← Book details Inda Rai Da Rabo Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 117 OF 198

Sashe 117

Inda Rai Da Rabo Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

A b’angaren Laila kuwa tana ficewa ya tadda Sultan na jiranta, front seat ya bud’e mata ta shige ta zauna...
“Toh ya..? Any improvement...?” Ya tambaya sanda take daidaita zamanta cikin motar...
Murmushi ta saki idanunta naga kwalta kana ta ware masa tafin hannunta tace “Siyama tana nan, tana nan tsakiyar tafin hannuna sai yanda na juyata a halin yanzu.... Ina mai tabbatar maka Sameer bai gabanta a yanzu...”
Murmushi mai sauti Sultan yai kana yace “Kinci sunanki Poison, kice kin gama poisoning zuciyarta....”
Ta kuma murmusawa tana jijjiga kana tace “I told you to trust me on that, yanzu abu na gaba zamu taking next step...”
Sultan ya kuma jinjina kai a hankali kana yace “Mai kenan....?”
Juyowa tai tana dubansa wannan karon kana tace “Zan zigata tasa Sameer ya rubuta mata takardan saki, idan tak’i zanyi amfani da nawa strategies d’in na sakashi ya saketa, Kaga you will finally have your chance, sannan nima zan mallaki Sameer ni kad’ai...”
Sauk’e ajiyan zuciya yai yana mai murmusawa kana yace “Da Bansan da mai zan saka miki ba idan hakan ta kasance....”
Laila ta kuma rausayar da idanu tana mai dubansa “K’iris ya rage burinmu ya cika.... “
***
A b’angaren Khalid kaw koda ya fice gidansu Baffah amininsa ya nufa.... Zaune suke su duka biyun a farfajiyan gidan saman fararen kujeru dake k’asar tapkeken bishiyar mangoro da yayiwa harabar k’awanya.... Ya d’auki lokaci yana shafa wayar salulansa ba tareda ya amsa tambayar da abokin nasa ya jefo masa ba... Baffah ya kuma d’ora k’afarsa d’aya bisa d’aya yana duban Khalid d’in da har lokacin natsuwarsa naga wayarsace..
“Khalid magana nake maka fah...?” Baffah ya kuma fad’i cikeda k’osawa...
Ba tareda ya dubesa ba yace “Ina saurarenka ai, ko ka mance kunne Ke sauraro ba ido ba, just go ahead and keep on talking, I’m listening to you... Mai ma kake tambaya...?”
Murmushi mai bayyan hak’wara wannan karon Baffah yai had’ida girgiza kansa kad’an “Idan bakai haka ba baka cika Khalid Mainasara ba.... Tambayarka nake miye shirye shiryenka na Bikin tinda Ammi ta rik’e wuta...?”
Wannan karon d’ago kai Khalid yai yana dubansa na wani lokaci kaman zaice wani abu sai kuma ya murmusa da gefen baki ya kuma maida kansaga wayarsa, saida ya kuma d’iban wasu dak’ik’ai, har Baffah ya cire rai bazai amsa shi ba sai kuma ya sinkayo muryarsa na fad’in “Tin jiya nake neman layinta but I couldn’t reached her...” Yai maganar damuwa na nunawa saman fuskarsa....
“Ita wa...?” Baffah ya tambaya.
D’agowa yai yanai masa wani duba kana yace “My teddy bear....”
Baffah ya murmusa a hankali kana yace “Toh ba sai kaje Kano ka dubata ba tinda zuwa Kano bai maka wuya....”
Kallon ya kuma watsa masa kana yace “Da inada halin yin hakan da nayi kaima ka sani.... Ammi tace idan na kuma tafiya Kano ba tareda saninta ba bazata tab’a yafemin ba.... Baffah do me a favor....”
D’agowa sosai Baffah yai yana dubansa had’ida ware idanu alamun yana sauraren abinda zaice.....
“Kaje Kano ka dubo min lafiyarta since I can’t call Sameer and ask him about her....”
Dariyar da tafi kama data almara Baffah yai kana yace “You can’t be serious.... Ni in d’auki k’afa in tafi har Kano sabida yarinyar da bakada tabbacin aurenta, Allah ya sawak’e bazanje ba....”
Tinda ya soma magana Khalid Ke danna masa harara “Kar ka sake cewa banida tabbacin aurenta tinda baka had’a sanida Allah ba....” Yai maganar yana mai mik’ewa tsaye....
Shima Baffah d’in tsaye ya mike yana dubansa “Ina kuma zaka....?”
“Babu ruwanka da yanda zanje Malam...” Yai maganar yana mai zira wayarsa cikin aljihun wandon jeans d’insa had’ida zaro car keys d’insa...
Bai kuma ceda Baffah komai ba yasa kai yai shigowarsa.... Baffah dake tsaye kameda kunkumi yana duban ikon Allah d’an bud’e murya yai yana ambato sunan Khalid d’in, amma ko tsayawa baiyi ba balle yai tunanin juyowa....
Gajeren murmushi Baffah yai had’ida girgiza kai, harga Allah bai tab’a tsammanin irin wannan ranar na zuwa ba, gaba d’aya wannan yarinyar ya canza Khalid... Lallai ya yarda soyayya ka iya canza mutum... Sauk’e gajerar ajiyan zuciya yai yana mai girgiza kai kad’an kana ya nifi cikin gida....

