← Book details Inda Rai Da Rabo Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 107 OF 198

Sashe 107

Inda Rai Da Rabo Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read

Murmushi da gefen baki Hafiz yai yana wani jijjiga shi kad’ai kana yace “Ku tabbata zaku cika alk’awarinku, don idan ba haka ba....” Ya kuma yin wata murmushi kana yace “Wllhi tallahi billahi zan mance ku iyayena ne, zan kuma iya zama barazanaga rayuwarku....” Daga haka sa kai yai ya fice daga gidan gaba d’aya....
Hajiya Haule da tashin hankali ya nuna k’arara ta fuskarta ta dubi mijinta “Kanaji abinda yake fad’i koh.... Toh wllhi tun wuri kasan yanda zakaida yaron nan don ko shakka banayi Hafiz zai aika dik abinda yace... Uban da yace kasashi maido da wancan hatsabibiyar yarinyar, sanin kanka ne idan yaso sai ya bankad’o duk wasu sirrika da muka jima muna aza masa k’asa...” Daga haka ficewa tai fuuu bata tsaya sauraren mijin nata ba...
Tashin hankali ne sosai ya wanzu saman fuskar Baba Alhaji... Tirk’ashi, aiko bazaiso Hafiz yasan cewa nada wani bak’in k’ulli a zuciyarshi ba, kama daga ‘ya’yansa har zuwa ‘yanuwansa kai harta jama’an gari sai sun k’yamacesa shida baida burin ya zamto mutumin da al’umma zatai alfahari dashi dukda hakan ya kasa samuwa a gareshi, wannan d’aukaka ta d’anuwansa da yake burin ya zamto shikeda ita sam bai samu ba, yanzu asirinsa ya tonu kuma ai shikenan babu mai kuma masa kallon yanada wani kima.... Yarfe zufan daya tsartsafo goshinsa yai kana ya mik’e ya shiga aza babbar rigarsa bai zarce ko ina ba sai gidan Abbah...

Abbah ya jinjina kai a hankali “Ban tari numfashinka ba Yaya, amma gameda Zulfa’u bazan canza zancena ba, zan kirawota muji daga bakinta, karka mance Shari’a ta bata damar zab’awa kanta miji, zab’an mijinta ba a hannunmu yake ba, iyakaci namu mu gudanar da bincike mu kuma bata shawari, amma banda maganar tilastawa...”
Kad’a ‘yar yatsarsa kurum yake yana duban d’anuwan nasa, baisan wace irin shegiyar taurin zuciya Usman kedashi ba, tin suna yara haka nan yakeda kafiya akan kalamansa, idan yayi magana toh ita kenan guda d’aya, sanin kansa ne wasu abin d’aga masa k’afa yake matsayinsa na wandake gaba dashi...
Baba Alhaji ya kuma gyara zamansa had’ida fitowa kad’an daga cikin kujeran ba tareda ya janye idanunsa daga duban Abban yake fad’in “Ina ita Zulfa’un take....?”

“Tana can Gwammaja gidan k’anwar mahaifiyarta Bara’atu...” Cewan Abbah dake k’ok’arin danna remote d’in tv sakamakon wutan nepa da aka kawo...
Shiru Baba Alhaji yai tamkar mai nazari kana yace “Lallai lallai ta tattara ta dawo gida, idan yaso gobe idan Allah ya kaimu sai mu zauna gaba d’aya mu tuntub’eta muji idan akwai wanda take so ne, idan kuma babu bazamu zuba mata ido ta tare gidan Bara’atu da ita kanta tarbiya bawai ya isheta bane, ni sam ban yarda da tarbiyarta ba balle har a bata rik’on yarinya.... Sannan shi kuma Sameer d’in idan ya shigo sai ka sanar dashi lallai lallai ina nemanshi...” Daga ida fad’in haka mik’ewa yai yana sab’a babbar riga ya nufi k’ofa...
Jinjina kai kurum Abbah yake yana mai fad’in “A sauk’a lafiya Yaya....” Ko amsashi bai sami zarafin yi ba ya fice cikin sauri tamkar wanda ake ingizasa...

Daga nan bai zarce ko ina ba sai gidan Hajiya Magajiya, yau zuwansa na uku kenan saidai tarban da ya samu yau yasha bambam da zuwan da yai sai biyu a baya.... Ta fito parlorn cikin kwalliya na kece raini kaman kullum, sai watsa k’amshi take dikda k’aurin hayak’in wuwi da sigari da hancinka ka iya shak’o maka, don k’amshin tiraren daban yake tashi haka ma warin k’ayan mayen, koda Baba Alhaji ya tambayeta sai ce masa tai yaran mak’otanta ne marassa jin magana saitin windows d’inta suke zuwa su hura hayak’insu.... Ta marairaice fuska sosai kana tace “Alhajina shin wai baka yarda dani bane...?”
Baba Alhaji ya murmusa “Na yarda dake mana Magajiya, ni abinda ban gane ba yau d’in naga sai b’ata fuska kike ko wani ne ya tab’a min ke....?”
Rausayar da idanu tai cikeda kisisina da salo na kashe murya take fad’in “Toh ba d’anka Hafiz bane yake gurza ma tilon d’iyata wulak’anci ba, har yau zaman doya da manja suke sam yak’i aminta da ita bacin duk magiya da kwantar da kai da take masa.... Ni tsoro nake kar yace zai kuma rabuwa da ita a karo na biyu...” Ta k’arashe tana wani rau rau da idanu tamkar budurwa mai tashen k’uruciya....

Baba Alhaji ya murmusa ya kurb’i lemu mai sanyi da aka kawo masa kana yace “Idan don wannan ne karma ki d’aga hankalinki, na riga na gama magana da Hafiz, kafin nazo nan ma maganar da mukai kenan, aurensa da Sawwama mutuwace kawai zata raba muddin ina numfashi... Ki kwantar da hankalinki kuma ki sanar da ita Sawwamar ta kwantar da hankalinta babu uban da ya isa ya raba aurenda na maida koda kuwa Haule ce....”
Wani shu’umin murmushi Magajiya tai kana tace “Da gaske Alhajina...?”
Jinjina mata kai yai yana mai janyo parantin cake da aka ije gabansa....
Dad’i kaman ya kashe Magajiya cikin sauri ta mik’e ta d’uki tray d’in tana wani kareraya take k’arasowa gabansa had’ida fad’in “A’a yi zamanka Alhajina bara na mik’a maka wannan ai aikina ne....”
Baba Alhaji ya kuma Washe baki yana kad’a kai cikeda jin dad’i yake fad’in “Allah ko Magajiyata... Anya kuwa bazaki sa na soma jina kaman saurayi d’an ashirinda ba....”
Ta kuma rausayar da idanu tace “Ai kafi haka a wajena, Allah dai ya nuna mana ranan da zan shiga gidanka Kaga soyayyar da baka tab’a cin karo da irinta ba....”
Haba nan fah Baba Alhaji yaci gaba da washe baki yana k’yak’yata dariya cikeda nishad’i yana mai ci gaba da kod’a Magajiya....

***
Chapter 107 · 0% Book details