni ce nan na mik’a shi hannun Dumba...”
Innalillahi wa Inn’ilaihi Raji’un.... Kalman da zuciyoyi sukaci gaba da nanatawa kenan.... Aunty B na kuka sosai take duban Mamy da tai mutuwar tsaye a wajen tana dubanta cikin rashin yarda da abubuwan dake faruwa....
Lokaci guda Aunty Bara’atu taci gaba da fad’in “Mamy inaso ki tuna mai ya faru a ranar da Ma’aruf zai b’ace....”
Mamy da hawayen dake idanunta suka k’afe a hankali ta soma furta “Babu abinda ya b’ace a kaina gameda wannan rana da abu biyu suka auku dani... Muhimman abubuwa guda biyu, RASHI da kuma SAMU.... Ranar da na rasa d’ahna Ma’aruf, kuma ranan da na haifi d’iyata Zulfa’u.....
Wata ranace ta Alhamis mai cikeda tsananin zafin rana...

_WAIWAYE_

Shekaru ashirin da Shida da suka Shud’e......

Zaune suke saman tabarma itada d’an nata da bazai haura shekaru uku ba, wata matashiyar budurwa tai sallama ta shigo... Da alama budurwar a gajjiye ta shigo hakan yasa ko gaisarda matar data tadda zaune saman tabarmar batai ba saima fad’i da take “Auchh! Gaskiya ana rana Mamy... Kinji waje kuwa... Wllhi badon jarabawa da muke ba da gobe bazanje poly ba ni wllhi na gaji...” Ta k’arashe tana matashi da jakkanta had’ida d’an kishingid’a gefe...

Matar data kirada Mamy murmusawa tai had’ida d’an muskutawa kad’an sabida bayanta da yai mata tsami sakamon zungureren cikin dake jikinta, haihuwa ko yanzu ko anjima

“Banda abinki Bara’atu mai kukai a karatu, yanzu fah kuka fara...Shekararki ta farko fah kenan, kuma ki godewa Allah cikinmu uku kin sami damar tafiya gaba da sakandare kagi da k’anan shekarunki tinda har yanzu baki kai ashirin ba, dan haka koda wasa kada kiyi sake da damarki kinji koh....”
Murmusawa Bara’atu tai kana ta mik’e ta rungume Mamy tana fad’in “Yah Mariya mai zanyi a rayuwar nan idan babu ke... Ina k’aunarki sosai ‘yaruwata shisa sam bazan iya zaman gidan Ya Abidah ba na zab’i na zauna dake....”
Murmusawa Mamy tai had’ida d’an dungurinta kana tace “Amma ai Yaya Abidar ita ta fara rik’onki kafin nima nai auren koh... Ita d’in uwace a garemu dukanmu dikda abinda ya faru....”
Cikin sauri Bara’atu ta janyo hannayen Mamy tana fad’in “Dan Allah kada ki soma tuno abinda ya faru baya kinsan likita ya hanaki shiga damuwa ko dan lafiyar abinda Ke cikinki sannan idan Abbah yazo ya taddaki cikin damuwa fad’a zaiyi shima...”
Mamy ta murmusa a hankali kana tace “Tabbas Usman shi ya dawo min da Farin cikin da na rasa a baya... Amma Bara’atu har yau na kasa cire alhakin mutuwar Fatima da Ma’aruf a wuyana.... Shin ta yaya zan bar yaro d’an shekaru shida da jaririya sabuwar baihuwa cikin tsumman goyo....?”
Aunty Bara’atu ta kuma kamo hannayenta tace “Babu laifinki Mamy, hakan Allah ya k’addara kuma kema kinyi iyaka naki k’ok’arin ganin kin kub’utar dasu amma Allah bai nufa sud’in masu rayuwa bane... Ina fata Yaya zata fahimci haka watarana, ta daina d’aura alhakin b’acewar d’anta Ma’aruf da kuma ‘yar autarmu Fatima a wuyarki....” Numfasawa Mamy tai had’ida da kai dubantaga Ma’aruf daketa wasan sa hankali kwance... Bara’atu ma kai dubantaga Ma’aruf d’in tai kana tace “Da Ma’aruf Babba yana raye k’ila da yakai shekaru goma sha da ya soma zama saurayi.... Nasan yanda kike k’aunar Ma’aruf Babba Mamy, kuma wannan suna Mamy shi ya saka miki har yabi bakinmu gaba d’aya....”