***

KANO

Suna zaune parlorn Mamy su duka ukun, kallon program d’in Ultimate Cake Off suke a tashar Real-time... Tayi tsuka kusan na uku kenan sanda ta hangi wayarta dake jikin socket ta kuma kawo farin haske ta d’auke, ya isa jikin socket d’in tana mai kuma jan tsuka a hankali... Tin shekaran jiya wayar tata take wannan haukar shisa mutane da dama basa iya samunta, gashi yau ta d’auke gaba d’aya.... Zulfah da hankalinta rabi kega tv rabi naga k’ofar shigowa dan tinda akace iyayen Akram mai neman aurenta sunzo gidan bata sami sukuni ba, sai duban k’ofa take tamkar mai jiran shigowar wani..... Duban ‘yaruwar tata dake jijjiga wayar salular nata tai kana tace “Wai mi ya sami wayar taki ne...?”
“Wllhi Addah k’ila battery taci k’ila kuma ta buga mai gaba d’aya ne...”
Mik’a hannu tai tana fad’in mu gani....
Babu musu Nabilah ta mik’a mata.... Sallamar Aunty Bara’atu ya mantar dasu batun duba wayar... Marliya ta mik’e a guje ta tafi ta rungumeta tana fad’in “Oyoyo Aunty....”
Gaba d’aya sannu da zuwa suka shiga mata had’ida gaidata.... Ta tambayesu Mamy sukace da ita tana kitchen...Jinjina kai tai kana tace “Shine ku na ganku a nan ba kitchen d’inba..”
Nabilah tai karaf tace “Yanzu shigowarmu mu mun isa Hajiya Mamy na kitchen muna kallo, ai da daga yau babu mai kuma kunna tv cikinmu...” Tai maganar tana kame baki...
Aunty B ta murmusa tace “Ai kekam maganinki sai Mamyn mijinki nada fama....”
Nabilah ta turo baki tace “Kai Aunty.. Toh ba sai ya shiga ya girka mana ba...”
“Tafi can ki rufe min baki” Aunty B tace tace kana ta dubi Zulfah “‘Yar gidan akwai maganar da zamuyi bara naga Mamy a kitchen ina zuwa....”
Jinjina mata kai kurum Zulfah tai ba tareda cewa komai ba... Ta kuma kai dubantaga Nabilah wacce Ke k’ok’arin yin filla filla da wayar salulanta k’irar samsung kana tace “Beels bani size d’in takalminki....”
Nabilah na Washe baki tace “Aunty takalmi zaki sai min....?”
Bata tsaya amsa shiriritar Nabilah ba ta nufi k’ofa tana duba size d’in takalmin da take tinanin nata ne...
Nabilah ta bud’e murya tace “Aunty 38/39 ne kar a sayo min kasasshe size d’in Marliya... Sai ni ‘yar gatan Aunty...”
Gaba d’aya darawa suka d’anyi kana Aunty B ta kuma jefo mata tambaya “Dogayen riguna fah, bani length d’insu, size d’in inners d’inki kam zan iya k’iyascewa....” Wannan karon da tsananin mamaki Nabilah Ke dubanta yayinda Zulfa’u da Marliya suka dubi juna murmushi saman fuskokinsu....
Take annurin fuskar Nabilah ya d’auke cak....
“Aunty harda ke a wannan auren had’in bakin da suke k’ok’arin yi....?” Tai maganar baki a ture