Mamy ta kuma murmusawa had’ida goge hawayen da suka gangaro mata kana tace “Ma’aruf d’ah na... Haihuwarsa kawai Yaya tayi amma inajin har k’asan zuciyata tamkar na fita k’aunarsa... Kuma ban cire rai ba INDA RAI DA RABON wata rana Allah ya kuma had’amu....”
D’an murmusawa Bara’atu tai kana tace “Mamy Ma’aruf ya tafi kuma Allah ya bamu wani Ma’aruf d’in... Dik irin k’aunar da kikewa Ma’aruf Babba ki had’asu kan Ma’aruf k’arami tinda dama shi d’an Gata ne wajen Kakarsa da iyayensa....”

Mamy ta kuma murmusawa tana mai duban d’an nata yanda yaketa wasan sa hankali kwance...
Muryar Bara’atu ne ya dawo da ita daga duniyar tinanin da ta tafi tana mai furta “Ma’aruf... Zo yaro na...!”
Dubanta yai sai ya mak’e kafad’a ...
“Aw bazakazo ba sarkin ‘yan k’iwa...”
Nanma mak’e kafad’a yai kana ya fad’a jikin mahaifiyarsa yana mai furta “O’o nidai Mammy.....” Cikin muryarsa da yake gwari gwari irinta yara....

Aunty Bara’atu tace “Toh ai shikenan dama na sayo maka motar wasa kuma bazan baka ba....”
Ambato mota da tai yasa yaron zuwa gareta a guje yana fad’in sai ta basa mota,
“Laaa Kaga yaro zai tara min jama’a Nifa wasa nake maka....”
Mamy tace “Ah toh aiko sai ki bashi tinda kin iya zolaya....”

Abu kaman wasa yaro ya dinga kuka sai an sai mai jiyin jiyin.... Baiji bai gani kuka yake....
Mamy ta dubeta tace “Kinsan mahaifinsa baya nan balle ya fita ya sai masa, kuma Kakarsa data k’wallafa rai akansa tanajin kukansa zaki ganta a nan tana sababi, ni kuma ga halinda nake ciki wllhi sam bansan tashin hankali, da kukan Ma’aruf zanji ko kuwa da fad’an Mamani zanji, ki tashi tun wuri tin dare bai maki ba kije ki nemo mota....”

Bara’atu ta mik’e tace “Aiko bara na tafi bakin kasuwa na sayo mai....” A haka ta zira mayafinta ta nufi k’of, yayinda Mamy taci gaba da rarrashin Ma’aruf da kaman an saka masa batir sai kuka yake....
Jim kad’an Bara’atu da dawo a firgice...
Mamy tace “A’a lafiya Bara’atu...? Har kin dawo....”
A d’an daburce tace “Mamy Dumba ce tazo daga gidan Yaya tace tana nemana kuma ba lafiya take ba...”

Mamy da damuwa ya nuna itama a fuskarta tace “Wai DUMBA bata wuce ba...? Inji tin shekaran jiya tace zata bar garin nan...?”
Bara’atu tace “Inaga sabida jikin Yayan ne yasa Ya Dumba bata tafi tin shekaran jiyan ba... Amma tace min yanzu haka akan hanyarta take shisa tazo kirana naje na zauna da Yaya Abida....”
Mamy ta numfasa tace “Toh Bara’atu ko zamuje tare ne....?”

Girgiza kai Bara’atu tai kana tace “Mamy sanin kanki ne Yaya ta miki iyaka da gidanta... Ga kuma halinda kike ciki... Dan Allah kada kije Yaya ta miki wani abinda zai d’aga miki hankali yai affecting d’an cikinki... Ki barni ni zanje kinji koh... Zan kula da ita....”

Jinjina kai Mamy tai jiki a sanyaye dikda cewa har lokacin Ma’aruf kuka yake “Toh shikenan Bara’atu, kije Allah ya tsare kinji koh... Allah kuma shi miki albarka....”
Chapter 136 · 0% Book details