Galala Aunty B Ke dubanta kana tace “Da waye yace ki kawosa da kika san baki sansa..? saikace ba kece kwanaki kikai kuka akan danginsa sun tasamma rabaku ba, yanzu dan iyayi zaki wani ishi mutane....”
Har lokacin bakin Nabila a ture ne... “Ni wllhi Aunty bani na kawosa ba shi ya kawo kanshi, kuma fah Aunty mamarsa ba k’aunata take ba, aike shaida ce....”
Jinjina kai Aunty Bara’atu tai don tuni Aunty Daula ta sanar da ita shirin Daddy kana tace “Idan Mamarsa bata k’aunarki Babanshi na k’aunarki kuma shima Khalid d’in na k’aunarki sannan Auntynsa tana k’aunarki...Sannan kinada ilimin zama da mutane...” Bata kuma tsayuwa sauraren Nabilar ba ta shige kitchen wajen Mamy...
Auntynsa da Aunty B tace yasa Nabilah kuma dubanta, batace komai ba sai d’an tab’e baki da tai kad’an, Zulfa’u ta d’an dunguri k’eyarta tace “Inye Kaga amaryar Haladun Mamani, shikenan yarinya sai Kaduna....” Marliya kaw sai dariya take yayinda Nabilar tai raurau tana duban Zulfah...
Saurin rungumeta Zulfah tai tana fad’in “You’ve us all baby sis, zaki tadda alkhairi In sha Allahu....”
Nabilah bata iya cewa komai ba sai lumshe idanunta da tai tana tunanin Wai Khalid ya kusa zama mijinta in less than 2mnths.... Abin kaman wani almara..
Marliya kaw fad’i take azo a ciro masu ankon gida ko ‘yar kamun nan a masu a k’irawo masu DJ dan basa son biki lami ehe... Banda uwar harara Nabilah bata danna mata komai....
Zulfah dai mik’ewa tai ta nufi d’aki yanda wayarta Ke faman ruri zuciyarta cikeda k’aunar ‘yan uwan nata....
Gabanta ne ya mugun fad’uwa ganin lambar Mr Unknown ne dan jiya tayi saving layinsa d’aya.....
Kasa d’aukar wayar tai sai ma k’ura mata idanu da tai....
Saida har tsinke tana nan tsaye a haka... Nan take aka kuma sake kira, sunan sai nunawa yake Mr Unknown... A hankali ta d’an fuzar da iska kana tai bismillah ta d’aga wayar sallama saman bakinta.... Yau kam batai gaggawan katse kiran ba kaman yanda takeyi a kullum... Cikin wani irin sanyin jiki take furta “Bawan Allah shin maiyasa kake kirana kayi shiru...? Mutum ne kai kokuwa Aljan...? Shin wani abu kake nema wajena... Kokuwa na tab’a maka wani laifi ne....? Idan babu ko d’aya, Dan Allah ka dena kiran wayata na rok’i arzikinka... Banajin ajikina kai d’in mai cutarwa ne... Dan Allah ka dena kirata haka nan... Allah shi bamu alkhairi....” D’if ta kashe wayar zuciyarta na bugawa da sauri da sauri... Kashe kiran keda wuya taji k’aran shigowar sak’o
_Zuciya mai muradin k’auna bata cutarwa..._
A hankali ta furta “Anonymous..” Fuzar da iska kad’an tai had’ida zama bisa gado tana mai kuma karance sak’on nasa, wani irin sanyi da yanayi maras fasaltuwa jikinta keyi a dik sanda ta amsa kiransa ko ta karance sak’onsa....

***
Chapter 117 · 0% Book details